← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 89

Sashe 67

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat ma kayanta akwai Kalar kayan mijinta Bash a jiki,Haka Nafeesat din Mashkoor komai a tsari sukayi,Sameera wacce itama hakance ta diga kyau tana ji an daura Aure tace Zawarci ya Kare Allah bamu zaman lafiya Kawayenta suna Mata tsiya da dariya Suka ce Kai marya.
Bangaren Yar China cikin Yan uwansu ne da Suka cika gidan suka fara kawo labari,Kanwar Babar Yar China Salamatu tace ga Ogana ya bugo waya Yar China an daura aurenku an gama kece ta karshe an daura,Yar China Wanda yanzu ma ta shigo gidan ta dawo daga makeup,ta Sha wani dakakken material Sea blue yafi Shaddar Tawaga dark sosai da adon Golden a jiki,Yana wani walwali Yana kashewa mutane Ido,daurin dankwalin da aka nada mata da Golden headtie tayi kyau kwarai,dama gata fara sosai,dukka Dangin su Yar China farare ne yawanci gado Suka yo Yan Fulani ne usul Yar China ce tayi Kama da yan China Kalar Idonta da Dan shape din fuskar sai ta Zama Kamar ruwa biyu irin Babanta Dan China Babarta Yar Fulanin Nigeria Haka ta zama,kawayenta masu yawan jaraba gari Guda,wani gida me kyan gaske da girma ya sha tiles ko Ina a Nan ta sauki bakinta abinci iri iri na Yan gayu ta bayar aka yo Mata na saukar Baki,su Friedrice with chickens ta Sha hadin salat,ga Waina da Miya,sinasir,wani faten dankalin turawa da nama,Jullof rice,Dan Iyayin Yar China harda fura da Nono me yawan gaske an zuba a robobi kamar rufaida dink,gurasa ta Sha cabbage da Albasa da tumatur,harda Dambun shinkafa,alala,Tuwon shinkafa,ga lemukan roba da ruwan Roba da sauransu Yar China har makwaftan da suke mutunci sai da ta sanar musu Kar suyi girki ranar bikinta kowa yazo a Nan zaici ya sha.

Yar China sabo da surutu da tsokana kowa ya santa ta kwashi jama'a da yawan gaske,tana shiga wajen Iyalle taje tace Iyalle Kinga kwalliyata yanzu na dawo nayi sauri sabo da kar Ina can a daura auren ban sani ba,Iyalle tace an daura fa ga Salamatu Nan ta fada Miki,Yar China tace ai nayi tunanin Wasa take min au an daura Iyalle? Iyalle Tace kwarai,Yar China Fuska ta rufe tana kyalkyala dariya dangi suna ta dariya Ana kallon ikon Allah,Iyalle tace Umma salamatu na Miki Alkawarin dubu daya kafin ki tafi gida,Salamatu tace Yar banza fitsararriya abinci fa an Kai duk abinda kika ce wajen kawayenki,Habiba ta Ajiye na angwaye daban suna can gidan suna ta tsare tsarensu na Yan karya irinku can,Iyalle Tace gayu gayu ai mu akwai Harkar girma, Ana zafi Yar China ta dauki mufici tare da mikawa wata Yar Budurwa yar gidan Salamatu Yarinyar zata Yi 14yrs tace ungo Marsiyya duk inda nayi kina bi na a baya kina min fifita bana son kwalliyata ta baci tun kafin angwaye su zo.

Haka Yar China take yawo da yarinya tana Binta da fifita Wai ita Amarya,tuni Yar China ta Shiga gidan da Kawayenta suke Suka lullubeta da tsiya duk gasu Nan Yan matasa masu tarin kuruciya sai haukarsu sukeyi,Yar China ta dauki plate da cokali tayi kida rakacal...rakacal sai ta tsaya cik tace duk ku saurara kuji an daura Aure tuni babu wacce naji ta min Addua,ihu Suka saki yeeeeee....sai Yar China wlh yeeew.....Duk sun Sha gayunsu sai kuruciya amma ba karya sunyi kyau,Habiba tace me Dj yazo dama munce ana daurawa zamu fara cashewa har lokacin Kai Amarya,Yar China tace iceko me Speakers Bakwai din Nan ne yazo? Suka ae mana,yawwa so nake a gigita kowa na unguwar nan so nake yau a San Yar China amaryace,Habiba kuje a fara sakin kida me fasa kunne,da fatan kunci Kun koshi? Suka ce ae har mun shirya na angwaye a palon da Muka ware za a sauke su,Yar China ta leka katon palon me kujeru na Alfarma ga girke girke daban daban an shirya na gayu gidan wata ce suna mutunci da Yar China shi yasa ta Basu gidan.

Su dai kawayen Amarya suna ta rawa da danginta suna murgude murgude,Ana ta liki Amarya tana Jan aji bata fita ba tukun,Bangaren angwaye Kuwa duk sunje gidajen amare an gaisar da surukai lokacin Aamna gidan su Yar China tazo Driver ya kawota a Arniyar mota ta zuba kyau na gaske cikin wata Shadda ta kece raini maroon,kowa Binta yayi da kallo Kamar me,gidan ta shiga ta Gaida su Iyalle ta musu Allah Sanya Alkhairi,fita tayi aka rakata wajen Yar China ta isketa a wani Palo tana Shan ac Wai Dan kar kwalliyarta ta baci,ga me fifita da mufici tana gefe idan ta fita waje tana fifita Mata.

