← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 90

Sashe 85

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari
Da wuri na kammala komai na shirya tsaf na zauna zaman jiran shigowarsa...........Cikin 'kananun kaya ya shigo ya shirya tsaf da shirin futa amma babu walwala a tare dashi.

Kauda 'bacin raina nayi na gaishe ya amsa yana gyara wuyan rigarsa Yace."Za muje asibiti da Jamila yanzu." A nutse nace."Me yake damunta."?

'Dan ya mutsa fuska yayi yace."Zazza'bin dare take sai kasala da rashin kwarin jiki." Nace." Allah sarki Allah ya bata lafiya ." Ya amsa da ameen yana kokarin fita.......Sunansa na kira yaja ya tsaya yana kallona.

Nace."Inaso naje gidan gaisuwar nan."? Shuru yayi yana kokarin bude kofar dakin. Nace." Kaga yau sadakar bakwai zan samu jama'a sosai sai nayi musu gaisuwa."

Cikin takaici yace."Ke yanzu idan akace dake kije sai kije."?

Rai a 'bace nace." Wace irin magana ce wannan ko babu haihuwa a tsakanina da mutumin akwai ala'kar aure data had'amu kada kuma ka manta irin hidimar da yayi mana nida Gwaggo wannan mutumin bai cancanci wulakanci ba."

A harzu'ke yace." Ke komai qabli da ba'adin da zaki kawo min babu inda zakije mutu'kar ni ne zan baki umarni idan kikayi masa addua ma a gida ta isa.

Yana gama maganarsa yasa kai ya fice daga dakin....Rasa bakin magana nayi kawai na tsirawa guri guda ido ina mamakin al'amarin.

Jamila ashe ciki ta samu sai bayan sun je asibitin likita ya tabbatar musu dashi Khalid yayi farin ciki sosai sai dai kuma likita ya kafa sharad'ai domin ingantuwar cikin nasu mahaifar Jamila bata da k'wari tana saurin budewa likitan yace kada ta dinga daukar abu mai nauyi babu zurga-zurga sannan shima Khalid din kada ya takura mata da fitina. duk abinda za suyi su bari cikin yayi 'kwari tukkuna.

Jamila rawar kai ya 'karu sai langwa'bewa take miji na rarrashinta Baito kakarsu 'kullo kaya tayi ta tare a gidan wai tazo tayi jinyar ta zuwan ta ne ma yasa nasan da samuwar cikin dan har sashena ta shigo tana yar min da habaici ni dai uffan ban ce mata ba ta gaji da surutan ta ta tashi ta tafi.

Tun da likita ya kafa masa wannan sharad'in ya takura min da fitina babu dare babu rana gajiya nayi na daina yarda yana wahalar dani da yake makiri ne sai wani shagwa'be wani sa'in har kuka yake min yayi ta rarrashina amma fa idan rashin mutuncinsa yazo sai ya sauke min sama da kwando goma hakuri kawai nake da zaman aure domin nasan ibadah ne.

Gwaggo tazo duba Jamila da 'yan kayan dubiyarta...... guri na ta fara yada zango muka gaisa sosai na bata abinci taci ta koshi sai bayan tayi sallar azuhur ne ta kalle ni cikin alhini tace."Ke kuma Sa'ida me yake damunki naga kinyi rama dubi kashin wuya ko dai kishi kika sa a ranki."

Girgiza kaina kawai nayi nace."Gwaggo wane irin kishi kuma Khalid ne kawai yake azabtar dani yaki bari mu zauna lafiya masifar yau daban ta gobe daban kullum babu sassauci."

Tace."Me yasa kin san halinsa ba zakiyi hakurin zama dashi ba ina nufin kiyi kokarin ganin kin kauda abinda zai kawo muku sa'bani a tsakaninku."

Girgiza kaina nayi nace." Gwaggo kenan ban san me zance miki ba amma ni nasan ta kowane 'bangare bana zalintar yaron nan shine kawai ya kasa kwantar da hankalinsa."

