Sashe 43
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sameera ta fara bashi a baki Yana ci suna kallon junansu.
Mashkoor Wanda duk ya fisu Jin sauki,Ahmad ya koma Room dinsa tare da kannen Jibson gefe Kuma ga yayar Mashkoor tana zaune,wata Nurse ce Yar kyakyawa fara Amma ba can ba ta Sha fararen uniform dinta Idonta dauke da farin Glass da Alama Hutu ya ratsata kana gani kasan ba talaka bace,baza ta wuce 22yrs ba,tana kamshi ta shigo ta kalli Mashkoor Tace ranka ya Dade maganinka fa? Fuska ya Bata yace Baku da Aiki sai durawa mutum kwaya,Ahmad ya dura Masa ashar yace Amma ai kasha marar amfani Malam ka karba,ya kalli Budurwar yace idan Zaki bani a Baki da kanki Zan Sha,Dariya ya Bata tace Indai zaka Sha me zai Hana,Ahmad Baki ya tabe tare da kwadawa Mashkoor waya a Kansa kadan,Kara yayi kadan,Nurse wacce ake Kira da Nafeesat ita ce ta bashi maganin da kanta sannan ya Sha,dama Ahmad ya Dade Yana kallon Mashkoor kullum Nurse din idan ta zo sai ya wani nutsu magana ma baya Wasa ko kadan idan a gabanta ne,Kallon Nurse din yayi a nutse yace na gode ya wani gyara t-shirt dinsa,Tace juya na wanke maka raunin Dake bayanka Zan Masa dressing, Mashkoor ya cire Rigarsa tare da juya Mata baya,Nafeesat jikinsa take karewa kallo wani luwai luwai da Alama Ana kula da jikin Nan sosai dama gasu duk Yan gayu ne,Shi kuwa Mashkoor Ido ya wani lumshe da Hannunta ya sauka a gadon bayansa,Sai da abin ya bawa Ahmad Dariya ya Harare shi sannan ya fita.
Room din Bash kuwa Ana gyara Masa inda kashinsa ya goce sai Ihu yake Yi,Yan Uwansa suna ta Masa dariya,Mamansa tana rike da shi..
Tawaga shima sosai yaji sauki Yan kannensa marayu sun yanyame shi wajen su goma Sha babu masaka tsinke sabo da shine jigon rayuwarsu Basu da matsala idan Yana Nan,Harda Yan Yara wasu duk sun Dane jikinsa suna ta wasa Yana ta dariya Umma tana musu fada Amma Ina,ai ko gida ya dawo da gudu zaka ga suna Fitowa ta kudu ta arewa suna Masa Oyoyo shi Kuma Yana daukansu Daya bayan Daya,Ummansa Tace Allah ya taimakemu da ace ka mutu da mun shiga uku,Dariya yayi yace ai Allah Yana Nan,Ahmad Daya shigo dakin sai da suka bashi tausayi matuka har da hawayensa ya goge kadan,Yaran suna ganinsa shima Suka dinga gudu Wajensa Suka yanyame shi suna Yaya Ahmad Ina wuni,Daukansu ya Shiga Yi Daya bayan Daya yanda suka Saba Yi musu,gaba Daya Suka taso har manyan maza da mata,Ahmad ya kalli Umman yace Umma yanzu kuka zo? Tayi murmushi Tace wallahi Kuwa Allah dai ya saka,ya muku Albarka,Allah ya baku lafiya da tsawon rai,Allah ya albarkaci rayuwarku, Inshaallah baza ku tabe ba,Ahmad yace Ameen Umma,Kanin Tawaga Yaja gefe Yace ya gidan namu akwai abinci ko? Yaron yace akwai komai wallahi,to ba Mai matsala? Yace babu komai,Yan makaranta fa? babu matsala Suma,Ahmad yace Good to yanzu ja Yaran Nan ku koma gida da Umma sai ku bar Sageer tunda shi Yana da girma Kuma Namiji ne,yace to,Umma ta ja Yaran Suka fita har Ahmad a Napep biyu ya biya kudin sannan ya bawa Umma 10k yace tayi cefane Suka tafi suna ta godiya.
