← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 90

Sashe 83

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina na share hawaye ta lalla'ba ta shiga toilet domin gyara jikinta shi kam yaji dadi sosai da ya samu budurcinta sai ya tuna lokacin daya keta budurcin auntynshi rintse idonsa yayi yana girgiza kanshi sam beso hakan ba yaso ace ta hanyar aure komai ya faru amma kaddara ta riga fata haka Allah ya shirya musu.

Yana gama kimtsa jikinshi ya fice daga dakin ba tare da ya bari ta fito daga bandakin ba hakan yayi mata masifar ciwo a hankali ta zauna gefan gado tana kukan bakin ciki yanda ya jigata ta ya bata wahala ta dauka ai zai tsaya ya rarrasheta amma da yake ba itace a ranshi ba har ya fice ya bar mata dakinta zuciyarta ta sake cika da kishin abokiyar zaman nata.

Khalid kuwa yana fita bai ko kalli Side din Auntyn nasa ba kai tsaye inda motocinsa suke ya nufa Yaron shi Chinedu ya mike da sauri yana mika gaisuwarsa motar ya bude masa ya shiga ya zauna shima da sauri ya shiga gurin zaman shi ya tashi motar kafin su fita daga gidan sai da ya sauke gilashin na motar suka gaisa da Maigadi Khalid bashi da girman kai da wulakanci yanda yake Mu'amula da jama'a abin zai baka sha'awa.

Sai yamma ya dawo gidan kai tsaye gurin Sa'ida ya nufa domin ya dubata.......Kallo daya nayi masa na dauke kaina a nutse ya karaso kusa dani ya tsaya tare da zuba hannuwansa a cikin aljihu.

Babu walwala a tare dani nace." Barka da yamma." ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace." Barka dai kinji shuru ban shigo na dubaki ba ko."

Shuru nayi hankalina akan Tv ya cigaba da cewa." Da wurwuri na fita kuma tunda na fita ban samu kaina ba ballantana na kira wayarki ina fatan kin wuni lafiya."

Ajiyar zuciya na sauke ina d'an jin sassauci a cikin raina nace." Lafiya lau na Wuni ina fatan ka leqa gurin Gwaggo."

Yace."Aa banje ba saboda uzirin daya sha kaina mybe sai gobe zan shiga mu gaisa.'' Nace." To Allah ya kaimu."

Zama yayi kusa dani na dan kalleshi sai naga kwarmin idanunsa sun zurma. " Ki bani abinci tun safe babu komai a cikina."

Cike da mamaki nace." Tun safe babu komai a cikin ka? amma kake yawo a haka."

Hannuwansa yasa ya rufe fuskarsa da fad'in."Ke dai ki bari kawai jiya na kwana banyi bacci ba yau kuma na yini da yunwa abubuwan sunyi min yawa."

Maganar ta bani haushi sosai sai kawai na kauda kaina na rabu dashi. Ya kalleni da fad'in." Ko dai ni zan shiga kicin din na dauk'o abincin."?

"Kaje kicin din ko kuma ka tafi gurin matarka tunda a dakinta ka kwana." " Wace irin maganace wannan."?

Shuru nayi masa gabad'aya haushinsa nake ji ko kunya yazo yana fadin ya kwana beyi bacci ba yaron ya gama raina min hankali.

Ganin yanda nayi watsi dashi a gurin yasa ya mi'ke ba tare da ya sake min magana ba ya kama hanya fita, 'karamin tsaki naja tare da bin bayansa da harara.

Yau tsayin kwana ki uku kenan bai sake shigowa inda nake ba, damuwa da kadaici suka dabaibaye ni gabad'aya hankalina ya tashi na rasa abinda yake nufi dayin hakan, kullum ni kenan cikin leqen sa a duk sanda zai fita ina kallonsa ko kallon Gurina ba yayi zai shiga mota dravar sa yaja motar su tafi........Duk yanda nake kokarin daurewa sai da na kasa zama nayi naci kuka na na k'oshi na dinga tunanin hanyar da zanbi gurin shawo kansa.

