← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 90

Sashe 15

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru nai mata ba wai dan bani da amsar da zan bata ba sai dan sanin da nayi cewa duk abinda zan fad'a mata yayi min ba yarda za tayi ba.

Gwaggo ta fito daga dakin tana fad'in "Me kuma yake faruwa nake jin hayaniya."? Ummatu da sauri tace." Gwaggo duba jikin Khalid ki gani sabida tsabar ita ta cika ishashshiya ta dauki ruwan wankinta ta watsa masa a jikinsa.

Gwaggo da sauri ta kalli Khalid jikinsa jagab! da ruwan daud'a! cike da mamaki! tace."Jarumi me ya had'a ku nasan dai ruwa baya tsami banza."?

Girgiza kansa yayi yace.''Gwaggo daka kawai zan taimaka mata da wanki shine tayi min wannan wulakancin.''

Tace."Haba Sa'ida me yasa kika aikata haka."? Rai a 'bace na d'ago ina kallonsu nace." Lokacib dana fito da wanki na bance kowa ya taimaka min ba akan me zai zo yasa min hannu sai kace sa'arsa dan wulakaci ya d'auki breziyata yace zai wanke."

Gwaggo ta ri'ke bakinta tana yi masa wani irin kallo mai kama da harara.....Ummatu tace"Ke Sa'ida kada kiyi masa sharri yaushe ya dauki rigar nonan naki bayan ke kika watsa masa ruwan daud'a da ita a ciki."

Nace."Ummatu kenan ba sharri nai masa ba da idonki fa kin gani amma zaki ce nai masa sharri."

Gwaggo tace."To duk dai magana ta wuce kada a 'kara tayar da ita kai kuma Khalid babu ruwanka da ita." Yace."Yanzu ke Gwaggo kin yarda zan aikata hakan? okey idan ma breziyar ta na d'auka domin na wanke mata meye a ciki? ai ba k'irjinta na ta'ba ba ballantana tayi min sharri ." Gwaggo tace."Aikuwa dai babu laifi a ciki tunda tace bata so sai ka kyaleta.

Tsaki yaja ya bar gurin yana fad'in "Daga Abin alkairi sharri ya biyo baya wataran ma cewa zakiyi na turmushe ki." Ummatu tayi saurin fad'in "Allah ya kiyaye." Bayansa tabi tana surutai itama Gwaggo dakinta ta koma ta cigaba da abinda take.

Tana zaune a d'an tsakar gidanta ya fito daga dakinsa cikin shirin fita yayi gayu cikin 'kananun kaya sai kamshin turare yake, Khalid akwai tsabta da kwalisa kayansa kullum a goge gashi bai yarda da fesa turare me arha ba.

"Khalid zo nan ina so nai magana da kai." A nutse yaje ya samu gefanta ya zauna. tace." Kana jina ko."? yace."Eh Umma ina jinki." Tace."Ni ba zan raba ka da 'yar uwarka Sa'ida ba amma inaso kayi nesa da ita dan gabad'aya ni yarinyar bata kwanta min a raina ba ina jin tsoro taje tayi lalata a waje ta laqaba maka sharri ka daina shiga sabgarta."

A sanyaye yace."Ummatu me yasa kike mata irin wannan zargin." ? Tace."Kai Khalid yaro ne kai baka san me duniya take ciki ba gabad'aya jama'ar gari kallon lalatacciya suke mata dan ni akwai wacce ta kawo min magana kancewa babu irin lalatar da ba tayi da maza a gurin aikinta wannan dalilin yasa nace kayi nesa da ita bana so taje tayo cikin shege ta d'ora maka."

Cike da mamaki! yake kallonta kafin yace."Ummatu amma banji dadin wannan magana ba dan Allah ki daina yarda da surutan mutane bana tsammanin Aunty Sa'ida zata zubar da martabar gidan nan."

Tace."Oho! dai Sa'ida tana bin maza bata bin maza ni dai nace ka rabu da ita dan naga kaima tana so taja hankali ka gashinan baka san laifinta.''

