← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 89

Sashe 9

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Aamna ta dawo gaba Daya kayan da taje asibiti da su har na jikinta ta cire ta wanke fes tayi wanka dama a koshe take,Zama tayi a gefen Mama,Lokacin Baba ya fito daga daki yace yanzu Zuhra tana can a dakin mijinta tana zamanta lfy Abinta,abin kunya Yaya Guda Bata da ko saurayi ko me Gadi babu Wanda ke zuwa zance,Mama Tace an Rubuta Hatimin Annabi Yusufa har an gaji Shuru kake ji sai Neman kudi,Iskanci ne Kawai da samun waje shi yasa Taki fitar da mijin,laifinta ne cewar Mama Kuma kudinki kwandala mun daina karba kije da abinki,Aamna tayi Shuru har Suka Gama ta Mike tayi waje zuwa Kofar gida a kasa ta samu ta zauna dirshan tare da kurma Ihu iya karfinta tana wayyooooo.....Allah.....na shiga Uku na lalace.....Ina samari suke ko Dattawa ku fito ku Aure Ni,Dan Allah gani sadaka ga me bukata,,Ko me tallan rake ko Shoe shiner ko me Gadi,me Mata uku ma yazo Zan Shiga a ta hudu.

Wasu ma tunaninsu tabin kwakwalwa ne ya kamata,sai Dariya akeyi Amma Aamna ko a jikinta,sai da taji Rana ta ishe ta sannan ta koma gida,tana Shiga Baba ya rike ta ram tare da zaro katuwar Sanda ya samu Aamna Kamar Allah ya Aiko shi ya shiga jibgarta kamar zai kashe ta,Mama tana Kara Mata Yar Iska mu Zaki kunyata a Unguwa,Ihu Aamna takeyi ga Yan hayar gidan ba kowa,Karshe ta tashi da kyar ba Mayafi jikinta duk kulun Sanda ne ko Ina da gudu tayi waje tana ihu,Baba baya gudun Abin kunya Kawai ya bita a million Suka zuba tsere layinsu rigarsa tana tashi Kamar mahaukaci Ana ta kallon ikon Allah,har saman Titi suna falfala gudu Baba Yana na koreki a gidana karki dawo daga Nan kiyi gaba,Aamna tana gudun masifa tana cewa wallahi sai na dawo me yasa aka haife ni,Ni Nace ku haife Ni Ina ruwana,Suna Haka zugar machininan su Ahmad Suka taho gaba Daya Suma sun kure wuta,Ganin Baba da Aamna suna falla gudu,Dariya ta kwacewa su Mashkoor, a wajen Suka ci birki,Ahmad ne ya bi Aamna da machine tare da sa hannunsa me laushi ya cafko Hannunta da karfi ya daga ta Kamar ya dauki tsinke ya cilla ta a bayan machine ta zauna daram,tana Jin dadi har da godiya Amma sai taga Ahmad yayi reverse ya juya da ita wajen Baba,Ta saki Ihu shi kuwa Baba zuciyarsa Dake tafarfasa yace Alhmdllh ya tsaya cak,a gabansa Ahmad ya Zana wani shegen kwabo da machine yaci birki sannan Aamna ta dire zata gudu Ahmad da shishigi ya samu ya yarfawa Aamna Mari ji kake gauuuu.....Nan take fuskarta ta kumbura ta zube a wajen kuwa,Baba yace na gode Dan Albarka,Ahmad ya kalli Baba da tsageranci yace Gata Nan Yi Mata dukan tsiya Ina Nan ba inda zata je,ko Kuma Ni yanzu nayi maka maganinta,Baba ya saki Baki yace Kai Malam Taya zaka marar min yata, Mace Budurwa ka mareta kalli yanda ka kumbura Mata Fuska,baka da hankali ne? Wata Mahaukaciyar Tsawa Ahmad ya yiwa Ba ba,Hey....tsoho,da sauri Baba ya rufe Baki jikinsa na mazari.

