← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 89

Sashe 27

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata Budurwa ce tazo Tace Aamna nazo siyayyar,Aamna Tace to shugo,Budurwar tayi layin bra da panties ai Ahmad Yana ganin Haka sai ya juya baya tare da rufe Idonsa ruf har sai da matar Nan ta Gama zaba ta biya kudin ta tafi sannan ya Bude Idonsa,Dariya ya bawa Aamna Yana jinta tana ta dariya,yau ya Dade sai Yamma lis ya koma gida,sai mamakin Kansa yakeyi Wai Kamar shi shine zai siyar da citta,Yana kwance a palonsa yace gaskiya na Gama fadowa nayi asara wallahi,Kansa ya dungure yace kayi asara kai Kam Ahmad.

Wasa Wasa kullum Ahmad sai yaje ya Taya Aamna siyar da Abu har wurin sati Daya,gaba Daya su Mashkoor sun daina ganinsa,idan sun Masa waya ma zasu zo gidansa sai yace Kar suzo baya gida ya tafi Unguwa,yafi so ya zauna shi kadai yayi ta tunanin Aamna Yana Jin dadi,Kwaya da giyar da yake Sha duk ya rage ba sosai ba sabo da tunanin Aamna.
Yau kin zuwa yayi gaba Daya Bata ganshi ba har duba Hanya takeyi ko zata hango shi Amma Shuru duk ta kasa sukuni ta shiga wani Hali,gashi Bata da number dinsa Kuma baza ta iya cewa ya Bata ba.
Sai washe gari yau cikin wata maroon suit ya fito kamar a jikinsa aka dinka yayi kyau matuka 3pm yazo wajen,Aamna ta taso da sauri tana murna a ranta a fili Tace me ya hanaka zuwa jiya? Ya rasa me zaice zuciyarsa tsoro yake ji....yace...ahmm...karya yayi yace kaina ke ciwo jiya,Tace Eyya Sannu ya jikin? Da sauki ya furta tare da tsayawa a gabanta Yana so ya fada Mata me yake ji a ransa Amma ya kasa....yace dama Ina so muyi wata magana ne,akwai abinda nake so na fada Miki,Aamna tace Ina jinka tana ta faman kallonsa,kasa fada yayi ta Masa kwarjini sai ya waske yace kina cin kifi tarwada? Dariya ta kamata Tace sosai ma ai Ina sonsa ya,girgiza Kai yayi Murmushi Wanda ya tafi da Imanin Aamna,yace to gobe Zan kawo Miki da yawa ko yau kike son ci? Aamna Tace goben ma yayi,Yana so ya fada Mata shifa zuciyarsa ta kasa sukuni Amma ya kasa sai yace Zaki Zama kawa ta?Aamna ta kalle shi tace me zai hana,murmushi yayi yace to daga yau mun Zama kawaye ko? Tana Dariya ta Mika Masa Hannu sukayi musabiha Tace na Zama kawarka kaima ka Zama aboki na,yace ae dama Ina so na dinga shawarwari Amma Banda kawa,Aamna Tace Ina abokanka fa?Tsaki Yaja kadan yace ai Bama wani haduwa yanzu sosai,taji Dadi a ranta Tace to shugo ka zauna,no tafiya zanyi Ina da wajen zuwa yau,Aamna Bata so hakan ba Amma Tace to shike Nan sai goben,ya hau machine yayi tafiyarsa gidan Mashkoor.