Tace."To kuwa idan hakane zaizo ya sameni ni bana son rashin adalci na lura dama kamar yafi karkata gurin kishiyarki to mutukar yace ba zaiyi adalci a tsakaninku ba yana tare da fushin Ubangiji."

Nace."Yana dai da kyau ki zaunar dashi ki masa fad'a ni na gaji da wannan masifar wallahi.'' Tace."Kada ki damu tashi ki rakani na duba jikin nata.

Hijabi nasa muka fita tare.........Kaca-kaca muka samu falon Baito da Ummatu da mahaifiyar Jamilan suna zaune sai hira suke sun ci abinci dik sun baja-baja dashi a kasan kafet Jamilan kuma na kwance akan doguwar kujera tana bacci.

Gwaggo ta samu guri ta zauna tana kallon Ummatu tace."Ashe nan kika nufo kema."? Cikin inda-inda tace."Eh wallahi nazo duba jikin nata ne " Tace."Ai babu laifi.''

A nutse na gaisa dasu suka amsa babu yabo babu fallasa Gwaggo kuwa babu wacce ta gaisar a cikinsu ya mutsa fuskarta tayi tace." Ku kuwa don Allah bakwa jin tsami da karni a falon nan wace irin rayuwa ce wannan kuzo gidan yara kuna 'barna a maimakon gyara."

Falon yayi tsit! cikin zuciyata nace."Gwaggo ba'a ci miki bashi........Ta cigaba da cewa." Ai amfanin zuwanku shine kuyi mata gyare-gyare ku sata tayi wanka ku kwantar mata da hankali amma duba don Allah sai hayaniya kuke kunyi kaca-kaca da gurin Haba Baito a wannan zamanin da ake saurin daukar ciwo ai idan su basu da hankali ke kina dashi sai ki tsawatar musu."

Baito ta 'bata rai da fad'in"Gwaggo Matsalata dake kenan shiga sabgar da bata shafe ki ba ina ruwanki da abinda idonki ya gane miki."

Tace."Babu ruwa na amma ni bazan ga abunda bai dace ba nayi shuru dole sai na fadi gaskiya koda zaku tsire da tsinken tsire ." Nace."Gwaggo dan Allah maganar ta isa haka.

Jamila ta mike zaune tana hamma! Gwaggo ta zuba mata ido tana kallo magana ce a bakinta amma dai tayi shuru.....Jamila kamar bata so ta gaisheta ni kuwa ai ko kallon inda nake bata yi ba." Gwaggo tace." Jamila ga kayan Lambu nan na kawo miki Allah ya kara sauki ya raba lafiya."

Gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah." Ta mike tana gyara lullu'bin mayafin ta "To ni zan tafi." mikewa nayi Baito da Ummatu suka ce "To shikkenan muma yanzu zamu tawo."
Tace."Oh!o kuna iya kwanciyar ku tunda zaman ku a gurin shine zai bata lafiya ciki dai ba akanta a kafara ba kuma ba za'a k'are a kanta ba."

Baito tace."Ramatu wannan habaicin ya isa haka ko don kinga nayi miki shuru ne ? ciki dai Allah ne ya bawa Jamila kuma babu mahalu'kin da ya isa yace ciki ba na Khalid bane."
Gwaggo tana kokarin magana na rufe mata baki da sauri na rike hannunta na jata muka fita daga falon........

*104*
Kamar 'Yar jagora haka nake jan hannunta ta fizge da fadin."Sakar min hannu ni ba makauniya ba sai jana kikeyi ina zaki kaini." ? Kallonta nayi tana gyara mayafinta nace."Gwaggo don Allah ki dinga hakuri da rayuwa wannan cacar bakin da kuke yi sam bai dace ba yanzu an riga an zama daya ni wallahi zuciya daya nake zaune da Jamila shiyasa kwata-kwata bana daukarta a matsayin kishiya sai 'yar uwa."

