← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar ya daga yasa a kunnensa had'a da sallama.....Alhaji Shamsu ya amsa masa a nutse suka gaisa da juna kafin yace."Alhaji Nura wane gagarimin laifi yarinyar nan tayi maka kayi mata saki uku a lokaci guda."?

A tur'bune yace."Kana so kasan dalili kenan."? Da sauri yace."Eh ai sabida inaso nasan dalilin yasa na kira wayarka domin dai nasan babu shakka ruwa baya tsami banza."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Ai Alhaji kune da laifi kuma banta'ba tsammanin zaku munafurce ni ba ashe yarinyar nan sai da ta gama watsewa da lalattatun maza a waje ku rufe min na aureta.

Cike da mamaki yace."Wace irin magana kake Alhaji Nura ban fahimci inda ka dosa ba yarinyar nan Sa'ida da kima da mutuncinta muka aura maka ita."

Da sauri yace." Waye ya fada maka haka? bari ma dai na daina rufe maka magana a ranar dana kusanci yarinyar nan na gane ba budurwa bace fanko ce. lokacin dana turketa ina tuhumarta tana kuka ta kawo min wasu hojojji wanda suka kashe min jiki har na yarda da ita na cigaba da zama da ita, a kwanakin baya yaron da nake zargin shi ya lalata ta yazo har cikin gidana sabida tsabar cin fuska har cikin d'akina na same su nan ma raina ya 'baci sosai na nuna mata kuskuranta hakuri ta bani ta nuna min babu wata alaqa a tsakaninsu sai gashi jiya Dr Maryam likitan ta ta tabbatar min da gaskiyar magana kuma itama Sa'idar ba tayi musu ba akan abinda ake zarginta dashi al'amari ya fusata ni sosai kuma naji takaicin abinda kukayi min na ha'inci wannan dalilin yasa na yanke alaqar aurena da ita."

Alhaji Shamsu ji yayi gumi na tsatstsafo masa bakinsa ya bushe qamas da kyar yace."Alhaji Nura ka dai fad'i wata hujjar amma ba wannan ba yarinyar nan Sa'ida bata san ko wane namiji ba lafiya lau muka aura maka ita kadai kara binkice akan maganarka."

Alhaji Nura yace."Alhaji a yanzu dai babu batun tashin-tashina a tsakaninmu tunda dai na yanke alaqar data had'a mu shikkenan magana ta 'kare dan Allah kada ka 'kara kiran wayata kazo min da maganar Sa'ida na sake ta saki uku babu ni babu ita."

A fusace! Yace."To sai me don ka saketa Alhaji Nura akwai maza a duniya da zasu aureta kuma wallahi ina mai tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abinda ka aikata."
Yana gama maganarsa ya kashe wayar sam baya bukatar sake jin wata magana daga bakinsa sabida yayi masifar 'bata masa rai."

Ummu Habiba kallonsa kawai take ko beyi mata bayani ba ta fahimci komai tunda wayar a hands free take.....Gumin goshinsa ya goge yace."Saboda kawai yana so ya rabu da yarinya sai yayi mata kazafin zina Habiba kina jin abinda mutumin nan yake fada akan yarinyar nan Sa'ida wai bai sameta da budurci ba to bai samu budurcinta ba me yasa tun farko bai fada ba sai yanzu da tayi watanni a gidansa ni nafi tunanin cewa ya gaji da zama da ita ne shiyasa ya shirya wannan maganar."

A sanyaye tace."Ni kaina al'amarin ya daure min kai kuma duk bayanin da yayi maka naji da kunnena dama can ba son Allah da annabi yake mata ba sha'awarta yake."

Ya dauki hularsa yasa da fad'in "Ai babu komai duk wanda yayi nagari kansa kiyi hakuri kuma ki cigaba dayi wa yarinyarki addua insha Allahu Allah zai za'ba mata abunda yafi alkairi a rayuwarta.