Ina lissafe Yau kwanansa bakwai a gurin Jamila ya gama mata kwanakinta zai dawo guri na tunda na tashi nake jin annushuwa da farin ciki abinci kala uku nayi masa nayi ado sosai irin wanda zai ja hankalinsa. sai dai me? Daf da magariba ya kira waya ta cike da zumudi da murna na daga wayar.

Ciki-ciki ya amsa gaisuwata yace." Yau girki ya dawo hannunki ko." ? Nace."Eh." Yace." Kiyi hakuri yanzu haka bana gari naje Bauchi tare da abokanan sana'ata zanyi kwana uku sai na dawo." Kafin nace wani abu ya kashe wayarsa.

Jiki a masifar sanyaye na zube a gado kawai naji hawaye masu zafi sun k'wace min. Na riga na gama cin buri nasa rai yau karshen matsala ta dashi zai k'are saboda na gama shirya duk yanda zanyi na sanya shi cikin farin ciki bayan haka kuma a matse nake don ni kadai nasan halin da na shiga tsayin kwanaki bakwai din da yayi a gurin Jamila......Ina jin wani irin d'aci a ma'kogwarona nasa hannu na dinga share hawayen dake zuba a fuskata.

Alhaji Nura cikin shiga ta alfarma yayi parking din motarshi a inda ya saba idan yaje gidan zance fitowa yayi daga motar tashi yana gyara babbar rigar dake jikinsa......Wayarsa ya dauko domin ya sanar mata da zuwansa, Ya kira ya kai sau nawa bata shiga sai ya hakura ya fara neman yaron da zai tura gidan. Kawu ne ya fito daga gidan sai ya ganshi a jingine a jikin motarsa cike da mamaki ya karasa inda yake. Alhaji Nura ya saki fuskarsa cikin mutunci da girmama juna suka gaisa da juna.

Kawu yayi shuru yana so yaji abinda yake tafe dashi. Alhaji Nura ya gyara tsayuwarsa a nutse yace." Kwana biyu bana gari wallahi ban samu na shigo mun gaisa ba jiya na dawo naje india shine yau nace bari na shigo mu gaisa inaso naga Sa'ida domin mu tattauna abin da yake gaban mu."

Kawu yace."Ayya ashe baka garin shiyasa baka da labarin al'amuran da suka gabata." Yace."Kwarai kuwa Kawu inaso yanzu a lamunce min na bada sadakin Sa'ida ranar juma'a mai zuwa a daura aure.''

Kawu ya jima kanshi a kasa kafin yace." Alhaji sai dai kayi hakuri da abinda Allah ya tsara domun dai a yanzu maganar da nake maka yau sati biyu kenan da daurin auran Sa'ida tare da Dan uwanta Khalid."

Alhaji Nura gumi ne ya tsinke masa ya cire hularsa yana firfita da ita kamar mara hankali yace." Ya za'ayi ayi min haka? Yarinyar nan fa ni take so tayi min alkawarin komawa gidana domin ta kula min da 'ya'ya na mai zai sanya ka tilasta mata auran d'anka wannan ai rashin adalci ne."

Kawu ya dinga kallonsa yana mamakin maganarsa........Alhaji Nura ya cigaba da cewa ." Wannan yaron naka mara kunya kwata-kwata bai dace da kamilar mace irin Sa'ida ba saboda haka duk yanda zanyi sai nayi na ruguza auran da kuka daura."

Kawu na 'kokarin magana Muryarsa ta bayyana a gurin ya jima da zuwa gurin basu sani ba......."Kai wane irin wawan mutum ne bagidaje mara hankali da nutsuwa."
Gabadaya suka juya da sauri suna kallonsa.

