← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 90

Sashe 25

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Bangaran Khalid kuwa yana fita kai tsaye can Na'ibawa 'yan lemo ya nufa gidansu abokinsa Salmanu wanda suka gama karatu a tare tun kafin ya isa gidansu abokin nasa ya kirashi a waya ya sanar masa zuwan nasa sai kawai ya kashe wayarsa yasa a jakar kayansa yasan dole daka gida a nemi inda yake shiyasa ya kashe wayar gabad'aya.

Kawu Iro yana fitowa daga gidan kai tsaye Gidansu Salim ya nufa babban abokin yaron nasa yana kokarin aika yaro gidan Salim din ya fito ganinsa yasa da sauri ya risina yana gaisheshi.

Kawu ya amsa tare da Tambayarsa ina abokinsa yake.

Salim yace."Wallahi baba nima yanzu na dawo gidan na tarar da key na adaidaita sahu wai d'azu Ya aiko yaro dashi a ajiye min da nazo mahaifiyata take min bayani shine fa yanzu na fito da sauri zan siyi kati nasa a waya na kirashi naji dalilin da yasa ya kawo min key din

Kawu yace."Ai tuntuni nima nake kiran wayar tasa taqi shiga amma dai jeka siyo katin ka gwada kiransa ko Allah zai sa wayar ta shiga."

Salim da saurin gaske ya nufi gurin sayar da katin gabadaya hankalinsa a tashe yake da abinda abokinsa ya aikata a daidaita sahu wuya take a gari shi ya samu an bashi sojan gona yana samun kwabo da dari amma saboda bashi da hankali ya dawo da key din.

Kawu Iro kuwa bayan wucewar Salim daga gurin sai ya samu gefan dakalin dake 'kofar gidan ya zauna yana jiran dawowarsa.
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*

*24&25*
Jiki a sanyaye ya 'karaso kofar gidan nasu Kawu Iro na ganin yanayin fuskarsa ya gane akwai matsala Babu walwala a tare dashi yace."Ka kira wayar ne."?

Salim ya girgiza kansa da fadin"Wallahi kuwa Na kira ya kai sau bakwai tana katsewa gabadaya hankalina ya tashi da abinda Khalid yayi baba kasan sai da muka sha wuya sosai kafin mu samu adaidaita sahun nan amma kuma Khalid ya dawo da mukkulin babu wani dalili mai k'arfi.''

Kawu Iro ya miqe da fad'in "Salim ka kwantar da hankalinka Khalid dai a yanxu ba za'a kirasa yaro ba yana da hankali yasan abinda yake adaidaita sahu kuma daya dawo maka da ita kansa yayiwa mugunta sai kayi gaggawar mayarwa da mai ita a samu wanda yake bukata a bashi."

Salim yace."Kawu kayi hakuri dan Allah zan jira Khalid din ya dawo daga dik inda ya tafi sai naji dalilin da yasa ya aikata hakan.

Kawu Iro ya girgiza kansa cikin takaici yace."Salim zaka wahalar da kanka domin abokinka yayi nisa saboda yasan rashin kyautawar da yayi sabida haka nake shawartarka da kayi gaggawar mayarwa da mai babur din nan key d'insa."

Salim a sanyaye yace."To shikkenan Kawu insha Allahu gobe zanje na kai masa key din." Kawu ya miqa masa hannu sukayi sallama da juna ya wuce ya barshi a gurin a tsaye yana mamakin maganarsa to wane irin abun kunya abokin nasa ya aikata da har zaiyi nisa da gida." da yaga bashi da mai bashi amsa sai ya juya jiki a mace ya shiga cikin gidan nasu.

A ranar Ummatu qin d'ora tunkunya tayi har wajen tara na dare babu labari Gwaggo ta hau surutai akan lamarin Ina daga kwance nace."Gwaggo dan darajar Allah da Annabi kada ki sake tada wata tarzomar ki rabu da ita tunda ba tayi girkin ba ki dauki taliya ki dafa tunda kina da ragowar miya ni dai bana tsammanin zanci wani abu."

