← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na amsa a nutse da fad'in "Khalid tsayin wattanin hudu kana ina ne? shin kasan halin damuwar ka jefe iyayen ka a ciki kuwa? Uwa uba Gwaggo na nan ta'ki lafiya kullum sai tayi kuka kafin ta kwanta bacci tana ganin kamar baka raye a duniya dan Allah ka dawo gida ni idan saboda ni ka tafi to ka dawo na yafe maka.''

A sanyaye yace." Aunty Sa'ida idan na dawo gida zaki aure ni."? Gabana ya fad'i nace."Khalid ashe har yau baka daina wannan tatsuniyar ba."?

Ransa ya 'baci yace."Ki daina kiran soyayyata da ta tsuniya insha Allahu sai ta zama gaske."

Nace."Okey to naji yanzu dai yaushe zaka dawo gida."? Yace."Kina so na dawo ne."? Nace."Eh ka dawo ka nemi afuwar iyayenka ni kuma na yafe maka."

Yace."Aunt Sa'ida idan na dawo gida zan takura miki fa." Nace."Khalid na amince zan aureka ka dawo gida."

Da sauri yace."Da gaske kike.''? Ajiyar zuciya na sauke cikin yaudara nace "Eh da gaske nake kana dawowa za'a daura aure."

Yana dariyar farin ciki yace."Okey ki bani Gwaggo mu gaisa insha Allahu zan dawo gida a satin nan.

Nace."To yanzu dai bana gida ina gidan 'kawata Hauwwa insha Allahu idan na koma gida zan kira ka sai ku gaisa."

Yace."Nagode auntyna insha Allahu zakiyi alfaharin aurena zan jiyar dake dadin duniya auntyna zan kula dake zan zama bawanki zan kwanta ki taka ni zan zama d'an aiken ki zan......Katse shi nayi nace."To duk naji na kuma gamsu da maganarka Ka bari idan ka dawo sai ka 'karasa.

Yar dariya yayi yace."Okey to shikkenan zan kira anjima idan kin koma gida." Ina kokarin kashe wayar nace"babu damuwa.

Hauwwa ta zuba min ido tana kallona tace."Sa'ida babu kyau yaudara fa ban so kikayi masa haka ba ya za'ayi kice zaki aureshi bayan kin san gobe daurin auranki."?

A sanyaye nace."Hauwwa ni nasan halin Khalid idan ba haka nai masa ba wallahi ba zai dawo ba ga Gwaggo taki kwantar da hankalinta dan har fargaba nake na tafi na barta cikin halin damuwa kullum da daddare sai na lalla'bata take bacci.'

Hauwwa tace."To yanzu idan yazo ya tarar kinyi aure fa wane hali kike so ya shiga."?

Kai tsaye nace."Sai yayi hakuri ya kaddara cewa ni d'in ba matarsa bace."

Hauwwa tace." A gaskiya da kamar wuya ya iya wannan hakurin dan yaron yana miki mahaukacin so." Nace."To hauwwa idan ba zai yi hakuri ba sai yayi abinda zaiyi." ta bini da kallon mamaki! na Kalli mai kunshin nace."Baiwar Allah ki cigaba." Ta kama kafata da sauri ta cigaba da akinta.

Khalid cike da farin ciki yake shedawa abokinsa Salmanu abinda ke faruwa. Salmanu na washe baki yace."Kai amma naji dadi wallahi to yanzu ya za'ayi naji kace a cikin wannan satin zaka tafi kuma gashi zamu fara buga wasa a Club kasan kana da mutukar mahimmanci a 'kungiyar nan ko zaka bari mu gama wasan in yaso wani satin sai ka tafi."

Girgixa kansa yayi yace."Salmanu hankalina gabadaya yayi gida wallahi kafin na tafi zan nemi shugaban kungiyar na fada masa uziri na idan za'a d'aga wasan nan da sati uku sai ayi min uziri idan kuma yana ganin da akwai wanda zai kawo a madadi na sai ya kawo dan gaskiya babu abinda zai hana ni tafiya gida.

