Sashe 41
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin farin ciki ta mike zaune tare da kar'bar wayar tana dubawa kamar wacce za ta ganshi a cikin wayar sai washe baki take da fadin"Allah ya sauke shi lafiya kamo min shi mu gaisa." Ummatu ta karbi wayar da fadin"Lokacin da ya kira babu network sosai da 'kyar ma naji abinda yake fada amma bari na sake kiransa naji.
Wayar ta dinga katsewa ta kalleta da fadin" Taqi shiga wayar bari idan anjima sai mu sake gwada kiransa.'' Tace."To shikkenan." Ummatu fita tayi daga dakin cike da farin ciki. Ita kuma ta shiga kiran sunana "Sa'ida kina ji ko Khalid na kan hanya." Shuru nayi mata gabana in banda faduwa babu abinda yake sam! bana so yaron nan yazo ya same ni a gidan ba.
Ido na bude da fadin"Gwaggo naji Allah ya kawoshi lafiya." Ta amsa tana 'yar dariya had'e da fadin "Ni kuwa dame zan tar'bi yaron nan."?
Shuru nayi mata tace." Sa'ida kina jina ina magana ko nace me kike gani zan shiryawa Khalid na tar'ba."?
Nace"Kiyi masa girki mai dadi mana amma kisa nama kin san halinsa kamar kure haka yake."
Dariya tasa da fad'in "Ni kuwa yaushe zan kasa fito da kudi na siyi naman miya bari anjima kadan sai naje gurin Isiyaku mai kayan miya nayi cefane."
Cikin zuciya ta nace."Aiki ya same ki. Kawu ne ya daga labulan dakin da sallama a bakinsa gabad'aya muka amsa na mike zaune ina gaisheshi so kawai nake naji yayi magana akan Alhaji Nura.
Kayan tea din dake Hannunsa ya ajiye kusa da Gwaggo da fadin" Gwaggo ga kayan shayi nan yanzu Rabi zata kawo muku ruwan zafin sai ku had'a ku karya.
Tace."Ibrahim me zai sanya kayi asarar kudin ka kasan ni fa bana ra'ayin cin wannan fulawar d'aure min ciki take."
Yace."Gwaggo yau dai d'aya ai sai ki daure kisha saboda Sa'ida yasa nace yau Rabi tayi muku shayi.''
Nace."Kawu nima zanfi sha'awar kunun ai.'' Yace."To babu laifi Allah ya kaimu gobe sai ayi miki."
Kokarin fita yake Gwaggo tace." Ibrahim d'azu Khalid fa ya kira wayar uwarsa yace yana kan hanya.''
Babu yabo babu fallasa yace."To Allah ya sauke su lafiya." ta amsa da ameen tana dariyar farin ciki. har ya fita daga dakin ba tayi masa maganar data dangance ni da aurena ba, raina ya 'baci sosai da kyar na iya had'a tea din nasha na koma na kwanta ina tunanin mafita.........Wato dai dama Alhaji Nura ba wani sona yake ba sha'awata yake tunda gashi tun ba'aje ko'ina ba har gishiri ya salance daga jiki kaza, zuciyata tace dani yanzu da ya samu budurcin ki ma wannan wulakancin zaiyi miki, kawai sai naji ina jin dadi da Allah yasa bashi ya samu budurcina ba domin akwai takaici ace ya samu abu mai muhimmanci a tare dani amma ya dinga wulakanta ni akan matarsa.
Ina can duniyar tunani Gwaggo ta gama kujigaba-kujigabarta tasa hijabi ta tafi cefane, sai fitowa tsakar gida nayi na sameta ta baza kayan miya a gaba gefe guda kuma ta hura huta a kurfoti (mangal) ta d'ora kasko tana ta soya nama. cikin takaici da bacin rai na dauki buta na shiga bandaki nayi uzirina na fito ta kalleni da fadin"Sa'ida kina gani aiki ya cakud'e min ba zaki taimaka min ba."
Ba tare dana kalleta ba nace."Gwaggo kaina ne yake ciwo.'' bina tayi da kallo kafin tace."Dole kanki yayi ciwo mana tun jiya kike kuka sai kace Alhaji Nura ne autan maza a duniya duk kin damu kan ki."
