Sashe 6
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu irin lallabawa da lallashin Aamna da Iyayenta Basu Yi ba Amma Taki cin abinci ko ruwa Bata Sha ba,Baba ya kalle ta yace Ki shirya Aamna gobe zamu je Kauye gaishe da Yan Uwana da abokan arzuka,Aamna Tace Amma ba a fada min da wuri ba na shirya,shike Nan Allah ya kaimu goben Amma kafin mu tafi Zan sanarwa ogar mu sabo da gudun matsala,Ba damuwa Aamna cewar Mama.
Aamna kwana tayi Bata ci komai ba duk da cewar taci a Restaurant dinsu,Washe gari da wuri ta nufi gidan su Saratu kawarta,Saratu tana bacci har Aamna ta Shiga aka Mata Sallama da Maman Saratu ta Mata bayani zasu Yi tafiya,Hajiya Tace Baki da matsala Aamna Amma kin San dai Baki da kudin fashin da zakiyi,a cikin Albashinki za a cire na Iya kwanakin da kika Yi bakya zuwa Aiki tunda kin San ba aikin Gomnati bane,Gomnati ce ake cin banza Ni Kuma ba Gomnati bace,Aamna Tace ba damuwa Amma,Hajiya Tace a dawo lfy ta Mike tare da haurawa sama,itama Aamna ta Mike ta tafi,dama sun Gama shiri Kaya Kawai ta canja wani lace ja me adon Golden, me Dan kyau Riga da skert,Ta sa takalminta na Sallah da jaka duka Golden,Zuhra Kawai aka Bari a gida sabo da makaranta suna Exam,Napep muka shiga zuwa Tasha daga can Muka hau Motar Sokoto tana ta Adduointa, sun Dade suna tafiya Amma sai kusan dare muka Isa can kauyen Su Baba da Maman su,Asalin gidan Iyayen Baba muka sauka a bangaren Baba,Dakuna biyu da toilet ne na Bulon Siminti Wanda Baba ne ya Gina ya sumulmule ko Ina da Siminti idan sunje can suke sharewa su zauna a gadon uban su,Ko wanne daki akwai Ledar tsakar daki da katifa katuwa da Bedsheet,sai kwanikan cin Abinci da Tukwane har da Reshio dinsu,komai na bukata akwai dai dai talaka,Mutanen gidan Suka tarbe su dake Babban gida ne a bangaren Kanin Baba wato Kawu Ismail muka sauka.
Sai da suka ci abinci suka huta sannan suka gyara bangaren Baba ita da Mama, Bedsheet din Yana wanke a cikin kayansu suka shimfida abin su,a saman Katifun dakunan Guda biyu,wanka suka Yi tare da Yin Sallar Isha,Baba suna Kofar gida shi da Kaninsa da sauran dangi,suma dakinsu Mata ne Yan Uwa aka taru suna hira sai ga Baba da Kawu Ismail,ba tare da Bata lokaci ba Baba yace ke Aamna taso muje Ina Maman taku ta taso mu tafi muyi abinda ya kawo mu ba dadewa zamuyi ba,Hijab me Hannu Aamna ta Daura saman Riga da skert Dinta na jar Atamfa,Mama kuwa Mayafi ta yafa tare da Fitowa zasu tafi,Baba ya kalli Mama yace wannan tayani gantalin Wato baza ki daina yafawa ba ko? Har yanzu fa da sauranki Baki Gama Expire ba,Dariya Aamna tayi tare da sadda kanta kasa sabo da fadan Baba da Mama ya rigada yabi jininsu,Mama Tace Kai ka sani dai,Baba yace ya kamata ki daina Narka kibar Nan ke ba Wani abinci kike samu me Gina jiki ba Amma kullum Hawa kike kamar ana buga Miki Iska,Mama Tace sai ka fara rage taka kibar tukun,Haka suka tafi Suna ta cacar baki,Kawu Ismail kuwa fada yake ta yiwa Aamna lallai ta fitar da Mijin Aure,yace abokan haihuwarki daga me Yara hudu sai me Yara biyar a Nan kauyen,ita Aamna Bata taba sanin Mama da Baba Basu Suka haife ta ba,tasan dai suna Dan nuna Mata banbanci tsakaninta da Zuhra,Haka Dangin Baba tasan Suma sunfi son Zuhra,Haka ma Dangin Mama,Sai wani gida da ake kaita tun tana karama a cikin Sokoto city wani me kyau gidan mutanen Sudan ance Wai Yan uwane suma
