← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 89

Sashe 12

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da aka zo shiga mota Ahmad yace Bayan anyi min gorin mota harda kwace motoci na a machine Dina zanzo,Daddy ne ya balbale shi da masifa Kai wanne irin banza ne Wai? Ana gabas kana Yamma dalla je ka shiga waccen motar,Ahmad yace wancan bakar Haba ai sai dai ku ku koma cikin bakar Ni da Mum mu Shiga fara ko na fasa tafiyar wallahi ku baku san wanka ba,Dole Haka Daddy ya kwashe sauran a Daya motar baka Sadeeq ya tuka su,Mummy kuwa suna fara ita da Ahmad sun hakimce a Bayan mota Driver Yaja Suka wuce sai sabon gidan su Aamna.

Aamna kuwa dama Mummy ta sanar musu da zuwansu sabo da Haka ita da Siyama Suka shirya abinci iri iri sannan suka Yi wanka,Aamna ta shirya cikin wata sabuwar bakar Truskysh gown me adon Golden,tayi masifar kyau sai ta fito Kamar wata balarabiya,Baba ma Tasha shaddarsa,Mama tasa Atamfarta maroon,Siyama kuwa an zuba lace dark Green,Mama ce ta ja Aamna Bedroom ta zaro wata laya ta makale Mata a kanta cikin gashinta,Aamna Kamar tayi kuka Tace Mama har yau Kuna wannan shirkar ga ta Rannan a kaina kin hanani cirewa layu har biyu,Mama Tace ke dalla ta farin jini ce,Haka aka sawa Aamna dole ta yafa mayafinta Wanda ta Sha acuci,Wani guru Mama ta sake dakkowa tace lallai sai Aamna ta Daura a Hips dinta, Aamna zata Yi kuka Tace wallahi kin San naci kashinki da fitsari idan na tsine Miki sai ta Kamaki,Zan tsine Miki idan Baki daura ba,Aamna tana gani ta dage Riga har wandon ciki aka daura guru sannan ta maida kayan ta fito palonsu hadadde Kamar zata Yi kuka ta zauna tana Danna Yar Wayarta Vivo.

Suna Haka Suka ji shigowar motoci,Aamna gabanta ya fadi,Siyama kuwa tuni ta leka ta window har Sanda Ahmad ya fito ta haukace gaba Daya tana lallai Aamna wallahi ku Larabawa ne da gaske gashi na gani,kalli danginki Kan uba kaga wani tantirin Dan Iska Amma duk yafi kowa kyau da iya wanka,Aamna ta Mike ta leka itama tace ai shine Angon,Siyama Tace Yau mun Shiga Uku kashinki ya bushe da gani Zaki ci Ubanki,Aamna Idonta ya kawo kwalla Tace wallah bazan taba sonsa ba,Dan giya ne,idan Kuma ya shiryu fa cewar Mama,Aamna Tace Idan ta dalili na ne sai na yarda Ina sonsa idan ya shiryu sai na gudu na barshi Kinga na taimaki Iyayensa,ko Dan Iyayensa Zanyi sabo da yanda suke mutanen kirki masu taimakon musulmai Bai ci ace suna da Dansu irin wannan ba,Siyama Tace bafa a Wasa da so,karki Bari ya kamu da sonki kice Zaki Wasa da zuciyarsa idan ya Gane ba sonsa Zaki ba kin Gama yawo,na Baki shawara idan Zaki so abinki ki soshi karki ce ban fada Miki ba Aamna ba a Wasa da zuciyar mutum a so,Aamna Baki ta tabe Tace wannan Zan so? Zan dai je da yanda Mukayi magana da Mum,ba ruwanku.

