← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 89

Sashe 45

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yace ba yau Zaki dawo ba? Tace Mummy ta min waya Tace na jirasu,Ahmad Yana son abinda Aamna ke so,Bai so ya Mata laifi sai yace kinfi so ayi komai idan kin koma? Aamna garin kunya tace ae harda wani Bata Rai ita bata so,yaji damuwa a ransa sai yaga Kamar Bata damu da shi ba,gashi Yana so shi ya rage zafi Amma Bata so idan yace zaiyi zai takurata ba a son ransa ba maida Mata rigarta Yana furta shike Nan,Aamna Kamar ta kurma Ihu ta cuci kanta,ta manta Ahmad Bai taba kula wata mace ba sai a kanta sannan shi baya Harkar Mata harkar gabansu sukeyi na shaye shaye Kawai.
Kasa magana tayi yace ko Zaki rakani? Ina zamuje? Yace Mummy ce ta aikeni gidan Yayarta Zan Kai Sako,ba damuwa muje na rakaka ta furta,tare da mikewa ta yafa mayafinta tare da daukan hand bag da takalmi me tudu Dark green.

Glass ta dakko ta saka wani light brown Nan ta sake canja dauri zuwa ture kaga tsiya,kyau Kuwa ba a magana,Fitowa sukayi ta Iske Mama a kitchen tana girki Baba Yana Zaune Yana gyara Mata wake,dama Watarana Yana Taya Mama Aiki ba sabon Abu bane Amma badan Allah yakeyi ba Wai Dan kar ayi Masa almubazzaranci sai ya zauna ya gyara da kansa,Mama ce ta juyo Tace Dan Allah Baban Zuhra ka bar wajen Nan Haka Haba me kwarin ma baza ka tsince ba sabo da tsumulmula,Baba yace naki na Bari a zubar min da dukiya a fake da kwari a dafa Mana da kwarin mýÿÿÿ

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~u,kwarin wake ance Kara karfin gani sukeyi Ana so Dan Adam ya dinga Cinsu.
Mama Tace a Ina kaji? A radio bababban Likitan kwari shi yayi bayani,shi fannin kwari ya karanta cewar Baba.

Baba ganin Ahmad sai yace ki dafa waken Nan sosai sabo da bani da wadataccen jini a jikina,waccen shekarar 2020 har jini na bawa wata a asibiti Amma 2021 Ni kaina nasan bani da jini,idan aka aunani za a ga jini na Bai Kai na Bara ba sabo da yanzu ba'a cin nama da abubuwa masu inganci rayuwa ta canja kowa ya kwanta cuta sai kaji ance Karin jini,daga shinkafa da Mai da yaji sai tuwo da Dambu ba Dole a rasa jini ba Ana cin Dambu ai a ka'ida Dambu abincin agwagwi ne suyi ta tsatsatsaga.

Ahmad murmushi yayi ya Gane Baba,Baba Kuwa yace tunda abin Haka ne asibiti zanje na karbo gyadar Nan ta Yara wacce ake karbo musu idan sun rame sun lalace sunki girma Nima ita Zan karbo na Sha nayi bulbul,gaba Daya na wani Zuke sai Dan ciki na kwajaja a gaba da ganin kibata an San Bata lafiya bace sai Dan ciki a gaba,Dariya Aamna Suka Yi Baba yace ba abin Dariya bane Kuna gani sai tsumburewa nakeyi bani da jini sai kace Wanda nake cin kasa Haba ya kamata a dinga kula da ni..

Ahmad yace Nima Baba Ana aunani nasan bayan rashin jinin harda shawara tana damuna Ana auna Ni za a ga shawara ta Gama dani,Nima ba ci nake Ina koshi ba,sai nayi kwanta kwanta ake bani kudin,Baba yace Kai kana Dan gidan Ajebo inji Yan Birni Dole fa ka siyo Mana Nama a gidan Nan duk wata shawararka karya kakeyi,Dariya Ahmad yayi yace to Kawai,Aamna Tace mun tafi Unguwa,Baba yace Halina da ke Aamna kin kasa wayewa wata kidahuma ce ke ace shekara kusan biyar a birni Amma har yanzu sai halin banzan ki na kunbiya kunbiya baza ki fito ki dinga fadan gaskiya ba yanzu idan gidansa zaku tafi Zan hanaki ne? Idan ma Hotel Zaki tafi me zamu ce tunda mijinki ne,Aamna ta bude Baki daga ji tasan Gulmar Baba ce Kawai so yake yaji inda zasu tafi Yana zarginsu,Mama Tace a dawo lafiya,Ahmad Yana gefe Yana jinsu saura shima ki ta Masa halinki na munafunci baza ki dinga Fitowa ki nuna kina son Abu ba,idan Kifi kike so kice ya dinga siyo miki,idan nama ne ko Madara ki fada Masa,Dariya ce ta kwacewa Ahmad su Wato Dole sai sunci kudinsa kenan shi yasa suke ta wannan abin,Baba da sigar lallami yace Yaron Nan idan mota kika ce kina so ya Siya Mana tsaf Zaki ga Allah ya azurta mu.

Ahmad Palo ya tsaya yace Ina jiranki,Ahmad Yana Jin Mama Wai tana sirri da Aamna tace to ke Soyayyar zamani ma ba iyata kika yi ba,Dan ubanki idan baki dage ba yanzu Mata sun dage kwacen maza sukeyi wata idan taga wannan zukeken ga kudi ai wallahi ke da kwanciyar hankali a duniya sai dai kiji a makwafta,da asiri za a rabaki da shi ko idan Suka fiki iya tarairayar Namiji shike Nan,Baba harda zaro Ido yace Sorrynki Aamna inji bature,kije Zuhra ta koya Miki zaman duniya,gata can da Adamun ta kullum mashaallah,bakiji sunan da take Kiran Adamun ba? Me lobuli,Dariya Aamna tayi Wai Baba (My Lovely ) yake nufi shine Me lobuli.

