← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 89

Sashe 30

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bucket Aamna ta kawo Masa har biyu ya nannade Hannun jallabiyarsa dake me dogon Hannu ce,agogonsa ya cire ya ajiye gefe,Yace Ina kayanki a nan? Aamna ta Tace ka gansu a nan,yace Miko ta kansu Zan fara,ai kuwa ta kwaso ta bashi a gabansa kala hudu sai su Hijab da Vest yace idan an Gama sai kije ki cire na jikinki suma a wanke su yau baza ki kwana da Kaya masu dirty a gidan Nan ba,Baba Yana gefe yace Uhmmm.....Sun kasa magana suna tsoro Dan kwaya ne sai ya birkice musu yanzu.

Ahmad wanki ya fara baya wanki Yana wanke kala Daya Hannunsa ya fara Dan fashewa Amma ya maze yaci gaba da abinsa,Kugunsa ne ya fara ciwo sabo da sunkuyo amma idan ya Kalli Aamna sai ya fasa mikewa ya huta sabo Kar ya Gaza,Haka ya wanke kayan Aamna fes ya kwashe kayan Baba da Mama Yana tayata suna wankewa ya kusa wanke na Baba,Mama ganin banza ta Fadi sai tace ke Aamna tashi ki barshi ya karasa wankin ki Shiga kitchen ki Mana girki,Ahmad yace ya Zaki ce ta tafi? Mama Tace Kai kace Super Man ne ai sai ka karasa ita ta Mana girki, to Aamna ta furta ta tafi ta bar Ahmad,tana tafiya ya Mike tare da dauraye hannunsa ya kwashe Takalminsa a Hannu da agogonsa da wayarsa,Mama Tace ya zaka daina aikin,dama yayi masifar gajiya,da masifa yace Ni na gaji bazan iya ba dama na gaji yayi tafiyarsa da sauri,Mama tana Kai...Kai....Amma ko juyowa baiyi ba ya hau machine dinsa ya bar gidan.

Mama da masifa ta shiga wurin Aamna Tace to ya gudu sai ki Koma ki karasa yace ya gaji shi,Dariya abin ya ba Aamna dama tasan karfin Hali ne Kawai Haka ta fito ta karasa Mama tana ta masifa taje taci gaba da aikin girkinta.
Ahmad kuwa a gajiye ya shiga gida Yana dafe Kugunsa ya Iske Mashkoor Yana kallo,Yana yatsina Fuska ya zare rigarsa daga shi sai Singlet da gajeren wando ya fada saman kujera Yana bawa Mashkoor labari yace yau wanki na tayata wash...bayana...taimaka ka siyo min pain killer a chemist kazo kayi min gashi da ruwan zafi wayyooo bayana My waist Yana magana da kyar yace yatsuna sun fashe ....Ni..Ni...nine nace Super man ne Ni, Mashkoor ya dinga dariya yaje ya siyo Masa ya dawo tare da hado ruwan zafi ya dinga gasa jikin Ahmad,shi Kama sai Kara da wayyo,Kwana Uku Ahmad Yana jinyar jikinsa kafin ya warke ya dawo normal lokacin Aamna Bata ganshi ba.

Yau Juma'a cikin sababbin dinkunansa yasa wata farar Shadda kamar ka sace shi yanda ya zuba kyau,calabarsa ya daure ya shirya Yana kamshi, Mashkoor ya kalle shi yace ban taba tunanin zaka ja Ni cikin Harkar Nan taka ba,kwana Uku ko Kofar gida ban leka ba wannan wacce masifa ce Wai,Gemunsa yake tajewa Yana shafe shi da wani turare Mai kamshi yace Ni fa na fara gajiya da Harkar wani Kawa da Abokin Nan ya kamata ta San me nakeji a Raina,Mashkoor yace ka bani dama Ni naje na fada Mata kana sonta,Baka da hankali an ce maka sonta nakeyi Kuma ko sonta nakeyi wani ne zai fada Mata Ina sonta ba Ni ba,ai Ni abinda nakeji a Raina game da ita Zan fada Mata ba Wani love ba.