A sanyaye ta amsa da " Ameeen Alhaji nagode sosai da kulawar ka akan yarinyar nan." Yace."Habiba ni na dauki Sa'ida tamkar ni na haifeta saboda ina tausayawa maraicinta ina kuma kwadayin ladan kula da maraya sabida haka kada ki damu zan tsaya tsayin daka akan yarinyar nan."
Tace."To shikkenan Alhaji Allah ya shige mana gaba kai kuma abinda kakeyi na alkairi Allah ya baka lada." ya amsa da ameeen ya Allah yana kokarin fita sai ta mike a nutse tabi bayansa domin taka masa.

Koda ta dawo gidan dakinta ta shiga ta zauna kan kujera babu kuzari a tare da ita ta dauki wayarta number 'yar tata ta nema ta shiga gurin kira.

Lokacin data kira ina bandaki ita kuma Gwaggo bata iya da waya ta ba kira ta dinga kwala min da fadin na fito ana kiran wayata.

A gugurje na fito daga bandakin na ajiye butar hannuna, wayar ta miko min da fadin."Kinga har ta katse sai ki duba kiga ko wanene idan Khalid ne kada ki daga ki shareshi kamar yanda nake masa idan ya kira ni."

Murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba na nufi dakin da wayar a hannuna ina dubawa

Ganin number Ummana yasa da sauri na zauna gefan gado na shiga gurin kira da alama wayar tana hannunta domin sau daya tayi ringing ta daga, yanda naji muryarta a sanyaye yasa nima jikina ya mutu a nutse na gaisheta ta amsa tare da fadin."Ya mukaji da wannan abu."

Nace."Alhamdulillahi Umma." Tace."Kiyi hakuri kinji ko kowane mutum akwai irin kaddararsa kisa a ranki cewa dukkanin abinda ya faru da rayuwarki kaddara ce insha Allahu wataran sai labari."

Hawayen da suka zubo min na share murya na rawa nace."Insha Allahu Umma ki taya ni da addua akan Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."

Tace."Sa'ida addua kullum akanta muke Ubangiji Allah ya amsa mana adduo'inmu na alkairi." cikin sanyin murya na amsa da ameeen Ummana." Tace."Ki gaishe min da Gwaggo da kyau." nace."To zataji insha Allahu.'' Sallama mukayi da juna......Gwaggo ta shigo dakin tana fadin."Dawa kike waya ne."? Nace."Umma Habiba ce tace ma a gaisheki.''

Kallona tayi da fadin."Ita kuma a ina ta samu labarin abinda yake faruwa."? Nace."Watakila ko Kawu ya sanar da mijinta ne.''

Tace."Eh hakan zata iya yuwu wa Allah dai ya kyauta.'' cikin mutuwar jiki na amsa da "ameeen ya Allah.

*BAYAN SATI DAYA*
Na d'an samu nutsuwa hankalina ya dawo jikina sai nayi tunanin kiran Hauwwa a waya domun na sheda mata abinda yake faruwa..........Sosai Hauwwa tayi mamakin al'amarin daga bisa ni tace." Yanzu dai kinga ne abinda ke da akwai ko? a yanzu dai kin fahimci cewa auran Babban mutum bashi bane tunda gashinan wata shida har anyi an gama ya rattaba miki saki uku wallahi da Khalid kika aura ba zaki fuskanci wannan matsalar ba babban tashin hankalin ma mutumin nan yayi miki sanadin aikin ki."

Nace."Ni wallahi a yanzu shine babban abinda yake damuna wata shida bai zama lallai idan na koma aiki su kar'be ni ba......Hauwwa tace ko zasu kar'be ki sai an kai ruwa rana amma babu matsala ni zanyi miki kokari kin san Shugaban makarantar yana zawarcina zanje har ofis d'insa na lalla'ba shi." Nace."Yawwa aminiyata nagode kwarai dan Allah kiyi min kokari." Tace."Kada ki damu mybe ma gobe idan mun tashi na shigo domin mu tattauna." Nace."To shikkenan sai kin shigo Hauwwa nagode Allah ya bar zumunci." ta amsa da ameeen ya Allah ki gaishe min da Gwaggo." nace."Za taji insha Allahu."

