← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 89

Sashe 25

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahmad kuwa Bayan Aamna ta bar gidansa shi Bai ji wani damuwa ba ko a jikinsa,ci gaba yayi da shakatawarsa musamman da ya samu Mummy bai ji ta Masa fada ba,Su Mashkoor suka dawo gidan suka tare kullum sai shaye shaye sukeyi,Ranar da Aamna ta cika sati Daya cif da barin gidan Ahmad ya fito a machine a hankali Yana tafiya a nutse,Aamna ta fito kenan tana aunawa wani yaro barkono karaf suka hada Ido da shi zai wuce,Ido ya tsura Mata itama Haka ya Mata kyau da yawa,Machine dinsa ya karawa wuta ya bar wajen,fasa zuwa yayi inda yayi Niyya ya koma gida abinsa,tunda ya dawo Aamna ce ke Masa gizo a fuskarta,Kawai fuskarta yake tunanowa,Tsaki Yaja ya shige Bedroom dinsa ya kwanta Nan take bacci ya kwashe shi,Mafarkin Aamna ya Shiga Yi suna zuba soyayya tana jikinsa a kwance.

A Matukar zabure ya farka Shuru yayi Yana tunani,yace ah....wannan wanne irin tsafi ne? Gashinsa ya girgiza Kamar Yana korar kuda Haka yake karkade Fuskarsa Yana masifa ki bar Fuska na daina ganinki,a'ahhh.....ki daina fito min a Fuska Ina kallonki,wannan wanne masifa ne Haka?.....Ni.....ya nuna Kansa da yatsa ni Zan zauna Ina tunanin mace,kamata Ni a'ahhhh....chaiiii......mikewa tsaye yayi ya kaiwa Iska Naushi yace Zan fasa Miki Baki fa......shi kadai yake ta abinsa a bedroom kamar sabon kamu,Zama ya sake Yi sai Kawai ya tafi tunanin Aamna...Tsaki Yaja yace again....Wai wannan wacce irin yarinya ce ki fitar min daga ido na daina ganinki....kasa ya sakko ya durkusa ya daga hannaye sama Yana Allah ka gani dai Yarinyar Nan sai Tunaninta nakeyi,Ina ta ganinta a Ido na,bazan Iya ba....nasan ni me laifi ne a gareka,nayiwa mutane da yawa laifi Allah karka Yi Fushi Dani ka jarabce Ni da yarinyar nan,Allah kasa na daina ganinta,Allah na tuba,ya Mike tsaye ya sake juyowa da karfi Yana tangadi yace Allah nayi Addua Kuma ban daina Tunaninta ba,kirjinsa ya dafe tare da furta wayyooo....my Heart woooo ....Ina ta ganinta fa ya Allah,Ya girgiza Kansa ya shiga zaga dakin Yana safa da marwa Yana Ohh....ohh.....Ni ta fita daga Ido na,ta fitaaaa.....a Haka ya yini Yana sambatu har dare yayi Bayan ya jero sallolinsa na yini Guda yace Bari na kwanta bacci da wuri ko Zan daina ganinta a idona,Yana kwanciya ya kasa bacci sai tunanin Aamna tana Masa gizo,Shi kadai yace kunga yau bazan iya bacci ba sai tunaninta yau an shiga Uku.....mikewa yayi zaune yace kaiii....yau bazan Iya bacci ba sai na ganta....naji idan ban ganta bazan samu nutsuwa ba,...Amma Bari naje na ganta nasan idan na ganta zan daina ganinta a idona...waiiii....ya akayi ne nake so sai na ganta,Kawai so nake Naga Yarinyar Nan yanzu yanzu,Kawai gidansu Zan tafi yafi sauki ai Zan Gane gidansu ko na Kira Mashkoor ya raka Ni gidan sabo da ai sunje daurin Aure zasu Gane gidan,a hankali yace Amma idan na Kira Mashkoor asiri na zai tonu Kuma na Gama kuri da cika Baki a gabansu abin kunya ne a ganni naje wajen mace,macen ma wannan yarinya,Amma fa gaskiya idan ban ganta ba bazan samu nutsuwa ba Dole na tafi,agogon Dake hannunsa ya duba yaga 9pm yace Bari naje ko ta katangar gidan ce na haura na ganta,gashi wani kunyarta nake ji da tsoronta bazan Bari ta ganni ba.

Cikin dare ya dauki pcap ya saka sannan yasa face Mark a Fuskarsa Wai Dan kar a ganshi yaji kunya an ganshi a wajen mace,Musa Wanda jiya ya dawo shi ya bawa key din machine yace Musa zuciyata yau wani Bugawa takeyi bazan Iya tuki ba kaini wata Unguwa,Musa ya karbi key ya hau shima Ahmad ya hau sanye cikin kayan baccinsa wando gajeren da Riga me gajeren Hannu ko a jikinsa Haka Suka tafi,Yana ta nunawa Musa Hanya da kyar ya samu ya gano gidan tunda an taba zuwa dashi sau daya,can nesa da gidan yace Musa ya ajiyeshi,ya sauka yace ka jirani a nan bance ka biyo Ni ba,Musa yace to Oga,Face mark dinsa ya gyara ya bi ta can bayan gidan,Kamar Biri Haka ya Dane saman katanga Dake Bata da tsayi Haka ya haura gidan su Aamna lokacin Baba ya fito zai rufe gida.