Mashkoor yace to yanzu fada Mata zaka Yi? yace ae direct Zan sameta gaba da gaba na fada duk irin abinda zuciyata takeyi idan na ganta yau yau din nan,Allah ya bada sa'a cewar Mashkoor,Fita yayi abinsa Musa me Gadi Yana a dawo lafiya ranka ya Dade,Ameen ya Furta yiyiwa Machine dinsa key ya fita zuwa Shagon Aamna,tana tsaye tana sallamar wata ta siyi kayan kamshi ta hango shi yayi parking,Murmushi tayi Tace Sannu da zuwa,Kasa magana yayi sai kallonta yake Yi har ya karaso inda take ya tsaya a gabanta daf da ita Kamar zai shige cikinta Kuma ya Bata Rai zuciyarsa ce Kawai take bugawa,kasa fada Mata yayi yace ya gida fuskar Nan a daure,Lfy Alhamdulillah ta furta tare da cewa shigo ka zauna Rana,shiga yayi Yana ta Fushi,Tace fushin me kakeyi yau Haka? Kadan ya kalleta Bayan ya zauna a farar kujera yace da zuciyata nake Fushi ita nake nunawa bacin Raina,Dariya ce ta Kama Aamna Yana ta kallonta a ransa yace kin cuceni zuciyata bazan yafe Miki ba Kuma yau Bari na koma gida sai kinci ubanki,Me ta maka zuciyar Aamna ta tambaya yace Ni kadai na San irin wulakancin da take mini Amma ba komai Yaja kwafa,Aamna ta sake kecewa da dariya Tace kana da abun Dariya wlh,Kawai sai ran Ahmad ya baci shi ga abinda ya dame shi ya fada ya kasa fada duk akan Aamna Dan rainin hankali ta sashi a gaba tana ta dariya,a ransa yace na komaýÿÿÿ

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ ma abin Dariya na koma Comedian ba komai yayi Shuru.

Har ta Gama dariyar ta dakko Gyada soyayya Tace ga Gyada muci,ganin tasa hannnu a Ledar ta Eba tana ci sai shima zai Eba Aamna Tace tsaya na bare maka,bare Masa tayi Guda biyar ta zuba Masa a tafin Hannu Tace to ci,kallonta yayi sannan ya zuba a bakinsa Yana daga zaune Yaja baya yayi wani tangal tangal Kamar zai Fado Aamna ta rike kafadarsa da sauri tana tambaya lafiya???yace Dadi ne ya kwashe Ni sabo da hannunki da ya shafi jikin gyadar nan,Dariya Aamna tayi Tace Kai Ni nayi zaton ma wani Abu ne,wani English novel ta dakko na love tana karantawa Tace ka San littafin Nan? Na Mene ya tambaya? Love Novel ne Baki ya tabe yace sai ku wannan ai,Mayafinta ne ya Dan zame kadan gashin Gaban goshinta ya bayyana wani yala yala,Hannu ya sa tare da jawo mayafin ya gyara Mata Aamna dai mamaki yake Bata kamar ba shi ba,duk irin kiyayyar Daya nuna Mata tana ina ne? A ranta Tace Anya ba Yana da manufa a kaina ba kuwa? Gaskiya Zan nemi shawarar Siyama.

