← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 89

Sashe 39

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aamna ita da hankalinta yayi nisa hannayensa ta rirrike tana Wasa da su Tace ka kwana Mana,Dariya ta bashi yace ke ki dawo Mana Ni na kwana a Nan so kike baba ya saka speaker ya sanar layi layi,Kuma ma ai Bai kamata ba,Aamna da shagwaba Tace to Mene a ciki ai Zan dawo ne akwai shirin da nakeyi,yace to Allah ya kaimu ki Gama shirin Amma bazan kwana ba,murmushi tayi Tace to muje na rakaka,Hijab dinta ta saka har kasa Suka fito ta rike Masa Hannu suna zuwa Palo ya zame hannunsa yace Baba ko Mama,Wai Ni ba matarka bace? Yace to kinfi so na musu rashin kunya Dan kina matata,Nifa nazo har gidanku,Bayan dakinki Dana Shiga duk Bai Isa ba so kike Baba ya dinga cewa Ni Dan bariki ne kina gani yanda Suka sa min Ido Ina shaye shaye ko ya nayi Abu zasu ce ai Ni Dan kwaya ne, Kuma dai ai su suka rike ki sune Iyayenki idan da Kara,karki Yi amfani da Suna takura Miki kiga Kamar Basu da hakki a kanki idan kika musu ba dai dai ba sai Allah ya saka musu,shi Dan Adam kowa akwai halinsa na banza Dana kirki Dole ne,so Dan Adam ne zai Iya kuskure,abinda yasa ban matsa sai kin dawo ba sabo da tun farko Ni na matsu sai kin bar gidana laifi nane.

Aamna ita dai mamakin Ahmad ya Gama kasheta wannan irin nisan hankali Haka Ana kallonsu a banza Ashe Dan baka zauna da su bane,gaskiya a daina zato da zargin banza tunanin da suke da shi Wanda basa Shan komai Basu Isa sunyi irinsa ba,ba kowa bane hakan, sai da suka fito zai tafi ya sake Rungume ta sannan ya hau Machine dinsa,Hannu ta sake Mika Masa Suka gaisa sannan ya tafi abinsa ya bar Aamna da sha'awarta da tunaninsa duk da cewa shima bangarensa hakan take.

Washe da Yamma 5pm gaba Daya su Jibson suna gidan Mashkoor har Ahmad,Jibson ya Sha wanka cikin farar Shadda kamar wani Ango Suma ta Sha gyara harda tsira wata hula Kalar Shaddar da Takalminsa,Sumarsa gata Nan ta baya da gefe da gefe me yawa,dinkin me dogon Hannu links ya zuba Uban kyau,Bash Shima yasha wani yardi Silver ya tsula kyau Dake Dukkansu babu mummunan sai hasken fata wani yafi wani haske Haka suke,Bash shine Dan rakon zance, duk sun Sha manyan Kaya kamar ba su ba Machine Daya suka hau Suka tafi,Tawaga yace Allah ya bada sa'a,Address suka bi tiryan tiryan har zuwa Kofar gidan su Sameera,gidan da gani gida ne na rufin asiri,yaro Suka tura zuwa gidan ya Kira musu Sameera,Sameera Bata San su waye ba,tana zaune Umminta Tace Jeki ki gani mana,Sameera ta saka Hijab dinta har kasa ta fito,Daga nesa Suka Kare Mata kallo Jibson yace wannan ai yarinya ce Bata fi sa'ar Aamna ba wannan ba ita bace sai dai ko Yarta ce ta fari,karasowa tayi inda suke tare da Sallama Suka Amsa Mata,Bash ya kalleta a ransa yace wannan chocolate kyakyawar Budurwa itace Baban Brown zai aura? Kai karya ne.

