Sashe 35
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aamna kwana biyu taji Shuru sai Kawai Tace Bari na bashi mamaki,5pm ta fito ta Sha uban wanka cikin wani Fari da bakin material cikin na lefenta me kyau da tsada yasha uban dinki Kamar Readymade,tayi kyau kamar a sace ta,Takalminta me tsini da jaka bakake,Mama Tace Ina zuwa Haka? Karya Aamna tayi Tace gidan wani bikin kawar mu zamu je da Siyama,Baki Mama ta tabe tare da Furta shine harda uban gayu Haka idan wani ya tareki a hanya yace Yana sonki fa? Shuru Aamna tayi Tace sai na dawo tayi waje,Already me Napep din data Kira Yana jiranta a kofar gida,Shiga tayi Suka tafi,a bakin gate din gidan Ahmad aka ajiyeta Aamna ta Shiga buga gidan,me Gadi baya Nan shi yasa Ahmad Bai fito da wuri ba,taci sa'a Yana gida,Sanye cikin black jean pencil da Riga t-shirt me gajeren Hannu wata ruwan toka ta Yan birni,Yana Gadara ya fito ya Bude kofa,ai mamaki yasa ya tsaya cak,Farin ciki ya lullubeshi,yace wow...My World.....oh....ya juya Tare da tafiya yayi Yar safa da Marwa yace ya akayi Baki ce min Zaki zo?Murmushi Aamna tayi Tace Surprise...kallo ya Kare Mata tare da furta Ohhh.....kinyi kyau Beb....duk wanka nane? Aamna Tace ae Mana,Hannaye ya Bude tare da Matsawa ya rungumeta kadan yace Sannu da zuwa,Yawwa Aamna ta furta tana Jin kunya tana murmushi.
Yace Feel free gidanki ne fa shigo ciki,ta na shigowa yace Yi Hakuri Bari na rufe gate duk ya rasa inda zai sa Kansa,Yana Rufewa ya dawo da sauri ya Sha gabanta Yana tafiya da baya da baya Yana cewa kece a gidan Nan yau? Kika zo wajena Kai yau kin Gama min komai My world,Dariya tayi shima yayi Dariya,Tsayawa tayi cak shima ya tsaya suna facing juna,tana Dariya Tace Ka nutsu karka Fadi,yace idan na Fadi a kanki wani Abu ne? Idan na Fadi ma Sai na tashi ai kin cancanta a Fadi a kanki,Rigarsa ya cire daga shi sai dogon wando,surarsa ta bayyana,Aamna a ranta Tace gaskiya Namiji ne,wow kalli jikinsu sumulmul,Da rigarsa yayi amfani kafin Aamna ta taka waje Sai ya share Mata hanyar da rigarsa Haka suke ta tafiya Yana cewa My World yana ta murna, Aamna tana ta dariya har Palo Suka shiga da sauri yasa rigar ya sake goge Mata saman kujera sannan yace to zauna,Zama tayi ya tsuguna a gabanta tare da daura Hannayensa saman cinyarta yace me Zan kawo Miki My world? Aamna Tace koma Mene,Alright ya Mike tare da daukan hanyar kitchen,har ya tafii sai ya dawo yace karki damu kinji yanzu zanzo,to Tace ya fada kitchen,abincin Daya dafa dazu Jullof rice ta Sha Vegetables da nama ya kawo Mata a plate tare da ruwa da lemo.
Plate dinma Kalar Design dinsa shape din zuciya akayi sosai ,Zata Bude abincin yayi saurin dakatar da ita ya Bude tare da nuna Mata plate din taga shape din love ne,Dariya tayi Tace wow....gefenta ya zauna tare da tsiyaya Mata lemon da ruwa a glass cup yace oya eat,Spoon ta dauka ta ebo abincin taci taji Dadi sosai Tace wow wannan Dadi Haka,Murmushin Jin dadi yayi Yana kallonta tana ta ci da sauri da sauri sabo da ya Mata Dadi,Santi ta fara Yi Tace Kuma Kai ka dafa? ae Mana ai kin San Ina girki na Iya, Aamna Tace gaskiya ne ta ebo a spoon ta Kai bakinsa Tace kaima ci mana,ganin ita zata bashi da kanta ya Bude bakin ta zuba masa,Bakinsa ya kulle Kam tare da fadawa saman kujerar ta baya ya kwanta flat Wai zata kashe shi da love,tana ta dariya yace Hannunki zai kasheni sai abincin ya Kara wani dandano,Mikewa yayi tsaye yace Dole nayi celebration Yana zaga palon Wai duk murna ce ta bashi abinci a Baki.
