← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 89

Sashe 46

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Masu siyar da Apple na Kan danja da masu popcorn etc sune suke daga musu Abu ko zasu siya,Ganin tayi Shuru yace ko Zaki ci wani Abu? ba tare da ta kalle shi ba Tace a'a Kawai ta kalli window,sunyi tafiya me nisa wani gida me kyau taga an Bude Masa gate ya Shiga,gidan ya hadu shima,Yan Yara ta hango su Uku zasu Kai 5-7yrs suna Wasa a wajen flowers,Ganin Ahmad ya fito Suka bisu da kallo Basu San waye ba da Alama,Wata bakar Budurwa ce ta fito sanye cikin Uniform da Alama Islamiyya zata tafi,tana ganin Ahmad ta furta laaaa Yaya Ahmad lallai Kaine yau a gidan mu,tab Dariya tayi Tace Yaya Ahmad Wai Kaine da kayan hausawa lallai ta tabbata Ashe da gaske Mummy take da Tace Aure ya gyara ka,Aamna ta kalla Tace ga Auntyn mu ma nasan ita ce,Ina yini? Aamna tayi murmushi ta amsa,Ahmad Kuwa dama miskili ne,Fuska ya Bata da yaji tace wani Wai aure ya gyarashi ta Raina Masa hankali,a ransa yace matsalar Yara Basu iya magana ba,Ko gaisuwarta Bai amsa ba yayi gaba abinsa,Ita kanta Yarinyar mantashi tayi shi yasa ta iya fada Masa Haka,tasan da a baya ne da tuni ta Sha Mari,Sum sum ta tafi makarantarta.

Suna Shiga suka Iske wata Mata Babba me Kama da Mummy da Alama ta girmi Mummy sosai sai dai ita baka ce Mummy Kuwa fara ce Amma suna Kama da Mummy sosai,Aamna kallo Daya ta Mata ta Gane ta lokacin da aka kawo lefenta harda matar, Matar da fara'a Tace ikon Allah yau Ahmad a gidana? Muna gari Daya Dan Iskanci sai na shekara biyar ban ganka ba sabo da kar na maka fada,sai yau lallai Aamna tayi kokari da gani ba sai an fada ba,jajayen Lips dinsa ya turo gaba yace nazo na gaida ki shine Zaki ce Haka gobe bazan dawo ba,Dariya tayi Tace na daina Barka da zuwa,Zama sukayi Aamna ta rusuna tare da gaisar da ita,cike da fara'a ta amsa,Tace Sannu da zuwa Aamna,yawwa ta furta,Ahmad yace Amma dama Mummy ce Tace nazo na gaisar dake,au Dan Iskanci ma ba Ganin damarka bace? Anya Kuwa zakuyi zumunci Nan gaba Bayan Bama raye, shine Ina Hospital da dumbun patient ka min waya kace lallai na dawo Sako zaka bani Ashe wannan ne sakon,Murmushi yayi har Aamna ya kalli Aamna yace Yayar Mummy ce Uwa Daya uba Daya,Aamna Tace Naga sunyi Kama ai Kuma na ganeta,Amma tace kwarai Kuwa da Ni aka Kai lefenki.

Bayan an tashi Yan makaranta Tawaga yaje dakko kannensa Yana zuwa ya dauke su ya fyalla da gudu kamar zai tashi sama,Yaran ya Kai gida yayi sauri ya dawo school din lokacin Yan Ss3 Basu tashi ba Ana musu lesson sabo da sun kusa Zana Waec,Jira yayi tunda yaga Yarinyar da Alama a Ss3 take,Sai da yayi 30mnt a Bayan wani gida Yana lekowa ai Kuwa ya hango me Kama da Yan China ta fito tana tafiya tana ta dukan wasu classmates dinta tana guduwa,suna cewa wallhi Yar China gobe sai mun Rama Zaki zo ne, Wasu duk an dauke su a mota sun tafi gida ita Kuwa ita kadai tabi ta wani lungu,tana ta gantali a hanya tana bin ta cikin Unguwanni.

Tawaga ya kunna machine dinsa ya bita a hankali Bata sani ba,Jin karar machine Taki karewa yasa ta juyo tayi Ido biyu da Tawaga Nan take ta Gane shi ta tsorata,takalmanta ta cire ta kwashe da gudu,Tawaga a nutse yake ta Binta har zuwa wani gida Haka na Bulon Siminti me Dan kyau dai na rufin asiri,Gidan ta fada da gudu Tawaga yaci birki ya sakko,Kawai gidan ya Bude shima ya shiga,wata tsohuwa ya gani tukuf tana zaune Yarinyar ganin Tawaga ya shigo har gidan ta Mike da gudu Tace Iyalle barawo tabi ta Kan tsohuwar ta fada daki tare da fatalar da kwanon abincin da Iyalle take ci,Tawaga ba ruwansa da wani gidan mutane a Haka ma sabo da ya dan shiryu Kawai yace Salamaualaykum Tsohuwa gyara kafarki Kar na karasa gawar da Bata tawa ba,Iyalle Tace Kai Malam barawo ne Kai?

