Sashe 19
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta ri'ke bakinta cikin mamaki tana kallon Gwaggo tace."GwaggoAshe har yau kina tare da Uwale."?
Da sauri tace." 'Kwarai kuwa ba kuma mai rabani da ita sai mutuwa." Tana gama maganarta tasa takalmanta ta fita ta barmu...Umma tace."Sa'ida ki cigaba da hakuri kinji ko watarana sai labari." Nace."Umma Insha Allah zan cigaba dayi nasan Allah yana kallo."
Ta mi'ka min ledar da fad'in " 'Karbi ki ri'ke mata tunda nayi niyya bazan fasa ba babu ruwanki da wanda zata bawa." ledar na kar'ba da fad'in "To shikkenan." sallama mukayi da ita tace."Lallai idan na fita na shiga d'akunan kishiyoyinta nai musu sallama.
Nace."To insha Allah zan shiga.
bakin gate na same su a tsaye ita da Baba Iro suna jiran fitowa ta ina ta kici-kici da jakar kayana yazo ya kar'bi jakar yana fad'in " Sai kiji da ledojin hannunki." Nace."Haba dai Kawu dan Allah ka ba kawo dik zan iya ri'kewa." Gwaggo tace."Au! ashe kayan naki suna da yawa tunda ga wasu nan a ledoji."
Nace"Aa wannan ledar taki ce su kuma wannan yanzu akayi min kyautarsu amma ni ba dasu nazo ba." hannu ta mik'a ta kar'bi ledar kayanta tayi gaba nabi bayanta ina mamakin 'karfin halinta.
Direba ya kar'bi jakar kayana yasa a bayan mota Gwaggo ta shiga ta zauna Kawu ya zauna kusa da direba ina kokarin shiga........Motarsa ta shigo gidan tsayawa nayi har direbansa yayi parking ya fito a nutse cikakken mutum kamili dogo ba'ki da kyau daidai misali saboda yanayin hutu da jin dadi yasa bakar fatarshi tayi wani freesh sai daukar ido take...... kwata-kwata Yaya Aminu baida izzah irin ta masu kudi dalilin ma da yasa kenan nake 'kara mutunta shi.
Fuska a sake ya 'karaso inda nake yace."Ranki ya dade dama kina nan."? murmushi nayi a nutse nace."Ina nan Yaya Aminu ya kake ya al'amura."? Yana min wani irin duba yace."Alhamdulillah wato dai ba zaki tambaye ni Iyali ba ko."?
Dariya na d'anyi nace."Yaya Aminu kenan to Ya Iyali." Cikin sigar tsokana nayi maganar ya amsa min da "Suna nan lafiya kalau kamar gaske.
Dariya nasa ina kallonsa shima sai yasa dariyar Gwaggo ta le'ko kanta da fad'in " Wannan kuma waye kike ta ya'ke masa baki."
Da Sauri nace."Yaya Aminu ne babban yaron Alhaji." "Au! koda naji." abinda ta fada kenan ta dauke kanta......Motar ya dafa cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa kamar bata so Ya mi'kawa Kawu Ibrahim hannu suka gaisa a mutunce, Ya dawo da hankalinsa kaina da fad'in "Tafiya zakuyi ne."? Nace." Eh wallahi."
Jim! yayi kamar da magana a bakinsa kawai ya basar yasa hannu cikin aljihu sabbin kudi ya dauko ya mi'ko min.
Nace."Dan Allah ka barshi." girgiza kansa yayi yace."Ki kar'ba mana ko katin waya kyasa ko." hannu biyu nasa na kar'ba da fad'in "Nagode Yaya Aminu Allah ya 'kara arziki.
A nutse ya amsa da ameeen to sai gani na biyu ko."? nace" Aikuwa dai tunda kai ganinka ha'bo ne baka zama a gari."
Yace."To ya za'ayi Sa'ida taurari na masu zagaye ne nima ba a san raina nake zurga zurga nan ba.
