← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 89

Sashe 14

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Aamna tasan tayi laifi Bata sake Fitowa ya ganta ba sai washe gari ta fito sanye cikin wani Lace fari Riga da skert daf da ita tayi kyau sosai Sanda ta shigayi tana tafiya a hankali,a main Palo ta Iske shi yayi Order Breakfast ya hada tea lafiyayyen gaske ga chips and Egg da farfensun kaji Yana ci hankali kwance,Aamna ta hadiyi Yawu ta fito a hankali yaji motsinta Amma ko kallonta baiyi ba yaci gaba da cin abinsa,a gabansa ta durkusa Tace Ina kwana Yaya Ahmad,sai lokacin ya kalle ta kadan Yaja uban Tsaki,tace Nima yunwa nake ji,wata Uwar Harara ya aika mata,Dan Allah San min ko na fita na siyo? Dama jiya na fita na siyo Abinci na manta ban nemi Izninka ba ka yafe min,Cikin tsawa yace Ina ruwana da rayuwarki Ni da Zaki tafi ma bangon duniya Ina ruwana,wallahi bazan je bangon duniya ba salon idan tashin kiyama yazo yajuju da majuju su fara ta kaina,Kinga ki daina Shiga harka ta,na fada Miki kiyi rayuwarki Mummy ce ta kawo ki to duk wahalarki sai ki fada Mata,Yar wahala Kawai,Yar walagigi Kawai,Ai kuwa Ni gaskiya Raina ya biya da wannan Abincin naka ka fada min Inda ka siyo naje na siyo ai Ina da kudi sannan ko ka bani naka na ci,Tana Gama fadin haka ta janyo plate din chips din gabanta ta fara ci Tace Dadi,sai ta dauke plate din ta gudu daki ta sa key,Ahmad ya dura wata Ashirya yace yau ba abinda zai Hana ban karyaki a gidan nan,Sa'anki ne ni? Aamna Tace ae daga bedroom,Sai da ta cinye tas ta fito lokacin ya bar gidan ma,ta kalli kwanikan Daya Bata duk abincin ya rage Bai cinye ba duka,ta zauna gaba Daya ta cinye sannan ta hau gyara gidan tana mita mutum sai yawon jaraba kullum Yana waje.

Duk wani Aikinta sai da ta Gama sannan ta zaro Yar Wayarta Vivo ta Kira Mama suka gaisa da Baba,ta Kira Zuhra ma Suka Sha Hira,Siyama ta Kira karshe,Siyama Tace Amarya bakya laifi kin tafi kin barmu da Aiki a Resturant,Yaya Mutumin naki ko anyi abin ne? Aamna Tace Allah ya kiyaye na hada jiki da Dan giya,ke Siyama wallahi baya kaunar Mace,wannan ko tsirara Zaki zo gabansa baza ki birge shi ba,Dariya Siyama tayi,wallahi Aamna ga masifa kullum Fuskarsa ba Rahma Abu kadan Kuma sai masifa,wannan bazai shiryu ba,banga abinda za a Masa ya shiryu ba,to Ina ma yake Zama da har zai fahimci wani Abu mutumin da sai ya kwana a waje can ko sai cikin tsakiyar dare zai dawo,ga Dan Ido na Guda Daya a manne,Suna ta surutu har suka Gama ta fara karatun Qur'ani,Jin yanda aka banko kofa tasan Ahmad ne ko Sallama dama bayayi Yana shigowa yace ke koma dakinki kiyi karatunki ko ki koma masallaci ki tare,Ganin yanda ya shigo a buge sai ta tashi tsam tayi bedroom shi Kuma ya kwanta a saman kujera,Ya kunna tv ya kure volume karshe kida ya cika gidan a manyan speakers Yana sani yayi Kuma dole Aamna ta hakura da karatun Qur'anin sabo da yanda kida yake dauke Mata hankali,Fitowa ta sake yi,ai kuwa ya Mike a fusace yace ba nace ki daina matsowa inda nake ba ya dauki Remote ya jefe ta da shi da karfi ji kake kwas a goshinta,sosai taji zafi wajen ya kumbura yayi Mata kulu,Itama ta dauka ta jefa masa a bayansa,ta gudu ya bita cikin zafin nama Amma ta kulle Kofa Haka ya rabu da ita yace Zaki fito ne.

