Sashe 32
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mikewa tayi tsaye tana Masa Murmushi Tace Kaine ka gyara min halaye na,kaci ubana da yawa sai lokacin na Gane Allah Daya,a hankali yanda baza taji ba yace ai Nima yanzu uban Nawa kike ci na Zama wani banza,Bakinsa taga Yana motsi Tace me kace? Cewa nayi Ni ba abinda na Miki kece kike min shishigi,Siyama ce tayi Sallama gabanta ya Fadi ganin Ahmad da Aamna a tsaye daf da juna kamar zasu Rungume juna,Fuska ta Bata tana Hararar Ahmad sabo da kishinsa,ita ba hassada takewa Aamna ba Kawai son Ahmad ne yayi tasiri a ranta taji dama ita ce.
Laaa Siyama kinzo cewar Aamna,Ahmad juyowa yayi Amma ko kallo Bata samu daga gare shi ba ya maida hankalinsa cikin Shagon,Nan Siyama ta shige ciki ta zauna tana satar kallon Ahmad,Ledar dake gaban Aamna take ta faman kallo taga kamar Abu na motsi ciki,Ahmad ganin tana ta kallon Ledar ya tabbatar Aamna sai tabawa Siyama kifin Nan itama ko su raba tare sai ya leka Daya shagon ya Kira wani yaro Wanda Ahmad yasan Yaron kusa da gidan su Aamna yake ganinsa shima gidansu makwafta ne,Yaron Yana zuwa Ahmad harda shafa Kansa yace Dan magyatso kasan gidan su Aamna? Yaron da Ahmad ya Masa suna da Dan Magyatso yayi dariyar sunan sabo Yaron Kalar yunwa ne,jikinsa tsilili cikinsa Dan kato sabo da Almajirin gidan Wasu ne a kusa da gidan su Aamna,yace ae nasan gidan Ina shiga ma idan an aikeni,Ahmad yace ka iya machine? Yaron yace sosai ma ai Ni nake yo cefane a machine din gidan Uwar dakina,Good cewar Ahmad yace ungo key din machine Dina jeka gidan su Aamna ka kaiwa Mama sakon Nan kace gashi inji Aamna,Yaron yace to ya karba ya hau machine din Ahmad ya tafi,Siyama ta so ace ta karbi kifin ko Quarter ne itama taje gida sun Sha farfesu Amma tana kallo Ahmad ya dauke Dan mugunta.
Tunda Siyama ta Shiga shi ya fito ya tsaya a waje,Aamna Tace ka shigo Mana yace a'a Machine Dina nake jira tafiya zanyi,Siyama ta kalla tace ina zuwa kawata ta fito Wajensa suka tsaya,tana ta Kallonsa a ranta tana ayyana irin kyansa,Shi kuwa ganin tana kallonsa harda Kara gyarawa Kamar za a dauke shi hoto,idan ta kalla ta kalla sai ya sake canja style din tsaiwarsa Haka yake ta Mata ya tafi da hankalinta sai daga baya ta lura da abinda Ahmad ke Yi Yana ta canja style din tsaiwa,Dariya ce ta Kama Aamna ta danne kadan tayi Murmushi Kansa ya shafa tare da mazewa kamar ba shine yayi ba,Hannunsa Aamna ta rike ya Janye hannunsa da sauri,Aamna tace lafiya? Kitsonsa ya Sosa yace ba komai Kawai Ni ba a taba min jiki kin sani ko kin manta ne?
Baki Aamna ta tabe Tace daga an Dan rike maka Hannu sai kace Dan gwal? Yace ai nafi gwal Ni,Harararsa tayi a ranta tace Dan ma na Dan nuna Masa caring shi illarsa Bai San arziki ba,Ganin ta harareshi yace Jaraba tare da miko Hannun yace ungo cinye shi ki huta,Bige Hannun tayi tana Dariya Tace bana so,Suna Haka Yaron ya dawo da Machine din Ahmad ya karba tare da bawa Yaron dubu biyu,ya dinga Murna yana godiya,Ina Handbag dinki? Ahmad ya tambayi Aamna.
Tana ciki yace dakko min ita,me zakayi da ita Fuska ya Bata yace ki dakko Mana Ni ba Mudubi ko powder dinki Zan gani ba nasan ku ba Uwar komai a jaka sai Kuna boyeta,Dakkowa tayi tare da Mika Masa yace Bude abarki ki rufe idonki Kuma,Aamna ta zuge jaka ta rufe ido,ganin Haka Siyama ta leko tana kallo Ahmad ya zaro kudi masu yawa Yan dubu dubu ya zubawa Aamna a jaka yace to Bude,Bude Idonta tayi taga kudi dama Bata da kudi tayi broke Bata da ko sisi gashi tana son siyen abinda ba a rasa ba na bukatar rayuwa,taji Dadi sabo da ya Bata lokacin da take bukata Tace Na gode Allah ya Kara budi Amma sunyi yawa kamar,Kansa ya dauke yace na tafi Mummyta ta aikeni tun dazu wani waje zanje na Mata Abu,Aamna Tace Kai dai kana son Mummy kullum Mummy,ai Mummy ta daban ce,Mummy na tafi Mummyn kowa cewar Ahmad,Aamna Tace Nima tawa tafi ta kowa,Murmushi yayi yace kin nemi Number Abbanki kuwa? Aamna Tace me Zan Masa tunda ya manta da ya auri Uwata ya Kuma haife Ni idan na karba me Zan Masa?