Tace."Haba Sa'ida ai wannan iskanci ne da wulakanci Ibrahim na iya bakin kokarinsa a gidan nan amma matar nan take kokarin tona masa asiri a unguwa yanzu bayan bakin cikin da muke ciki tana so mu kwanta da yunwa kenan."

Nace."Gwaggo ki kyaleta kada ki biye mata kinga rashin kunya take miki ni kuma zuciyata bata dad'i watarana idan ta 'kure ni dole na mayar mata da martani shiyasa bana so kina biye mata kuna fad'a ma'kota na jinku."

Tsaki tayi ta girgiza ta fara kokarin mi'kewa......Fita tayi ta dauko 'yar tukunya ta dawo dakin da fad'in "Ai sai ki kunna min gas din ko." Motsawa nayi na mike zaune ina ya mutsa fuskata, cikin kulawa tace."Yana da kyau dai ki sake shiga cikin ruwan d'umi idan kuma baki daina jin zafi ba gobe sai muje asibiti a dubaki dan na lura yaron nan ya gwada miki mugunta.''

Nace."Gwaggo babu wani asibiti da zanje idan kin sauke kisa min ruwan zafin ya isa." Tace."To ai shikkenan Allah ya kyauta." ciki zuciyata na amsa da ameen tare da kar'bar ashanar hannunta na kunna mata 'karamin gas din ta dora tukunyar akai.

Tana sa taliyar a cikin kunyar Kawu ya daga labulan dakin. tace."Ibrahim ka dawo kaga har yanzu ja'irin yaron nan bai shigo gidan ba."

Yace."Gwaggo bana tsammanin fa Khalid na kusa dan tun dazu ake kiran wayarsa a kashe abokinsa Salim ya tabbatar min da cewa ya mayar masa da mukkulin adaidaita sahun da ya samo masa shin gwaggo duk me ya janyo haka? Khalid yasan bashi da gaskiya shiyasa ya gudu."

Tace."Ka rabu da ja'iri Ibrahim ai duk guje-gujen da zaiyi dole ya dawo gida ya same mu hukunci kuma kada ka fasa yi masa domin ya aikata abinda da ya zama dole a hukunta shi."

Kawu ya kalli inda nake kwance cikin kulawa yace."Sa'ida ya jikin naki ina fata dai babu wata matsala."? Kafin nai magana tace"Tun d'azu take ya mutsa fuska tana tafiya da 'kyar shine nace gobe muje asibiti a dubata ko yayi mata rauni tace ba za'aje ba xata cigaba da shiga ruwan zafi."

Shuru yayi yana me sunkuyar da kansa 'kasa hakika wannan al'amari ya tsaya masa a zuciya....a sanyaye yace."Sa'ida kiyi hakuri aje asibitin a dubaki kada kuma wata matsalar ta afku."

Murya na rawa nace."Kawu ba sai anje asibiti ba insha Allahu babu matsala." Girgiza kansa yayi yace."To shikkenan ai dama haka ake so.....Kokarin fita yake sai ya kuma yatsa yana kallon tukunyar dake kan gas yace."Gwaggo me kuma kike dafawa da dare haka."?

Da sauri na rigata magana da fad'in "Taliya ce nace ta dafa min ina sha'awa." Yace."To na fahimta." sai da safe yayi mana ya fita daga dakin.

Ummatu na 'kuryar dakinta tana sa'kawa da kwancewa ya shiga yana kiranta tana jinsa tayi saurin kwanciya tare da rufe jikinta, rufe idonta tayi kamar mai bacci yazo ya tsaya a kanta yana fad'in "Rabi tashi ki dauko min abinci na dawo da yunwa."

Ta bude ido cikin yanayi na masu bacci tace."Ai sai dai kayi hakuri dan wannan fargabar ita ta hana ni na shiga kicin nayi wani abin arziki nima a haka zan kwana da yunwa."

