← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 90

Sashe 4

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabad'aya ji nayi yawun bakina ya bushe! na dinga kallonsa ina mamakin tsagerancin sa Murmushi yayi ya had'e yatsun hannunsa yayi heart 💘 Ilov u auntyna muuuuhhhh!." ya hura min iskar bakinsa. kafin nayi aune har ya fice daga gidan, kaina na sunkuyar 'kasa gabana ya dinga bugawa sosai al'amarin ya firgitani anya kuwa yaron nan bai fara shaye-shaye ba! ? ni kam ina zan kai kaina da wannan abin kunyar dole sai na tasar masa a tsaye zai daina yi min wannan iskancin, jikina a mutukar mace na mike na shiga dakin na kwanta ina tunanin matakin da zan dauka a kansa..

*Masoya ayi min sharing a groups👏🏼*

*IDAN KINA BUKATAR KARANTA LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP GRUOP#600 NORMAL GRUOP#300 ACCOUNT... 0542382124...BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

*_Ya Allah kayi mana katangar 'karfe tsakaninmu da ma'kiya! Ya Allah ma'kiyi wanda na sani da wanda ban sani ba Allah ka katange ni dashi👏🏼 Ubangiji Allah ka tsare gabanmu da bayanmu Allah dukkanin mai nufin mu da sharri ko wane iri ne Allah ka mayar masa kansa, Allah a gida da waje ka kare mu damu da zuriarmu Ameen ya hayyu ya 'kayyumu👏🏼_*

*6*
"A'a Sa'ida bana san sharri! A ina kuka had'u da Khalid d'in da har zakiyi masa wannan gundumeman sharrin yaron da tun d'azu ya fita dan babu yanda banyi dashi ba ma ya zauna yaci abinci yace baya ci sannan kawai kizo kice yana k'okarin lalata dake a soro."

Ina 'kokarin magana Ummatu ta bankad'a labule ta shigo dakin da fad'in"Wace magana naji kunayi kuna kuma kiran sunan Khalid." Gwaggo tace."Ke! Rabi abinda ba'a sa da kai ba dad'in kallo gareshi a'ina kikaji mun kira sunan Khalid da har zaki bankad'a labule kishigo a fusace."

Murmushi tayi tace."Gwaggo kenan duk fa maganar da kuke a kunne na ke Sa'ida ki shiga hankalinki dani wallahi wato Khalid din zakiyi wa sharri sabida baki da kirki to tun wuri kije ki nemi d'an iskan da yake lalubeki a soro amma ba Khalid ba."

Ido na zuba mata har ta 'kare maganarta ban tanka mata ba, Gwaggo tace."To tunda dai kin fad'i abinda ya kawo ki tafi kuma wallahi kada naji maganar nan a bakin kowa mutukar maganar nan ta fita dukkaninku sai ranku ya 'baci."!

Ummatu ta'be bakinta tayi ba tare da tace uffan ba ta kad'a kanta ta fita daga d'akin.

Duk yanda naso na daure kasawa nayi hawaye na zuba nace."Gwaggo wato nice 'yar iska lalatacciya ko? dukkaninku baku yarda Khalid zai iya aikata abinda na fad'a ba kun goya masa baya ya cigaba da bibiyata ko okey to shikkenan Gwaggo yanzu na gane matsayina a gurinki dan gashinan a zahiri kin nuna min cewa kinfi kaunar Khalid a kaina alhalin duk kece kika haifi iyayenmu to babu komai Gwaggo kinji na rantse da Allah duk ranar da Khalid yayi kuskuran sake ri'ke min hannu sai na d'auki tsatstsauran mataki a kansa.''Cikin zafin zuciya nake maganar.

Tace."To me zakiyi masa idan ya ri'ke miki hannu naga dai shine zai aureki to meye abin tayar da hankali kuma." Da sauri nace."Dake dashi zan kai ku gurin alkali sai kiyi masa bayanin da kikayi min yanzu."