Kallonta yayi yace ke Mamanki Zaki Kira Mana Muka ce ba ke muke Nema ba,Sameera Tace ban Gane ba? Ai Sameera akace tazo ko? Jibson yace ae kwanon cin Abinci ba,wata bazawara wacce mijinta yayi hatsari ya mutu tana da Yara biyar,Sameera ta zaro Ido Tace to ai nice,Kuma Ni ko Yaya bani da ita sannan Ni yaro Daya na taba Haifa Kuma yau sati Uku ma da rasuwar Yaron,Jibson a ransa yace Allah raka Taki gona Daya mutu,yace malama Sameera ke wacce irin Sameera ce me Hannun karfe ce ta yayi ko kuwa me Hannun Roba ce? Matashiya Sameera ta kalle su tayi dariya da farko Bata Yi Niyyar kulasu ba Amma dariyar da Suka Bata yasa Tace Hmmm Kawai.

Bash ya gyara tsaiwarsa yace da farko dai Ni Sunana Bashir shi Kuma babban me kaunarki Wanda yayi zurfi a cikin begenki sunansa Jibril abokina nane,Muna Unguwar Rigasa a Nan garin,Kamar yanda kika ganmu mu talakawa ne sai rufin asiri babu karya a tsarinmu,nasan ku Mata Kuna kaunar Mota to Allah Bai hore Mana ita ba,idan Za'a so mu a so mu Dan Allah yawwa shine magana kawai, Jibril ya Dade Yana kaunarki tun kafin kiyi auren fari cikin rashin sa'a mirgayi tsohon mijinki Allah ya Masa Rahma yayi Mana shigar sauri,Jibson yace ai shishigi ma yayi Mana da katsaladan ya aureki Ni nasan Rabo na ce ke shi yasa Allah ya karbi rayuwarsa,Sameera taji wani sanyi Haka Kawai taji sun Shiga ranta musamman Jibson,Tace Ni kaga shekarata 25,bayan na Gama Diploma aka min aure na Haihu Daya cikin hukuncin Allah Mijina yayi hatsari ya rasu,Yau kwana goma da Gama Takaba ta Kuma Yaron ya rasu shima sanadiyar cutar Malaria,Jibson Kamar mutumin kirki yace Kash banji Dadi ba Danmu ya rasu Allah yaji kansu,Kai Bash laifinka ne Kai da kake yawan zuwa Unguwar Nan ya kamata ka sanar Dani,Bash yace Nima banji ba sai yanzu,na San dai rasuwar Mijin nata.

Jibson ya kalli Sameera ya furta Sannu kinyi rashi Rasuwa irin ta hatsari ai ba Dadi,Sameera Tace wallahi na Gama abincin Rana kenan naji Ringing din waya,Jibson yace Uhmm Ashe bakar waya ce,Tace Wlh sai sanar min akayi sai da hantar cikina ta kada,yace Allah ya taimakeki Bata hada da koda ba sunyi gware da shike Nan kema,Dariya ta Kama Sameera,Jibson yace ai Nigeria Sam Bata Yi ba,Bamu da hanya me kyau ga mutane suna tukin ganganci suna kashe Al'umma,mutum yasan motarsa ba lafiyayya bace sai ya lodo mutane ciki ya kashe su,Ni kwata kwata wallahi banji Dadin yancin kasar nan da amurka ta Bamu ba,gwara da ta Hana mu yanci munyi zaman mu a Hannunta da tuni munfi Haka ci gaba,Bash yace ai da Muna Hannun America da yanzu Sunana George,Jibson yace Ni kuwa bazan wuce Jack ba,Baba Kuma ko Harry kaja Jack Harry,Sameera ta dinga dariya Tace Ni Kuma fa? Jibson yace ai baza ki wuce Selena ko wata Eliza ba, Sameera Tace sai ma idan kanajin turancin Tafawa balewa ranar da aka karbi yanci Yana wani Wai the.... political.... independent.... Nigeria is Inadequate....