Shuru yayi yana girgiza kansa! Tace."Yaushe ne zaku koma makaranta."? Yace."Ai kin san da tuni mun koma wannan yajin aikin da aka tafi ne ya janyo amma naji gwamnati tayi magana cewa kowane dalibi ya koma makaranta ranar mondy."

Tace."Jibi kenan zaka tafi."? Yace."Eh insha Allahu." Tace."To shikkenan kafin ka tafi kaje can babban gida ka gaishe su." Yana kokarin mi'kewa yace "To insha Allahu zanje."

'Kamshin turaransa ne yasa nayi saurin juyowa muka had'a ido dashi, saurin dauke kaina nayi ina mamakin a'inda ya samu kudi ya siyi turare mai tsada irin wannan nafi jin 'kamshinsa a jikin Alhaji Nura. Cigaba da shanya kayana nayi har ya fice daga gidan sai kawai na tsinci kaina da bin bayansa da kallo gaskiya dressing din yayi masa kyau sosai. kawar da tunaninsa nayi daga cikin raina na cigaba da abinda yake gabana.

Ina tsaka da share inda nayi wanki yaro ya shigo."Wai Salisu mai kanti yace a bashi lagwanin." Nace."Shiga dakin ka fad'a mata. muryarta naji tana fad'in "Bama sai ya shigo ba naji bari na kawo maka ka kai masa."

Yaron yace."To gwaggo." ta fito hannunta rike da leda viva ta mika masa da fadin"Kace dan Allah yayi hakuri banyi masa akan lokaci ba." Yace."To Gwaggo zan fada masa."

Fita yaron yayi ta kalleni da fadin"Sa'ida yau sha'awar sakwara nake ko zakiyi mana da ragowar doyar can." Nace."Banda kudi da zan sarrafa.''

Tace." 'Dari biyu zata isa ayi miyar."? Kaina na girgiza mata alamun ba zata isa ba, tace."Aikuwa dari biyu zan iya bayarwa ayi cefane." tafada tana kokarin shiga daki sallamar Almajirin gidan Alhaji Nura ta dakatar da ita.
Washe bakinta tayi tana kallonsa ya 'karaso inda nake hannunsa ri'ke da ledoji yace."Aunty Sa'ida ina wuni."? na amsa ina kokarin wanke hannuna yace."Daga kasuwa nake Alhaji yace na kawo miki wannan." Hannu nasa na kar'bi ledojin da fadin."To Rabi'u kace masa nagode sosai." Ya amsa da ameen tare da juyawa Gwaggo tace." Rabi'u babu gaisuwa ka shigo kawai ka wuce gurin uwar dakinka."Murmushi yayi yana kallonta yace."Gwaggo Dan Allah kiyi hakuri wallahi hankalina ne yayi gaba ina fatan kin wuni lafiya."?

Tace."Lafiya lau Rabi'u ya Alhajin ina fata dai lafiya dan Allah kace masa muna godiya da hidima." Rabi'u yace."Insha Allah zan fad'a masa."

Yana fita ta karaso inda nake tana fad'in "Kai amma naji dad'in wannan aiken wallahi nasan harda nama da kayan miya a ciki kinga na huta 'batar da kudina.

A nutse nace." Gwaggo wai dan Allah me yasa kike da san abin duniya ne inace d'azu kika gama zagin mutumin nan amma yanzu kinga kayansa duk kin gigice."

"Sa'ida kada ki fad'a min magana mana kin san dai ba zan bar nawa na na za'be shi ba, ni nafi kaunar ki auri Khalid amma da babu maganarsa a tsakani zan baki goyan baya d'ari bisa d'ari ki auri Alhaji Nura domin ya cancanta.''

Nace."Wallahi har mamaki kike bani idan naji kina cewa wai na auri Khalid gwaggo kina tunanin ko maza sun'kare a duniya zan auri wannan yaron........"Shima ba zai aureki ba tsohuwar guzama dake." Muryar Ummatu ce ta katse maganar da nake. duk muka juya muna kallonta....Fuska a murtuke ta karaso inda muke tsaye tace."Sa'ida ke har wata cikakkiya ce da har zaki dinga k'yamatar auran Khalid me kike dashi na matantaka bayan duk kin gama rabawa abokanan aikin ki maza."