Yana zuwa ya samu Mashkoor shi kadai, Mashkoor yace Kai me Zan gani yau Kaine da wannan shigar lafiya king? Kafadarsa Ahmad ya buga yace ba lafiya ba yanzu ma taimakonka nazo Nema,ku kawo min agajin gaggawa, ka tashi mu tafi gidana akwai magana,Mashkoor yace to,Giyar da Mashkoor yake kurba ita Ahmad ya tiltila a cup ya Sha ya sake Sha yace muje,a machine suka tafi gidan Ahmad.
Aamna tana so ta fada Masa anjima da yamma zata tafi Sokoto ganin Dangin Babanta Amma Bai zauna ba bare ta fada Masa Amma sunyi waya da Mummy ta San da tafiyar.
Shi kuwa Mashkoor Yana palon Ahmad suna zaune Ahmad yace kasan Kai abokina na ne Zan fada maka ne Kawai sabo da yanda muke da Kai,Kai kadai Zan fadawa halin da nake ciki,Mashkoor da muryar Yan kwayarsa yace Ina jinka King,Ahmad ya kwashe kaf abinda yake ji a zuciyarsa game da Aamna ya fadawa Mashkoor,Mashkoor tsoro ya kamashi Yaja da baya Yana tangal tangal a zaune yace Sarkin namu Guda ah'ah,Ahmad cikin rada yace Ina fada maka idan na ganta zuciyata sai naji tana wani kida tana rawa tana wani foli..fafo..lifo...fil...fil....dardariya Mashkoor yake Kamar me,yace ah'ah duk Kai kadai?

Ahmad yace Ina fada maka Dan uwarka Yana dukan kafadar Mashkoor kana ganin Wasa ne bafa Wasa nake ba kana wani Yi min Dariya Dan Iska Kawai wallahi zaka bar gidan Nan, Mashkoor yace na daina Ina jinka,Ahmad yace Ina fada maka ba sai naji Ina tsoronta ba,Ah'ah Mashkoor ya furta da karfi yace wannan Yarinyar da ko Nonon kirki babu? Duka Ahmad dirka Masa a baya yace be careful matata ce ba Budurwa ba, Mashkoor yace dalla ba so bane sha'awarta kakeyi Kawai kaje ka dakko ta ka lallabata kaci abinka ka barta,Wani dukan Ahmad ya kaiwa Mashkoor yace Kai dalla Ni ba wannan nake so ba,baka ganewa Ni Kawai nafi so mu zauna tare da ita idan Dan wannan ne zamu iya shekara Nawa da ita sai Sanda take so zanyi wannan fa ba Maganar Wasa bane,Mashkoor yace cab abin Babba ne asiri tayi maka,Haushinka taji daka koreta ta maka asiri.

Ahmad yayi Shuru,Mashkoor yace Zan taimaka maka akwai wani malamin Baban mu zamuje da Kai Nan take zaiyi maka Rukiyya a cire maka tunaninta ka dawo normal asirin data maka ya karye,Ahmad sai ya tuno layoyin Daya taba gani a Kan Aamna,yace Mashkoor kaima kayi magana tashi mu tafi wajen malamin Nan Yarinyar Nan Yar bori ce muje a gwada, Mashkoor yace yawwa kasan yanzu duniya ta canja Wai Yan Mata Dan masifa da bin malamai suna shirka suna tsafi akan maza,Wai mace taje tayi shirka Dan wani ya aure ta ko taci kudin wani,wata ta mallake Miji etc,kawaye sai su cika Mota suyi Kauye Wai an tafi wajen Malam akan wani ya aure su ko taci kudi,ko ayiwa kishiya da yaranta,shi yasa aure yanzu baya Zama Ana ta Yi Ana Sako Mata barkatai,duk macen data auri Namiji da asiri ta sani wallahi idan ya karye sai saki,yanzu shirka Kawai akeyi an ma daina cewa malamai sai bokan Kan dutse,mutane suna ta maida kansu arna Basu Sani ba.

Tafiya sukayi me uban nisa zuwa wani Dan Kauye,Wani dattijo kazami Ahmad ya gani,Mashkoor bayan sun gaisa ya Gabatar da Ahmad da abinda ya samu Ahmad,tsohon yace ku bada dubu biyar kafin alkalami,Ahmad ya zaro ya bawa Malam,Malam yace saura kudin Aiki dubu goma,Ahmad yace Aiki baiyi ba za a baka kudi? Dattijon yace Kai ka cika son kudin tsiya ka bada kudi a rabaka da masifa,ciwon so ai masifa ne,Ahmad yace Nifa ba soyayya nakeyi ba,nace maka tunaninta Kawai nakeyi,Ni nayi love Allah kiyaye, gashi nan yarinyar ta Gama kashe maka zuciya cewar malam,Ahmad ya bada dubu goma shi Sam da gani yasan karya ne wannan cin kudi Kawai zaiyi.