Tawaga yace duk abinda kika Yi tunani a ranki Haka nake,Iyalle Tace to Kai Dan shaye shaye ne naga Alama,Iya Lallai kina da kwanya gyara kafarki cewar Tawaga,Kai yaro ko gidan Ubanka ne ai sai Haka,Shege ne ni bani da uba Tawaga ya furta tare da tsallake Iyalle yayi cikin dakin ya nemi Yar China ya rasa.
Cikin wani karamin Sip irin na da ya Bude sai ga Yar China bul a ciki tayi zuru zuru ta hada zufa,Iyalle Tace Dan Allah yaro karka Dakar min jika Yar China marainiya ce Bata da Uwa Bata da uba,nice nake rike da ita sai kanina da yake kula da yake Dan kula da mu sama sama,shi Kansa ba karfi ne da shi ba,abinci ma wallahi da kyar muke samun sau daya ko sau biyu a Rana,Yar China tsokana ce da ita Amma tana da saukin Kai kayi Hakuri Dan Allah,sakaki nane yasa take da Rashin kunya nice sangartata,Tawaga yace ban Santa ba ta zageni dama nace har karkashin gadon uwarta sai na bita Ni ba ruwana da wani gidan matan Aure ba Wani ganin darajarsu nakeyi ba,Iyalle ta Bude Baki Tace matan auren? Tawaga yace Ina ruwana da Iyalin wani bani da mutunci ya Furta Yana zarowa Iyalle kyawawan idanuwansa.

Ya sake cewa Iya Dan fa Baki Sanni bane da a wata Daya Baya ne da na amsa Sunana na Tawaga Dake da Yar Chinan Zan hada na zubar muku da hakora,Iyalle Tace yaro Ina Naga hakoran da zaka zubar Dan Ubanka kalli Baki na Iyalle ta wangalewa Tawaga bakinta yaga ba hakora duk sun zube,Iyalle da lallashi Tace Yi Hakuri Dan jikana Ni yanzu da zaka Bamu na kokon safe ma da ka kyauta,dama Ina ganinka na Gane addu'ata kanka ta fada Allah ne ya turoka ka Bamu na Shan Koko da safe,Kuma jikata kagani wallahi an kusa rufe musu jarabawa zasu Zana ta fita mun rasa yanda zamuyi mu biya Mata tayi kuka har ta gaji.

Yar China ce ta fito Sadaf Sadaf ta fada jikin Iyalle tare da fashewa da kuka tana Iyalle kudin Waec wallahi jibi Za'a rufe,na shiga Uku na lalace,Baki Tawaga ya Bude Kiri Kiri sun Raina Masa hankali,Kallon Yar China yayi tana faman kuka har wutsil wutsil tana cewa Babana ya mutu tun Ina karama,Babata ma ta mutu duk bani da wayo Suka mutu shi yasa bazan samu Ilimi ba ni bani da gata,Tawaga a ransa yace kaji mutane sun bige da maula, kallon Yar China ya sakeyi a ransa yace shegiyar yarinya sai farin fatar tsiya ita ba Wani kyau ba,Harara ya galla Mata tare da daka Mata Tsawa ya fara Mata magana Wai da yaren Yan China tunda ance sunanta Yar China Kuma da su tayi kama,Yace Chan chan hu whaaaa? Harda gwadawa da Hannu Yana ci gaba da cewa Jiji chan huuuaaaa? Yar China ta kyalkyale da dariya harda rike ciki Bata San shima haukarsa ya hada ba Tace Kai bana Jin Yarensu wallahi Kawai Allah ne ya halicce ni nake Kama da su tsaya kaga hoton Babata da Baba na, Daki ta fada da gudu ta dakko hoton Babanta da babarta ta nuna Masa ka gansu,Lekawa yayi yaga Babarta wankan tarwada ce,Babanta ne fari Amma danfulani ne usul Bai Kama da ita ba Sam,Tace mu yan Kebbi ne asalinmu.

Tawaga yace to Ina ruwana da Kebbinku Allah yasa a Minner kuke karewa Yaja Tsaki ya juya zai tafi sai ya fasa ya dawo ya zubawa Yar China Rankwashi ta kwalla ihu,Iyalle Tace Yi Hakuri jikana,Hannu yasa a aljihun Jean dinsa ya zaro Dubu biyu ya damkawa Iyalle a Hannu yayi tafiyarsa,Ai Yana tafiya Iyalle harda rawa Tace wallahi yau sai na raba dare Ina Nafeela Ina godewa Allah mun samu kudin Abinci na kwana Biyar,ko matar Yaron Nan kanina Bata kawo Mana ba sai mu siya muci,idan Kuma ta kawo Wanda bazai ishe mu ba sai mu Kara da ko garin kwakwi ne,Yar China sai murna takeyi Tace Alhmdllh zamu dinga cin abinci sau uku a Rana,kwana Nan Zan murza kiba,Kuma Iyalle nasan zanyi kwana Uku ko biyu kina bani ashirin kudin makaranta,dama na dade banci ko Aya ba a makaranta.

Tawaga yana jinsu sabo da a soro ya labe yaji me zasu ce,sai Suka bashi tausayi duk irin kallon gidansu da yakeyi sai yaga ashe su a Rahma suke,Tafiya yayi abinsa.
Mashkoor Kuwa ya makalewa nurse Nafeesat tun Bata wani kulashi har ta dawo Yana birgeta Kuma a cikin kankanin lokaci Suka Shaku sosai har Tace ya kamata yazo gidansu,Ranar Bai fadawa abokansa ba ya shirya shi kadai cikin Shadda milk ya wani coka hula Malam ya wuce gidan su Nafeesat, Mashkoor yayi tunanin dama su Nafeesat masu kudi ne Amma baiyi zaton kudinsu ya Kai Haka ba,gidansu ko Ina Securities ne, sannan Unguwar da suke ta masu Hannu da shuni ce sai ka shahara kake Zama a Nan.
Chapter 46 · 0% Book details