Ahmad ya labe Bai ganshi ba,Baba ya kulle ko Ina ta gidan,Bai San ya rufe kofa da barawo ba,Ahmad yace yanzu Ni ba abin na shigar musu gida ba,Kuma yanzu Taya zata fito na ganta? Ai wallahi idan Zan kwana bazan tafi ba sai na ganta,Yana tsaye har wurin minti goma sai yaga an Bude kofa an fito sai yaga Aamna ce sanye cikin kayan bacci ta fito da bucket,Ahmad ya Kara labewa ya gyara tsaiwa Yana kallonta Yana zuba murmushi yace kalli Hanci Dan Allah me kyau a Nan wajen.....Uhmmm .....Allah yayi baiwa, panties yaga ta Shanya Guda Uku da Bra Guda biyu,Aamna tafi so ta Shanya Rana ta dake su sabo da kashe kwayoyin cututtuka,Bata son Shanya su a inuwa tasan gobe Rana zata dake su.

Ta Gama shanyawa Yana ta kallonta Mama ta fito tace Aamna ki shigo da kujera ciki Tace to,Ahmad yace kaji sunan ma Aam....nah.....my Aamna...no sunan gayu Ahmnaa....Yes...Ahmnna vs Ahmad...A&A kenan a'a wannan Dadi Haka.....kumatunsa ya Mara kadan yace to yanzu Zan Iya tafiya nayi bacci,Zabura yayi yace Kai Nafa haukace,wannan fa hauka ce,Ahmad Ni king Haka Kawai na zauce akan Yar Yarinyar nan,Tsaki Yaja yace Nafa haukace gaskiya....lallabawa yayi ya sake haurawa ya bar gidan,Musa ya hango shi ya taho Yana ta murna Yana murmushi Bai San dalili ba,Machine ya hau Suka koma gida,ranar wani irin bacci yayi me dadin gaske.

Washe gari Yana farkawa da Aamna ya farka a ransa,Tsaki Yaja yace Wai na ganta ma bazan huta ba...Haba zuciyata me yasa Wai kike min Haka ne,jiya kinsa naje na ganta yanzu ma so kike ki Kara ganinta Baki koshi ba wannan wanne irin tsafi ne Yarinyar Nan tayi min ne,da safe sai na farka da ita Haba which kind juju be that? Ni ba sonta nake ba duk harkar love...love ba ruwana da shi Amma Kuma so nake na sake ganinta Haba nooooo.....ya Furta cikin karaji,Sannan cikin slow Yana yarfe Hannu yace idan na ganta anjima ai shike Nan Kuma sai na huta,ai abin kunya ne kamata Ina son ganin Yar yarinya,zuciyarsa ya dafe yace sai wani tsoronta nake ji zuciyata tana wani bugawa Haka Kawai idan na ganta to daga yau bazan sake zuwa ganinta ba aikin banza,tunani ya shiga Yi yace Naga kamar ma samari na zuwa wajen Baby dinsu da Kaya Decent,to Amma Ni ai ba Baby na bace,Kuma fa sai taji Dadi idan idan ta ganni da kayan hausawa? Murmushi yayi ya koma Gaban Mirror ya duka Yana karewa Kansa kallo ya shafa calabarsa yace gani kyakyawa ai dole ma na birge ta,hannayensa ya Buda a Gaban mirror ya saki murmushi yace chaii....see fine Boy.....oh..oh....baya Yaja sosai Yana kallonsa yace huuuu...Kalar birgewa kaga Kalar birgewa yesss.....Bari nayi wanka, Fuska ya Bata yace to Mene sai wani murna kakeyi zaka ganta aikin banza,Ni wallahi wani banza ne ma akan mace Subhannallahi ya Dan Mari kumatunsa kadan yace Bari na gwada Kalar murmushin da Zan Mata Nan fa ya shiga sakin murmushi kala kala Yana kallon kansa a karshe ya Dan yake kyawawan hakoransa yace ae tsaya dai dai Nan wannan yayi yawwa ae....sai ya wuce toilet.

Tunda ya shiga ciki Yace yau wankan na musamman ne so nake na Kara haske Nan fa ya shiga dirzar fatarsa ba ji ba gani,yace bana wanka da soso yau Zan koma Yi da soso sabo da na fita fes,dubawa yayi bashi da soso,towel ya daura Bayan ya dauraye jikinsa ya fito a Haka daure da towel har wajen me gadi,kudi ya mikawa Musa yace ungo maza ka siyo min soson wanka,karka sake ka dakko min na jarirai me laushi me karfi zaka siyo Wanda Ina wanka Ina Jin radadi,Musa yayi Dariya yace irin namu na talakawa kenan? Karka Bata min time sauri nakeyi Ina da abin yi akan wannan soson wallahi Zan iya sallamarka daga Aiki Matukar baka siyo Wanda zai wanke min fatata sosai ba,Musa ya karba da sauri ya fice,Minti biyar ya dawo da soso me shegen karfi ya bashi.
Chapter 25 · 0% Book details