Aamna sai kallon Yar China takeyi tayi kyau fiye da tunanin me tunani Kuma a tunaninta ma Yar China ba Wani gyara kanta zatayi ba tunda taga kamar Bata da nutsuwa sai taga sabanin Haka Yar China ma kamar tafi duk Amaren yin kyau,shigarta da dinkinta ya birge,Aamna ko Yar gidan Gomna abinda zata Yi kenan,Bayan sun gaisa ta Mata Allah Sanya alkhairi,Yar China tace Aunty Balaraba dama Zaki zo? Gani kin ganni cewar Aamna tana dariya,Yar China wajen abincin ta nunawa Aamna tace ki zuba abinda kike so Aunty,Aamna tace na koshi,ai Yar China ba Wani tunani tace ai Kuwa karya ne wlh sai kinci duk Wanda yazo bikin Yar China sai ya koshi,Aamna a ranta tace Direct karya ma nake Yarinyar ta fini wauta Sanda Ina budurwa,Hannun Aamna Yar China ta rike tace nasan mu talakawa ne shi yasa baza kici abincin mu ba wallahi sai na fadawa Yaya Tawaga sabo da yasan irin zaman da zaiyi dake,Aamna ba shiri ta shiga bude abinci tayi mamaki komai na Yan gayu harkar girma,harda wata Green spaghetti ai Yar China tafi ma sauran Amaren yin abincin girma,dama bikin da kake sa rai bazaiyi armashi ba shike yin kyau,Wanda kake ýÿÿÿ

! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  tunanin zaiyi Dadi Kuma sai kaga ba shine ba,Aamna dai taga zahiri Kuma taji tsoro tasan tsaf Yar China zata fadawa Tawaga idan Ahmad yaji Kuma tasan sauran bai iya Fushi ba,sai ta ebi gurasa,ta zuba dankali daban yasha nama, ta zauna taci da yawa tare da Shan lemo da ruwan,Yar china tace to kin taimaki kanki wallahi da Baki ci ba sai na Kai kararki wajen Oganki direct,Aamna tayi Dariya Tace na fita sul to,Yar China cewa tayi ai har cewa zanyi kin harareni Ni da Iyalle ta,Aamna tana dariya tace Allah ya rufa min asiri King wlh Bai Iya Fushi ba sai ki jaja min,Dariya Yar China tayi tace to ki kiyayi tabani wallahi sai na kulla Miki sharri Dan Baki Sanni bane bani da kirki ban San na gida ba,komai sanina da mutum ya min laifi baruwana cinnaka ce ni,Aamna tace Allah baki hakuri suna dariya Yar China tace muje yau sai kinyi rawa,ta ja Hannun Aamna Suka fita wurin Dj.

Suna zuwa wajen angwaye suna zuwa a motoci a Nan suka Sha kallon shagali sauran gidajen Amaren duk ba mutane ba kida kamar ba biki ba sabo da sunce auren yazo ba shiri,ai Nan Suka ga bataliyar Yan Mata an dau wankan sugar ba karya,sai ka kula matar aure baka sani ba kayi zaton Yan mata ne,su kansu bikin sai ya birge su,suka bige da kallo Ana ta rashin kunyar rawa,ga fararen mata na tashi sabo da Yar China danginsu ga Kawayenta na musamman sun Shiryawa bikin,Tawaga motarsu Daya da Jibson da Ahmad sauran Kuma su Brown ga wasu frnds na daban ma,Tawaga Yar Chinansa ya fara hangowa yaga Ana ta Mata fifita Ana take Mata baya ta rike Hannun Aamna gam,Dariya yayi yace Uhm kaga Ruhina can,abokai duk Wanda yaga Yar China akace amaryarce sai yayi Dariya tana ta hada hada,Fitowa sukayi Ana ga angwaye sunzo Ana ta kallonsu amma Ina Yar China biki yayi biki tuni ta kutsa Kai cikin filin rawar,aka tsaya da kida,Mc tayiwa magana abinda zaice da Yan bikin.

Ai Kuwa Mc yace Amarya tace tana yiwa kowa Barka da zuwa wannan bikin nata me Albarka,tace a fada muku a madadinta ita Amarya Sadiya Yar China da Angonta Aliyu Tawaga Uban tafiya duk Wanda yazo bikinta Bai ci abinci ya koshi ba baza su yafewa kowa ba,sannan Basu daukewa kowa rawa ba a wannan fili ko tsoho ko tsohuwa.

Dariya aka dingayi Wanda Suka San Yar China sun san zata aikata,angwaye suna ji Suka dinga dariya, Amarya aka Kira tsakiyar fili da angwaye,tunda Suka fito ake kallon matasan musamman Ahmad kamar Mata zasu cinye shi da kallo Nan take Aamna gaba daya farin cikinta ya dauke kishi ya kamata,Kamar zata Yi kuka,Ahmad Yana kallonta yayi Murmushi ta sake hade rai yasan dalilin,Yar China ma ta kula rada tayiwa Aamna tace ki saki ranki Dan Allah duk Nan wace ta fiki kyau? Babu me aure Miki Miji haba yau Naga mayyar miji,ba shiri Aamna ta saki ranta tasan halin Yar China yanzu sai ta tona Mata asiri.

Angwaye ne Suka shiga suna zuba Yan dubu dubu kowa da bajintarsa,ana kwashe kudi Ana ta yiwa Amarya liki,Amarya batayi rawaba ko kadan Wai aji take ja,duk Amarya me rawa bata da aji cewar Yar China shi yasa Kawai Hannunta Tawaga ya rike Suka tsaya a tsakiya Ana musu liki, ta yafito babbar kawarta Habiba da Hannu.
Habiba ta karaso filin tasan Shirin Kawai ta fara liki itama,Haka kawaye Suka shigo Suma,Tawaga Hannun Yar China ya riko ya Bata Yan dubu dubu itama tana lika masa,sai da suka gama Suka fito daga filin tare da tsayawa a jikin mota gaba Daya har Yar China.
Chapter 67 · 0% Book details