Sallama sukayi aka amsa kowa ya shigo a nutse,Baba Yana musu Sannu da zuwa,Nan da Nan Su Siyama suka cika gabansu da Abinci sai lokacin Ahmad ya shigo ya tsaya Yana waya a waje,Ganin Aamna ya bashi mamaki yace Kai keeee......Aamna ma Tace kaiiiii......Ran Ahmad ya baci yace Wai Mum dama gidan wannan zamu wani zo? Daddy yace zauna Malam,Ahmad yace Ni bazan zauna ba Ku Gama mu tafi Ina da abin Yi,Siyama Tace tab a ranta,Zuhra ce ta shigo Amarya taci gayu Adam ya sauke ta,Itama gaisawa akayi ta zauna,Ahmad fafur kin Zama yayi ya zuba Hannu biyu a Aljihu ya tsaya kerere Kuma ba Wanda ya gaisar ko kallon arziki Bai musu ba,Baba shi Kam murna yakeyi Aamna ta samu Miji sai ya kalli Ahmad yace Sannu Sarkin matasa,na baka Sarautar Sarkin matasan Nigeria,Ahmad wani murmushi ya saki ba shiri,Aamna ta wani washe Baki itama ganin irin kyan da yayi,a Haka Daddy ya bada tarihin Aamna da dangantakarsu da Ita,Tsaki Ahmad ya ja tare da zaro Yar karamar kwalabar giyarsa a Aljihu ya kwararawa makoshinsa,Aamna ya kalla ya galla Mata Harara tare da cewa daina kallo na,Tace na kalleka din Kai da wanne idon ka kalleni,ransa ya sake tunzura ya kwada Mata Mari a saitin Idonta Nan take ta durkushe ta saki kuka,Da sauri taro ya watse aka dauki Aamna zuwa Asibiti,shi kuwa Ahmad a waya ya Kira Mashkoor ya dauke shi a machine suka Yi tafiyarsu.

Daddy kamar bakin ciki ya kashe shi ransa ya baci ganin yanda aka mannewa Aamna Ido Daya da auduga da plasta Kuma akace Nan gaba sai an Mata aikin Ido,Tunda suka koma gida Basu ga Ahmad ba har kwana biyu ta cika Wanda itace Ranar daurin Aurensa Bai Sani ba.

Mummy a waya ta Kira Ahmad ta sanar Masa da Aurensa,ya zaci Wasa ne ya dinga dariya yace Mummy kina da abin Dariya to idan hakane a daura Auren na Amince, Mummy tayi Dariya Tace ka yarda kace? Yace Yeah..Yana dariya Wai Wasa ne, Daddy kuwa ya tattara mutanensa Dana Baba a masallacin Unguwar har Mashkoor ya sa aka Nemo su duka sabo da Suma su Zama Shedu,Ahmad Yana can gidan Mashkoor Yana ta sheka bacci, Ranar Juma'a Ana Idar da Sallar Juma'a da Shedu walliyan Amarya da wakilin Ango suka karbi Aure Nan aka Daura Auren Aamna Rahil Menk da Ahmad Ja'afar Yabalash, Kan sadaki dubu dari,Su Mummy lefe suka yiwa Aamna na gaske Akwati goma Sha biyar,Ahmad ranar ya dawo gida sai gani yayi su Baba duk sun Hada kayansu zasu tafi ba Wanda ya kulashi,Mummy ce ta shigo Bayanta Aamna Amarya ce sanye cikin wani material Brown yasha kyau,idon Aamna Daya yasha plasta a manne da Daya take gani,Yana ganin Aamna ya Mike yace me wannan takeyi a Nan Mum?Mummy ta Bata Rai matuka Tace matarka ce Ahmad,Daddy ya shigo yace yau Shedu sun sheda an daura maka Aure da Aamna Yar uwarka Kuma marainiya sannan da Amincewar aka daura, ta Zama Amana a wajenka,ka sani Aure ba Wasa bane,idan kayi shirme Allah bazai Barka ba,Kuma wallahi ka koreta ko ka Mata Illa ban yafe maka ba Ahmad.
Mummy Tace gata Nan wallahi kaji bazan rantse a banza ba babu Wasa yau aka Daura muku Aure shi yasa nace Rannan ka bimu muje na kaika ne Dan kaga surukanka,Nima kaji na rantse Idan ka koreta ko kayi gigin sakinta bani ba Kai ban yafe maka ba,Kuma Matukar ka saketa Allah ya Isa Nono na daka Sha,sabo da Haka gata Nan Amana da kayanta,Nan Ahmad yaga me Gadi Yana ta shigowa da kayan lefe Yana kaiwa sama Daya dakin da ba kowa Wanda Mummy ta zabawa Aamna a matsayin nata,duk abin bukatar Aamna an kawo Mata abinta,daga Nan Mummy Tace Mashkoor ku shigo,Suka shigo suna tangadi,Mummy ta kalle su Tace gwara da kuka zo yau nasan ku shaida ne a gabanku aka Daura Auren Ahmad sabo da Daddy da Kansa ya gayyace ku Kuma Kun gani,Mashkoor yace kwarai King a gabanmu aka Daura muna ta so mu fada maka Amma wayarka Taki Shiga gaskiya ba a kyauta Mana ba,anci Amanarka King a gabanmu muna gani aka Daura Sadaki dubu Dari Daddy ya bada cewar Jibson.

