← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 89

Sashe 10

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana yin Sallama Mama ko kallonta Bata Yi ba,kayan miyar ta Ajiye zata juya Mama ta rike Hannunta caraf,Tace wa kike wa raini Wai? Waye sa'anki a gidan Nan Dan Kan uwarki,Aamna tayi Mukus Mama ta shiga zuba Mata Rankwashi ba adadi sannan ta saketa Tace tashi ko na nayi ball da ke, Aamna ta Mike ta fada daki tare da sake fashewa da kuka,Ita kuwa Mama girkinta ta shirya shinkafa da Miya da salat.
Wato Islamiyyar Asabar da lahadin ma kin daina zuwa ko Aamna cewar Mama,Aamna Dake kwance a katifa ta fito Fuska a kumbure Tace na girmi Islamiyya Ni,Duk abinda ya kamata na sani na sani na addini sabo da Haka zanci gaba da saurarar wa'azi Kawai a gidan Radio ya isheni zaman duniya,a kyale Ni inji da matsalata,Ni yanzu ba karatu ne a gaba na ba,Alhadisissani,salisu duk na Iya ya ishe Ni,Sira da Ishmawi na haddace quarter,Zikiri na iya,Qurani saura Izu goma nayi sauka to me Kuma zanyi,gishirin zaman duniya na sani ya ishe Ni,Mama ta rike Baki Tace tab ke Baki ji kunya ba 25yrs Baki sauka ba,to ai da a sauke ba a Aiki da shi gwara ka samu Izu goma kayi Aiki da shi,Bulala Mama ta dakko Aamna ta jawo kujera ta zauna daram Tace a tafke Ni ai na Saba,kamata kullum a Duke Ni to a Dake Ni,Mama kuwa itama akwai zuciya Nan ta dinga tsulawa Aamna Bulala iya karfinta,har ta Gama Aamna ko motsi Bata Yi ba ta tashi a nutse ta shige dakinta,Haka Baba da dare bala'i yakeyi Kamar me,Ita kuwa Aamna washe gari sai da taje chemist aka Bata magunguna,tana dawowa ta Hado kayan sawarta a Akwati ta fito sanye da Hijab Tace Zan bar muku gidanku gwara na shiga duniya.

Baba ko a jikinsa yace a gaisar da Yan bariki maza Kar dare yayi a dawo lafiya,Mama ta tabe Baki Tace sakarai,Aamna tana ta jira a lallashe ta ko ace Kar ta tafi Amma taji Shuru,Tace Zan tafi fa bazan dawo ba,Baba yace to,Duniya fa Zan shiga Mama,Mama Tace madalla,Juyawa Aamna tayi ta fara tafiya ba Wanda ya kulata har taje bakin kofa,Tace baza ku kirani ba Wai? Tsaki Baba ya ja,Aamna tayi waje kenan taga wata dalleliyar mota me tsada,Wata Dattijuwa ce ta fito a motar,da wani Dattijo shima fari ya fito,Aamna taji an kirata,Matar ta kalla sai taga Mummyn Ahmad ce cikin shiga ta Alfarma,Aamna fara'arta ta karu har kasa ta zube tare da Gaida su,Mummy Tace ga Baban Ahmad,Aamna ta sake Gaida shi tare da rike Hannun Mummy Suka Shiga gidan.

Baba da Mama sunga masu kudi Nan Suka rude,Baba yace laaaaaa Alhaji Ja'afar Kaine a gidan Nawa? Wanda aka Kira da Alhaji Ja'afar yace ikon Allah Malam Hussaini Umar dama a Nan kake yanzu? Baba yace ae wallahi,me ya kawo ku?Aamna dai da Mummy suna mamaki aka shimfida musu Tabarma,Aamna ta kawo musu pure water da lemo,Nan ta ebo musu shinkafa da Miya da salat ta Ajiye,Tace Baba kasan su ne? Baba yace kwarai kuwa zauna kiji labari.

