← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahil ne yayiwa Daddy magana da larabci Wai ya gaji da masifar Baba zai yi tafiyarsa inda ya fito,Daddy ya tabbatar Rahil bashi da Imani yanzu wato Dole ma aka Masa yazo,Haushi yasa Daddy da hausa ya fadawa su Baba me yace ,Baba yace au haka kace ma? Yar China ce tace dan Allah Baba ku bashi abincin yaci ni Allah tausayinsa nake ji,Aamna ce tayi magana Tace na yafe maka koma mene kaje Kawai tunda dama Dole aka maka,kallon Aamna Rahil yayi rin mamanta sak,murmushi yayi tare da Furta na gode yarinya ta,Mama Tace rufe Mana baki wani yarka me ka kawo Mata tsaraba tun daga Sudan ko Dan lallensu baka kawo Mata ba domin ta dinga yiwa mijinta kwalliya ko Yar muhallabiya babu gata can tana tashi a can a banza,Baba yace sai ka dakko wani bushashen jikinka ka taho zikau zikau,Kiran Sallah aka kwala na Magrib,Daddy yace muje ayi Sallah mu dawo a karasa abinda ya kawo mu,Alwala sukayi gaba Daya su mazan suka fita masallaci Matan kuma Suka Yi a gida.

A hanyar dawowarsu Baba ya kalli Rahil Dariya taso kwace Masa yanda ya ganshi Yana tafiya kamar Yana tausayin kasa,Baba yace Rahilu kayi tafiyarka sosai kasa fa ba kyaleka zata Yi ba Matukar ka mutu aka binne ka matsar Nan sai ka shata,Sai kallon Rahil yakeyi Dariya tana kamashi,Baba yace Rahilu da gani kana ji a jikinka,a cikin yaranka ka kawo min da daya na rike maka shi,Rahil yace to Zan baka wallah,Baba ya sheke da dariya tare da dafa kafadar Abbu yace Rahilu anji wuya Dan gandal uba to bazan rike ba tunda baka da mutunci kai ai wallahi sai dai wuya ta kashe ka Ni Nace ka auri matan kana can kana Dancewa da su kana danno Yara duniya sannan kace na rike maka,Aamna ma da muka rike Allah ya karba,Daddy yace ai bazan Bari ma ka karbi wani Dansa ba wa yace ya tara Yaran,shi ga ayu to Kai ka jawa kanka,Baba ya sake dafa kafadun Rahil yace kayi Hakuri Rahilu Ina ci maka Fuska Kaine ka jawo.

Kafin su koma gida su Aamna sun shirya kayan ciye ciye a palon sai abinda ka zaba,abincin Suka zagaye Yar China Tace Ni Zan yi Serving kowa,haka kowa ta zuba Masa abinda yake son ci,Baba yace Ni bazan zaba ba komai Ina ci a zuba min komai zanci akwai waje me fili a cikina,Yar China tace ashe Muna iri daya da Kai Baba,kema haka kike? Baba ya tambaya tace ae komai Zan cinye,kin birgeni cewar Baba,Yar China tana zuwa kan Rahil ta cika Masa plate kamar zai zubo abincin har wani tsiri yake Yi a plate tace ci ka koshi Abbu in Allah ya yarda kafin ka koma Sudan gidan jiya ka danyi bulbul,idan ka koma sai kowa yace America kaje,mu Nan ba yunwa akwai abinci Kuma Abbu ba ruwanka da Yaranka bare su cinye maka rabonka,Baba yayi Dariya Yar China da tsiya take yace da zai yarda yayi wata Guda a Nan Ina tabbatar muku kafin ya koma can sai ya saka Leda a kafarsa kafin ya cire wandonsa sabo da kiba,Rahil ya kalli abincin da aka zuba Masa yace bazan iya cinye wannan ba ai ko quarter bazan ci ba,Ni ba Jaki bane ya sa spoon ya Dan kwashi ganyayyakin Vegetables yana ci sai fruits.