Bash yace Kuma Daddy yace kayi aure yanzu mu rage zuwar maka gida wannan fa ba Adalci bane King,Ahmad da yayi mutuwar tsaye yace shima cikin kwaya me yasa Baku Hana an daura Auren ba,me yasa Baku rotsewa liman Kansa ba,Daddy ya kawo securities ko Ina King,Ahmad yace Good za aga abinda ba a so kuwa,Mummy Tace kaji dai gargadi Kai ka sani,ta kalli su Mashkoor tace lalatattun banza ku fita muje marasa tarbiyya,Haka Suka fito ransu a bace,Ahmad Yana kwalawa Mummy Kira kizo Mummy ki tafi da Yar mutane,Zan Mata Illa,Zan kashe ta ne,kizo ki tafi da ita,Mum....Mummyyy.....Ahmad ya dafe Kansa kwaya ta motsa Nan ya Shiga hauka da tangal tangal a palon,Aamna tana kallonsa a ranta Tace kaddara ta hau kaina na shiga Uku,me yasa na yarda aka Daura Auren,Wayar Hannunsa ya tarwatsa da kasa,Wandonsa Kamar zai Fado zabar Ass down na iya shege,Ya kalli Aamna yace ke bi Mummy ki tafi kafin na kashe ki yanzu,Aamna Tace wace zata bi Mummy? Ai wallahi Zama daram sai dai mu mutu tare,Zan Miki Illa fa,Illa ai ka rigada kayi min ita tunda ka nakasa Ni ka maida Ni me Ido Daya,waye zai aure Ni a Haka,ai Ina Nan a matarka Zama daram wallahi yaro baka Isa ba kayi kadan Aamna ta Furta da karaji tana dukan Table,yace ke Ni Zaki nunawa hauka,Kai din wa Kai din me,me ka Isa kayi,Ai ransa ya Gama baci ya bita da gudu Suka tafi tare,ta haura Sama da gudu zuwa dakinta tana shiga ya damko gashinta,Tace wallahi ai dambe ne Nima na Iya Suka rukuma kokawa.

Kici kici suna Nishi Kamar zakaru,ya dauketa ya makata a saman Bed,ya bita zai jibgeta ta samu tare da makalkale shi ta cikwikwiye shi,Taki bashi damar dukanta,gata da karfi itama Suka dinga kokawa Baji ba gani,sai da suka gajiyar da kansu sannan ya saketa ya dawo Palo ya zauna a kujera Yana maida numfashi kamar Wanda yayi tsere Itama palon ta dawo gashinta ya watse ta zauna tana Nishi itama taji jiki.
Yana Nishi yace kin gaji kenan?,Tace na gaji a Ina ai ban gaji ba sai dai mu mutu wallahi,yace to Bari na huta na samo power kiga yanda zanyi da ke,Aamna Tace Nima Bari tawa power din ta dawo ka gani idan Zan kyaleka.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYA TAĪ)\Ī)\

21-25

FREE PAGE

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
08033933642

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

BESTYNBEELAT
UMMU LATEEPHA
M BELLO
SA'ADATU TIJJANI
UMMI DEEJAT
NAFEESAT UMAR MUHAMMAD.
Chapter 12 · 0% Book details