← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 90

Sashe 88

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**** Aunty Murja bata sare da al'amarin duniya ba sai da ta samu labarin irin mutuwar da Aziza tayi ta dinga kuka tana nadamar rayuwa tunda tsohon mijinta ya mutu ta zama saliha ta kasance kullum cikin addua da nema afuwa gurin Ubangiji babban burinta ta daidaita da 'ya'yanta domin ta gane sune farin cikinta yayin da su kuma yaran suke masifar nadama fitowa ta tsatsonta suna jin bakin ciki a nuna ta a matsayin mahaifiyarsu...... *105* Bayan sati uku Al'amura sun d'anyi sauki Ya rage wulakanci dalilin rashin lafiyar Gwaggo ya sanya kullum burinshi bai wuce mu samu zaman lafiya ba ni kuma a lokacin ne nake jin mugun haushinsa tunda na fahimci ina da ciki shikkenan na tsane shi duk sanda ya kusance ni sai munyi rigima na tsani kamshin turaransa gashi ya'ki ya daina amfani dashi duk da na fada masa cewar bana so amma kamar kara tunzura shi nake......B'angaran sa kuwa shi sam be san tana da ciki ba tunda bata fada masa ba kawai dai yaji gabad'aya ta sauya masa ni'imar ta tafi ta da yana masifar jin dad'inta duk sanda yake gurin Jamila ya dinga bacin rai kenan sai yayi ta neman ta da rigima idan ta biye masa sukayi fad'a sai ta kulle masa kofa wanda dama shi hakan yake so sai kawai ya tafi gurin auntyn nashi ya dameta da fitina Khalid sam baya gajiya da sex kullum kamar kara masa karfi da kuzari ake..............Yau Yini nayi ina bacci sai bayan la'asar na tashi nai wanka da salolina doguwar riga mai hula nasa kai tsaye kicin na nufa domin samawa cikina abinci, daidai cikina nayi tunda bani ke da girki ba a kicin din na zauna naci na rage wanda zanci da daddare, falon na fito na zauna ina duba waya ta text messages dinshi na gani yana tambayata gida wai ya kasa aikata komai sai tunani na. 'Karamin tsaki naja ina mamakinsa tunda mukayi aure bai ta'ba fad'a min kalmar so ba sai yau da alama akwai abinda yake bukata aikuwa yau da rigima kenan domin ba zan lamunci shiga hakkin wani ba......Kafin magariba ya dawo gidan a maimakon ya wuce gurin mai girki sai ganinsa nayi ya shigo ido jawur sai kace wani bugagge. babu fuska nayi masa sannu ya zauna kusa dani yana ya mutse fuskarsa, Jin zuciyata tana tashi yasa na mike da sauri na bar gurin. dakin ya biyo ni rai a bace yace."Wai meya sa kike min hakane." ? Ba tare dana kalleshi ba nace."Bana son warin turaranka." Babu sukuni yace." Wannan ba hujja bace me yasa tunda nake amfani da turarena baki ta'ba gudu na ba sai yanzu." Shuru nayi masa Ya matso jikina da fadin ." Tunda na fita nake tunaninki gabadaya na kasa aikata komai kinzo kin tsaya min a raina." Kallonsa nayi da fad'in." Ina fatan baka mance cewa ba girki na bane.'' Yace." Ina sane auntyna ke kadai nake bukata Wallahi manège kawai nake da Jamila bata gamsar da ni." Nace."Hakanan za kayi hakuri kaje gurinta." hannuna ya rike murya na rawa yace."Ba zata iya ba wallahi kece zaki iya ki taimaka min." Nace." To jeka tambayeta idan ta amince sai kazo." Shuru yayi yana kallona nace." Ko tsoronta kake.'' Murmushin takaici yayi yace." Ni nafi karfin naji tsoron macan dake karkashina kema ba karfi na kikafi ba kawai ina lallaba'ki ne.'' Nace."Okey to kaje kawai." Mikewa yayi ya fita minti biyar da fitarsa naje na kulle kofar palon na shige daki nai kwanciyata.............Jamila tana zauna a falon ta ya shigo dauke kanta tayi tana kumbura fuska shima bai kula ta ba ya bude dakinsa ya shiga ya watsa ruwa ya shirya jikinsa ya fito massalaci ya nufa sai bayan isha'i ya dawo gidan. Gurin cin abinci ya nufa yaga babu komai akai falon ya sameta tana kallo yace."Ke baki abinci bane."