Salmanu jikinsa yayi sanyi sam baya so abokin nasa ya tafi yana ganin kamar damar da suka samu zata iya kufcewa gashi ogan nasu kullum sukaje training yakan fad'a musu cewa yana so su mayar da hankali sosai domin a wannan karon ne yake so ya za'bi za'kwa'kurai a cikinsu da zasuje america su buga wasa to
wannan dalilin yasa gabad'aya Salmanu baya so a bokin nasa ya tafi domin jikinsa na bashi kamar zasu samu nasara.

Khalid yace."Tashi ma muje chamber d'in Allah yasa mu sameshi." Salmanu ya mike yana kokarin cire kayan jikinsa ya sanja wasu.

Sun ci sa'a sun sameshi yana horar da wasu suka samu kujeru suka zauna bayan sun gaisa....Oga Labaran yace."Khalid me yasa yau baku shigo da wuri ba."?

Yace."Wallahi oga mun je gurin aiki ne kasan dama sai da mukayi maka bayani cewa asabar da lahadi ba zamu dinga zuwa da wuri ba saboda muna zuwa gurin aiki da wuri.

Oga Labaran yace."Eh hakane na manta da wannan bayanin dama inaso kuzo mu tattauna ina fata dai kuna cigaba da shirye-shirye kamar dai yanda na fada muku cewa Mr William zai zo a ranar da zamu buga wasa na k'arshe kuma a ranar za'a za'bi muzakkarai a cikinku domin kuje ku fatata da 'yan wasan dake can america.

Khalid yace."Oga sai da ni ayi min uziri wallahi cikin satin nan nake so naje ganin gida."

Oga Labaran da sauri ya kalleshi cikin yanayi na damuwa yace."Khalid me yasa zakayi mana haka? kana fa d'aya daga cikin 'yan wasan da nake alfahari dasu, ka iya buga 'kwallo sosai shiyasa nake so kai ka zama zakaran gwajin dafi nasan ko munje america ba zaka bani kunya ba sai kuma kazo min da wannan maganar.""

Yace."Oga wallahi uziri babba ne zai kai ni gida ayi min alfarma." Oga Labaran ya girgixa kansa da fad'in "Khalid dole fa kayi hakuri domin ba zaka sa nayi asara ba ka bari muyi wasan nan mu gama lafiya a za'bi wanda suka dace ayi dasu in yaso sai ka tafi kafin lokacin tafiya american ya tashi."

Khalid yayi shuru tare da sunkuyar da kansa tunani yake akan lamarin.....Yana son aunty Sa'ida baya so ta kufce masa gefe guda kuma ga wata babbar dama ta same shi wacce yake saka ran samun nasara wai shin ya zaiyi ne?

Oga Labaran ya kalleshi da fad'in "Khalid kayi shuru kada fa ka bani kunya khalid."

Ya dago kansa da fad'in "Oga zanyi nazari akan al'amarin insha Allahu kafin lokacin zan yanke shawara." Yace."To shikkenan Allah yasa naji alkairi."

Har sun miqe da niyyar tafiya ya hana su yace su sanya kaya suyi wasa. ba tare da 'bata lokaci ba suka bi umarninsa suka shiga d'akin da suke shiryawa suka sako kayan kwallo suka fito kai tsaye filin wasa suka nufa su shiga shiga cikin 'yan uwansu Oga Labaran ya mike yana zagaye gurin tare da addua akan Allah ya daukaka 'kungiyarsa ta Kano pillas.

****
Ina komawa gida na fad'awa Gwaggo cewa Khalid ya kira waya sai ta kwantar da hankalinta yana raye bai mutu ba, ba tare da tace min komai ba naga ta mike ta dauki buta ta fita, alwala ta dauro ta dawo dakin ta gyara dadduma ta tayar da sallah, ina zaune ina kallonta tayi raka biyu ta jima a sujjadar karshe tana addua kafin ta dago....ko bayan da tayi sallama ma sai da ta daga hannu sama ta dinga godewa Allah tana share hawaye.....na cika da d'umbin mamakin irin kaunar da takewa yaron

Mi'kewa tayi ta fita daga dakin minti uku suka dawo tare da Ummatu tana washe min baki tace."Sa'ida ashe Khalid ya kira ki a waya ko."? Nace."Eh wallahi d'azu da rana mun jima muna waya har yace yana so yayi magana daku nace ya bari na koma gida.