Gidan wani mutum suka je Malam me Almajirai,Bayan sun zauna Aamna sai ji tayi Baba suna ta Masa bayani akan bata samu Mijin Aure ba,Kuma ko zancen Aure akayi Aamna Bata kauna,Malamin Yana tauna goro yace Ashsha Aljan ne namijin dare ne wallahi take fama da shi,Mama Tace biri yayi Kama da mutum,Baki Aamna ta Bude tana kallon Iyayen Nata,Malamin yace yanzu Zan kwana Uku ba bacci Ina wani Aiki Amma dole aikin Nan kullum sai an yanka zakara Guda Uku har na kwana Uku,Baba duk talaucinsa sai yace dama na samu wasu kudi Nan take ya biya kudin zakaru tare da bawa malamin dubu goma kudin Aiki,yace Nan da kwana Uku ku dawo ku karbi wata laya wacce zata soke ta a cikin gashinta,Fuska Aamna ta Bata kamar zata saka kuka,Ace Allah Bai kawo lokacin Abu ba Amma Iyayen nata basa gani.
Suna Fitowa Kawu Ismail yace saura wajen Malam Kare Aiki,Wannan malamin sanatoci layi suke Yi a Wajensa,Aamna ta girgiza Kai Tace Baba wallahi ba kyau,Wannan shirka ce baza a fadawa Allah bukata ba sai Malam,Baba ya kalleta cikin duhun dare yace ai ke Aljanu gareki sun aureki Bai ma dace a saurare ki ba sabo da ba a cikin hayyacinki kike ba,Yo ka biyewa sakarai cewar Mama,Kawu Ismail yaci gaba da cewa inshallah Kuna komawa zata samu Miji itama,Wannan malamin da suka je Wajensa Rubutu yayiwa Aamna a tafin Hannu yace lashe ai magauta ne Suka mata asiri kuma makwaftan ku ne,Takaici yasa Aamna Tace Allah ya tona muku asiri masu hada fada tsakanin Musulmai,Rankwashi Mama ta zubawa Aamna tayi Shuru,Lashe Kawu ya furta Yana zaro Mata Ido,Haka ba a sonta ba Tace Allah na tuba bana nufin kowa da sharri sannan ta lashe su Baba suna ganin Aljanu ne ke hanata Sha,Haka Suka je wajen wani malamin shima yayi nasa sannan suka jira Bayan Kwana Uku Suka karbo duk wasu Magungunan da aka hada Suka dawo ,Duk wani Rubutu da magani da Suka bawa Aamna Kan tayi amfani da su sai ta samu jikin katanga ta zubar babu Wanda ya sani,Laya Kuma Haka ta soketa da pin a gashinta sabo da kullum Mama sai ta duba gashin dole ta soke Laya a gashinta.
Su Baba Basu Sani ba suna ta jira suga saurayi yazo neman Auren Aamna Amma Shuru,ga Kuma bikin Zuhra yana ta gabatowa,duk sunyi Anko da Dinku Nan su na biki duk wani shiri da za ayi mun Riga sunyi,Baba ya siyar da manyan shanayensa Guda hudu dake Kauye sabo da Haka ba Harkar Talauci sunyi komai cikin rufin asiri,Adam Ango ya hada musu Dinner zazzafa me kyau ranar Saturday,Sunday za a daura Aure a Kai Amarya,daga Aamna sai kawarta Siyama bata gayyaci kowa ba,Amarya dai taci Uban gayyar kawaye wurin Dinner,Biki saura kwana daya a fara Aamna tayi lalle da gyaran gashi,amarya kuwa ta Sha gyara sai sheki take zubawa,dangi na nesa sun zo sai tsiya ake yiwa Aamna kanwa zata Yi aure ta bar Yayarta,Haka suka Sha bikin Zuhra da Angonta Adam anyi an Gama lfy tare da Kai Amarya da gararta,gidan Adam madaidaici ne me kyau harda gate yayi kyau gidan,ga Yar motarsa me kyau Toyota,Itama Zuhra Baba ya Dage ya Mata Kaya masu kyawun gaske.
