← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 90

Sashe 69

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*91*
'Yan uwan Aunty Murja hankalinsu ya tashi sosai a lokacin data shiga gidan da takardar sakin a hannunta babbar yarsu mai suna Hajiya Mairo ta rufe ta da fad'a sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba tace lallai akwai babban dalilin da ya sanya mijin nata ya yanke mata irin wannan hukuncin. Aunty Murja na share hawaye tace."Wallahi Hajiya ni ban san komai ba kawai yazo ya rufe ni da fad'a daga karshe ya bani takardar saki uku tare da fadin albarkar haihuwa ce tasa ba zaiyi sharia dani ba saboda haka kada na kuskura koma gidansa."
Hajiya Mairo tace."Kin dai janyo mana abin kunya Murja Allah yasa ba zargin da jama'ar gari suke miki ba ya samu labari ba ko kuma ya gani da idonsa."

Murja na kuka tace."Haba Mairo wace irin magana ce wannan? wane kuma zargi jama'ar gari suke min babu sata ballantana maita."

Hajiya Mairo tace."Kinga Murja maganar ta isa haka yanzu zan kira Saminu a waya yazo ya kira Mijin naki domin muji dalilin da yasa ya sake ki."

Murja gabanta ya tsananta faduwa sai taja bakinta tayi shuru tana zazzare ido.

Alhaji Saminu ya shigo gidan Hajiya Mairo duk ta zayyane masa abinda yake faruwa hankali a tashe ya fito da wayarsa ya nemo number wayar Alhaji Nura domin ya kirashi su tattauna."

Kiran duniya Alhaji Nura yana gani yaki dauka Alhaji Saminu jiki a sanyaye ya kashe wayarsa yana kallon 'yan uwan nasa yace."Da alama mutumin nan a fusace yake kuna dai ji na kira wayarsa yafi sau biyar bai daga ba babu shakka ruwa baya tsami banza.'"

Hajiya Mairo tace." Gaskiya ne maganarka Yanda Alhaji Nura yake ganin kima da mutuncin mu babban abu ne zai sanya yaki dauk'ar wayarka."

Alhaji Saminu ya kalli Murja da tayi tsuru-tsuru jikinta dik yayi sanyi yace."Hakika Murja kin cutar da kanki duk da ban san abinda ya hadaki da mijinki ba amma jikina na bani cewa kece mara gaskiya insha Allahu ba zanyi zuciya ba zanje har kasuwa na sameshi domin mu tattauna maganar.

Tace."Dan Allah kada kaje masa da wata magana kawai ka rabu dashi tunda ko kaje gurinsa ba gyara auran za'ayi ba tunda saki uku yayi min saboda haka kawai ka kyaleshi kawai wanda ya zalinci wani Allah zai saka masa." Yanda ta fadi maganar zaka dauka tana da gaskiya. gabad'ayansu sai jikinsu yayi sanyi da maganarta.

*BAYAN KWANA BIYU*
Murja ta dinga kiran wayar Hajiya Aziza tana gani taki d'auka sai al'amarin ya dinga bata mamaki dama tana so ta kira ta ne domin ta fada mata cewa auranta ya mutu text ta tura mata cewa tazo gidansu ta same ta tunda an share zaman makoki.

Hajiya Aziza ta bata amsa da cewa ita yanzu tana Abuja sai dai idan ta dawo." Murja jikinta ya mutu ganin irin wulakancin da aminiyarta ta take mata.

Shiryawa tayi ta nufi can gidan mahaifiyar Tsohon mijin nata domin ta duba 'ya'yanta....Koda ta shiga gidan lokacin Yusura tana bakin gate tana aiki sai ta 'bata fuska ciki-ciki ta amsa sallamar ta dauke kanta.

Tace."Yusura kina gani na amma kin dauke kanki me yake faruwa ne."? Yarinyar ta share hawaye masu zafi tace."Mommy bana son kallon fuskarki kin cuce ni." Da gudu ta ruga cikin gidan.