Gwaggo tace"Dan Allah ki kirasa 'yar albarka so nake naji miryarsa.

Nace."Gwaggo babu kudi a waya ta bari a samu yaro ya siyo kati.'' Da sauri Ummatu tace"Ga dari biyu a siyo katin." kokarin kwance bakin zaninta take nace"Haba dai bari ba sai kin bada kudi ba bari na duba yaro." Gwaggo tace."Sa'ida na dauka gurin siyar da katin babu nisa inace gurin Auwala ne." Nace."Eh tace."To bani na siyo da kaina." kallonta nayi naga duk ta tashi hankalinta na koma na zauna bakin gado ina gwada siyan kati ta banki babu network ko kad'an na mika mata kudin ta yafa mayafi da sauri ta fita.

Ummatu kuwa tsayawa tayi tana jana da hira na dinga mamakin matar ta saki jikinta dani a yanzu ta daina jin haushina kullum kuma na gaisheta da sauri take amsawa komeye dalili oho.

Gwaggo ta dawo gidan da katin mtn a hannunta da sauri na kar'ba nasa a wayar.......Muryar wani mutum naji a kunne na. nace."Dan Allah Khalid fa."? Yace."A yanzu dai suna filin wasa sai dai idan sun fito." ko kafin nace komai ya kashe wayar.

Gwaggo a sanyaye tace."Ya akayi."? Nace."Wani mutum ne ya dauki wayar yake cewa wai khalid din yana filin wasa.

Gwaggo da Ummatu suka had'a baki gurin fad'in "Ina ne kuma filin wasa."? Nace"Watakila gurin ball yake nufi kun san dama Khalid akwai naci ball a lokacin da yake gida.

Gwaggo tace."Eh hakane kuwa to an jima sai a sake kiran wayar. shuru nayi ina duba waya ta Ummatu tace." To bari naje na karasa ayyukana."Gwaggo tace."To shikkenan daga zarar wayar ta shiga zan fito na fada miki." Ummatu tace to shikkenan a yayin da take kokarin barin gurin.

Kallonta nayi a nutse nace."Gwaggo a yau da daddare nake so naje gidan Ummana nayi sallama da ita." Gwaggo tace."Ba zaki bari ba gobe idan za'a kai ki dakin ki sai na raka ki." Nace."Aa Gwaggo gwara naje yau din." Tace."To shikkenan Sa'ida ai ni ban ta'ba ganin biki irin naki ba sam baiyi farin jini ba.

Nace"Saboda me kike ce haka."? Tace."Ai gani nayi gidan nan yaki cika da mutane makota ne kawai suke shigowa a tsaitsaye suyi Allah ya sanya alkairi su fita."

Nace."Gwaggo wannan kuma kanki zaki tuhuma ina dangin suke."? Tace." Sa'ida kenan ai ni dangina duk sun mutu saura qalilan dama bamu da yawan zuria ko baki gani bane."?

Nace."Hakane amma ai Ummana tana taro a gidanta ita da 'yan uwanta'' Tace."Aikuwa mu dai sai gobe idan an daura aure zamuyi namu taron."

Shuru nayi tace."Dan Allah ki zauna a dakin mijinki lafiya tunda dai Allah ya had'aki da kishiya mai mutunci to ki 'ki ji ki 'ki gani babu ruwanki da 'yan bani na iya kada 'kawar data zugaki ki dauka.

Nace."Insha Allahu Gwaggo zan bawa mara d'a kunya." Tace."Allah ya sanya alkairi Ya bada zuria dayyu'ba." a zuciya na amsa da ameeen.
Chapter 34 · 0% Book details