Nace."Hakane to Allah ya taimaka." Ya amsa da "ameeen tare da daga min hannu da sauri ya wuce cikin gidan......Ina shiga motar ta rufe ni da fad'a " Sa'ida wato kin mai damu marasa galihu ko kinga kudi duk kin gigice kin barmu zaune a mota to bari kiji wallahi komai abunki ba zaki sanjawa towo suna ba."
Uffan bance mata ba ta cigaba da sababi tana fadin" Yana fama da 'bakar fuska yazo ya tsayawa mutane to idan ma sonki yake sai dai yayi hakuri dan ba zaki aureshi ba ehe! ba naji ubansa na wata magana ba Kai Ibrahim kada ka kuskura ka tunkari Alhaji Nura da wata magana Sa'ida bata da miji sai Khalid da yardar Allah."
Nida Kawu Iro shiru mukayi mata uffan ba muce ba ta 'karaci surutan ta ta gaji tayi shuru tana gyangyadi. sai da muka isa gidan na tashe ta ta fito tana mita......Khalida dake can tsallaken gidansu Salim ya karaso gurin, hannunta ya ri'ke suka shiga gidan sai magana take masa 'kasa-'kasa...Yace." To shikkenan Gwaggo magana ta wuce zan fita daga harkarta. har daki ya kaita ya karkade mata shimfidarta ta kwanta tana mita wai kafafunta ciwo suke mata da sauri yace."Bari naje na siyo Roob sai na shafa miki a kafafun.
Yana kokarin fitowa daga dakin ni kuma ina 'kokarin shiga mukayi karo dauke kaina nayi tare da bashi hanyar wuce wa.....ba tare da ya kalleni ba ya fice daga gidan.
Tana mitar ciwon kafafu tana fama da redio sai shuuuuuu! takeyi ta'ki kamawa da alama batir din yayi sanyi, da 'kyar ta yunkura ta mi'ke tsaye da fad'in "Ai dole na fita na siyo batir." Da sauri na kalleta tana kokarin yafa mayafi nace."Gwaggo yau d'aya dai ai sai ki hakura kuma yanzu fa Khalid ya fita mai yasa bakice ya siyo miki batir din ba."
Tace."Sa'ida bana san takurawa Khalid bashi da kud'i shiyasa bance ya siyo min ba." Nace"Idan kika bashi kudinki zai siyo miki ba lallai sai da kud'insa ba.'' Girgiza kanta tayi tace."Bai zama lallai ya kar'ba." Nace." Ki daiyi hakuri da jin redion ki barwa gobe."
"Aa ba zan hakura da jin taskar labarai ba." Hanyar fita ta kama cike da mamaki na bita da kallo maganarta naji a tsakar gida tana fad'in "Eh fita zanyi na siyo batir na redio na yayi sanyi ta'ki kamawa."
Muryar Kawu naji yana fad'in "To koma ki huta bari naje na siyo miki.'' Tace." To yawwa Ibrahim nagode Allah yayi maka albarka."
Dakin ta dawo ta zauna tana dai sake mummurd'a redion sai shuuuuuu take amma taki hakura.
Khalid ya shigo dakin da sallama a bakinsa itace ta amsa masa dan ni ko inuwarsa ma ban kalla ba....ya mika mata batir din da fad'in "Gashi Baba yace a kawo miki." kar'ba tayi ta fara sawa a redion ya zauna kusa da ita tare da mi'kar mata da 'kafafunta a nutse ya bud'e Roob din ya fara shafa mata. addua ta shiga yi masa kafin naji sun fara magana 'kasa-'kasa 'karamin tsaki naja na fita daga d'akin buta na dauka na shiga band'aki ina jin takaicin abinda suke.
"Gwaggo na fad'a miki fa magana ta 'kare zan fita daga harkata amma kuma ba zan daina so da kaunarta ba wannan nasan a jinin jikina yake......Tace." Kuma ka kwantar da hankalinka idan ka koma makaranta kayi karatunka lafiya maganar Alhaji Nura Gaibu ce.
Murmushin takaici yayi yace."Gwaggo qaddara ma Akawai aure a tsakaninsu to ni kuma mutukar ina raye sai na hanata jin dad'in aure wallahi."
