Sashe 40
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa Karamar jaka ya dauka tare da shirya kayansa, Mashkoor ne ya kaishi Airport,sanye yake cikin wata Gezna Sea blue,Fadin kyan da yayi Bata Baki ne,kitsonsa dai Yana nan,Da Yamma 5pm Mummy tana zaune a katafaren palonta tare da Humaira sai gashi ya buga Sallama,Mummy da tsananin mamaki Tace Ahmad nake gani ko wa? Dariya ya saki ya tsaya a Gaban Mummy ya wani juya ya juyo tare da yin safa da Marwa a Gaban Mummy yace ya kika ce Mummy,Mummy Tace Wai Kaine da gaske? Shekara Nawa Muna fama da Kai kazo ma gida kaki sai yau Katsam,Yace dama surprise na muku shi yasa naki fada muku,Mummy Tace uhm Kaine kake magana Haka a nutse Kuma cikin shigar hausawa wow,Humaira sabo da murna harda tsalle ta Rungume shi tana Sannu da zuwa Yaya,Yace sis kin Kara girma fa,Mummy ya Rungume tare da aniye jakarsa a gefe,Mummy Tace Humaira sauri ki Kira Daddy kice yazo ga Ahmad yazo yaga abin mamaki,Zama Ahmad yayi kusa da Mummy.
Daddy ne ya fito tare da tambaya me Zan gani Ahmad Yau Kaine a Lagos? Abin mamaki kaine,Dariya Ahmad yayi tare da mikewa ya wani sarawa Daddy Kamar Yana Gaban babban soja yace Daddy nine Mana,Sabo da farin ciki Daddy Rungume shi yayi yace Dole yau muyi Celebration yau King Guda a Nan gidan,Daddy gwada yanda suke magana ta Niggogi yayi yace Fresh Boy,the King of Guys Ahmad yace yes ooooo na me,Daddy Yace aje a shirya girki yau Ranar murna ce,a Kira Saddeeq da Mufeeda su zo,Haka aka shirya girki iri iri suka zauna a Dining Saddeeq,Mufeeda,Ahmad, Mummy,Daddy da Humaira Ana ci Ana Hira Ahmad ya fara Basu labarin Aamna,Mummy Tace dama Aamna ce? Gaskiya nayi murna.
Ahmad Yana cin abinci yace Ina Baku labari da kuke gani na Haka harfa masallaci nake zuwa Sallah, Saddeeq cikin murna yace Inyeee, Mashaallah cewar Daddy,Ahmad yace Kuma shaye shayen da nake Yi duk na rage saura kadan shima Zan daina Nan gaba,Mummy Tace Alhmdllh,Ya daki kafadar Sadeeq yace ae naji Dole na fada gaskiya Daddy Yarinyar Nan Ina sonta duk ta canja Ni abinda nakeyi duk na rage Ina ta Zama mutumin kirki kullum,Humaira harda tafin Jin dadi,Daddy yace duk itace tayi aikin Nan Wanda munyi shekara da shekaru mun kasa,Ahmad yace sosai itace Kai Daddy Haka idan time din Sallah yayi zata kirani a waya,Muryarsa ya makale Wai irin muryar Aamna zai gwada musu Tace Kaje kayi Sallah a Jam'i Babyna,Ni Kuma idan banje ba sai naga Kamar ma ba sonta nakeyi ba sai na tafi,ai Sanda Sonta ya kamani Daddy na Sha fama,lokacin Baku ga danku ba,susucewa fa nayi,Dariya suka saki,Mummy tace gaskiya tayi Aiki,yace Bari na Kira muku ita kuyi Mata godiya,Nan take ya Kira Aamna ta daga yace kunji zakin muryarta ya saka Wayar a Handsfree kowa na ji Aamna Tace Babyna kaje lafiya,Mummy ya kalla yace a hankali kunji kunji ko yanda take ji dani, Saddeeq ya kalla yace ji Murya dan Allah,Dariya Saddeeq yayi yace to anji,Mummy ce ta karbi Wayar Suka gaisa da Aamna ta dinga zuba Mata godiya da Addua,Daddy ma yace bani ita nima,Haka su Humaira da Mufida tare da Saddeeq duk sun Mata godiya.