Brown dama suna da Dan Hali su Basu da matsala Kuma Ahmad ya biya kudin Hospital,Allah sarki shima danginsa suna tafe,Bash ma Basu da matsala komai normal.
Ahmad kuwa kullum acan yake yini acan yake kwana wanka ne Kawai ke maida shi gida,Yana musu komai da kudinsa da lafiyarsa,Me Hannun kwano ma da ita ake jinya tana tafe da Abinci kullum,ko wanne room mutum Daya ne a ciki,Kuma suna ta samun lafiya kullum.
Aamna Shiryawa tayi itama zata je dubiya,Mummy ce ta fada Mata Hospital din da suke,Sabo da tana sa Rai zata ga Ahmad wani Arnen wanka ta dauka cikin dankareren farin lace me tsada na lefe Wanda Bata taba sawa ba,dinkin Riga da skert komai fari ta sa har takalmi da jaka lady in white tayi ta tafi,Da Nafeesat nurse ta fara haduwa ta tambayeta,ai Kuwa duk ta nuna mata,Dakin da Tawaga ke kwance ta fara shiga Yan Yara kanana su Uku ta hango da Dan shekara bakwai,takwas,sai me biyar suna Wasa a jikin Ahmad dukansu mata,Ahmad Kuma Yana Zaune a gefen Tawaga suna ta Hira suna dariya yace ai Kai sunanka Me Marayu Allah zai dafa maka da wuri Tawaga yanda kake kula da Marayun Nan haka,Aamna tsayawa tayi tana kallonsu sun Matukar birgeta,kawarta ta tuna Siyama yanda taci amanarta ta rabata da masoyinta abin kaunarta,kafin ta Gama tunanin taga Yan Uwan Tawaga suna ta sintiri Yara da manya suna ta zuwa ana tafiya da su gaskiya suna ji da shi,Yan Yaran Dake Wasa wata Yar Budurwa ta kwashe su kaf ta bawa kannenta suka tafi da su gida,Ita Kuma ta dawo ciki,Budurwar baza ta wuce 19Yrs ba kyakyawar gaske suna Kama da Tawaga sai dai ta Dan fishi haske kadan dake mace ce,Shima Wala"Allah Dan Yana shaye shaye ne.
Budurwar me suna Hafsat ta kalli Aamna wacce Taki shigowa tun dazu Tace baiwar Allah kin Dade a tsaye ba dubiya kika zo ba ne? sai lokacin Ahmad ya juyo Sabo da sun juya baya,Aamna ya gani sai da zuciyarsa ta buga,yaji wani sabon sonta ya sake shigarsa,Wutar sonta tana ruruwa a zuciyarsa,Itama Haka Aamna ji take Kamar ta kurma Ihu sabo da sonsa da Kuma yanda zuciyarta ke bugawa ba kakkautawa,Tawaga ne yace Aunty Balaraba karaso Mana,Hafsat tashi tayi Tace zauna a Nan ita Kuma ta zauna kusa da Ahmad Tace Yaya Ahmad na siyo Mana Whot kullum zamuna Yi da marasa lafiya sabo da su samu nishadi,Dariya Ahmad yayi yace kin kyauta Hafsat,Aamna ji take Kamar ta mutu sabo da murmushin da yayi ba karamin kyau yayi ba,,Hafsat Tace Yaya Ahmad give me Five ta Mika Masa Hannu zasu tafa caraf Aamna ta rike Hannunta cike da kishi Tace ba muharraminki bane Yan Mata,Tawaga yayi Dariya ya kyaftawa Hafsat Ido tace na gode da tunatarwa Aunty.