Wayar na kashe ina jin sassauci a cikin zuciyata.....Gwaggo dake kad'i ta kalleni da fad'in." Naji kina magana komawa gurin aiki Sa'ida ke yanzu sai ki koma cikin maza bayan zargin da ake miki."?

Nace."Gwaggo kina so kenan na zauna a gida babu aikin fari bare na baki ko."? tace."Oh!o ni nafi so ki samu miji kiyi aure Sa'ida.'' Nace."Gwaggo kada kiyi min maganar aure a yanzu domin dai bashi ne a gabana ba'' Tace."To ai shikkenan idan lokacin auran yazo sai ki hana Allah ikonsa." shuru nayi mata domun nasan neman magana take.....Ummatu ta daga labulan dakin da waya a hannunta tana fadin."Gwaggo ga d'an d'akinki ya kira waya wai yana so ku gaisa.'"

Tace."Ke Rabi raba ni da wannan yaron ki fada masa ni bana bukatar magana dashi a yanzu." Tace."Gwaggo me yayi zafi."? Tace."Rabi duk irin kulawa da rarrashin da nakewa yaron nan besa yaji maganata ba to ni kam me zaice dani ai na daina wahalar da kaina a kansa."
Ummatu jikinta a mace ta bar gurin...Gwaggo taja tsaki da fad'in "Kawai kin d'auko wata kod'add'iyar yarinya kin nana masa ya aura yarinya sai kace zabiya tana yawo sai kace takand'a babu kumari babu 'kira da cika irin na mata.'"

Dariya nasa ina kallonta nace."Gwaggo kefa naji kina kod'a yarinyar kina cewa sun dace da juna gata kyakkyawa mai kuruciya."

Tace."Ai ni banta'ba 'karewa yarinyar kallo ba sai ranar da ta zo gaishe ni lokacin yana nan be tafi ba ranar nayi azimin litinin yaje ya dauko ta wai tazo tayi min sannu da shan ruwa tsabar haushi ko kayan data kawo min ban duba ba na bawa al'amajirai."

Nace."Yanzu dai kina nufin bakya kaunar al'amarin kenan."? Tace."Yo Sa'ida me Jarumi zai samu a jikin yarinyar nan jiki a bushe ko'ina babu kumari sai qashi shi kuwa kato dashi tubarkallah ai yana da kyau ya samu 'koshashshiyar mace yanda zai more kuruciyarsa.

Dariya nayi sosai ina kallonta nace."Gwaggo wai dan Allah me yasa bakya kunyar fadar magana ne? Tace."Sa'ida wace kunya kuma ai gaskiya na fad'a.'' Nace."To Allah dai kyauta Gwaggo ni dai shawarar da zan baki ki kauda kanki daga al'amarin nan idan kika ce zaki zuga Khalid ya bijirewa umarnin mahaifiyarsa zaki jefe shi a masifa sannan Ummatu da 'yan uwanta zasu dinga jin haushinki."

Tace."To dama Sa'ida ni ina ruwana yaje ya aureta nasan duk daran dad'ewa sai ya sake aure tinda ni nasan halin fitinarsa wannan siririyar yarinyar ba iyawa za tayi dashi ba."

Ina dariya nace."Gwaggo ai ba'a nan take ba sai kiga mace mara qiba amma sai ki sameta da juriya da kuzari ita kuwa mai qibar sai ki sameta da raki da rashin juriya.''

"Ummm! tace ta cigaba da abinda takeyi a jiyar zuciya na sauke a hankali nace." Gwaggo ni dashi Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi ki tsananta dayi mana addua.'' Tace."Insha Allahu Addua ba zamu bari ba har sai ranar da numfashi ya fita daga gangar jikinmu."

[3/24, 11:39 AM] +234 703 008 7807: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
Chapter 50 · 0% Book details