Ahmad Wayar ya kashe yace Kuma k
Ullum dare muke rabawa Muna waya,Babu kalmar Dake tsaya min a Rai irin idan zamuyi bacci Tace Sweet Dreams Baby har dodon kunne na sai yayi rawa Karrrrr....Dariya suke ta Sha Yana ta Basu labarin komai dama ba kunya yake ji ba,karshe yace gaskiya Maganar Serious Yarinyar Nan kuyi Mata gagarumar kyauta sannan kuje har gida ku gode Mata.
Daddy Yana dariya yace zamu je ne sai Nan gaba,yanzu tunda ka gyara halinka kuje da Saddeeq wurin siyan mota ka zabi motoci ko Nawa kake so sababbi Zan siya maka,wancen Dana kwace sun tsufa latest zaka zaba,yace thanks Daddy.
Tunda Ahmad yaje suke Shan labarin Aamna kullum,har kwanakin Daya kwasa Suka cika,Mota Daya tal ya zaba wata muguwar jibgegiya me tsada baka,kowa yaga motar yasan ka hau mota,kafin ya dawo an kawo motar Kd an hadata an Mata duk abinda yake bukata,Su Jibson sai murna suke Yi.
Ranar da ya dawo Kd Bai je wajen Aamna ba sai washe gari ya dau uban wanka cikin wani black trouser pencil da rigarsa me dogon Hannu,Irin kyan Daya zuba ba a magana,Sabo da Iya shege su Baba suna tsakar gida sai gani sukayi Ahmad ya shigo ya Bude gate da Kansa ya koma ya shigo da wata azababbiyar mota,Dukkansu tsaye suka Mike har Aamna Dake Shanya wanki,Mama tana gefe,Idonsa ya rufe ya manta Yana Fitowa daga motar ya Rungume Aamna,itama Haka ta kankame shi suka ki sakin juna,sai da Baba yayi Gyaran Murya,Sannan Ahmad da borin kunya yace na manta ban kula ba Sannan ya rusuna ya gaisar da su,Mamaki ya Kama su Mama bayan gaisuwa harda rusunawa mutumin da ko kallo Basu ishe ba,Baki Mama ta tabe,Aamna ta kalli motar Tace wannan fa? Yace au mota? Yace dama Ina da su da yawa ma Baba ne ya kwace Dana ki shiryuwa,Murmushi Aamna tayi Tace tayi kyau,ko kina sonta ya tambaya,Tace a'a ai kayanka Kamar Nawa,idan kina so ki fada min sai na bar Miki ita,Aamna Tace na gode Baba ya galla Mata Harara Yaja kwafa ta musu asarar mota,je ki shirya muje yawo,Aamna da sauri Tace to tana murna taje ta cakare ta fito cikin Atamfa taji dinki cif ita,Da Kansa ya Bude Mata mota ta Shiga sannan ya rufe suka tafi,Wuraren hutawa sukaje suka dinga holewa Suma idan ka gansu abin sha'awa.
Tunda ya dawo kusan kullum sai ya Kai Aamna Wuraren hutawa,Haka Siyayyar kayan birgewa ko yaushe Yana dawainiya da ita.
Bangaren su Jibson kuwa bayan sun bar wajen Sameera sai bayan sati Daya Sameera ta Basu damar komawa,Wannan time din harda kaisu wani palon Baki,Bash ya kalli Jibson suka Yi Signa, Sameera ta dau wanka Kai sai ka rantse Bata taba aure ba,Lemo ta kawo musu da ruwa ta zauna,Jibson yace me Hannun karfe da Alama na jefa na cafke,Dariya Sameera tayi tace ae,Jibson yace to ya Maganar Dattijon naki? Sameera Tace na daga Masa red card,Jibson yace kin birge ni ai tsoho sai tsohuwa,Bash yace sai na dinga hango ku a High table Ana wedding Dinner,Cikin rashin sa'a sai ga Baban Brown yazo zance shima ya Sha shaddarsa tare da wani Dattijo abokinsa,Baban Sameera dake abokansa ne Direct palon ya shigar da su sabo da Bai San da Baki ba,ai suna shiga Suka yi Ido hudu da su Jibson suna ta Hira da Nishadi,Baban Sameera yace ai ban San da Baki ba Nan ya janye su Baban Brown suka koma dakinsa,Jibson ya kalli Bash suka kyafta ido,sai Suka Mike suka Mata Sallama suka tafi da sauri,Shima Baban Brown cike da bacin Rai ya tafi gida tare da Kiran Mubaraq yace lallai su zo tare da su Jibson,Babu Bata lokaci Brown,Jibson da Bash Suka Amsa kiransa,suna zuwa ya dinga bala'i yace Dan wulakanci Baku San bazawara ta bace? Jibson yace yo Baba Allura cikin ruwa me Rabo ka dauka,tunda Nema kakeyi muma shi Muka je.