Nace."Gwaggo dole nayi kuka na shiga damuwa mana tun jiya mutumin nan bai kira waya ba kuma bai zo ba ai dole hankalina ya tashi gashi Kawu yace dole sai na hakura da aikina."
Tace." Sa'ida nifa wani sa'in bana jin haushin abinda Alhaji Nura yayi miki dama hausawa suna cewa duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubda ruwa haka kurrum kika 'ki d'an uwanki kika za'be shi *AI GA IRINTA NAN!* Tun kafin aje ko'ina ya nuna miki halinsa."
Hawaye na share nace''Gwaggo dan Allah ki daina wannan maganar kada ki sake tunzura min zuciyata Khalid yana d'aya daga cikin mutanan da suka hana ni samun kwanciyar hankali a gidan aure na."
Kallonta tayi baki a bude tace."Au! tana nan kuma kika 'bullo.''? Da sauri nace."Eh Mana Gwaggo da Khalid bai raba ni da martaba ta ba, to bana tsammanin Alhaji Nura zai yi min irin wannan wulakancin."
Shuru tayi ba tace komai ba ta cigaba da gyara kayan miya, labulan dakin na daga na shiga na zaune tare da daukar waya ta ina duba gurin text burina kawai naga wani sa'ko daya dangace shi, abin takaici text din Khalid na gani har biyu inda yake sheda min cewa zuwa La'asar zasu sauka.
Ajiye wayar nayi ba tare dana bashi amsa ba.
Kafin La'asar Gwaggo da Ummatu sun gama aiki tsaf sun shirya masa abinci har kala uku da zo'bo wanda suka sa masa k'ankara Gwaggo sabbin kwanikan ta na silba ta dauko aka jere masa kayan abincin a guri guda yanzu shi kadai kawai ake jira.....Al'amarin ya dinga bani mamaki yana daure min kai ganin yanda suka shirya masa guri sai kace wani cikakken mutun magidanci gabadaya tsabar haushi da kishi naji zaman gidan ya fita min a rai sai kawai na hau shirye shirye ta kalle ni da fad'in "Ina kuma zakije da yamma."?
Nace." Zanje can gidan Ummana ne." Girgiza kanta tayi fuska a 'bace tace."Aa Sa'ida ba zaki mayar damu 'kananun mutane ba da auran mutum akanki ki dinga yawo."
Nace."Gwaggo gidan Ummana fa nace zani ba wani guri ba."
Tace."Eh ai na fahimta babu inda zakije har sai munji ta bakin mijinki tukkuna."
Takaici yasa kawai na zuba mata ido ina kallonta. Kayan kad'inta ta dauka tana gyarawa mukaji sallamar yara a cikin gidan.
Gwaggo da sauri ta amsa tare da daga labulan dakin........Yaran sun kai su hudu biyu buhu ne a kawunan su biyu kuma jarkokin manja da man gyada ne a hannuwansu.
Gwaggo tace."Waye ya aiko ko da wa'innan kayan." Daya daga cikinsu yace."Khalid ne ya dawo yana waje shida abokanansa."
Da sauri ta cilar da kayan kad'in ta miqe tana fadin"Alhamdullilahi Allah nagode maka." Hijabi tasa ta kama hanyar fita Nace."Gwaggo ai kya bari ya shigo ko."
"Aa Sa'ida gwara naje na tar'beshi." tafada tana kokarin fita, kallo na bita dashi ina girgixa kaina.
Gwaggo na kokarin fita suka buga karo. rungumeshi tayi sai kuma ta fashe da kuka tana kiran sunansa....Hannunta ya rik'e yana rarrashinta suka shiga gidan
Ummatu na tsaye a bakin kofar ta fuskarta yawalce da fara'a take kallon yaron nata sai taga duk ya sanja ya kara girma da hasken fata....Yace."Ummana kina mamakin ganina ko." Murmushi tayi tace."Khalid dole nayi mamaki." Cikin jin nauyi ya sunkuyar da kansa kasa yana gaisheta ta amsa cike da kulawa.