Labari

AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYA TAĪ)\Ī)\

16-20

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

MAMAN SAMHA
ZAINAB SABO
BK
UMMEEN SADEEQ
BASMAM GLAM
ALHUSNA(MRS IDRIS)

Ni Hussaini Umar kamar yanda kika sani mu Uku Mahaifiyar Hajiya Maryam ta haifa,Kuma mu kadai ne a wajen Mahaifinmu Malam Umaru,Ni Yan biyu aka haife mu Ni Hussaini da Hassan,Hassan tun Muna jarirai Allah ya Masa Rasuwa sai Ni,daga Ni aka Haifo Kawunki Isma'il sai Kanwar mu Kursum wacce kika Sani a kauyenmu Sokoto take aure,Munyi karatun Muhammadiyya har muka girma Noma da kiwo muka gado, tun baya dama mu Bamu taso a cikin kudi ba sai rufin asiri,sai da muka girma lokacin aka hadani aure da Aishatu Yar Uwa ce itama auren zumunci ne,daga Nan Bamu samu Haihuwa ba har Ismail yayi Aure shima a can kauye,sai da ya haifi Yara uku sannan aka yiwa Kursum Aure a kauyenmu itama ta Haihu Daya,duk Ni Allah Bai bani Haihuwa ba har Iyayenmu Suka rasu sai Yan Uwa da dangi,wannan da kike gani Shine Alhaji Ja'afar Wanda shima a Sokoto na sanshi Amma Asalinsu Yan Yemen ne kasashen Larabawa,kasuwanci ya kawo su Nigeria Sokoto suna da company Wanda a lokacin suna da Company na Yogourt da Kuma kamfanin Dake sarrafa Fulawa,sabo da Haka suna bi kauyuka suna siyen madarar shanu da Alkama Wanda a lokacin sana'ar mu kenan a wajen mu suke siya,mun Saba sosai muna mutunci da Alhaji Ja'afar lokacin ya Dade da Auren Mummy har da yaronsu Ahmad Yana shekara bakwai lokacin,su dama masu kudi ne da danginsu duk suna zuwa,ita Mum Yar Sokoto ce,bafulatana ce ya ganta ya aure ta sabo da sonta da yake Yi,Tun Bai Jin hausa har ya koya ya Zama Kamar bahaushe shima ga matarsa bahausa,Tunda yayi Aure ya dawo Nigeria gaba Daya da Zama Amma yanayin Lagos ya fiye Masa Dadi shi yasa yayi gida a can komai nasu a can,Ni Kuma mun Saba mun Shaku,Ja'afar yana tausaya min rashin haihuwa,lokacin akwai wata Yar Uwarsa Hajiya Sumayya,Sumayya marainiya ce gaba da baya sai Dangi Su Ja'afar kenan, Danginsa ce Amma Iyayenta sun rasu,a cikin Dangin Summayya Ja'afar shi ya taho da ita Nigeria ta Dan zauna a Wajensa na Dan watanni, a Nan ta samu wani Wanda shi a Nan Nigeria yake shima Kuma a Sokoto Amma shima asalinsa Dan Sudan ne,ganin balarabiya fara sai ya zauce sabo shi Yana da duhu ma bakin Balarabe ne,aka hada su Aure da Sumayya,Dan Sudan dai yayi Aure Bayan shekara Uku Sumayya ta Haifi Yarta mace kyakyawar gaske aka sa mata suna Aamna,Idan baza ki manta ba Aamna Ina zuwa dake wani gidan Yan Sudan a Cikin garin Sokoto birni,duk Hutu Ina kaiki wajen wasu Dattijai,Aamna Tace ae,Baba yace to kakanninki ne na wajen Uba Aamna,Wannan Ja'afar da kike gani Shine Dangin mahaifiyarki Sumayya wacce ta Dade da rasuwa,Katsam Bayan ta haife ki da shekara Biyu Babanki Rahil menk ya gudu ya bar kasar,aka Neme shi aka rasa,sabo da taurin Kaine da shi,bashi da tausayi, Jaafar ya Shiga Bincike

Ashe karya yayi ya auri Sumayya matansa Uku a Sudan da yaransa manya,Ashe Auren sha'awa yayi ya gudu ya barta,lokacin Jaafar ya bani Amana Kan na kula da Sumayya,Muna Haka ciwon Hawan jini ya kamata daga Nan sai ta kamu da ciwon sugar Bata Dade ba sai ta rasu,Ja'afar yayi kuka dangi suka zo suka tafi da gawar mamanki aka binne ta a can kasar su,ke Kuma kina Yar shekara Biyu Ja'afar yace tunda bani da Yara Allah Bai bani ba Kawai na dauke ki ya bani ke halak na kula da ke.