? A kumbure tace." Nayi daidai cikina na cinye." Yace."Saboda me."? Cikin tsiwa tace." Saboda bana bukatar kaci kaje gurin matar so ta baka." Ransa a bace yace."Ke zanci ubanki wallahi ni kike d'agawa murya." Sai ta fashe da kuka tana nuna kirjinta take fadin." Yaya Khalid ni kake zagi."? Yace." Ko zaki rama ne."? Tana share hawaye tace."Duk dai wanda ya zagi uban wani nasa ya zaga." Wani bahagon mari ya kwad'a mata yana huci! yace." Tuntuni na gaji da zama dake domin Baki da wani amfani a gurina saboda haka ki tashi ki fitar min a gida bana bukatarki tunda baki da mutunci." Gabanta na faduwa tana kuka take bashi hakuri rufe idonsa yayi yaki sauraranta yace maza ta tashi ta fitar masa daga gida sai ya neme ta. Jamila na kuka wurjajan ta hada kayanta cikin akwati ta yafa mayafi ta nufi gidansu cikin tsananin tashin hankali.......Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta ya kulle sashen kai tsaye gurin auntyn nasa ya nufa. Ya jima a tsaye a kofar falon yana bugu da dai yaga bata da niyyar bude masa kofar sai ya yanke shawarar kiran wayarta nan yaji wayar a kashe takaici kamar ya kashe shi ransa a masifar bace yaje ya lalobo spire key yazo yana kokarin bude kofar falon yafi awa guda kafin ya samu wanda ya bude kofar shiga yayi ya mayar da kofar ya rufe.........Kai tsaye bedroom dinta ya nufa ya tura kofar ya shiga tana kwance tana bacci sadidan, gadon ya haye ya janyota jikinsa ya fara abinda yake muradi....Cikin wani irin yanayi na tureshi daga jikina zaune na mi'ke na kunna bedlamp dakin yayi haske, tsira masa ido nayi ina kallonsa zuciyata na wani irin tashi, jikinsa na kyarma yasa hannu zai janyo ni na janye ina watsa masa harara. a sarqe yace." Kince na tambayi Jamila idan ta amince to na tambaye ta ta amince min da biyan bukatata." Nace." Ban yarda ba." Zaune ya mike da fadin."Kada fa ki sanya na gwada miki karfina ba zakiji dadi ba." Mikewa nayi na shiga toilet nai uziri na na fito na kwanta kan Sofa na barshi zaune a gadon yana bina da kallo! Cikin kunar zuciya ya sauko daga gadon ya isa inda take. "Kina so na mutu ko? ki duba kiga yanda hallitata ta fito." kallon inda yake nuna min nayi na d'auke kaina da fadin." Bari na kira yarinyar a waya naji daga bakinta." da sauri yace."Baki isa ba." Nace." Ai dama nasan karya kake kana satar kwana kana kawo min saboda rashin tsoron Allah.'' " Kada ki sake k'aryata ni." yafadi maganar a kufule. Nace." To idan kana da gaskiya ka bari a kira ta a tambaye ta mana." Tsugunawa yayi a gabana a sanyaye yace." Ko kin kirata ba zata saurareki ba saboda tana cikin fushi." Nace."Khalid wallahi kaji tsoron Allah kana azabtar da iyalinka kana kuma dorawa kanka nauyin zunubi." Ya jima yana kallona kafin yace."Wace irin azaba nake muku? kuna so na kwanta a kasa ku takani kenan.''