Ajiyar zuciya ta sauke tace."To naji dadi da kika fad'i haka saboda haka sai ki cigaba da zama da ita da zuciya daya idan ma ita ta nufe ki da sharri zai koma kanta, sannan kina magana akan su Baito kin dai san halina ni ba zan ga ana ba daidai ba nayi shuru da bakina sai na fad'a musu gaskiya sai dai duk abinda zasuyi suyi.'' Nace."To gurin fadar gaskiyar ki san irin maganar da zaki dinga fad'a dan Allah." Shuru tayi nace."Muje nasa driver ya kai ki gida ko."

Tace."To dama zaman me zanyi tunda nayi abinda zanyi sai dai idan Jarumi ya dawo ki fada masa cewa ina nemansa domin da kyar idan zai je inda nake tunda ba kullum yake zuwa ba."

Nace."To shikkenan Insha Allahu zan fad'a masa." Ina tsaye dravar yaja motar maigadi ya bude gate suka fita daga gidan, ajiyar zuciya na sauke tare da juya da niyyar komawa cikin gidan.

"Baito wai menene naga tunda na shigo kike shan kunu ko kin gaji da zaman jiyyar kina so ki tafi gida."? Khalid ne yake wannan maganar a lokacin daya dawo gidan.

Cikin b'acin rai tace." Khalid raina ne a 'bace wallahi saboda bayan fitarka daga gida kakar ka Gwaggo da matarka suka zo har nan inda nake suka ci mana mutunci harda kiran zuriarmu da makwad'aita matalauta 'kazamai kai babu irin cin mutuncin da ba suyi mana ba 'Karara suka nuna bakin cikinsu akan cikin dake jikin Jamila Al'amarin ya bani mamaki sosai."

Shuru yayi yana kallonta da nazarin maganarta yasan halin Gwaggo da fadin gaskiya da kuma rashin hakuri amma baya tsammanin za tayi irin wannan cin mutuncin kuma tunda ta samu labarin cikin Jamila take farin ciki da adduar sauka lafiya shiyasa yake nazarin maganar.

Baito tace."Ai dama nasan ba yarda za kayi ba tunda kai kullum baka son laifin kakar ka 'kiri-'kiri ka nuna mana cewa tafi mu muhimmanci a rayuwarka."

Yace."Baito kiyi hakuri don Allah zanyi binkice akan maganarki idan na gano da sanya hannun Sa'ida a cikin al'amarin zan dauki mataki domin ni babu wata mace da zan aura ta raina min dangi."

Baito tace."Ai shikkenan tunda ka 'karya ta maganata sai kaje kayi ta binkicen." Shuru yayi mata ya mayar da hankalinsa kan Jamila dake xaune a gefansa tana faman ya mutsa fuska......"Ya jikin naki ina fatan dai lafiya."? a shagwabe tace."Lafiya lau amma fa babyn nan naka yana wahalar dani ko ba haka bane Baito.''?

Tace."Kwarai kuwa hakane wannan cikin ai tsirfar sa yawa gare ta." Yace."To ko zakuje asibiti idan Allah ya kaimu." Baito tace."Aa ai ba sai anje asibiti ba laulayi ne kawai kuma duk mai yaron ciki tana irinshi mu dai babban fatan mu yarinya ta haihu lafiya." Yace."To shikkenan Allah ya kara lafiya ya kuma sauketa lafiya." Gabadaya suka amsa da Ameeen.

Mi'kewa yayi da wayoyinsa a hannu yace."Ni zan shiga na watsa ruwa na kwanta na huta sai da safe in Allah ya kaimu." Baito tace."To Allah ya tashe mu lafiya." Jamila kuwa shuru tayi tana bin shi da kallo wani irin bakin kishi yana taso mata gaskiya ta kusa ta karya dokar likita dan ba zata iya jure rashin mijinta ba.

Jin motsin shigowarsa yasa nayi saurin kallon bakin kofar..........Ido muka had'a dashi a lokacin da ya shigo falon. a nutse nayi masa barka da zuwa ya amsa tare da nufar bedroom d'inshi.
Chapter 85 · 0% Book details