Sai da ta Gama ci ya kwashe kwanikan ya maida kitchen ya dawo tare da Zama a gefenta,birgeta yayi sabo da yanda ba ruwansa da jikinta ya nuna ba jikinta yake so ba ita yake so, Gaskiya Zan dawo ka koya min irin girkinka,tagumi yayi tare da zuba Mata Ido Yana ta kallonta Yana murmushi,tafin Hannunta ta saka tare da rufe fuskarta tana Dariya tana cewa Wai Mene na wannan kallon haka? Hannunsa yasa cikin slow dinsa ya cire Hannun data rufe fuskar yaci gaba da kallonta, kafadar sa ta ture gefe cike da shagwaba yace Ni ki kyale Ni na kalli abuna...,Ci gaba yayi da kallonta kamar Yana Gaban tv ya sa yatsa ya taba Hancinta,ya taba girarta,Murmushi tayi tana Wasa da yatsunta,Mikewa taga yayi Zumbur kamar zaiyi duka ya daki Center table da hannunsa yace idanba sai na kwana Ina kallonki ba kafiri nake,ta sheke da dariya,Yana tsaye a gabanta ya Dan zaga kujerar da take zaune yace kutmar an Gama kure karshen kyau,ke Zan Iya mutuwa idan na rasaki,Aamna ta Bude Baki ya Buda hannaye Yana tsaye a gabanta yace da gaske Hmmm,da sauri ya koma ya zauna ya girgiza kitsonsa,Aamna tana kallonsa Yana ta Bata Dariya,tunani ta Lula da manufar data Amince sai taji tausayinsa,Hannunta ya rike tare da Tambaya My World me yake damar min ke? Murmushi ta kakalo Tace ba komai Kawai na tuna Abu ne,Okay Amma Bai Kamata Muna tare kina tuna wani Abu ba ko? Kai ta daga Masa tare da jingina da jikinsa ta kwanta tana lumshe ido,ita dai tana mamakin su Ahmad tsafta iya tsafta duk cikinsu kowa Dan gayu ne,a ranta Tace sai Hali yazo Daya ake Abota.
Bacci zakiyi ne ya tambaya? Kai kawai ta daga Masa yace ai yakamata kiyi Balance Beb ya fada da Dan karfi sabo da su maganarsu kusan basa yinta a hankali sai sunga dama ko ansha me sa Slow,Saman doguwar kujerar ya zauna tare da Mike kafafunsa sosai ya Kuma ya Bude su sannan yace to kwanta,ta baya ta kwanta sosai a jikinsa kanta Yana saman kirjinsa,Hannayensa yasa ta cikinta ya rungumeta,tana ta baza Ido taga ko ta saman Kirjinta zai rungumo hannayensa Amma Ina sai taga cikinta ya Rungume,a kunne ya rada Mata yace My world me kike so? Ba komai ta furta gaba Daya jikinta ya mutu wani Iri take ji a jikinta gaba Daya sha'awarsa take ji,ta rasa me yasa ko ya zai taba ta ko ya matso daf da ita sai taji gaba Daya hankalinta Yana Neman guduwa daga jikinta sumamman kamshinsa,shi Kuma yaki ganewa ko romancing dinta yayi,a ranta wata zuciyar Tace to Ina ruwanki da Romance dinsa ke da ba sonsa zakiyi ba canja shi kawai zakiyi.