Sai bayan Sallar Isha Aamna ta fito sanye cikin doguwar Riga Yar kasar masar,me shape sosai wata silver,ba karya tayi kyau,Mayafinta tayi Rolling ta dauki kudi ta fito,yau ma tayi sa'a sai ta ganshi a kwance Yana cin green Apple,Aamna cike da tsoro ta karaso inda yake wani kamshi yake na musamman,a gabansa ta tsuguna Tace Sannu da hutawa zanje siyo Abinci,Baki ya tabe sai da ya dauki mintuna yace Ina ruwana,mikewa tayi ganin masifa yake ji kadan yake jira sai tayi tafiyarta kuwa,taje tayi take Away sharp sharp ta dawo,Lokacin Yana Zaune Yana kallon wani American film, Sakwara da miyar kifi, ruwa Eva da fruits salat,tana ci tana kallon Film, .

Wayarta ce ta hau Ringing tana dubawa taga Mama,da sauri ta daga,bayan sun gaisa Mama Tace Aamna ga fa kudin sadakinki Baki karba ba,Aamna Tace Ina sane da abina,suna Rai na,a ciki ki dauki dubu Goma kyauta,ki Bawa Baba dubu Talatin,Zuhra a Bata dubu bakwai,Siyama kawata a Bata dubu Uku Kinga dubu Hamsin ta Kare ko? Mama Tace Haka ne,to dubu Hamsin din a ciri dubu biyar a bayar Sadaka Allah ya Kai ladan kabarin mamata sumayya Allah ya Mata Rahma,a sake cire dubu biyar Abba na Daya gudu ya barni ayi Sadaka nayi tawasili da ita Allah ya shirye shi ya canja Hali,Mama tayi Dariya Tace ai duk kin rabar da kudin ba Haka akeyi ba,Zan dai cire na Bawa kowa abinda ya Dace sauran ai naki ne,Aamna Tace to koma dai mene abinda aka barmin a kaiwa Kawu Isma'il can kauye ya Siya wake da Alkama a ajiye idan sukayi tsada sai na siyar na samu riba,Nan fa Ahmad yace tab Riba kudin riba ai masifa ne, ka siyi Abu ka boye sai yayi tsada kazo ka siyarwa mutane,Wannan ba Business bane,Aamna Tace Kai baka ga laifinka ba barasa kwalaba Nawa kake dirkewa cikinka wlh kayi hankali Kar Hantarka ta tabu tam,Hannu yasa ya murde Mata kunne ta kwalla Kara,Mama ta waya taji Kara Tace lfy? Mama wani kwaro ne ya firgita Ni.

Can Baba ya fisge Wayar yace ke Aamna Dan Ubanki kiwa fa mijinki biyayya,duk abinda yace kiyi bana son sakarci,Kuma ko me Zaki shuka ki shuka gaskiya kiyi gaskiya ato sabo da mu dangwali arziki da kyau,Aamna Tace yo Baba ai Gaskiya Ni a jinjina take da ita aka haife ni,dankwalin Aamna ne ya zame layar ta Guda biyu Dake soke a kanta suka bayyana,Ahmad Yana gani ya girgiza Kai a zuciyarsa yace mashirkiya,Ita dai Aamna abincinta take ci tana Dan juyowa ta kalle shi kadan sabo da faratansa na Hannu Dana kafa Daya Tara sunyi tsayi Kamar Arne Amma da gani suna Shan gyara wani fes da su sai dai ba a Yankewa,Allah yasa kayi bacci sai na yanke wannan uban faratan Aamna ta furta a ranta.

