← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 89

Sashe 57

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Mama Basu Gama Kai karshen kallo ba sai da suka Shiga cikin gidan Ahmad La'ilaaaaah tsayawa lissafi Bata Baki ne an narkar da dukiya wajen kera gidan da furniture abin ba a cewa komai,kitchen Kuwa wani mugun katon gaske har Guda biyu ne shi ma,kayan da suke ciki sai wane da wane,gaba Daya color din gidan Milk and Golden ne,komai Yana daukan Ido Yana sheki,shi kanshi tsarin steps din da zaka hau sama abin birgewa ne,gadaje na alatu,kujeru na nunawa sa'a,toilet Kam sai dai a rufe Baki,bangaren sauran gidajen Kuwa milk and Brown ne sannan furniture da komai iri Daya ne,Aamna ta Zama Yar kallo.

A Palo aka ajiye Amarya ba a Dade ba sai ga su Ahmad sun shigo su shidan cif,Zama sukayi Suma a kasa su Daddy suna kujera,Humaira tana ta yiwa Brown signa suna kallon juna,Daddy ne ya kalle su gaba Daya yace Bismillah samari a bude taro da Addua,sun fara kenan sai ga Saddeeq da mufeedansa Suma sun shigo da Sallama,Addua akayi aka shafa.
Daddy yace Alhmdllh mun godewa Allah daya nuna Mana wannan Rana da ranmu gamu mun gani Ahmad Guda king yau an wayi gari ya shiryu tare da guys din nasa gaba Daya,an samu yau kowanne cikinku ya daina Shan komai Wanda Ahmad silarsa Matarsa Aamna ko ta Nan mun Kara tabbatarwa aure Rahma ne,aure Yana gyara mutum daga mutumin banza ya koma mutumin kwarai,sannan ku Kuma shiriyarku ta hanyar hatsari kunga mutuwa kuka saduda dama wani baya tuba sai yaji wuya mun godewa Allah.

Abinda yake Kara birgeni da ku tun a baya gaku Kuna shaye shaye Amma Allah ya baku hankali da basira,Allah ya baku zuciyar Imani da tausayi,biyayyar Iyaye,kula da Iyaye da yan uwa marayu wannan kadai Allah bazai Bari ku tabe ba,ga rikon Amana a tsakaninku Wanda yanzu itace tayi karanci,Wanda basa shaye shayen sai kaga suna tafka haukar da sunfi me shaye shaye rashin hankali,akanku na Gane cewar Dan kaga mutum a wani Hali karka dauke shi a banza sabo da Allah Bai halicci banza ko dolo marar amfani ba,duk lalacewar mutum Allah ya bashi baiwarsa ta daban,Yanzu mu dauki gidan Kai Tawaga ba karamin darasi bane,Babanku yayi Aure aure tun Yana da Rai Kaine jigon gidan,yazo ya rasu ya bar maka dunbun marayu Amma baka Gaza ba tare da taimakon abokanka kuka rike su kuka yiwa rayuwarsu gata,iya Maraya Daya ka dauki nauyinsa Allah ne kadai yasan iya adadin ladanka bare marayu Haka Yan uwanka,Kuma a Haka ka hadu da Budurwa itama ka daura nauyinta a kanka ka tallafeta baka ce kaima naka sun ishe ka ba,Haka kake kula da ita gashi babban taimako zaka aureta,iya gidanku Tawaga yakan sani zub da Hawaye musamman idan Naga kannenka idan ka dawo gida yanda suke turuwar fitowa taronka Ana maka Oyoyo ta kudu ta arewa kowanne yana rige rigen ka dauke shi,Iyayenka sunyi farar haihuwa,na jinjina maka kwarai dalilin wannan gidan Ahmad da yake damuna cewar gidansa ne a Nan zai mutu na baka gidan Nan halak malak ka kwashe marayu da mahaifiyarka su koma wancen gida zai ishe su zasu sake a ciki sabo da Babba ne,Komai ya koma mallakinka ka saka kannenka da mahaifiyarka.

Na dawo kanka Jibson kaima mahaifinka na raye da mahaifiyarka Amma Kai kake komai na gidan ka dauke musu nauyi da taimakon abokanka,Mahaifiyarka ta rasu tana sa maka Albarka Kai Kam ka Dace sannan mahaifinka yayi Rashi ka tausaya Masa Zama shi kadai kuka samo Masa Mata daidai shi kuka Yi komai na auren aka daura,an baka gida ka sadaukarwa mahaifinka Kai ka hakura Zaka nemi naka gidan daban,ka samu mace Amma bazawara Kuma sabo da Allah ka so ta kana saurayi zaka aureta ba kowa zai iya wannan ba a Yaran zamani, weldone Jibril,gashi tun da wuri Allah ya Buda ma limaminku ya baka gida da komai na auren wannan falalar Allah ce ya fara saka muku tun a gidan duniya.

Bashir,Mashkoor da Mubaraq ku Kuma Kuna da rufin asiri da iyayenku Baku da matsala babba amma rikon Amana da sanin darajar abokantaka da lafiyarku da dukiyarku Kun tsayawa abokanku Kun bada gudun muwa wajen shuka abin Alkhairi ,Ana samun Haka da yawa mutane suna kallon masu shaye shaye a banza wallahi mafi yawa sunfi Wanda basa Shan komai Hali me kyau da sauran dabiu masu kyau,ga taimako,ga rikon Amana,da kaunar junansu Amma mu mutane maimakon a jasu a jiki masu karfi su tallafa musu Wanda ke Neman agaji da sauransu sai dai mu zage su,mu tsine musu sannan mu kyamace su,aure ma baza a Basu ba sai marar galibu Bayan da yawa in sukayi aure shiryuwa sukeyi musamman idan Suka fara Tara iyali,ya kamata mu gyara muma karka tsinewa wani Dan Yana Abu ba daidai ba,Kamar yanda surukin Mashkoor yayi Haka ake so a kasance,yasan kana shaye shaye Amma yace ka nemi yarsa,yasan kuna shaye shaye ya Baku kudi ya tallafi wani da kudin aure da gidan Zama,Rashin wannan shi ya kawo yanzu muke wannan halin na sama basa taimakon na kasa,sai zagin juna da aibata juna tare da hassada iri iri,Wannan Hali naku yayi kuci gaba da taimakon na kasa Haka ake so sai rayuwa ta inganta.