Duk da Haka kasa sukuni tayi sai mutsu mutsu takeyi,tayi mikar ta sake yin Mika Amma ina,Kara tayar Mata hankali yayi yanda yake ta Mata rada a kunne Yana cewa mene ne ko Baki da lafiya ne? Kince zakiyi bacci Kuma sai mutsu mutsu kike yi ko bakya Jin dadin kwanciyar ne? Aamna Tace ae Ni canja kwanciya zanyi,yace to a ya kike so ki kwanta Kuma? Aamna Tace Ni irin kwancinyarka zanyi ta ruf da ciki,Dariya ma ta bashi yace a jikin nawa? Ae ta furta yace to ai ko me kike so,Juyawa Aamna tayi suna facing juna sai ta lalace a kallon kyawunsa kuma,Sajensa ta taba ya matsar da Fuskarsa gefe tare da rufe Ido yace kunyarki nake ji,Badan kece kika taba sajen Nan ba My world ai da wata ce yau idan na dinga dukanta a gidan Nan sai ta Gane Allah Daya ne,kin San ba karamin raini bane mace ta tabawa namiji gemu da Aljihu,Dariya ya bawa Aamna Tace akan gemun? Yace kin San Nawa yake ci kuwa a kullum? Aamna Tace a'a yace to a bar kaza cikin gashinta kawai, tsokanarsa Aamna ta sake Yi taci gaba da tabawa tana shafawa ta ja kadan,Yace Hmmm kiyi ta yi ai yanzu kin rainani wuyanki ya Iska yanka,Su Jibson ne suka banko kofa tare da shigowa gaba Daya.
Wani Kara Suka saki, Mashkoor ya koma jikin kofa ya manne a jikin Kofar ya riketa Gam Yana me Zan gani,Jibson ya murza idanuwansa yace tare da dafe kirji ya Nuna ta da Yatsa yace daga Amsar soyayya shike Nan har anzo Nan wajen? Yanzu abin har yayi nisa yazo Nan kwana Uku kacal? Baki Aamna ta bude tace Ina ruwanku Wai ba mijina bane budurwarsa ce Ni da zaku ce Iskanci mukayi? Tawaga yayi mahaukaciyar Dariya yace ke Aunty Balaraba karki zo ki lalata Mana Oganmu baya kula Mata shi,dama kin jawo ya shiga wani Hali a Kan sonki wallahi kika ci amanarsa sai mun soke ki da mashi, ki kula ba'a Wasa da mu,mun San halinku mata, Mashkoor ya galla Mata Harara yace Bamu shirya Haihuwa yanzu ba,mu ba yanzu zamu Tara Yara ba sai mun Gama inganta rayuwarmu yawwa,Aamna dama ta Saba da iya shegensu Tace matsalarku ce ta maida hankalinta Kan Ahmad,Ya kalli su Tawaga yace ku koma Daya palon Kuma idan kuka sake Mata magana anyhow zaku sani,Baku da hankali She is My Woman fa,Yi Hakuri master an daina daga yau Dariya sukayi da murmushi Suka kalli Aamna Suka ce Sannu Aunty Balaraba Allah ya Kara girma ayi Mana afuwa,Ahmad ya koma kallon Aamna suna ganin ya daina kallonsu suka dinga gallawa Aamna Harara suna Jin haushi Dan su Basu yarda da Mata ba mayaudara ne zata yaudari abokinsu,daya palon suka koma.
Wurin Magrib Aamna Tace tafiya zanyi dare ya fara,Fuska ya bata Yana Zaune ya saki wani jiki Yana ta shagwaba kamar Yaron yaye ya turo Baki gaba Yana wani motsa Kansa yace Ni ban gaji da kallonki ba idan kika barni Ni kadai Zan Zama......sai ya canja muryar Yara Kuma da Waka yace Lonely....... Lonely.....oh....lonely.....Dariya Aamna keyi kamar sabon kamu,Tace kasan Mama zasu min fada fa...lokacin Mashkoor ya fito zai dakko lemo yaji abinda Aamna Tace karaf yace wannan Yafi Mama power a kanki ko a wajen Allah Shi yake da iko a kanki ba wata Mama ko Baba ba,kin Gama Raina shi Yana aurenki ki dawo gidan Mana idan gaskiya kika kulla a ranki,Ahmad ne ya cire ta kalminsa da sauri ya wulwulawa Mashkoor zai kwada Masa, Mashkoor ya goce takalmin ya Fadi a kasa,Tafiya yayi da Niyyar cin uban Mashkoor Amma Mashkoor ya gudu wancan palon,Tsaki Yaja yace yi Hakuri muje na ajiyeki a gida to.