Mene zaka damu?
Brown yace Baba Kamar takara ne Kuma cikinku duk Wanda ya same ta murna zanyi sabo da idan Kaine zanji Dadi tunda Baba nane,idan su ne Kuma abokai nane, ai takarace ku gwabza Kawai Wanda ya lashe zabe muje muyi Masa Allah Sanya Alkhairi,Dattijon yace okay Wato na gano ku shi yasa Yarinyar ta juya min baya,idan naje Bata saurarata Ashe kune kuke hure Mata kunne,Bash yace au Baba ta fara juya Maka baya? Baba bai San murna zasuyi ba yace ae Mana,ta daina kulani ko naje sai Harara,Ihu Bash yayi yau akwai Party za Sha Zanku dance,mun lashe zabe,Baba yace zanyi maganinku nasan me zanyi ku tafi ku bani waje mutanen banza lalatattu masu takara da ubansu,Kai kuma Mubaraq Wato abokai sunfi uba ko zaka zo ka sameni,tafiya Suka Yi suna ta dariya an Juyawa Abba baya.
Ahmad kuwa yau Saturday Shiryawa yayi ya jibgowa Aamna siyayyar kayan makulashe zai je,Lokacin 5pm Zuhra ta zo da Siyama ga Mama a zaune suna Hira,Ahmad yazo Kofar palon hannunsa dauke da ledar take away,zai shiga kenan sai ya tsaya cak Jin an Kira sunansa Siyama Tace Aamna baza ki hakura da Auren mutumin Nan ba,tunda kin Gama chanjashi ki kyale shi Haka,Aamna Tace ai Bai Gama shiryuwa ba,jira nake sai na Gama canja shi gaba Daya sai na zare jiki na,Siyama Tace yanzu shine ya kamata ki zare jikinki,Zuhra Tace Aamna Baki da hankali wallahi dabba ce ke wallahi Baki San me kike Yi ba Kuma duk da kin girmeni, Ae naji Ni dama Dan na canja shi ya shiryu na Amince da soyayyarsa Kuma ai na taimaki Iyayensa,Ahmad ya Gama ji tsaf,Nan take zuciyarsa ta hau Bugawa da karfi,hankalinsa ya tashi,Idonsa ne yayi ja sosai,jijiyoyinsa Suka firfito,kasa hakura yayi gwara ta San yaji,Palon ya banko kofa da karfin ya shigo ciki, duk suka juya a tsorace suna Kallonsa.
Wani haki yakeyi da huci Kamar zai mutu duk sai da suka tsorata,Aamna wacce tuni ta fara kuka sabo da ta tabbatar yaji me suke tattaunawa,Bata taba nadama irin wannan ba a rayuwa,Kallonta yayi Idonsa ya ciko da kwalla Yana Ina Ina duk ya rude yace ki fada min abinda naji kina fada yanzu karya ne,cikin karaji yace kice mafarki nakeyi,kice karya ne abinda naji....Aamna tana Rusa Kuka Tace tsaya tsaya Zan maka bayani,cikin tsantsan tashin hankali yace bayanin banza,me Zaki fada min,me Zaki fada min,Kansa ya nuna yace Ni...Ni.....Wai Ni kika yiwa Haka....kin San karya ne kika ce kina so na?...sai da kika dagani sama sannan kika sake Ni na Fado....me na Miki Haka?....Wai duk abinda nake Yi a kanki ?...kujera ya daka da karfi yace Bari kiji Ina mugun kaunar Mummy na fiye da komai a duniya Amma duk abinda Tace nayi bana Yi,Amma ke duk abinda kika ce sai nayi,sanadinki yanzu Sallah Bata wuce Ni,Shaye shaye sabo da na faranta Miki na daina.....Amma....Amma....rasa me zaice yayi Idonsa ya zubo da Hawaye yace tunda na San kaina ban taba zubar da Hawaye ba sai yau kika sani Yana magana cikin karaji duk ya girgiza su ya haukace musu gaba Daya,Mikewa Aamna tayi tana kuka Tace wall....