Tawaga ta gaisar ta Masa ya jiki ya amsa da fara'a,Ahmad take ta faman kallo,zuciyarsa ce ta kasa Jurewa ya tashi tsam ya bar room din a fusace ya koma Room din Mashkoor Wanda daga shi sai Mashkoor,Aamna tana gamawa Tace Bari naje na duba sauran ta musu Sallama,Bayan Aamna ta fita Tawaga yace Hafsat matarsa ce fa? Dariya Hafsat tayi Tace lallai Dole ta ji haushi na,Amma fada Suka Yi? Ae Kawai Tawaga yace,Tace me ya hada su? Tawaga yace bana son gulma fa Ina ruwanki so kike naci Amanar abokina na fada Miki sirrinsa,Sorry Yaya ta furta,yace kinyi Assignment din naki? Ae ta furta yace Good so nake Yi kema ki Zama Nurse ki dinga tsira Mana tsinken bature,Dariya Hafsat tayi.
Aamna dakin Mashkoor ta shiga Bata Yi zaton Ahmad Yana ciki ba, Mashkoor yace Aunty kece? Murmushi tayi tace nice ta gaisar da shi tana ya jikin? Yace da sauki,Ahmad ya Bata Rai Kamar zaiyi duka, Aamna jikinta ya sake sanyi,Aamna da kyar take danne zuciyarta Kar tayi kuka tace Mashkoor Allah ya kiyaye gab.....Hawaye ne ya zubo Mata ba tare data shirya ba,Ahmad ganin kukanta hankalinsa ya Kai Matukar tashi Amma Daya tuna kalamanta na ba sonsa nake Yi ba na karbi soyayyarsa ne sabo da na canja shi,sabo da na taimaki Iyayensa sai ransa ya sake baci,zuciyarsa tayi bakikirin, Mashkoor Kuwa tausayin Aamna ne ya kamashi da gani tana son Abokin nasu matuka Amma tuna abinda tayiwa abokinsa Tace ba sonsa takeyi ba Kawai sai ya share,yace kiyi Hakuri Aunty komai zai dawo normal,Maganar Mashkoor yasa ta danji sanyi tana shesheka Tace da gaske kake Yi? Yace Inshaallah very soon,Murmushi Aamna tayi,ganin Haka Ahmad ya fice daga dakin a fusace.
Haka ta duba duka Brown,bash da Jibson ta fito zata tafi ta hango Ahmad a wajen Nafeesat Nurse suna magana tana rubutawa da Alama magunguna za a siyo,tafiya Aamna tayi abinta.
Bayan Kwana biyar Aamna da Yamma Shiryawa tayi ta tafi gidan Ahmad lokacin ya shirya zai tafi hospital ya ganta ta shigo tana tafiya Sadaf Sadaf,da sauri ya koma palonsa sabo da Bai so ya ci Mata mutunci a Gaban me Gadinsa Bai Dace ba tana matarsa, palon ta shiga da masifa yace me ya kawo ki gida na? bana bukatar sake ganinki a rayuwata ki fita harkata,Aamna gwiwoyinta ta zube a kasa tare da hade Hannayenta biyu tana zubar da Hawaye tana Rusa Kuka Tace Dan Allah,Dan girman Allah ka yafe min,kayi Hakuri da abinda nayi maka wallahi Allah shine sheda Ina sonka....Ina sonka Ahmad....wallahi Kaine rayuwata,Ina sonka wallahi abinda na fada ba Haka ne a Raina ba na rantse da Allah ta karasa da kuka,Cikin hasala da karaji yace da kunne na naji, idan da wani ne ya fada min bazan yarda ba zaki Raina min hankali Get out bana kaunar sake ganinki,mayaudariya makaryaciya fitar min a gida,idan kika sake shugo min gida sai Kinga abinda Zan miki,tashi ki bar min gida,Tana durkushe tana kuka Tace Ahmad ka saurare Ni Dan Allah......Tsaki Yaja a Matukar hasale ya yo kanta ba shiri ta Mike ta fice da sauri tana ta kuka,Musa Yana kallo ta bashi tausayi,yace kayi Hakuri Oga Yarinyar ce akwai naci,Ahmad ya daka Masa Tsawa yace kai matar tawa zaka ce Mata me naci wallahi Zan sallameka a aiki,Shuru Musa yayi Ahmad ya fita Yana ta Fushi Yana Jin haushin Musa yace Aamna ce me naci,ya ja tsaki. Aamna kuwa tun kafin ta koma gida zazzabi me zafi ya lullube ta.