Ni da Aishatu munyi murna muka dinga kula dake sosai sabo da Alkawarin Dana dauka shi yasa kika ga na barki kinyi har HND na dage na biya Miki sabo da bana so kiyi kukan Rashi,sannan takurar Aure da kika ga mun dage sai mun Aurar dake muna gudun kar wata masifar ta afka Miki ya Zama kin lalace a Hannun mu,shi yasa muke so mu rabu lafiya,Aamna Hawaye ya shararo Mata Tace Amma Baba ita Zuhra fa Kuma me yasa kuka fifita a kaina? Baba yace Zuhra Bayan kin shekara Hudu a Hannun mu Allah ya bawa matata ciki ta Haifo min Zuhra,kin San zuciya da Kuma son Kai da son da na daban ne,wallahi bazan boye Miki ba,muna haifar Zuhra gaba Daya Muka ji tafi shiga ranmu,a Haka ma kokari mukeyi muna danne zuciyarmu Dan kar ace kin lalace a Hannun mu Amma har ga Allah Aamna munfi son Zuhra da ke,shi yasa Baba Ni ka Bari nayi school Wato na lalace ita Zuhra iya secondary tayi aure,sannan har Sweety Zuhra kake ce Mata fa.

Mama Tace ae ai munyi kokari ma duk abinda kike Mana ke rike kin ma ai munyi kokari bazan ji tsoron ki ba,Aamna Tace tunda na taso nasan Kuna duka na ku hantare Ni Ashe duk fakewa kukeyi da naki aure Ashe dama tsana ce?Mama Tace ke dalla fitsararriya lokacin da Danginki suka Yi watsi da ke shi Kansa Alhaji Ja'afar din gashi Nan ya sake zuwa ko duba ki,in Banda Dangin Babanki da muke kaiki kaf Dangin Uwarki ba Wanda ya sanki domin tunda Ja'afar ya Bamu ke ya tafi sai labari muka samu sun bar kasar ba a San Ina suke ba,sai dai Hana rantsuwa Muna Jin sunansa a Radio Yana tallafi iri iri a kasar nan.

Alhaji Ja'afar dattijon kirki me Kamala yace Bari Nima nayi magana,lokacin Dana Baku Aamna yarda da aminci tare da tausayawa yasa na Baku ita Amana,ku kanku Kun San Ina da arzikin rike ta,Kuma Dana Baku ita sai Dana Baku makudan kudade Wanda Aamna zatayi karatu har matsayin Degree,Kuma Ni bazan ce ba kuyi kokari ba koma Mene kunyi kokari Kuma mun gode Allah ya saka,Amma Kun San dai Aamna na bada gudunmuwa na kudin daukan nauyinta,Baba yace kwarai muma min Sha wahala da ita,Bata da kunya Bata da tarbiyya gata Nan,Aamna Tace ai tarbiyyar kuce Ni Kuma wallahi Ina da tarbiyya, Haka tunda na taso nayi wayo nasan Kuna nuna banbanci tsakanin Ni da Zuhra,Ni za ayi ta dukana har girma na,Ja'afar ne yayi murmushi yace ya Isa Haka,ke Aamna Har abada Iyayenki ne ban son sakarci,Mummy Tace ikon Allah Ashe Aamna ce Yar Sumayya shi yasa na rasa Ina na santa mashaallah,Ja'afar yace lokacin da Muka Baku Aamna bayan mun koma lagos Arziki na ya bunkasa,daga Nan Kuma Mummy ta Haifo Kanin Ahmad Saddeeq,na tattara Muka koma Colombia da rayuwa,a Nan aka haifar min Auta Humaira Wanda Candy zata Yi kwana Nan,Haka Saddeeq shi nutsatse ne yayi aure da matarsa harda yarsa,Zaman da Muka Yi a Colombia shi ya jawo Babban Dana Ahmad ya lalace da shaye shaye,na rasa yanda zanyi da shi wallahi,mun rasa ya zamuyi ya shiryu,abin ya dame mu,Alhaji Ja'afar ya nisa tare da cewa yaki aure bare yayi wani Aiki Sai dai kashe kudi ya sani Kawai da shaye shaye.
Chapter 10 · 0% Book details