Saman Tabarma yasa Ahmad ya zauna,Bayan ya zauna ya Bude Qur'ani ya dinga karatu a Kan Ahmad Yana zaga shi sai da ya Dade sannan yace an Gama Alhmdllh Aiki yayi kyau kuje gida daga yau ka Gama da shafinta, Mashkoor Yana murna ya dinga godiya,Ahmad Baki ya tabe shi baiji canji a ransa ba,Sai dare Suka koma gida,suna dawowa wanka sukayi Suka ci abincin da Suka siyo a hanya,Ahmad ya kalli Mashkoor yace Mashkoor Nifa so nake yanzu Naga Yarinyar Nan,Da mamaki Mashkoor yace ah'ah Kuma dai? Yanzu duk aikin da Malam yayi har kanajin ta a ranka? Ahmad yace tashi ka rakani gidansu Zan haura katanga idan ban ganta bazan iya bacci ba yau dole sai naji muryarta ko na ganta,Mashkoor yace dare fa yayi ka duba lokaci 11pm fa,idan zaka rakani to idan baza kaje zanje Ni Daya,Dan kaga Ina fada maka sirrina zaka wulakanta Ni,Mashkoor yace muje Amma idan munje me zaka ce da su a wannan Daren me zamu ce? Ahmad yace muje Kawai,machine suka hau a daren Suka tafi Kamar mayu.

A bakin gate Suka tsaya tare da kwankwasa gidan,Baba ne ya fito Jin bugu yaki karewa Yana budewa tsoro ya kamashi ganin su Ahmad ya tabbatar giya suka Sha shi yasa Suka zo da wannan Daren yasan basa hayyacinsu,lafiya? Baba ya tambaya,soshe soshe Suka Kama Yi, Mashkoor yafi Baki shi yace dama...dama..munzo duba Aamna ne sabo da munji labarin Bata da lafiya,Baba yace sabo da kwaya ta gaya muku karya sai kuzo min gida a wannan daren? Kun firgita mu Ni da matata,to Aamna Bata Nan ta tafi Sokoto tun yamma dazu tace ta sauka tana can Dangin Babanta sai Nan da kwana hudu zata dawo,Kirjin Ahmad ya buga Kamar zaiyi kuka yau bazai iya bacci ba Matukar Bai ji muryarta ba,Baba zai juya yace sai da safe da Sauri Ahmad ya kalli Mashkoor ya Masa rada kace ya Bamu number dinta,Da sauri Mashkoor yace Dan Allah Dan Bamu number dinta Muna so muyi Mata ya jiki,Baba yace Wai uban waye yace muku Bata da lafiya fatan ba takura Mata zakuyi ba,da sauri Ahmad yace a'a Kawai Sannu zamuyi Mata,Baba ya Harare su sabo da Bai so Haka ba Amma sabo da kwarjinin Ahmad yace bani waya na sa maka,da sauri Mashkoor ya Mika wayarsa Baba ya sa Masa number a ciki Yace kuje garam ya rufe gidan,Ahmad ko a jikinsa sai murna Suka hau Machine suka koma gidan Ahmad.

A Palo Ahmad yace Kira ta awaryarka muji, Mashkoor ya kalle shi da mamaki yace da wannan tsohon Daren? Ahmad yace Dan Allah ka kirata naji muryarta Ni bazan iya Mata magana ba zuciyata bugawa takeyi,kayi magana da ita kasa a handsfree idan naji muryarta shike Nan Zan samu nayi bacci yau,Amma Matukar banji muryarta ba yau bani ba zaman lafiya, Mashkoor yace abin har ya Kai Haka mun shiga uku?Tsaki Ahmad ya ja, lokacin Aamna ta kwanta ta fara bacci taji Wayarta tana ta Kara,dubawa tayi taga bakuwar Number

AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYA TA AAMNAĪ)\Ī)\

46-50

FREE PAGE

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

MASU SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

RUKEY MUAZ
LEEMAT
~-
MINERH
KHADIJA DANDAWAKI
HUMAIRA MUHAMMAD
AMINA ADAMU USMAN
Chapter 27 · 0% Book details