Ha'barta ta ri'ke tana girgiza kanta tace."Lallai Sa'ida ni zaki kai gurin alkali."? "Kwarai kuwa mutukar baki daina daurewa Khalid gindi ba wallahi sai na dauki wannan matakin." shuru tayi tana kallona, nasan mamakina take, dan na 'kara tsoratata nace" Yanzu ma bari na kira wani abokin aikina wanda d'an uwansa yake aiki a kotun musulunci ta kasuwa na fad'a masa dukkanin abinda yake faruwa." Da sauri ta rike hannuna tana kokarin kar'be wayar tace."Sa'ida ashe baki da hankali kina so ki tona mana asirin gida."

Nace." Wane irin zan tona asiri ai gaskiya ce idan munje gaban alkali sai kuyi bayani dake dashi wanda kike daurewa gindin."

Hannunta na rawa tace"Yi hakuri dan Allah abar kaza cikin gashinta domin hakan yafi mutunci zan samu Khalid din naja masa kunne ya daina ta'baki tunda dai ba'a d'aura aure ba."

Nace."Shin yanzu kin yarda da maganata akan Khalid din ko kuwa baki yarda ba."? Da sauri tace."Haba na yarda mana dama sabida kada maganar tayi tsayi ne yasa kikaji nace ban yarda ba amma nasan Khalid zai aikata kuma zanja masa kunne kiyi hakuri kinji ko."

Ajiyar zuciya na sauke nace"To wannan karon dai na hakura idan ya 'kara kwatantawa to zaiga abinda zai biyo baya." Tace."Bama zai 'kara ba insha Allahu.''

Mi'kewa nayi na fita daga dakin ina jin tana fad'in"Kizo ka abincin naki ai tuntuni na shigo miki dashi daki." Nace."Wanka zanyi tukkuna." Da sauri tace."To shikkenan sai kin fito." Bakin rijiya na nufa na cika bokiti da ruwa na dauka na kai bandakin, dakin na koma domin cire kayan jikina.

Bayan sallahr isha'i kasancewar ana zafi a gari gashi babu wuta sai mukayi shimfid'a a tsakar gida muna hira, Ya shigo gidan cikin rashin 'kwarin jiki ya zauna kusa da ita da fad'in "Wash Allah Gwaggo na gaji wallahi nayi mutukar galabaita."

Zaune ta mi'ke tana gyara daurin dankwalinta tace."Yaron kirki ina kaje ne kuma me kayi ka gaji kana yawo cikin ka babu komai ina fata dai ka samu wani abu kaci."?

Ajiyar zuciya ya sauke 'kasa-'kasa ya d'an kalli mutuniyar tasa kafin yace." Wallahi Gwaggo har yanzu banci abinci ba Yau Salim ne ya jani yawo cikin adaidaita sahunsa." Tace."Allah sarki to ina fata ka samo d'an kwabo da d'ari.'' Goshinsa ya murza yace." Na samu me kike bukata."?

Baki ta washe tace."Ina bukatar Gashashshiyar kazar Malo mai nama." Dariya yasa yana kallonta yace."Gwaggo kina san dad'i a rayuwarki duba dan Allah kin iya fad'ar Malo mai nama." itama dariya tasa harda tafa hannu tace."To yaron kirki waye baya san dad'i ai mutukar ban takura maka ba to ka siyo min kazar malo mai nama." Khalid ya dinga dariya yana kallonta.

Takaicin abinda suke ya isheni sai kawai na dauki wayata ina dubawa, naji yace."Gwaggo ko kudin kenan yau sai kinci kazar Malo." Yun'kurawa yayi ya mi'ke tsaye yana kokarin sa takalmansa yace."Auntyna ke me kike so."? Banza nai masa, Tace."Sa'ida kina ji ya nayi miki magana ko babu dai kyau gaba."

Ba tare dana kallesu ba nace."Bana bukatar komai." Tayi sauri tace."Kaji wai bata bukata." Yace."Okey to babu damuwa ai " hanyar fita ya nufa tace"To ina jira dan Allah kada ka fita abokai su ri'ke ka har nayi bacci." Yace."Yanzu zan dawo nima yunwa nakeji ai." tace."To kafin ka dawo bari na fito maka da abincinka." Ba tare da yace wani abuba ya fita daga gidan

Mi'kewa tayi ta shiga daki ta dauko masa fulas din abincinsa kana ta dauko kofin silba ta ciko masa da ruwan randarta tazo ta ajiye a kusa da ita.