Da yatsa Ahmad ya nuna Baba yace Kai tsoho baka Sanni ba Zan sa yarana su babbalaka,Baba yayi Mukus,Su Mashkoor suka saki Ihu da sowa,Kallon Aamna Ahmad yayi tana kuka,Tsawa ya buga Mata Dan Uwarki Ina Mayafinki? Irinku ne kuke sawa Ana yiwa Yara fyade a kasar nan,Dan uban Babanki Ina Mayafinki eyeeee yayi kanta da hargowa,Aamna ta Mike tsaye tana kuka Tace baka Gane Ni bane nice fa wacce nayi jinyar mahaifiyarka,wani dariyar hauka yayi yace ke dalla Ware so what Dan kinyi jinya,kyauta kikayi? Bar Nan wajen ko yanzu na Tara Miki gajiya,Aamna Tace wallahi sai dai mu Tarawa juna gajiya,Kai Malam Nifa ba ruwana muyi kokawa ba komai bane,baka Isa kaci min mutunci da Mahaifi na ba,sai mu Buda Nima fa Yar Tasha ce,tashancin Nan na Iya shi ta Furta tana dukan kirjinta,Tace baka San har yankan Aljihu nayi ba a kasuwa,su Mashkoor suka hangame Baki,Suka ga Kuma Ahmad Bai sa sun Mata duka ba,Jibson da Maganar Yan kwaya yace King kana fa jinta kana kallonta ka bamu Dama mu sassarata.

Mutane tunda suka ga su Ahmad babu Wanda yayi gigin zuwa kallo Dan sun San halinsu,Baba ne ya cire Rigarsa daga shi sai wando dogo da Singlet ya mikawa Aamna yace lulluba mu tafi gida,Aamna Tace Ni a Haka Zan koma ba Kaine ka kwance min zani a kasuwa ba,ka biyo Ni Muna ta tsere Ana kallo duk da dama ai mun Saba,Baba zuciyarka bata da control Wai? Baba yace ai kece Aamna Yar Iska ce,kiyi aure kinki Ni fa duk na washe ki ma wallahi,shekara ashirin da Hudu zuwa da biyar ba ko saurayi,25yrs shine girma tsoho? Mashkoor ya tambaya,Baba yace ae ,to Jibson Yana tangadi yace to ke kiyi auren Mana,Aamna sai da tayi Dariya yanda ya fada da muryar maye,Baba yace ai Bata iya magana ba,Bata waye ba,kwana Nan Muka dawo birni,shekarar mu hudu kenan a birni,sai cin mutuncin samari takeyi na rasa yanda zanyi da ita tafi karfi na,Ahmad yayi Murmushi tare da da shafa gemunsa Yana wani rangaji ya furta Tsoho Bari na kaji idan tayi laifi Kawai ka kirani ka fada min har gida zanzo na kera maka ita,Baba yace na gode Dama ta ishe ni,ta gagareni,Aamna mamaki ya kamata,Tsawar data razana ta taji ance yafa rigar tsoho,jiki na Bari ta karba tare da yin Mayafi da ita,Tace wallahi sai na Rama Nima na iya tashancin,Baba yace kuce Mata ta taho mu tafi gida,da yatsa Ahmad ya nuna Mata Hanya ta juya salin alin tabi Baba suka tafi.