Daddy Kuwa Ahmad ya kalla yace My son Ban taba tunani kana da hankali da tausayi Haka ba,Ban taba ganewa kana da wannan halin ba sai daga baya,Ashe Kai gaba Daya mutumin kirki ne fahimta ne bamuyi ba,sa'ar Haihuwa yanzu mun San munyi sa'ar Haihuwa Kuma Allah ya muku Albarka ya sake hada kawunanku Amanar Nan Taku ta dore har abada,Ameen kowa ya Furta,Daddy yaci gaba da cewa Wannan gidan da kuka gani Estate Guda naku ne, Mashkoor ga naku can guba biyar kowanne da motarsa Kuma an saka komai na bukata a cikin gidan,duk Wanda aka tashi kawo Masa Amarya Nan za a kawota kowa ya zabi bangarensa gashi ga keys Daddy ya basu har da key din mota kowa da nasa,yace naga Kuna kaunar juna,idan na dauke Ahmad na raba Abota Allah ne ya hadaku,shi yasa na muku gida Haka sabo da ku zauna kusa da juna.
Mummy Tace Kuma yanzu Daddy zai na Dan hutawa kamar yanda kuka gani munje daku katafaren building dinsa Wanda kuke masu kula da komai na dunkiyar Daddy, Saddeeq an bashi kasonsa kaima Ahmad gashi Nan an Gina muku Naku Office din Rabin harkokin Business na Daddy ya dawo hannunka abokanka zasu taimaka maka zaku kula da shi,Gaku Nan office Dinku ma a building daya kuke kowa da Office dinsa sai ku ragewa Daddy aiki kuma,masu aikin Gomnati Kuma nasan da kanku zaku ajiye aikin Gomnati sabo da yawan abinda zaku samu,kanfanonuwa ne da dama a karkashiinku yanzu,Amma sai Bayan 4months za a karasa hada komai kunga lokacin Kun Gama Amarci dunmkda biki ya matso,Godiya mukeyi sosai.

Daddy dai Aamna ya kalla ya fara Mata nasihar zaman aure tare da Angon, yace har ku ma su Jibson a karshe ya rufe da Addua tare da furta game da aikinku da zaku fara da kaina Zan dinga Guiding Dinku komai,Godiya Suka dinga zubawa,Mummy itama tata nasihar tayi Haka Amma ma,sai Baba yace Gaskiya Naga darasi a rayuwa Nima nayi hankali yanzu shekarata Kusan sittin Amma sai yau na Gama hada hankalina cif,na nutsu Nima Kuma Zan koma gefe nayi shuru abina...

Dariya akayi Mama tace Nima sai kwana Nan na hada Nawa hankalin ta kalli Ahmad tace Dan Nan Muna kallonku Baku da hankali Ashe kunfi kowa hankali,Ahmad yace ai Kuma Kuna da naku kalar, Baba da sauri yace Kai yaro Bari Ina wani hankali a wajen mu,da Muna da shi ma aikata abinda muka aikata a baya? Su Jibson suna ta dariyar Baba,yace ke Aamna Allah yasa dai kema kin waye kin iya magana nasan halinki abinda kika ga dama fadawa mutum kikeyi to ki kula wannan samarin ba irinmu bane kishiya sukeyi da wuri,Aamna kunya ta kamata ta boye Fuska Baba yace daga baya kenan Allah ya dawo da Babanki shima wani bakin Dan Iskan gantalalle ace shekara ashirin da wani Abu kaki waiwayar jininka,Dariya Baba yake ta Basu wannan zagi Haka cewar Daddy,Baba yace Allah ya kawo shi kasar nan duk Randa ya kuskura yazo zai ci ubansa a wajena,bushashen banza Yana tafiya Kamar Iska zata dauke shi wuya kamar sillen karan dawa,Shi Sam baiyi Kama da Yan Sudan din Bama Allah Kalar bakin fatarsa irin na Yan Kenya ne karya ne ruwa biyu ne Babarsa ko babansa ciki Daya bazai wuce Fulanin Kenya ko Senegal ba,sai tsayi Kamar rakumin dawa,aka dinga dariya har Aamna Ana ta kashe tsohonta da ba'a ita Bata sanshi ba ma,Baba yace ai ke Kam Aamna bangaren Sumayya kika gado su Daddy amma da kin gado bangaren Ubanki babu ta yanda za ayi kiyi kyau,sabo da kaf dinsu babu me kyau ga Baki, Hanci kwabal,ai wallahi an cuci larabci cewar Mama.

Baba yace Haba ke dai Bari Aishatu idan naji Baban Aamna Yana larabci lokacin Nan inda kisan na sa Sanda na sheme shi Haka nake Jin haushi Wai Balarabe ta gidan uban wa? ba gwara ace nine Dan Sudan din ba ya kika ce? Mama tace tuni ma labanil mara'i kullum babu Yankewa Madara me Dadi,Almara'i ga tuffa Yar kasar madina.
Chapter 57 · 0% Book details