Kiran Sallah aka kwala Sallar Juma'a,Aamna ta kalle shi tace yanzu za'a fara khuduba sai muje Sallah ko? Da sauri ya girgiza Kai yace a gida zanyi anjima,Jam'i Yana da Lada fa? Yace na fiki sani ai, kin San kuwa Islamiyya Nawa nayi a duniya? Kin San saukata Nawa? Aamna Tace Dan Allah muje tare,a ransa yace Yarinyar Nan fa zata fara juyani karka sake wannan Yar tatsitsiyar ta juyaka a banza,ai ba sonta kakeyi ba da har zata juyaka,wata zuciyar tace Amma idan kaje Sallar zata ji Dadi zata samu farin ciki,Kumatunsa ya Mara a hankali yace Kar ka Bari ta juyaka ka dawo hankalinka,mikewa yayi yace Zan tafi,Tace Nima tafiya zanyi zanje gidan Zuhra,yace kin fiye yawo to na fasa tafiyar Zama ya koma yayi Dole ta zauna,Lokacin Sallah yayi Yana kallo tayi Alwala tayi Sallah a Nan shagon,tana idarwa yace Sannu da kokari,Fuska ta Bata tace Dan Allah kayi Sallah Kar lokacinta ya wuce,Shuru yayi Kuma yaki tashi sai yaga tayi Fushi ta zauna,Fuskarta ya leka kadan a ransa yace akan Haka har tayi fushi,Bari to na Yi Amma badan fushinta ba,Mikewa yayi tana kallo yayi Alwala ya Tada Sallah murna tayi ta saki ranta ta juya tana kallonsa a nutse yayi sallarsa kasancewar Bai Sha komai ba,Yana idarwa ya Mike ya fice tare da tafiya ko Sallama bai Mata ba.

Mashkoor kuwa Yana can a gidan Ahmad tare da su Jibson gaba Daya Yana ta Basu labari yanda Sarkinsu ya lalace,duk sukayi tagumi suna jimami,Jibson yace ai kuwa sai munje har inda yake tayata siyar da citta mun kure shi,yanzu King ne ya lalace Haka abin haushin Akan wannan Yar Yarinyar Aunty Balaraba cewar Bash,Mashkoor yace yanzu idan kaga shigarsa Daya canja kamar Limamin masallaci,Salati suka saki Tawaga yace duk akan Yarinyar nan lallai sai munci ubanta kuwa tunda ta mayar Mana da King Haka, Mashkoor yace Uhm Baku gani ba har wani sharemu yake Yi ba Amma muyi Masa Uzuri ai King ne sai abinda yace,Allah sarki masu shaye shaye da hankalinsu sun San Amana da abokantaka duk abinda dayansu ke so suna so,sannan basa mantawa da Alkhairi da zaman tare,shi yasa sun Shaku da juna sosai.

Ko da Ahmad ya shigo ya Iske su tafawa sukayi ya haura sama,Yana shiga wayarsa ya dauka tare da Kiran Sis dinsa Humaira,Humaira Tace Yaya na? Ya kake? Ba lafiya sis Dan Uwanki ya fada cikin bala'i,Humaira ta tsorata sabo da Bata taba Jin yayanta Haka ba,Kamar zata Yi kuka Tace Yaya mene ya sameka? Sis wata ce Nan idan na Ganda zuciyata kamar zata fito ta fado,sai ta dinga Yi min kida me zaki,Humaira Tace Kamar ya? Yace idan fa ban ganta ba bana iya bacci,sai na ganta nake samun nutsuwa,Haka idan naji muryarta sai naji Kamar wani kidan goge sabo da Dadi,gashi tsoronta nakeyi sai naji na kasa fada Mata me nake ji,Yanzu ya zanyi? Humaira tayi zaton zaice Aamna ce Amma yace Mata wata,Amma duk da Haka tayi murna yayanta ya fada soyayya,Tace Yaya kaje ka sameta karka ji tsoro Kawai ka fada Mata me kake ji,ka daure Haba Yaya kamarka wace zata ce baka Mata,Sis Nifa ba sonta nake Yi ba Kawai dai Ni na fada Miki abinda nake ji,Humaira tayi Dariya tare da furta ka fada Mata karka ji wani shayinta kaji,yace to sis Zan gwada ya kashe wayar,lokacin da yayi wanka su Jibson sun tafi sai Mashkoor sai shi.
Chapter 30 · 0% Book details