Ya shiga gogewa gwaggo hawaye yana fad'in "Gwaggo dan Allah ki daina kuka haka ai gani na dawo cikin koshin lafiya dan Allah ku gafarce ni."
Ta dinga kallonsa tana girgiza kai tace."Khalid na kuwa sheda haka tunda gashinan na ganka kayi girma ka sanja kayi haske sosai kamar wanda yake cikin hutu.''
Murmushi yayi yace."Gwaggo godiyar Allah ce kawai da kuma tasirin adduoin da kuke min shi ya janyo haka.'' Tace."To Alhamdulillahi Khalid naji dadin ganin ka cikin koshin lafiya gashinan harda abin arziki." Tafada tana bin kayan dake jibge a tsakar gidan.
Yace."Gwaggo na san ki da son doya shiyasa na siyo miki buhu guda.'' Dariya tasa da fadin"Aikuwa naji dadi d'an albarka Allah ya 'kara maka wadata." ya amsa da ameeen ya rabbi.
Tace."Muje daki kaci abinci ka huta ko."? yace."To uwagidana." murmushi tayi ta rike hannunsa suka kama hanyar dakin....Ummatu kuwa murmushi tayi cike da farin ciki ta shiga gurinta.
Jin motsin shigowarsu dakin yasa da sauri na daidaita nutsuwata ba tare dana dago kaina ba na amsa sallamar shi.
A jikina naji cewar kallona yake a fizge na daga kaina na kalleshi yana sanye da k'ananun kaya kamar ko da yaushe sai kawai na tsinci kaina da kasa dauke idona daka kansa mamakin girmansa nake wata biyar kacal yaro ya sanja ya zama 'kato dashi da gaske ya sake girma da hasken fata.
A nutse ya zauna inda aka tanadar masa Gwaggo sai wani ji dashi take tana gyara masa gurin zama, shi kuma gabadaya hankalinsa na kaina ina kallonsa ta gefan ido sai kallona yake.
"Auntyna ba zakiyi min barka da zuwa." maganarsa naji ta daki kunnena.
Na kalleshi babu yabo babu fallasa nace."Khalid ya hanya."? fuska a sake yace."Alhmdulillahi aunty ya fargaba da alhinin dana tafi na barki dashi.''?
Share maganar nayi na dauki waya ta ina dubawa.
Gwaggo ta hau bude kwanunkan dake gabansa tana fad'in "Jarumi kaci abinci gashinan." Yace."Gwaggo duk wannan nau'in abincin duk ni kadai."
Tana mirmushi tace."Khalid kafi karfin komai a gurina burina kullum ka kasance cikin farin ciki."
Yace."To gwaggo naji dadi sosai ina rokon Allah yaja min da ranki." Tana kokarin zuba masa abincin a plate ta amsa da ameen d'an albarka.
Abincin ta zuba masa da yawa tasa masa miya da uban nama. yace."Gwaggo abincin nan yayi min yawa." Tace."Ka dai ci ka koshi."
Kallona yayi cikin kulawa yace."Auntyna zo ki taya ni ci." Ko kallonsa banyi ba ballanatana na bashi amsa.
Tace."Khalid rabu da ita don Allah kaci abincin ka."
Girgiza kansa yayi yace."Gwaggo ya za'ayi amaryata tana fushi kice na rabu da ita ko dai kishi kike."?
Bani kadai ba Ita kanta Gwaggo sai da gabanta ya fadi! shuru tayi jikinta duk ya mutu data tuna da yaudarar da akayi masa.
Gani tayi ya mike daga inda yake ya dawo kusa dani ya zauna. ni da ita dik jikinmu ya mutu. a sanyaye yace."Auntyna menene? ki fad'a min matsalarki gani na dawo na share miki hawaye."
Kallonsa nayi zuciyata ta dinga tafarfasa! ina tuna irin cin mutuncin da yayi min a ranar da zai gudu! 'kwalla ta cika kwarmin idona! kansa ya girgiza min cikin sigar rarrashi yace."Kada kiyi min asarar hawaye domin yana da mutukar daraja a gurina ki gafarce ni auntyna nasan dole idan kika kalli fuskata ki tuna abinda nayi miki na rashin kyautawa."