← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 89

Sashe 55

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mummy gaba Daya ta Hana Ahmad Zama Kawai abubuwa take sa shi,ko Daddy sau daya yaga Ahmad suna tare da Mummy suna shirye shiryensu shine dalilin da yasa Aamna taga Shuru sai dai suyi waya sau Daya kullum,hankalinsa gaba Daya Yana Kan Aamna amma Mummy da Daddy sun Hana suna can suna shirya Masa abubuwa,Kuma har su Jibson ake komai,koma Mene oho.
Ahmad ya gaji kullum Suka fita sai dare suke dawowa ranar da Suka cika 3days Ahmad da safe ya Iske Mummy a bedroom ta shirya tana jiransa zasu fita cike da shagwaba ya sameta Yana cewa Mummy Dan Allah yau ki barni naje wajen Aamna pls ko 5mnt ne,murmushi Mummy tayi Tace baza kaje ba sai ranar data tare idan Kuma ban Isa da Kai ba to,Fushi yayi ya zauna Yana jiranta ta Gama shiryawa Suka fita Mummy na cewa Dan iskanci Ana shirya muku rayuwa me kyau Kuna Iskanci kafi so a dinga baka kana kashewa kawai.
Daddy da shi aka je tsaida ranar Auren Jibson da Mashkoor,Shi Kuwa Brown tunda yaga Humaira Kanwar Ahmad ya nace Mata itama Humaira mugun sonsa takeyi dama ita Yana birgeta shima akwai Izza ga daukan wanka,Ahmad ne ya dinga Murna,Harda Kiran Humaira gefe zasuyi sirri.

Yace ke Dan na bawa Brown ke Kuma wallahi kika ce bakya sonsa sai na tattaka ki,sabo da Haka an kusa bikinki Kawai nine waliyinki,Humaira tana Dariya Tace Yaya Ina sonsa fa dama Kawai aji nake ja,Ajin banza mu mun fiki aji yarinya cewar Ahmad ki godewa Allah Zaki samu irin mu,Humaira tana ta dariya yace Kinga tuwona maina Kinga sai a kawo ki Nan Muna tare abinmu a kd, Humaira tana Dariya Tace ae.

Abban Jibson tunda yaga bazawararsa ya gigice duk kyan Ummati wannan ta fita ga daukan wanka ai itama matar Hajiya Rahinatu tuni Abban ya Mata abinka da Auren Manya ko sati ba ayi ba aka Daura Aure,tariya kuma sai ranar da Za'a kaiwa Jibson Amarya itama sai ta tare.
Shi Kuwa Abban Brown abokinsa ya samu a kasuwa ya fada Masa komai tsakaninsa da Yar China,shima ya dinga dariya,Abba Yaja kwafa yace Allah ka are min Rana na samu wasu makafin kudi Yaran Nan na nuna musu ruwa ba sa'an kwando bane naje Saudiya na auro balarabiya,Kuma a ka'aba za a daura auren,tunda sun tare matan kasar nan ko wacce sai su shike Nan suje da na Nan Ni Kuma Zan fashe haushi na da Balarabiya.

Mashkoor ma Ana ta shirye shirye da Nafeesat ma, Kamar yanda Malam yayi Alkawarin yiwa Jibson komai Haka yayi ya bawa Jibson kudade masu nauyi sannan ya bashi gida Kato kyauta me gate part biyu ne a gidan,Ahmad yace wannan gidan Jibson ya Bawa Abbansa su koma ciki tunda gidan su Jibson na Haya ne Kuma Bai da kyau ga yara,Jibson yace to tunda yasan Ahmad yace Haka to akwai shirinsa na daban,Haka ya fadawa Malamin surikin Mashkoor,Malamin yace duk yanda sukayi dai dai ne shi dai ya bashi kyauta,Haka Abba ya dinga Murna Yana sawa su Jibson Albarka,kannen Jibson murna Kamar zasuyi hauka,babu Bata lokaci Suka fara Kai Kaya sabon gida Ana tsara shi gashi Jibson da kudinsa ya zuba musu furniture masu kyau komai Shar shar cikin rufin asiri.

Tawaga Kuwa Son Yar China ne ya kamashi a hankali,gajiya yayi ya tafi fada Mata,Bayan yasha wanka yaje gidan,tana Jin karar machine Yar China ta fito da gudu tana Masa Sannu da zuwa sabo da gaba Daya sun Saba, ta daina Masa tsokana sai rashin ji sabo da yarinya ce,Tawaga Bai taba kula mace da sunan so ba,Kawai Yar China tana gabansa ya kalle ta yayi Mata irin ta Yan shaye shaye yace Kee....to ya akayi ne.....Yar China tayi Dariya tare da furta ya akayi Kuwa,Yace... to... ya ake ciki ne aehhh..... ko Baki gane bane aeee? Yar China Tace me Zan Gane? da masifa yace ke karki Raina min hankali mana ya Zaki min wani ae yane?.....Haba dalla yawa kike....Yar China ta sake tuntsurewa da dariya sai ya fusata tana Masa dariya Kawai sai Mari taji feesssss....ya fesa mata Mari,kumatu ta dafe tana kuka,a fusace yace Ni Zaki rainawa hankali kice Baki Gane me nake nufi ba ke dalla Ware ko na farfasa Miki jiki,Yar China da gudu tayi gida tana kuka shi Kuma a Nan ya tuna Bai kyauta ba,a fili yace me yasa Zan mare ta,can Kuma yace to Dan uwarta ya zata ce Bata Gane sonta nakeyi ba,machine dinsa ya buga ya tafi Yana ta masifa a hanya.

