← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 90

Sashe 87

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Girgiza kaina nayi a murtuke nace."Babu rashin ci babu rashin sha a gidanka sai dai akwai rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.'' Ya kalleni da jajayen idonsa yace." Ko zaki fada min abinda ya janyo miki rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin."?

"Wannan kuma kai za'a tambaya namiji shike kawo nutsuwa da zaman lafiya a gidansa idan yaso idan kuma beso ba zai iya kawo akasin haka."

Tsaki yaja da karfi yace."Tun sanda kika fahimci cewa Jamila nada juna biyu kike fushi da b'acin rai shin waye yake bada haihuwa idan ba Allah ba me yasa Zaki sanya kanki a cikin damuwa saboda kawai kishiyarki nada ciki ke baki dashi gashi kin janyo jamaa nayi min wani irin kallo.

Cike da takaici da bacin rai nace." Khalid cikin matarka baya gabana ballanatana na damu dashi haihuwa da rashinta duk Allah ne yake yi saboda haka idan ma tunanin da kake kenan to ka daina domun ni nayi imani da Allah da manzonsa."

Yace."Idan kinyi Imani da Allah da Manzonsa kuma kin dauki Jamila a matsayin 'Yar uwarki me yasa har yanzu baki saki jiki da ita ba? me yasa kullum kike cikin damuwa da 'bacin rai."

Girgiza kaina kawai nayi na mike da niyyar bar masa gurin.....Ya tare ni da gangar jikinsa kallonsa nayi da fadin."Bani hanya na wuce.'' Yace."Wato kin mayar dani mahaukaci kenan." dauke kaina nayi yasa hannu ya juyo da fuskata ina kallonsa......"Kada ki sake zuwa ki kai 'kara ta gurin Tsohuwa bana bukatar 'bacin ranta." fuskata na fuzge da fadin." Dallah malami matsa ka bani guri kullum kana 'kara girma da shekaru amma ka'ki kayi hankali."

Baki ya bud'e yana kallona na buge kirjinsa da ya tare ni dashi bedroom d'ina na bude na shiga na kwanta kan gado bakin cikin duniya ya isheni.
Tunda ranar ya dauke min wuta ya daina kula ni ko shigowa sashen yayi baya shiga sabgata zaiyi abinda ya zaiyi ya fita gabadaya ya tare a gurin Jamila ya ma daina kwana a gurina hakan yayi min dadi sosai dama takura min yake gashi ba cikakkiyar lafiya gare ni ba.

Sati guda da faruwar al'amarin Jamila ta tashi da ciwon mara mai tsananin gaske kafin ma suyi wani yunkuri jini ya yanke mata hankali a tashe suka nufi asibiti suna zuwa cikin ya fita sosai tasha wuya kuma ta zubar da jini mai yawa........Baito ta dinga kuka saboda rashin tawakali sai suka d'orawa Uwale sharri suka ce ai gyad'ar data kawo ce tayi sanadiyar zubar da cikin wai had'a baki sukayi da Gwaggo tunda 'kawarta ce......Shima khalid din da yake bashi da tsinkaye sai ya yarda da maganarsu ya dinga cika yana batsewa da fadin." Sai yayi sharia da ita.......Gwaggo tare da Uwale suka je asibitin domin duba Jamilan Baito da sauran 'ya'yanta suka dinga sakin habaici dan wata mara kunya ma a cikinsu har sai da ta zagi Uwale da fadin." Duk sharrin da suka k'ulla cikin ya zube sai Allah ya tona musu asiri.....Uwale ta dinga share hawaye tana fadin." Ni kuwa me Jamila za tayi min da zan bata guba a cikin gyada." Gwaggo ranta a bace ta kalli Baito da fadin." Wallahi ku dai 'kananun mutane ne marasa tawakalli masu yarda da jita-jita kawai." Baito tace."Asiri dai ya tonu baku da bakin magana."

Rai a 'bace suka bar asibitin.....Bayan sun koma gida da daddare Khalid yaje gidan yana tashin hankali wai wallahi Sai ya daure Uwale tunda ta bawa matarsa gubar da tasa cikinsa ya zube .

Tashin hankali yasa Gwaggo ta fad'i hawan jininta ne ya tashi, hankali a tashe suka nufi asibiti ganin halin da Gwaggon nashi take ciki yasa jikinsa yayi mugun sanyi.

Ni kam in banda share hawaye babu abunda nake masifar yau daban ta gobe daban gashinan garin rashin hakurinsa matsala ta afku gabad'ayanmu hankalinmu bai kwanta ba sai da aka sallami gwaggo daga asibiti.......Kawu ya dinga yi masa fad'a da fadin." Mutukar 'bacin ransa ya kashe masa mahaifiyarsa sai ya hukuntashi. Khalid dai hakuri kawai yake bashi yana fadin." Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.

****
Hajiya Aziza a gurin harkar lesbian ta hadu da wata mata mai suna Elizabeth suka kulla abota ashe 'yar mafiya ce bata sani ba ta saki jikinta da ita sosai suke sha'aninsu matar na sakar mata kudi sosai Hajiya Aziza ta dinga cin duniya da tsinke tana jin dadin duniya..........Rana tsaka k'ungiyarsu ta mafiya ta 'bukaci da Elizabeth ta bada mutum dodon tsafinsu na bukata ba tare da tunanin komai ba ta mika musu Hajiya Aziza a daran ranar dodon tsafin ya shanye mata jini tas Aka wayi gari da gawar ta, Elizabeth ta dinga kuka tana kiran Jesus 'Yan uwanta arna suka taimaka mata gurin had'a gawar ba tare da sun sallace ta ba suka sa a akwati sukaje suka binne suna wa'ke-wa'ke.......
*Duniya kenan Allah kasa mu gama lafiya*
Chapter 87 · 0% Book details