Shuru tayi ba tace masa komai ba ya mike da fad'in "Ni zan tafi kallon ball." tace."To dan Allah kada kayi dare." yana kokarin fita daga dakin yace."Da wuri zan shigo gida insha Allahu.
Ri'ke da buta na fito daga band'akin santsin ruwa dana takalmin 'kafata yayi yun'kurin kayar dani salati nasa nayi saurin ri'ke kyauran bandaki dik da haka sai da nayi zaman da'baro a gurin. 'Kuguna ya buge sosai na rintse ido ina kiran sunan Allah.
Gurin ya 'karaso kawai naga ya sunkuya yana kokarin dauka ta....duk yanda naso dana hanashi kasawa nayi saboda naji jiki sosai jikina sai kyarma yake......har bakin kofar dakin ya ajiye ni ba tare da yace min komai ba ya juya ya fita daga gidan.
Jiki a sanyaye na bishi da kallon mamaki!
To washe gari da safe kadaran kadahan muka tashi gaisuwa ce kawai ta had'ani da ita sai da na shirya tafiya makaranta nayi mata magana, tace."Ba zaki tsaya ki karya ba ga ruwan kunu na d'ora a wuta."
Nace."Gwaggo idan na tsaya karyawa zan makara zan samu wani abu naci a ofis." Tace."Ai ke idan ba dan kina da kurman jiki ba to da tuni kin zabge kiyi ta zama da yunwa ko damuwa bakya yi."
Murmushi kawai nayi na gyara jakata dake kafad'a nace"Sai na dawo." tace."Allah ya bada sa'a." na amsa da "ameeen." Ina kokarin fita yana kokarin shigowa dakin baya na koma na bashi hanya ina d'an satar kallonsa yana sanye da 'kananun kaya ya goya jaka a bayansa kafarsa sanye da boot ya taje tarin sumar kansa sai kamshin turare mai sanyi yake.....babu walwala a fuskarsa yace."Auntyna barka da asuba." Ba tare dana kalleshi ba nace."Barka kadai ka tashi lafiya."? a tsanake ya amsa yana kallona da fad'in "Zan koma skull yau." nace."Allah ya bada sa'a." da sauri na fice daga dakin dan bana son wata duguwar magana a tsakaninmu.
Gwaggo kamar za tayi kuka haka sukayi sallama ta rakashi har soro tana ta zabga masa addua.....a daidaita sahun Salim ya shiga yana daga mata hannu shima yasan zaiyi kewar kakar tasa sosai ya sha'ku da ita akan mahaifiyarsa.
*BAYAN KWANA BIYU*
gidan ya samu nutsuwa domin a washe garin ranar dana koma gidan Ummatu ta dawo da daddare babu laifi dai zaman da akeyi a gidan tsakaninta da Gwaggo gaisuwa ce dan har yanzu ta kasa sakewa a gidan ni kuwa kullum idan mun had'u na gaisheta bata amsawa hakan bayayi min ciwo saboda dama tuntuni na riga na saba.....sosai naji dad'in tafiyar Khalid domin na sake a gidan ina abubuwan da raina yake so kai tsaye zanyi daurin kirji na fito tsakar gida ba tare da fargabar wani abu zai faru ba..Gwaggo kuwa ta hakura da turara haya'kin tunda na gargad'e ta a gidan Ummana ta kiyaye muna zaune lafiya yanzu sai dai amma kullum cikin zagin Alhaji Nura take tana kwashe masa albarka idan kuma yayi min ake tare da ita muke cinyewa.
To koda Kawu Iro ya samu Alhaji Nura da maganar sai ya nuna farin cikinsa sosai yace dama shima abinda yake ta sauraro kenan saboda haka tunda lamari ya kasance a haka zai turo da kudin sadaki i dan yaso in ya dawo daga tafiya sai ayi hidimar biki."
Kawu Iro yace."Hakan yayi insha Allahu kuma zamu saurari zuwan wakilan ka." Cikin mutunci suka rabu da juna Kawu Iro ya kira wayar Alhaji Shamsu ya sheda masa duk yanda sukayi dashi.....sosai yaji dadin hakan kuma yayi fatan alkairi tare da jimirin jiran zuwan wakilan nasa.