Gwaggo tace."Rabi wannan wace irin banzar magana ce."? Da sauri tace."Gwaggo ranar wanka fa ba'a 'boyan cibi ke kin sani kuma kin fad'a da bakinki hakanan kuma jama'ar gari sun sani Sa'ida bata da kamun kai to me zai sanya kice lallai sai Khalid ya aureta."

Rai a 'bace Gwaggo tace."Rabi kada ki 'kara yi mata 'kazafi ni kaf zuriyata babu lalatacce idan Allah ya kaddara auran Sa'ida da Khalid babu yanda zakiyi sai hakuri."

Murmushi takaici tayi tace."Gwaggo sai dai kuwa idan bani na haifi Khalid ba." Tana gama maganarta ta bar gurin tana wani irin huci!

Ido jawur! na kalleta nace."Kinga abinda kika janyo min ko."? ''Kinga Sa'ida rabu da Rabi bata da cikakken hankali kuma wallahi sai na fad'awa Ibrahim ayi muku tsakani da ita kada ta 'kara jifanki da mummunar kalma."

Nace.''Gwaggo da Ummatu ba taji kina fad'a min haka ba to ba zata fad'a ba tun farko ke kika nuna kina zargina da iskanci a gurinki taji gashinan kin janyo min cin mutumci."

Tace."Kiyi hakuri na fad'a miki zan had'ata da Ibrahim zata gane bata da wayo." nace"Gwaggo kada ki had'ata da mijinta a kaina ki kyaleta kawai ni zan yanke hukunci da zakuyi farin ciki."

Tace."Sa'ida wane irin hukunci zaki yanke."? Murmushin takaici nayi nace."Idan na yanke zaki gani." barin gurin nayi naje ina duba abinda yake cikin ledojin .....kayan tea ne komai da komai sai uban kayan miya da nama mai yawan gaske a cikin wata katuwar takarda.
Kallonta nayi nace.'' Kinga nayi wanki na gaji ba zan iya dukan sakwara ba zan dafa miki ita kawai kici da miya."

Tace."To shikkenan had'a kayan miyan ni da kaina sai na miqa markad'an gidan Lubabatu." Mi'kewa nayi na dauko d'an maidaidaicin baho da wuka na zauna ina gyara kayan miya ta nufi daki tana fadin" bari na 'karasa d'an abinda nake kafin ki gama."

To duk k'ulafucin Gwaggo ba taci doyar da yawa ba duka -duka uku taci ta ajiye wa mutumin nata miya cikin silba duk ta kwashe masa naman 'kyaleta kawai nayi domin ni nasan abinda na shirya mata.

Ganin tana gyangyad'i nace."Gwaggo ki gyara kwanciyarki mana." Da sauri ta bude ido tana kallona tace."Ina jiran Ibrahim ya shigo ne shiyasa ki kaga bankwanta."

Nace."Gwaggo Ummatu ni ta ciwa fuska kuma gani tayi ki nayi min saboda haka dan Allah kada kice zaki fad'awa mijinta ki had'asu." Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai kiyi Sa'ida Sai fa na fad'a masa fa Ummatu zata san da ni take zancan."
Shuru nai ina kallonta.........ta cigaba da gyangyadin tana nema ta tintsira nace."To ki kwanta idan ya shigo zan tashe ki." Ajiyar zuciya ta sauke tace."To mi'ko min fillo na d'an matse." da sauri na mi'ka mata ta kwanta tana kiran sunan Allah.

Shuru dakin yayi na tsayin minti goma sha biyar na tabbatar tayi bacci na mike a tsanake nasa hijabina jakar dana san na had'a dukkanin kayana na dauka a hankali na fita daga d'akin.......Kai tsaye babban titi na nufa ina addua a kan Allah yasa ina fita na samu adaidaita sahun da zai kaini hotoro gidan Mahaifiyata......

?‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_

*14&15*
Wayarsa ya d'auko daga aljihun shart din dake jikinsa sai ya nemo number ta ya shiga kira.
Chapter 15 · 0% Book details