Baba ya kalle shi yace Rahilu wa zaka ji kunya a nan kaci abinka karka zo kana dana sani,Wai mu zaka kife ai da ganinka an San baka Jin dadin rayuwa,Wai Kai nufinka Balarabe ne? Rahil yace sosai ma,Kana cutar kanka Kuwa mu idan sama da kasa zata hade baza mu yarda ba,asalinka Dan Kenya ne,Rahil ya Bata Rai har da buga plate da cokali cikin hausarsa wacce bata fita dai dai yace Allah kiyaye Ni...Ni... hadani da Kenya... baka ganewa Sudan can... ni Sudan Yana daga Hannu sama.

Baba Yana cin nama Yana dariyar gwarancin Rahil,Rahil harda cewa Dan an rike Masa yarinya za a dameshi,shi idan hakane a bashi yarsa ya tafi da ita,Baki su Baba suka bude yace gata Nan dauke ta ku tafi idan ka isa,a ka'ida ma Rahil Kara ya kamata mu kaika kotu Amma Muka Yi maka alfarma,Rahil ya Bata rai,Baba jinjina Kai yayi yace wannan da a Isra'ila yake harbe mu zaiyi,Yar China ce tace Kuma jirgi ya hau yazo Nan? Baba yace ae Mana,tab ai da akwalar mota ya dace a ganshi ciki,Mummy ce tace gidanku kaji yarinya a gabansa ga yarsa babban mutum,yar China da sauri Tace Yi Hakuri ai nufina yafi dacewa yazo a Private jet Yar China ta wayance,kowa Dariyarsa ya kunshe.

Sai Bayan Isha sannan duk Suka tafi gida,Yar China tace sai Nan gaba Zan dawo yau Baki sun Hana suyi hira,Aamna tace to Allah ya kaimu,Daddy da Rahil da Mummy,Humaira gaba Daya suka tafi masauki,su Jibson duk sun tafi saura Aamna da Ahmad a gidansu an barwa Aamna tarin wanke wanke da gyara Palo,na gaji Ahmad ya furta tare da mikewa saman sofa,Aamna ta kalle shi tare da cewa Ni kadai zanyi aikin My King ko dan tayani baza kayi ba,Fuska ya yatsina yace I'm sorry bazan iya ba idan kema kin gaji ki barshi da safe sai kiyi,Rabani da kwana da uban dirty haka,Aikinta tayi ta Gama ta Iske yayi bacci,Aamna girgiza shi tayi da karfi ya farka Idonsa cike da bacci,tace baza kayi min baccin wuri ba kazo cikin tsakiyar dare ka farka ka hanani bacci ba,Cikin shagwaba ya furta please Baby ki barni nayi bacci na,Aamna tace Ni Allah ka tashi kawai,ba Kya tausayina? to ai ba Aiki kake zuwa ba da Zan tausaya maka ba,tashi muje wanka,Ido ya rufe zai koma baccinsa Aamna sai hakura tayi tasan bazai tashi ba Kansa ta dage a hankali tare da zama a kujerar ta maida Kansa saman cinyarta,da muryar bacci yasa hannayensa tare da rungumo hips dinta yana Furta so sweet yaci gaba da baccinsa,Gashinsa take Wasa da shi tana kallon Nigerian Film dinta,tunda ya fara bacci Bai tashi ba sai 9pm tana ta kallonta,taji Dadi da Bai dade ba Yana baccin,Kallonta yayi Yana murmushi yace thank you My world for your cinya,murmushi tayi tace sai wanka ko? Kai ya gyada Mata Yana cire Mata wani dan abu a gefen idonta kayan kallon Suka kashe tare da haurawa sama.