Murja gwiwarta tayi sanyi salo-salo tabi bayanta, Hajiya Dayyiba tana zaune a falo Yusura ta zube a jikinta tana gurshe'ken kuka.!

Da sauri ta dago ta tana fadin."Yusura lafiya menene? kafin ta rufe bakinta Murja ta shigo da sallama a bakinta.

Hajiya da kyar ta amsa sallamar ta dauke kanta.....Murja babu kuzari ta zauna kan kujera a sanyaye tace."Hajiya sannu ina wuni ya gida da yara."?

Ba tare da ta kalleta ba ta amsa. tace"Me ya kawo ki gidan nan."? Murja baki na rawa tace."Nazo ganin yara na ne."

Hajiya Dayyiba tayi mata wani irin kallo rai a 'bace tace."Tur da uwa irinki Murja Allah ya shirye ki idan zaki shiryu.''

Murja tace."Hajiya me nayi da zaki dinga la'antata kada fa ki manta kema kin haifa."

Tace."Eh na haifa amma bana fata zuria ta ta dauki irin munanan halayen ki Murja munyi nadamar hada zuria dake ."

Murja fashewa tayi da kuka baki na rawa tace."Hajiya nifa har yanzu ban san meye laifi na ba sai zagi na kuke kuna aibata ni uwa uba anzo anyi min saki uku sakin wulakancin "

Hajiya Dayyiba tace."To meye amfanin zama dake Murja? ai kin zama annoba tunda kika aikata abinda Allah ya haramta saboda tsabar son zuciya ki haifi 'ya a cikin ki amma ki lalata ta sabida bakya jin tsoron Allah da Annabi."

Sunkuyar da kanta tayi kunyar duniya ta isheta tace."Ni fa Hajiya ban fahimci inda maganarki ta dosa ba na haifi yarinya a ciki na kuma ta yaya zan lalata ta."?

Hajiya Dayyiba tace."Kinga Murja ki tashi sawun ki a likkafa ki fice min daga gida bama bukar ki wa'innan yaran kuma da ana canza uwa to da sai mun sanja musu wata a madadin ki."

Murja ranta ya 'baci sosai tace."Hajiya zan tafi dama ai ba zama nazo ba tunda babu wata alaka a tsakaninmu sai ta haihuwa naji dadi sosai da baku isa ku sanja musu uwa ba dole dai nice uwarsu ko kun so ko kunqi ba zaku sanjawa towo suna ba.

Hajiya Dayyiba tace." To naji maganarki mara kunya kawai wacce bata tsoron Allah ki tashi ki tafi tunda kinyi abinda ya kawo ki." Mi'kewa tayi ta kalli Yusuran tace."Wato har dake a gurin shirya min makirci ko dan ubanki me nayi miki da har ake kira na da suna fasiqa."

Sunkuyar da kanta tayi a sanyaye tace."Mommy me yasa idan Mommy Aziza tazo gidanmu kuke hawa sama ku kulle kofa ku dade baku sauko ba ranar da Babanki ya rasu data zo gidan bakya nan shine tace nazo nayi mata tausa da muka hau saman sai ta rufe kofa ta tu'be min kaya na ta...........Kuka ne yaci k'arfinta ta kwanta kan cinyar kakarta tana girgiza kanta.

Murja zaman da'baro tayi a gurin wani irin gumi mai zafi ya shiga yanko mata bakinta sai rawa yake tana so tayi magana tsabar rud'ani ya hanata sai girgiza kanta take kafin wasu zafafan hawaye su shiga karakaina akan fukarta.

Cikin takaici da bakin ciki Hajiya Dayyiba tace."Kukan banza da wofi kike yi ai dama duk wanda ya bijirewa Allah sai ya gani a 'kwaryar cin abincinsa ke a tunanin ki abinda kuke aikatawa da k'awarki babu wanda zai fahimta to bari kiji idan kowa bai ganku ba Ubangijinku yana ganin ku kuma shine ya tanadi irin zabar da zaiyi muku a ranar lahira sabida haka tun wuri ki tuba ki nemi gafarar Allah akan abinda kika aikata."