Rai a 'bace yace."Saboda ke zaki iya kwanciya da yunwa sai ki azabtar da rayuka tun safe da zan fita na baki kudin cefane bayan tsabar abinci da nake dashi a gidana amma saboda wani dalilin ki na banza da wofi kin ki yin girki a gida kina so nida mahaifiyata mu kwana da yunwa kenan."

Zaune ta miqe tana kuka tace."Ibrahim dan Allah ka saurara min haka naji da wannan masifar da take damuna wallahi ina hakuri a gidan nan mahaifiyarka a d'azu babu irin cin mutuncin da ba tayi min ba akan kawai na kare d'ana daga zargin da ake masa ni wallahi har yanzu ban yarda Khalid ne ya aikata abunda kuke zarginsa dashi ba.

Rai a 'bace yace."To idan bashi ne ya aikata ba mai ya hana shi dawowa gida? kuma mai yasa ya kashe wayarsa Rabi wai me yasa kike da son zuciya ne yarinyar nan Sa'ida itama haihuwarta akayi mai yasa kike fifita d'anki a kanta kema uwa ce ya kamata ki dinga adalci a cikin al'amuran ki a zahiri yaro ya aikata abu kuma ya nuna kansa amma sabodo son zuciyarki kice baki yarda ba k'azafi akayi masa."

Komawa tayi ta kwanta tare da juya masa baya alamun duk maganganun da yake basu gamsar da ita ba, Kawu Iro cikin 'bacin rai ya fita daga dakin kai tsaye hanyar fita daga gidan ya nufa ba zai zauna da yunwa akan yaron da bai ji tausayinsa ba.

Gwaggo ta fito daga bandaki da buta a hannunta tace."Ibrahim ina kuma zakaje ai na dauka ka shigo gida sai da safe."

Jim yayi kafin yace."Gwaggo zan fita na nemi abinda zanci ashe wai Rabi bata baku abinci ba."? Tace."Eh ka rabu da ita da halinta kada kaje ko'ina zo muje daki kaci abinci ko baka ga ina dafa taliya ba."

Yace."Na gani Gwaggo.'' tace."To muje daki kaci ka koshi ka shareta da bak'in halin ta.'' Girgiza kansa yayi yabi bayanta d'akin suna maimaita maganar.

Salmanu shuru yayi kawai ya tsirawa abokin nasa ido yana kallonsa. Khalid yace."Salmanu ka tsananta lallai sai na fad'a maka damuwata na fad'a maka kuma ka tsira min ido kana kallona."

Salmanu yace."Khalid dole na kalleka saboda abinda ka aikata yanzu dan Allah ina soyayya take a nan? ashe dama duk irin haukan da kake a kanta sha'awarta kakeyi yanzu kai baka ji kunyar haike mata ba? bayan kullum kana ikiririn so da 'kaunarta me zai sa ba zaka so abinda take so ba."

Gumi ya goge a sanyaye yace."Salmanu hankalina ya gushe tunani na yayi nisa a lokacin dana aikata wannan al'amarin nasan ban kyauta ba amma ina ganin hakan da nayi shine daidai domin ina tsammanin dole su janye maganar auran da zasuyi mata su nemi inda nake."

Salmanu yace."Khalid wannan ba dubara bace komai na rayuwa ana bin sa ne a sannu a hankali ba'a gwaggawa Khalid duk abinda kaga mutum bai samu ba a duniya ba to ba rabonsa bane kai mai yasa baka hakura da qaddara ba kabi son zuciyarka ka aikata abinda zai jefe zuk'atan iyayenka a damuwa kai ma duk da kabi son zuciyarka a yanzu nasan babu wanda ya kai ka nadama gami da damuwa yanzu kasan a wane irin hali na damuwa da bacin rai iyayenka ke ciki a gaskiya ni kam banji dadin wannan abu daya faru ba wallahi kuma ban ta'ba tsammanin zaka iya cutar da aunty Sa'ida ba sabida irin son da kake mata."
Chapter 25 · 0% Book details