Ita kuwa Yar China tunda Tawaga ya dauketa direct shopping ya kaita ya siya Mata abinda take so sannan tace Yaya ka manta Icecream din,Komawa yayi ya dakko Mata guda Uku manya ta karba tana murna tace Thanks alot.
Tun a mota ta bude abinta tana Sha Tace Kar ya narke,a spoon ta ebo tace Yayana,Tawaga Uban tafiya,Yar China sai Tawaga haka Tawaga sai Yar China,Dariya Tawaga yayi yace haka yake Yar Chinata,to Sha ta bashi a Baki Yana driving tana bashi a baki Yana Sha itama tana Sha.

Yar China tace Yaya Wai kaji Yar Aamnan nan da iyayi Wai Ni zata koyawa wani darasi,Maganar Aamna ta gwada sabo da Aamna akwai Iyayin jaraba tunda me gyara ta koya Mata shike Nan,Yar China tace Wai a gaban saurayi nutsuwa akeyi ana Jan class,Allah na tuba Ni har a gayamin class Ni da kwana Nan na zana waec to ta Daya nake zuwa a aji,wanne ajin take so Naja idan ba na A.b.u Zaria take so na ja ba,Tawaga a ransa yace Zan Sha wahala kafin ta gane ya zanyi Ina son abata haka,a hankali zata canja,a gida ya sauke Yar china tare da rakata har Gaban Iyalle yace Iyalle ga Amanarki na dawo da ita,Iyalle tayi Dariya tace to an gode,sai da ya tafi Yar China ta fara bawa Iyalle labarin inda Suka je da Tawaga.

Kwana Uku Daddy da wasu dangin su Jibson aka Kai kudin auren Jibson,Humaira da Yar China,a Nan aka tsaida ranar aure gaba Daya Rana Daya dana su Jibson da Mashkoor,Ahmad yace baza ayi party ba tunda shima nasa ba ayi ba walima zasuyi iya abokai,Ranar da aka tsaida ranar aure Yar China Bata sani ba sai da ta dawo daga Islamiyya Iyalle tace to Yar Jikalle an kusa girma bikinki watan gobe an Kai kudin aurenki dubu dari da arba'in Yar china Tace me ya cinye goman? Dan jaraba su cika Mana ya koma dari da Hamsim,Iyalle tace uwaki Yar China Dan Iskanci to wasu ma dubu sittin ake Kai musu,sai kace ragon layya wallahi idan nice na fasa aurensa haba Iyalle dubu sittin fa? Ai gwara Kawai a bashi Ni Sadaka,Harararta Iyalle tayi Yar China tace yanzu fa Iyalle kwana Nan za a dinga ce min Amarya? Kwarai Kuwa cewar Iyalle,to gyaran Amarya fa ya za ayi ne Iyalle?

Iyalle ta rike Baki Tace oh yaran zamani mu a zamaninmu ai ko magana yarinya Bata Isa ba,idan aka Kai yarinya gidan miji sai miji ya kwana Uku Bai ga fuskar Amaryarsa ba tana lulle cikin gyalenta,Yana shigowa zata rufe kanta,Yar China ta kyalkyale Dariya tace hmm ai wallahi da nice sai na sa reza na Dan yanka gyalen idan na lulluba sai na dinga leko idona ta Yar kafar Ina ýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿ kallon Tawaga na,yanzu Kuwa Iyalle ai zamani ya canja idan kika zo gidana shayi Zan hada Miki me kauri na barki a Palo Ina can wurin Tawaga na Muna ta Jan zuga abin mu,Baki ji sunansa ba Tawaga Uban tafiya ma'ana ya ja runduna,Yaja zugar mutane shine uban tafiya,Dariya Iyalle tayi tace to kije kuyi magana da kawayenki akan gyaran Amaryar,Wanne kawaye ai wlh ba ruwana sai dai na gayyace su biki amma ni Zan Kai kaina wajen gyara,ai nasan Mata da yawa,ga makwafciyar mu Nan Ummin Zainab can zanje ta gyarani fes,Zaki ce Wani kawaye so kike su aure min miji Dama anyi candy duk gamu Nan jiran kadan mukeyi.
Chapter 63 · 0% Book details