Tana kuka na fitar hankali ta dinga kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Aziza ta cuce ni ta lalata min 'Yata na shiga uku na lalace."! Kuka take sosai tana sa bakin zani tana fyace majina sai wani irin gumi takeyi.......Yasir ne ya shigo da kayan Islamiyya a jikinsa ko da yaga Mahaifiyarsa tasa cikin halin damuwa bai nuna damuwarsa ba sai ma ya dauke kansa yana k'okarin wuce ta sai ta janyo hannunsu ta rungumeshi sosai a jikinta tana kuka da fad'in "Yasir ku gafarce ni dan Allah nayi muku laifi kada ku 'kullace ni kuyi min aikin gafara." Tana kuka ta janyo Yusuran ta rungume ta a jikinta sai hakuri take basu tana fyace majina.
Hajiya Dayyiba sunkuyar da kanta tayi tana kokarin mayar da hawayen idonta wannan wace irin kaddara ce? ko da yake dama duk wanda ya kaucewa dokokin ubangiji dole ya fukancin Fushin Allah ita kam ta rasa da wane ma'auni zata auna al'amarin bahaushe yana cewa son zuciya 'bacin ta. Allah kasa mufi karfin zuciyoyinmu ameeen.

Murja kasa hakuri tayi ta sake neman number wayar Hajiya Aziza domin ta nuna mata cewa ta fashe ta gane abinda yasa ta gudu daga gari saboda abun kunyar data tafka.....

Kamar ko da yaushe Hajiya Aziza taqi daga wayar Murja ta fusata! kawai sai ta shiga WhatsApp d'inta ta duba taga tana onile voice note tayi mata na rashin mutunci muryarta sai rawa take tace."Wallahi banta'ba tsammanin za kiyi min haka ba Aziza ashe babu amana yanzu ki rasa wacce zaki lalata sai 'yar cikina me zaki samu a jikinta me kika rasa a duniya wannan abun kunya dame yayi kama."

Hajiya Aziza a fusace! tace."Kinga Murja wannan shouting din ya isa Aa ya kike wannan maganar ne? yanzu ke har kin manta yaran da kika lalatawa rayuwa? ashe laifi ne don nayi sha'awar Yusura na kawar da kwadayi na a kanta meye a ciki? Sauran yaran da muke lalatawa ashe ba iyaye ne suka haife su ba." A fusace! tace."Kinga Aziza ki daina wannan maganar don na lura kina so ki kare kanki ne yanzu ke ba zaki iya kawar da kanki akan yarinyar ba sai ki dinga yi min wata maganar banza su yaran da muke mu'amula dasu ai ba dole mukayi musu ba sune suke kawo kansu da kansu kuma kudi ake basu sai me kuma."?

Aziza taja tsaki da fadin."To tunda kin kasa fahimta ta ni zan kashe waya ta domin ina da uziri." Rai a 'bace tace." Yar iska mutsiyaciya macuciya insha Allahu sai kinyi mutuwar wulakanci."

Hajiya Aziza ta fashe da dariya da fadin." Ni dake za muyi mutuwar kaskanci wallahi 'yar iska kawai dole ne ki girbi abinda kika shuka." tana gama maganarta tayi blocking din number ta taja tsaki!

Murja shuru tayi da waya a hannu abin duniya yayi mata yawa sai kawai ta fashe da kuka tana girgiza kanta yanzu wai ya za tayi ne? babu aure babu yara ga 'yan uwa da dangi sun juya mata baya jama'ar gari suna mata wani irin kallo wace irin rayuwa za tayi ne.? Gefan zanin ta tasa ta goge hawaye tana kiran sunan Allah a zuciyarta.
Chapter 69 · 0% Book details