Kallonta nayi rai a 'bace nace"Gwaggo keda zaki sanja masa fuska saboda laifin da yayi shine harda dauko masa abinci ko da yake ai nasan kin manta tunda kinga ya samo kudin siya miki kaza idonki ya rufe to har yanzu ina nan akan bakana."

"Aa Sa'ida ban manta ba ina sane inaso yaci abinci ya huta sai nai masa maganar." "Umm! nace naja bakina nai shuru! jin maganarsa shida abokansa a soro yasa na mi'ke na shiga daki, yana shigowa kai tsaye 'kofar Ummatu ya nufa da fad'in " Gwaggo ina zuwa."

Da sauri tace."Aa zo ka bani leda ta kafin ka shiga bana so ta za'be abinda ka shigo dashi.''! Dariya nasa ina mamakin 'karfin halin Gwaggo mata ta haifi d'anta amma ta fita iko dashi.....Dawowa yayi da baya ya mi'ka mata leda guda tace."To yawwa yanzu naji magana ka fito ga abincin naka." Yana 'yar dariya yace."To Gwaggo." Gurin mahaifiyar tasa ya nufa domin itama ya bata tata ledar.
kwance a d'an tsakar gidanta ya sameta da Mafici a hannu tana firfita shigowarsa yasa ta mike zauna tana kallon ladar hannunsa.....Zama yayi gefan tabarmar da take zaune yace."Ummatu me zai sanya ki takura kanki bakya fita babban tsakar gida kisha iska sosai."

Girgixa kanta tayi tace."Khalid 'kyaleni anan yafi min kwanciyar hankali akan na fita Gwaggo ta fad'a min ba'kar magana."

Yace."Ummatu idan da sabo yaci ace ki saba da halin Gwaggo wata irin macace mai wani irin hali bayan haka kuma akwai rikicin tsufa a tare da ita." Girgiza kanta tayi tace."Khalid dama ai kai baka ganin laifin Gwaggo duk abinda tayi daidai ne a gurinka."

Girgiza kansa yayi yace."Ba haka bane wallahi Ummatu yanzu a matsayin na shekarun Gwaggo dole ayi mata uziri shiyasa kikaga duk abinda tayi nake biye mata saboda samun nutsuwarta ba wai bana san laifinta bane."

Tsaki taja tace."Duk da da akwai tsufa to da akwai iskanci wannan tsohuwar guda ce Khalid ni kad'ai nasan irin takaicin da take kuntuka min a gidan nan."

Yace."To kiyi hakuri dan Allah komai mai wuce wa ne gashi kema na siyo miki nama." Kar'ba tayi tana duba ledar tace."Sai da ka kai musu suka za'ba tukkuna ni aka kawo min saura ko."

Girgiza kansa yayi yace."Aa Ummatu duk d'aya ne wallahi dake da Gwaggon." Tace."Ai kamata yayi ka daina daidaita ni da ita tunda ni na haifeka idan kana neman albarka sai kayi min biyayya."

Yace."Ummatu dan Allah ki daina irin wannan maganar wallahi dake da Gwaggo duk daya kuke a gurina ke kika haifeni dole kina da martaba ta mussaman a gurina Gwaggo kuma itace ta raine ni har na girma Gwaggo bata san 'bacin raina komai ta samu nawa ne abinci wannan Gwaggo bata ci sai tare dani sai dana na tafi makaranta tukkuna muka raba kwano da ita Gwaggo takan iya hana cikinta abu ta ajiye min Ummatu kada ki manta Gwaggo itace tayi rabin dawainiyar Karatuna idan tayi sana'arta haka zata tattara kudin ta bani nayi hidimar makaranta dasu duk lokacin da nazo hutu sai ta bani kudi wata bukatar zata taso Gwaggo tayi Baba yayi a haka fa akayi ta tafiya har Allah ya kawo ni wannan lokacin da nake daf da kammala makaranta kinga kuwa dole na kyautata mata domin ta taka muhimiyyar rawa a rayuwata."
Chapter 4 · 0% Book details