Su Jibson suka Kama Dariya yace lallai kin rike turancin nan,...yanzu dai Ni da gaske aurenki zanyi sonki nakeyi,kaunarki ta Gama ratsa Ni,ya kike gani? Sameera tace Uhmmm to dai zanyi tunani,Ko wani tsohon ya kasa Ni? Sameera Tace akwai dai wani Abokin Babana da Abba yake so na aura,Ni Kuma gaskiya Bai min ba,Yana Nan ance Dansa ma yayi Kamar ku Banda sauran Yara, Kuma Ni gaskiya Bai min ba,Kakar mu ta yanke saka,wannan da gaske yake a shirye yake da aurenki idan kin Amince cewar bash,Sameera Tace yanzu bazan yanke hukunci ba sai dai Nan da kwana biyu,Jibson yace ba damuwa yanzu Bamu number dinki,Nan take Sameera ta bashi number suka Yi exchange,Sameera Tace Kuma tsohon ma yaransa da matarsa sun tsaneni har karya aka fada musu Wai Haihuwata biyar Zan tafi musu da Yara gida,Jibson yace to ke kinfi karfin Babansu ma rabu dasu,Kamarki me zakiyi da tsoho,Nan suka tsaya suna ta zance Sameera Basu Dade ba ta Saba da su sannan Suka tafi.

Bayan wasu kwanaki Ahmad ya fara rage shaye shaye Sam yanzu sai ya kwana biyar Bai Sha komai ba sabo da ya birge Aamna sannan Yana yawan samun Sallah a jam'i,gashi yanda yake dawainiya da Aamna kome take so zaiyi.
Yau Tace zata kawo Masa Ziyara,sai murna yakeyi yasa Musa ya sake gyara ko Ina na gidan harda daukan wanka yasa wasu Riga da wando marasa nauyi rigar armless me hula,ya sauke hular a bayansa,Yana kwance a palo sai Sallamarta yaji tare da shigowa gaba daya,ta zuba kyau cikin rigunan da ya Siya Mata ta Sako Maroon Gown ta tsula kyau, Mikewa yayi tare da rungumeta tana murmushi tace muje kitchen please ka koya min Jullof din Nan,Fuska ya yatsina tare da Furta sai Sanda kika dawo gidan nan,Zama tayi a gefensa tare da kwantar da kanta a kafadarsa,Hannu yasa tare da kwantar da ita a saman cinyarsa,Kansa ya sunkuyo zuwa kumatunta Kiss ya manna Mata a kumatu a hankali ya Kira sunan My world? Na'am ta furta yace Ina so naje Lagos gida zanga Daddy da Mummy,Murna Aamna tayi sabo da ita Bata San ya rage shaye shaye ba,Sallar ma Bata san Yana zuwa Masallaci ba,Kuma gashi Wai zaije gida wajen Mummy,tunda suka dawo kasar nan Bai taba zuwa wajensu ba ,sunyi sunyi har sun gaji Wai abin mamaki yau shine zai je da Kansa,Aamna Tace wow gaishe su zakayi? Yace ae sannan Zan musu magana a kanki,Aamna Tace ya kamata ka karbi aikin da Daddy yace kaga sai ka dogara da kanka,Murmushi yayi Yana Wasa da wani botin din rigarta yace a'a Ni anan Zan bude wani Abu? To wacce sana'ar zaka Yi? Yace Resturant Zan bude,Dariya ta dinga Yi shima Haka,yace bazan Iya barin garin Nan ba sabo da abokaina,yanzu ki shirya muje Lagos tare muyi 3days,Kafada Aamna ta noke tare da furta ka fara zuwa Kai kadai Ni Nan gaba Zan bika muje,Aamna a ranta tasan ba Zama zatayi wajensa ba baza taje ba,Shi Kuma Bai kawo komai ba yace to ba damuwa zanje sai na dawo,gobe Zan bi flight,Tace Allah ya kaimu

Hannunta ya rike tare da janta kitchen,Suna Shiga ya dauke ta tare da daura ta a sama kusa da Sink,hannayensa bisa cinyoyinta yace Zan fara girkin kina kallo kinji,Kallonsa takeyi ba ji ba gani Wani Farin ciki takeji,Jikinta ne taji Yana wani yam..yam,Yana magana Amma shi take kallo,a hankali ta matso da fuskarta saitin tasa da Niyyar Masa kiss har ya wani lumshe Ido da sauri ta dawo hayyacinta sai ta fara wayancewa tana dariya,Sharewa yayi shima ya fara girkin,ita Kuma tana ta faman kallonsa,Sai da Yamma ta ebi abincin a flask ta tafi da shi gida Wai yayi Dadi.
Chapter 39 · 0% Book details