? Girgiza kaina kawai nayi Yace."To mu bar wannan maganar muyi wacce zata taimaka mana." Nace "Kasan Allah yau kome za kayi ba zaka samu abinda kake so ba bani ma da lafiya ta kaina nake." A marairaice yace."Don Allah ki bari nayi ko Allah zai sanya ki samu ciki wallahi haihuwa nake so." Kallonsa nayi ya wani langwab'e kai sai lumshe idanuwansa yake. " Kayi hakuri ka bari sai girki yazo hannu tukkuna." Wani irin kallo yake min fuskarsa ta rikid'e da bacin rai yace."Saboda kinga ina sonki kike wulakanta ni." ? Kokarin bar masa gurin nake ya rike min hannu "Ba zan kara tunkarar ki da wata bukata ba." cikin zuciyata nace." Dama haka nake so." Hannuna ya saki yaje ya kwanta kan bed komawa nayi kan Kujarar na kwanta ina sauke ajiyar zuciya sosai naji dadin yanda yayi zuciya dama haka nake so ya kyaleni na huta.......Washe gari da safe babu yabo babu fallasa muka gaisa cikin rashin kuzari ya zauna yayi breakfast, yana shiga wanka kira wayarsa dake samar mirror, Ina dubawa naga sunan Ummatu. ajiye wayar nayi yana fitowa na fad'a masa, daukar wayar yayi ya zauna kusa dani..............."Rai a b'ace naji maganarta "Khalid ni zaka tozarta ko? me Jamila tayi maka kace ta fice maka daga gida."? Yace." Ummatu ki kwantar da hankali yanzu zan shigo na sheda miki dukkanin abinda yake faruwa." Tana kuka tace."Aa ai zuwanka bashi da amfani tunda ban isa na baka umarni ka dauka ba kana so ka tozarta ni ko to shikkenan kaje duniya ce." Kafin yace wani abu ta kashe wayarta. Shuru yayi da wayar a hannunsa nace."Me tayi maka da zaka kore ta a gidanka." ? Hannu ya daga min da fadin." Ba abinda ya shafe ki bane." Nace."Ya shafe ni tunda ya shafe ka." Tsaki yaja ya mike ya nufi wardrobe kayansa ya dauko yasa yana d'acin rai Nace."Don Allah duk abinda tayi maka kayi hakuri ka dawo da ita dakinta ina amfanin hakan idan laifi tayi maka bata wannan sigar zaka hukuntata ba tunda kaga 'yar uwarka ce.'' Uffan bece min ba ya kwashi wayoyinsa da key na mota ya bude kofa ya fita ya barni da mamaki...........Baito har kofar Gwaggo ta shiga ta dinga zazzaga masifa Gwaggo tace."Baito ni dik abinda yake faruwa bani da labari amma kuyi hakuri dukkaninmu mu jira zuwansa domin muji laifin da tayi masa. Baito tace."Bayan daukar kwanan da yake yana kaiwa Jikarki duk hakan be isheshi ba sai da ya koreta to wallahi daku da malamin dake muku aiki sai munyi maganinku." Gwaggo tace."Baito kece kika yarda da shirka da surkulle ni Allah kadai na gazgata saboda haka dik abinda zakuyi kuje kuyi." Baito na numfarfashi ta fita daga gurin...Ita kuwa Gwaggo hawaye kawai take sharewa tana jin bakin ciki da takaicin abinda yaron yayi.........Kwata-kwata Ummatu kin sauraran uzirinsa tayi ta rufe shi da fad'a Baito tana taya ta Jamila tazo ta fada musu karya da Gaskiya sun yarda da maganarta sosai al'amarin yayi masa ciwo ya kuma kudiri aniyar sakin yarinyar tunda ta zame masa annoba....Koda ya shiga gurin Gwaggo ma rufe shi tayi da fada tace."Wannan ai shashanci ne saboda kawai kun samu sa'bani da yarinya sai ka koreta wannan ba hukunci bane." Yace."Gwaggo yarinyar nan fa rashin kunya take min sam bata ganin girmana Sa'ida da take da shekaru sama da
Chapter 88 · 0% Book details