You are not Serious Haka aka ce Miki Iyaye suna laifi?Shuru Aamna tayi Watarana tana mamakin Hankalin su Ahmad,gasu dai suna tafka abin tsiya sai Suna Abu Kuma na basira da hankali, a fili tace Suma Yan Uwan nasa Dana je Sokoto nace su bani number dinsa Suka ce wallahi wurin shekara Uku kenan duk sun kasa Samunsa sai dai suna Kiran Yan Uwa na can kasar sunce yana Nan lafiya Kawai dai yanzu yayi retire a aiki Bai da aikin Yi ga Yara da Mata sun Masa yawa wahala ta kamashi,Ahmad ya girgiza Kai yace tab nasan yanzu ya sake kanjamewa Allah Sarki Abbinki,Aamna Dariya ya Bata ta bigeshi a kafada kadan Tace Wai Mene Haka ka dameshi Akan ramarsa, Murmushi yayi yace Bai yuwa ya rasa waya sai kace a Nigeria ai can ba a wannan talaucin, Ni Zan nemo Miki number dinsa,Aamna Tace Okay thanks, Machine dinsa yayiwa key tare da tafiya abinsa.
Siyama tana zaune ta kumbura tayi fam kamar ta fashe tace ke dai Aamna kinyi asara,wallahi Baki da hankali to wannan abinda yake nuna Miki ba so bane,Kar ma ki yaudari kanki Ahmad bazai taba shiryuwa ba ko jiya naje wajen Jibson a club Suka kwana suna shaye shaye suna rawa,Aamna Tace karya kikeyi Siyama wallahi Ahmad baya rawa,Yana Jin kida Yana bin Waka Amma in Banda ya Dan kada Kansa ba abinda ya taba Yi na rawa,Da kike cewa bazai shiryu ba kece Allah,Ina ruwana da Club dinsa,Siyama Tace Iyye to Bari kiji idan Baki sani ba Neman Mata suka koma Yi yanzu,kije ki tambaya Ahmad lallabaki yakeyi ki saki jiki da shi ya samu biyan bukata,Aamna Tace karfa ki manta Mijina ne,ko ma me yayi Hakkinsa ne ko ciki ya min akwai me zagina a duniya? Wai me yasa kika tsani Ahmad Haka ne Siyama? Siyama Tace sabo da Ina sonki kawata Ina kaunarki bana so ki fada wani Hali,Aamna tayi shuru....Tace to yanzu me kike so nayi? Karki bashi dama Kawai Kuma karki yarda da shi karki Bari Zuciyarki ta fada sonsa cutarki zaiyi,ki kiyaye Aamna bana so na ganki cikin wani Hali,plan suka hada Miki,Ahmad tun Yana yaro kangararre ne a Haka ya girma a tunaninki dare daya zai shiryu sabo da ke? Kiyi tunani fa,wanne duka da wulakanci ne Baki Sha ba a Wajensa? Ai Ni nake tsokanarsa Aamna ko a lokacin Ni ke shiga harkarsa da ban kulashi ba babu abinda zai min,Siyama tayi Dariya Tace kina Abu kamar yarinya 25yrs Sam Baki da wayo Baki da hankali Ni Naga wani Tsoronsa kike ji ma kina wani biye Masa,Dan giya irin wannan Dan kwaya abin kyama cikin Al'umma mutanen da Basu San darajar kansu ba bare ta wani Nan fa Siyama ta dage ta dinga zuga Aamna tana fada Mata karya,har ta Gama sannan Aamna Tace Ni fa bazan iya wulakanta shi ba,Kuma bazan iya masa komai da zai Bata Masa Rai ba,Kawai dai nasan bazan Bari na fada sonsa ba,ko cewa yayi Yana so na Zan Amince Amma badan so ba Zan Amince Dan nayi kokari na canja shi ya dawo mutum Kamar kowa ya daina wannan shaye shayen shine Kawai abinda Zan iya Dan na taimaki Iyayensa,Siyama tace ya dai fiye Miki Ina Baki shawara karki fada sonsa.
Bayan wasu satikai Ahmad Haka yake ta wahala da zuciyarsa ya kasa fadawa Aamna idan yaje da Niyyar fada sai ya kasa babu irin plan din da Basu hada ba da su Mashkoor Amma idan Ahmad yaje Gaban Aamna sai ya kasa furtawa,Yau Suna zaune da Mashkoor suna shaye shayensu Mashkoor yace yau shine Plan na karshe King idan baka iya fada Mata ba wallahi gidan Nan Zan Bari kaje ka karata,Ahmad ya daki Center table yace yau Dole ne na fada ma Dole babu fashi mene plan na gaba?wayarsa ce tayi Kara Yana dubawa yaga Bash ne abokinsu dagawa yayi yace ya akayi ne guy? King ku fito Umman Jibson ce ta rasu a asibiti ciwon Sugar dinta ne ya tashi Ana kaita Hospital ta fece wallahi,Ba ko Salati Ahmad yace yanzu Ummati ta ware itama? Yace kwarai kuwa Kun manta yau Kuma ake Sadakar Arba'in din Baban Tawaga da ya Dier shima ya kamata ku fito fa Jibson Yana wani Hali, Mashkoor ya kashe waya tare da kallon Mashkoor tashi mu tafi Ummati ta arce itama shikenan mijinta yayi asarar matarsa Allah sarki Shan maganin Mata ya Kare Abbin Jibson Kuma karya ta Kare Dadi ya kare Masa ya Gama Shan rabonsa, Mashkoor yace Kai tsohuwar Nan ai ta godewa Allah ai su Kam sunci duniyarsu me zasu ce da Allah mu ware kawai.