Aamna tafiya tayi tana cewa Nima na iya ai ban fara bane,sabo da ke ga Yar me taurin Kai ko? Cewar Mama,Aamna King ta samu Tace let's go,Suna tafiya Baba yace ai yanzu tunda auren Nan na Aamna ya koma mutu ka raba to dagewa zakiyi ki Mata gyara irin na Iyaye sannan ki koya Mata salo da dabarun kauna sabo da ta Haka ne kadai zamu samu harka,idan Yana Jin dadinta babu abinda bazai Mana ba a duniya,Duk da kema wata kidahumar ce baki iya komai ba Nima maleji nakeyi Amma ki koya Mata dai Kamar yanda kika yiwa Zuhra,Mama Tace au ci min mutunci zakayi? Da me kika iya? Karya nayi? In Banda ta'adin Omo da Ashana me kika kware? Mama Tace to Kai din wanne Jin dadin ka nuna min abinda Hakuri nakeyi da Kai.

Amma ke dai Butulu ce Aishatu wanne tsoho kika taba gani kamata me koyi da Sunnar Annabi Irina? Da girmana Amma idan Ina gida sai na tayaki girki,yanzu ke kika sani? Amma na zauna Ina gyara Miki wake,sannan nine yanka Miki Albasa,Alayyahu,fere Miki dankali da doya,har kabewa nake fere Miki duk Baki gani ba,Mama ta dauke Kai Tace ai Dan kar a maka barna ne,.
yace raguwar Banza raguwar wofi yarinya Daya kika iya haifar min,tun da kuruciyarki kina shekara14 aka aura min ke Amma da an tabaki sai kuka wayyo...wayyo...ki bare Baki Kamar Ramin kurege,Duk nayi zaton kuruciya ce Ashe Kya ce kaci Ubanka Husaini har girmana Haka aka halicce Ni.

Mama Dariya tayi Tace to babana ne ya jawo da aka haife Ni wanzami aka bashi Ni ya yanke min beli,Ashe Bai iya ba,ance Dan redar kadan akeyi shi ya yanke da yawa,Da sauri Baba yace wanne Ya yanke da yawa ai gaba Daya ya jijjige shi ai Allah ya tsinewa wannan Wanzami wallahi tallahi bazai ga Annabi ba.

Ya rasu fa cewar Mama,Baba yace ina ruwana da mutuwarsa Nima Nan gaba mutuwa zanyi kowa ma Haka Kawai ya cuceni,Hannu Baba ya daga Yana rokon Allah yace Allah kasa walakiri ya ta jibgar Salele Sarkin aska har tashin kiyama sanadiyar abinda yayi min,gashi Haka na hakura ban Kara aure ba babu Yara da yawa ga ba Wani dadin aure nake ji ba,Mama ya nuna da yatsa yace asiri kika min muguwa shi yasa na makale sai ke kadai,Mama Tace Hakuri ne Kawai irin namu na mutanen da,zaka ga ba'a Jin dadin rayuwar aure da komai Amma anyi Hakuri an zauna mutu ka Raba.

Baba yace Haba ai na ciji yatsa da ba Dan zamanin yanzu bane ni gashi sai yanzu ake ta santalo Mata zalla zalla gasu Nan suyi ta giftawa sai hange daga nesa,Mama ya gallawa Harara yace ku Kuwa daga me Hanci a karkace sai baka wuluk,sai me katon goshi,sai me Kai kamar kwallon goruba,fata kamar Bayan Bishiya duk gaku Nan taron tsintsiya ba shara,yanzu Kuwa kaga Iyaye munana Amma sun Haifo kyawawa da naga wata Rannan tazo da Yarta shago na sai da na rantse Sato Yarinyar tayi Ashe Wai Tata ce,da har Zan kurma Ihu nace jama'a barauniyar yara.

Ni gaba Daya na tsani kaina ma sabo da banzo a yanzu ba,Mama tana Dariya Tace to ya zakayi aikin Gama ya Gama gani auren zumunci ko ka koreni sai an sasanta,Baba yace ai ni duniya na hakura da Jin dadinta naji a lahira Allah yasa mu Dace.

Aamna Kuwa fitowarsu kenan Kofar gidan taga wata sabuwar motar galleliyar gaske tafi wacce akayi hatsari da ita komai da komai ruwan toka,a baya Ahmad da Kansa yake Bude Mata kofa sai ta Shiga zai rufe ya dawo shi ya shiga Amma wannan lokacin sai taga ya shige mazaunin Driver ya barta,taji ba Dadi a ranta tunda ta Saba da yanda yake ji da ita Yana Nuna Mata tattali,Shiga Kawai tayi itama ta rufe,Motar ya ma key ya fara Driving cikin nutsuwa,Kallonsa takeyi jefe jefi Wanda da abaya ne shine zai ta kallonta Yana Driving har sai ta Masa magana ya kula da Driving sabanin yanzu taga ya wani dawo da takamarsa da izzarsa sai wani basarwa yakeyi,Bata ga laifinsa ba tasan ita ta jawowa kanta,a nutse yake Driving Yana satar kallonta ba tare data lura ba,ganin ta Lula tunani tayi Shuru kamar ba ita ce ba, Murmushi yayi a ransa kawai.
Chapter 45 · 0% Book details