Ahmad Yana kwance a makeken Gadonsa Yana zuba bacci,wayarsa ta dinga ruru gashi ya kasa tashi sai da kyar ya farka ba tare da ya Bude idonsa ba ya jawo wayarsa yaga number Mummynsa dama ta fada Masa zata zo ta ganshi a kaduna ita kadai kasancewar Daddy,Saddeeq da Humaira suna Saudiya Umrah,Cikin Muryar bacci ya Kara Wayar a kunnensa tare da Furta Hello Mummy......Muryar Namiji yaji yace da Allah me wannan Wayar sunyi Mummunan Hatsari Driver ya mutu ita Kuma tana asibiti da Allah ayi sauri azo,Firgigit ya farka Yace what....?cikin gigita yace please fada min Address din Asibitin,Nan take ya fada Masa,Da sauri Ahmad ya figi machine dinsa sanye da wando 3qutr da Riga t-shirt fara tas sai asibiti,a gurguje ya fada ciki Yana tambaya aka kaishi Emergency Nan ya Iske Mummy Rai a hannun Allah.
Aamna Yau da matsanancin ciwon Mara ta tafi wurin aikinta gudun kar a hanata kudinta cas sabo da ba aikin Gomnati bane,a Haka take daurewa tun tana aikinta da karfin Hali har abin ya fara gagararta,Siyama ta kalla tana rumtse Ido Tace Siyama dole Zan hakura da aikin yau Hospital Zan wuce a duba min marata ya kamata ayi min scanning a gano min mene a wajen Nan,Siyama da tausayawa Tace Allah ya Baki lafiya kawata a dawo lfy sai munyi waya,Aamna ta daura After Dress a saman Uniform dinta Riga da wando ta fita tana tafiya a hankali ta Isa bakin Titi tare da Shiga Napep zuwa Asibitin da suke ganin Likita idan lalura ta taso,asibiti ne na Gomnati Amma ba laifi akwai kyau.
Tana rike da mara hankalinta baya jikinta tana zuba Uban Sauri tabi wani Corridor,Gaf taji tayi Karo da mutum,wani kamshi me jarabar Dadi ya daki Hancinta,da sauri taja baya ko kallon Wanda ta buge Bata Yi ba,shima Bai ko kalleta ba hankalinsa baya jikinsa,Bayan tayi magana da wani Emergency ta nufa tana matse kwallar wahala gashi Bata fadawa kowa a gidansu ba,Karo suka sake Yi da juna kamshin mutumin dazu ta sake ji ya cika Mata Hanci Kamar Kar ta daina Shaka,Tsaki Yaja sosai yayi cikin Emergency Yana ta faman yiwa Doctors masifa,Yana cewa a bani Mummy na dole ne,Ni Nace bana son wannan Hospital din me Araha,a bani Uwata wannan so kuke ku kashe min Mummy a Asibitin Gomnati, Wallahi Mummy na ta mutum sai na daure ku,wani babban Likita ne yace Haba Malam Ahmad kake ko wa? Da masifa yace karka sake ce min Malam,Ni ba Malam bane,a masallaci ka ganni Ina Kiran Sallah ko Tafsiri kaga Ina Yi? Idan zaka iya Call me king,Doctor yayi Murmushi sabo da daga ganin Ahmad kasan inda tarbiyya take ma Bai nufa ba,Cikin tausasawa Doctor yace kayi Hakuri zamuyi Aiki iya yin mu a samu ta farfado wallahi Matukar ba a Bata agaji ba ka dauke ta to kafin kaje da ita wani Asibitin zaka iya rasa ta kayi Hakuri idan aka samo kanta sai ka dauke ta idan kaga dama ma ka tafi da abarka China.