Ganin tana ta Kallonsa Yaja Tsaki tare da mikewa ya dauki key din machine dinsa zai fita,Aamna Tace Ina zaka je da daren Nan Haka?Ni tsoro nake ji gaskiya,Kwafa Yaja a ransa ya furta Mummy ta Gama Dani,idan na Mata Illa tsinuwa ta hau kaina,juyowa yayi a fusace yace Allah ya taimakeki Ina son Nonon Mummy Dana yasha yabi lafiyar jikina Amma da kin Gane kurenki,Aamna ta kyalkyale da Dariya Tace au har yanzu Nonon Mummy Bai Gama bi maka jiki ba? Sanda aka haife Ni ko yaye Ni ba ayi ba aka samu cikin Saddeeq shi yasa ya cuce Ni na Sha gubar cikinsa,Aamna sake kecewa da dariya Tace ko shi yasa aka ce ka Dade a tsumbure baka girma ba Dan Mummy Tace har cutar koshokwo kayi Haka Kawai Aamna tayi karya Tace Mummy ce ta fada Mata,ai kuwa shi da saurin Fushi kwaya tana sashi saurin Fushi ai Kan Aamna ta rufe baki yace uwar Koshokwo nayi,Aamna ta Mike zata gudu Suka dinga zaga palon Nan sai ya kamata ya dake ta Itama ta guduwa,ta samu tayi waje Compound da gudu,fita yayi Yana huci ya hau lifan dinsa ya fice sannan Aamna ta dawo ciki abinta.

Bayan Sati biyu da Auren Aamna kullum fada sukeyi da Ahmad ba Wani mutunci, Mummy ce ta Kira Aamna Tace,bayan sun gaisa Aamna ta saki kuka Tace Mummy wallahi kullum sai munyi fada ya Duke Ni saurin duka ne da shi Kuma yaki siyo kayan abinci kullum sai dai naje na siyo ko na aiki me Gadi shima Haka Mummy, Dariya Mummy tayi Tace Kuma wallahi Ahmad ya Iya girki sosai a haka,kin San nice na sallami Peter me dafa Masa abinci, Aamna ki Kara Hakuri,bazan turo Miki kudin Abinci ba Yana da kudi,kece Zaki San yanda zakiyi Masa dole ya Baki kudi ki zuba abinci a store kin Gane,ae naji to ta furtawa Mummy,Bayan sun Gama Wayar Aamna ta zauna tayi tagumi tana saka Taya zata sa ya siyo Mata kayan abinci ko ya bada kudin ta siyo tunda kudin hannunta sun kusa karewa.

Bayan tayi Shirin bacci cikin wata Riga da wando farare masu laushi ta zuba kyau ciki,a Palo ta zauna tana jiransa ai kuwa taci sa'a yau Ana Sallar Isha ya shigo gidan Yana tafiya da kyar da yanda yake Gadara ya nuna yau baiyi shaye shaye da yawa ba,Sannu da zuwa Aamna ta Furta,ko kulata baiyi ba Direct sama ya haura ya fada toilet,wanka yayi ya fito tare da Gabatar da Sallar Isha ko Addua baiyi ba ya Mike ya saka wasu kayan bacci dark blue me digon fari Riga da wando,fresh milk ya sha sannan ya kwanta a Gadonsa Nan take bacci ya kwashe shi me nauyi,Aamna ta biyo shi dakinsa Wanda Bata shiga sai idan zata gyara,a hankali tayi knocking Shuru taji,tayi Sallama Shuru,sai ta bude Kofar a hankali saman bed ta hangoshi ya wani Yi dai dai Yana baccinsa,Aamna tayi murmushi Tace Allah sarki yayi bacci,a gefen bed din ta zauna a hankali gefen kafafunsa,Nan take ta tuna da taga faratansa ya Tara sun Sha gyara,Room dinta ta koma ta dauko razor blade sabuwa dal ta bare,a tsorace tayi shahada ta Dan rike Yatsansa kadan sannan ta fara yanke Masa farcensa daya Tara Yana gayu da abinsa,ta fara yanke su Daya bayan daya,gashi da nauyin bacci har ta Gama hannaye Bai ko motsa ba Kawai baccinsa yake Sha,ta dawo kafa ma ta yanke Masa tas ta gyara ta kwashe farcen data yanke ta zuba a trash da razo din duka,ganin Bai da Niyyar tashi ta hakura itama ta koma dakinta Bayan ta kashe Masa hasken wuta ta Dan rufa Masa blanket sabo da taji sanyin ac yayi yawa.
Chapter 14 · 0% Book details