Ko da ya hau titin kwalta ma ko ya wani ya Masa overtaking sai zagi ya fara dura Masa ashariya yau Yar China ta Bata Masa Rai,Ko da ya koma wajen su Jibson yaje ya Basu labari yace Dan iskanci wai Tace Bata Gane ae yane ba,Yawa ta min Ni Kuma na kwashe ta da Mari,ya dan rainin hankali Ina Mata maganar ya ake ciki tana wani sharewa,su Jibson Suka dinga dariya Kamar me,Nan ma yaji Haushi.
Washe gari Haka ya koma da Yamma horn din duniya Yar China tana jinsa Taki Fitowa, Iyalle tana ta Mata fada taje Amma taki,gashi Tawaga son Yar China ya dame shi ai ya sake Danna horn sannan Yar China ta fito tana Fitowa ya kwada Mata Mari tare da nuna ta da Yatsa ke Dan kutmar....kina jina Ina kiranki tun dazu amma kika Shanya Ni? ai Yar China takawa tayi zata koma gida da kuka ya riketa caraf,juyowa tayi tana kuka ya kalle ta Itama Idonta cikin nasa da masifa yace kalli cikin kwayar Ido na...Yar China ta kalla sosai yace Baki ga wani Abu ba? Yar China tana shesheka Tace Naga kwayar idonka baka wuluk idonka fari tas,Ran Tawaga ya sake baci yace kalleni sosai Baki ga wani ae yane ba? Yar China Tace ban gani ba zata Yi Dariya yace Zan mareki wlh,Hannunta ya Kama tare da dorawa a kirjinsa yace Baki ji wasu kalmo mi na tashi ba? Yar China ta Kara sakin Dariya ya hade Rai sai tayi Shuru ya sake danne Hannunta a kirjinsa yace tun ranar da kika taba zagina a gate din makarantarku zuciyata take bugawa Haka,tana furta Miki kalamai,Yar China Bata kawo komai ba Tace Tsoro na kaji Kawai,ai idan aka ji tsoron mutum shine zuciya ke wannan bugawar,Yace na mareki ba Haka take nufi ba,wasu kalmomi take ta fada Miki tun ranar Amma bakya ganewa ke, Yar China Tace to me take cewa? Tace ki gano mana da kanki Yace cewa fa takeyi Ina sonki...Ina sonki.....
Yar China da yarinya ce sai ta dinga dariya Tace me zanci da ita Ina da tawa zuciyar Nima Allah ya min,Ran Tawaga ya sake baci kamar yayi me,Yar China Tace Ni wallahi Ina da tawa ta isheni rayuwa,Tawaga tafiya ya sake Yi ransa a bace.

Yar China ta shige gida tana ta dariya tana bawa Iyalle labari,Iyalle Tace ke shashasha ce Yar China ai nufinsa sonki yake yi,Kuma aurenki zaiyi Alhmdllh kinyi Dace jikata,Yar China ai sai ta tashi ta Kama rawa tana murgude murgude,Yatsa tasa a bakinta tana rausaya kanta Tace dama Allah Iyalle Ina sonsa gashi Dan gayu Iyalle kullum kamshi yakeyi,Iyalle Tace ai fa gashi kyakyawa,idan ya dawo kice kin Gane nufinsa kema kina sonsa,Yar China Tace Ni kunya nakeji wallahi Ina fada Masa Zan gudo gida abina,bangaren Tawaga ko da ya tafi gida da dare sake dawowa yayi zai fadawa Yar China Kawai Yana Sonta,Yana zuwa ta fito da gudu,yace bana hanaki gudu ba? Yi Hakuri Yaya,murmushin Jin Dadi yayi yace dazu Baki Gane nufina ba sonake na fada miki,Idonsa Tawaga ya rufe Kam tare da maida Kansa gefe ya karasa da cewa so nake nace Miki Ina sonki Ina kaunarki Zan aureki idan kin Aminc....kafin ya karasa ya buga machine dinsa ya Sha kwana,Yar China da mamaki ta daga Murya da karfi yanda zai ji ta Tace Ina sonka Nima Yaya,I love you Haka wata kawar mu take fadawa saurayinta Nima I love You....Baki ta cuno yanda ta tuno kawarta tana yiwa saurayinta a waya Wai kiss Tace Yaya Muahhhhh ...Tawaga Yana dariya da karfi shima ya Furta Yar China Nima Muahhhh.....
Yau Tawaga yayi kwanan farinciki su Jibson sun Sha labari,cikinsu Bash ne Kawai Bai da wacce zai aura,Brown yace Bash yayi kwantai jama'a a samo Masa tasa Bai kamata mu angwance ba shi ba,Tawaga yace tun yaushe ya likewa Kanwata Hafsat kullum suna tare ya hanata karatun kirki,da Hafsat a class itace ke daukan na Daya Amma tunda Dan Iskan Yaron Nan ya fara zuwa wajenta na Uku take zuwa yanzu,Bash Dake zaune ya dinga dariya yace ai kyaleku nayi ku Gama haukar ku Ina da gwana ta Nima.
Chapter 55 · 0% Book details