Rai a masifar 'bace yace." Ka jima kana kira na da mara tarbiya shin kai d'in menene sunanka? Kana gadara da dukiya ko? to inaso na sanar maka da cewa a yanzu idan nayi Ra'ayi ba zaka koma gidan ka ba zan sa a daure min kai har karshen rayuwarka."
Kawu ya daga masa hannu da fadin."Ya isa haka kowa ya bawa zuciyarsa hakuri.'' Khalid shuru yayi sai wani irin huci yake yana jin kamar ya shaqe wuyan Alhaji Nuran ya had'a masa jini da majina bai ta'ba ganin mutum mai mugun naci kamarsa ba.

Kawu ya kalleshi da fadin." Alhaji idan rai ya 'baci ba'a sauran yanke hukunci ya kamata kayi mana uziri sannan kuma ka dauki kaddara komai kaga ka samu a duniya dama rabonka ne idan kaga baka samu abu ba to dama baka da rabo saboda haka sai kayi hakuri ka barwa Allah al'amarinsa.

Gumin goshinsa ya goge rai a bace yasa hularsa ya bude motarsa da karfi yaja Kawu yayi saurin matsawa yana kallon ikon Allah sai da ya bar gurin ya juyo yana kallon yaron nasa yana tsaye bakin kishi ya cika masa rai idanuwansa sunyi jajawur.

Yace." Yau shigowar dare kayi kenan."? ajiyar zuciya ya sauke yace."Eh kasa hakuri nayi sai da safe ina so naga Gwaggo ne." Yace." To babu laifi nima yanzu nan na fito daga gurin nata. Yana kokarin shiga kofar yace."Bari a gurguje na shiga mu gaisa Allah yasa ba tayi bacci ba." Kawu yace." Bana tsammanin hakan."

Gwaggo na gyangyad'i ya shiga ya sameta, kamshin turaransa taji da sauri ta bude idonta tana kiran sunansa.

Kusa da ita ya zauna yana gaisheta ta amsa cikin kulawa tace."Kwana uku ina lissafe baka zo inda muke ba."

Yace."Nayi tafiya ne Kuyi hakuri yanzu dawowata kenan na kasa hakuri na shigo na duba ku." Tace."Jarumi za kayi tafiya amma babu labari ko baka bukatar adduarmu."?

Yace." Gwaggo kuyi hakuri nayi laifi tafiyarce babu tsammani ina fatan na sameku lafiya." Tace."Lafiya kalau alhamdulillhi Ya iyalin naka."?

Yace." Duk suna nan kalau." Tace." To masha Allah sai ka tashi ka tafi gurinsu su ganka kada ka shiga hakkinsu."

Yace." Tom ki bani abinci naci." Girgiza kanta tayi tace."Aa babu ruwana ba zan baka abinci ba mai girki taji haushina.

Yar dariya yayi yace." Gwaggo bana sha'awar komai sai abincin ki kawai ki bani idan da akwai."

Jim tayi tana nazari tace." Bari na baka kadan idan kaje gida sai ka 'kara wani."

Yace." To ki had'a min bari na shiga gurin Ummatu mu gaisa na fito." Tace." Tom shikkenan sai ki fito.

Da 'Kyar Gwaggo ta kore shi ya tafi dan bayan ya gama cin abincin kwanciya yayi kusa da ita tana bashi labarai sai dariya yake kyalkyalawa ganin dare yayi beda niyyar tafiya gida yasa tace ita kwanciya za tayi ya tashi ya tafi gurin iyalinsa da kyar ya tashi ya tafi cike da 'kaunarta a cikin ransa.

Sai da ya fara duba Jamila tukkuna ya nufi Gurin ta.

Duk da nasan yau zai dawo gida Ban yi tsammanin zai shigo inda nake ba wannan dalilin yasa ban zauna zaman jiransa ba na shige daki nayi kwanciyata.

Maganarsa kawai naji a kaina, da sauri na bude idona ina kallonsa, ganin fuskarsa a murtuke yasa gabana faduwa ni kam Allah yana jarrabata da masifaffun maza.
Chapter 83 · 0% Book details