Su Aamna suna tafiya wata Budurwa ta taho da gudu wajen Ahmad Tace Dan Allah kaga wani can Haka Kawai ya dameni da naci sai Maganar Batsa yake min nace bana sonsa yaki hakura Wai sai na bashi kaina ko yayi min fyade Dan yaga Kawai Ina tallan gyada tunaninsa Yar Iska ce Ni ta karasa da kuka,Ahmad Fuska a Murtuke yace Yana Ina guy din? Da yatsa ta nuna musu,Ahmad yace Boys kuje ku min maganinsa,ai kuwa Suka tafi Kamar an Aiko su Suka hau jibgarsa,sai da suka Masa ligi ligi sannan Ahmad ya karasa wajen tare da yarinyar,yace Kai Dan uwarka wannan kake so?Kai Dan Iska ne?zaka lalata Yar wasu Tace Bata sonka dole ne? Matashi Yana Nishi jikinsa duk jini Ahmad yace daga yau idan kaga wannan yarinyar hanyar da take idan kabi wallahi sai na yankaka,Matashin yace bazan sake ba,Zan gyara halayena,ayi Hakuri Oga,Ahmad ya Shure shi da kafa yace bace a Nan,ya tashi ya fece da gudu,Yace wa Yarinyar ki dinga saka Hijab idan Zaki talla,Tace to na gode yanlabai,ki daina talla ki Shiga makaranta ko kiyi aure,Tace to ai an kusa biki na Kuma Ina Islamuyya yace Good Ware ke ban son surutu,da sauri ta tafi tana murna.

Tafiya sukayi sunyi nisa Suka samu wani yaro ya fisge Wayar wani a Hanya,Ashe Ahmad yaga abinda Yaron yayi ya arce,Sai da ya Bari Yaron yasha kwana sannan yabi bayansa,ya sauka a machine ya cafke Yaron a nutse ya dinga kashe Yaron da Mari yafi a irga tun Yana gani sai da Yaron ya sume,Wayar da Yaron ya fisge Ahmad ya karba tare da kwarawa Yaron ruwa ya farfado yace Kai barawo ko Nan take ya Kira police Suka Yi gaba da Yaron shi Kuma ya maidawa Babban mutumin da aka satar Masa,mutumin ya dinga godiya,yace yaro daga an kirani na dakko waya Kawai naji ya fisge,Ahmad Bai kulashi ba ya wuce gidansa Kawai su Mashkoor suka rufa Masa baya.

Tunda suke tafiya Aamna kuka takeyi jikinta duk rauni,Baba yace kece dai kika jawo Kuma kin San Halina wallahi Sai in Miki jina jina,Aamna taci gaba da kukanta tana tafiya,Baba yace Jeki ki Siyo kayan Miya da Salat ki Shiga da shi gida,Aamna Tace bani kudin tana kuka,yace a aljihunki Ni Ina da kudi ne an fada Miki,Nima yau bazan ciyar da kowa ba wallahi tunda aka Dake Ni ta furta tana shesheka,Zan tsine Miki wallahi Aamna Naga kin rainani,Aamna tayi banza da mahaifinta,kwafa Yaja ya juya ya tafiyarsa inda zai je yace yunwa ta kashe ku, Zaki sani Zan dawo gidan ne,Aamna tayi tafiyarta da rigarta a kanta har Gaban me kayan miyar kusa da gidansu tana goge Hawaye tana sheshekar kuka Tace Dan...tala....Dantala... ba....bani kayan Miya na dari hudu.....Salat na na ... Naira dariiiiiiiiiiiii......sai ta karasa da sakin Kuka me karfi a Gaban Dantala,Dantala ya saba da halin Aamna yasan Kuma yanda dama suke fada da Babanta,Yace kiyi Hakuri,ita rayuwa ko da wa zaka zauna sai kayi Hakuri Aamna,da girmanki da shekarunki haba Haba,Aamna ta sake fashewa da kuka Tace Wal....wallahi....wallahi tallahi yau bazan ci abinci ba da yunwa Zan kwana,Kuma na rantse bazan Taya Mama Aiki ba,Dantala Ina da zuciya,Kawai duk an bi an tsaneni akan ban samu Miji ba,a kauyen mu kowa sai ya fada min bakar magana bana Iya Shiga cikin dangi na sakata na Wala,Haka a gida ace Iyaye sun tsaneka,Dantala yayi Dariya yace sai hakuri Aamna,Tace wallahi Watarana za a ga na mutu a tsinci gawata Kawai,kiyi Hakuri cewar Dan tala ya zuba Mata kayan Miya ta bashi kudin ta tafi gida.
Chapter 9 · 0% Book details