← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 89

Sashe 17

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari 9am ya tashi kasancewar baiyi shaye shaye ba,Room din dake cike da kayan Exercise ya shiga Yana ta motsa jikinsa sai da ya Dade sannan ya fito sanye cikin kayan gym dinsa bakake yayi kyau,Yana Fitowa ya Iske Aamna har ta Gama gyara ko Ina na ciki,kamshi yaji a kitchen lekawa yayi ya hangota tana ta soye soye, Shiga yayi fuskar Nan ba Rahma cikin Muryarsa ta Yan kwaya yace bani kasko zanyi girki,Aamna Tace ga wasu Nan ka dauka Mana Kuma ma ai gashi Ina girkin da Kai sai muci wannan,cike da bala'i yace da wannan nake so nayi,gidanki ne ko Ubanki ya Siya min kayan kitchen ne? ai kayan Mijina Kaya nane Kuma wallahi bazan baka ba,baka Isa ba kayi kadan kayi karami da yawa na baka kaskon nan, sabo da Nan gidan Mijina nane Kuma gida na yawwa eheee ....Mari ya dauke ta dashi garin Jin zafin Mari Aamna ta saki ludayi ya Fado saman kafarta gashi yasha Mai na suya me zafi Nan take ya kone Mata wani Dan bangare a kafarta,Ihu ta saki ta durkusa kasa Amma duk da Haka Bai kyaleta ba ya tallafe Mata keya ya dauke kaskon da man Baki Daya da dankalin ciki ya watsa a cikin Sink,har kankon ya Bari cikin Sink,sabon kasko ya dakko ya fara Girkinsa,Aamna ta Mike cikin bacin Rai da Hawaye a fuskarta ta tattaro karfinta ta durma Masa duka a gadon baya ta arce da gudu,shi ko jin zafin dukan ma baiyi ba,ita Tunaninta ta Rama,Zuma ta dakko tare da shafawa a kafarta iya inda ya kone,Palo ya dawo da kwansa soyayye da tea da wani snacks Kamar bread,Aamna Fitowa tayi dama tasan shi Bai zuwa Dining Sam,Yana Palo zaune saman kujera ya wani kishingida a Haka yake cin abinci,Aamna a ranta Tace duk abinda ya shafi Sunnah da dabi'a ta Musulmai baya Yi Sam,abinci a kwance za a ci,a kasan center carpet ta zauna tare da nannade kafafu kamar wacce zatayi karatun Qur'ani ta zuba Masa Ido,Hannu ta zura da sauri ta zari soyayyen kwai fefe Daya,ta fisge snacks ta balli Rabi ta Ajiye Masa,ta Buda tsakiya ta sa kwanta ciki ta rufe,Bai ko kulata ba,tana ta ci yasha tea da yawa saura Rabi ta dauke cup din ta gudu,dama ya koshi shi take uban gudu da tayi zamanta ma shi baida time dinta yanzu.

Mama zaune take a Palo tana gyara wake Baba yayi wanka ya Sha Yar shaddarsa zai tafi kasuwa ya daga Hannu sama yayi wata Hamma tare da Mika yace Alhmdllh Aishatu sakayau nake jina,Kamar wani sabon musulunta,ji nake Kamar yau aka Yi min wankan tsarkii,sabo da mun Aurar da Yaran Nan mun huta Kuma Alhmdllh Bamu siyar da akuya ta dawo tana goge Mana danga ba,Mama Tace Bari Kai dai Baban Zuhra ai idan na tuna musamman Zuhra tana can tana zamanta lafiya sai naji Ni kamar Ina cikin watan Ramadana Naga Kuma Daren lailatul qadri,ita kuwa Aamna mun fita ko ba soso ba Sabulu,ta koma bangaren danginta suje can su karata,gashi Dake so suke su Aurawa Dansu Dan Giya har da bani jarin Million Uku cewar Baba shima,Mama Tace yo ai mun gano wayon badan Allah aka Bamu ba,harda wani gida ,Baba yace ai Ina sani na kwantar da Kai na nuna musu mutunci na hada dabara nace su bawa Aamna auren Ahmad zai shiryu.

Hahaha Mama tayi Dariya Tace Dantijara wannan ai bazai taba shiryuwa ba,ita Kuma Aamna nasan kwadinyin tsiyarta shi zai zaunar da ita shi yasa kaji shuru,ko mun Mata waya sai Tace lafiya suke,Munafuka cewar Baba tana can tana Shan wahala,yanzu da zamu je sai Munga ta rame,Kaga yanzu har tayi kusan wata Guda da Aure, kudin Sadakinta data Bamu mun karbe ba ruwanmu sauran Kuma da Tace a siya Mata wake a ajiye a Kauye fa? Baba yac ae gobe fa zamu je gidan Aamna sabo da karta gano cewar Bamu damu da ita ba ko Bamu dauke a matsayin 'ya ba sai mu tafi Mata da kudinta mu Bata muce Kar tayi wannan sana'ar Kawai ta kashe kudinta,Mama Tace ita a dole me Neman kudi Ubanwa zai barta tayi Sana'a, Dan taga kudin sadakin Zuhra mun siya Mata Saniya a Kauye Ana kiwo shine itama tace a siya Mata wake,Mama Tace ai baza mu Bari ta Gane komai daga wajenmu ba,kamar yanda ta taso a Hannunmu ba yabo ba fallasa ita Bata Isa Tace Bamu sonta ba Kuma Bata Isa Tace muna sonta ba to yanzu ma hakane,musamman yanzu da ta auri jinin kudi,a hankali zamu dinga zararta kudi,so nake Nan gaba ta Bude min katafaren shago na siyar da kayan sawa na Mata cewar Mama,Baba Yana dariya yace ai Ni Kinga na samu jari.

Amma naga Harkar tayi min kadan dole Nan gaba Nima ta Kara min jari,Mama Tace na karbo wasu layu da guru idan munje Zan sa ta Kara daura su so nake sai na mayar da ita Yar bori da wayo sabo da idan Mijin nata ya gani yace malamai take bi kaga bazai taba sonta ba bare ta zauna a daula,lokacin mun yagi rabon mu,idan ya sako ta sai ta dawo ta zauna a shago na Wanda Zan Bude Nan gaba da kudin surukanta ta dinga siyar min da kayan.
Baba Yana dariya har da buga kafa yace kin iya planning,tunda Bata auri talaka ba Allah ya canja lamarinsa Kinga muma harka ta Bude sai mubi a Haka mu yagi rabon mu.

Siyama kwance take saman tsohuwar katifarta sai faman Juyi takeyi tana murmushi ita kadai tare da matse pillow a hankali Tace Kai idan ban ganshi ba yau bazan samu nutsuwa ba,Wasa Wasa a hankali sonsa ya Shiga Rai na daga ganinsa sau biyu sau uku,wata zuciyar ce ta gargade ta tace to Faisal din naki fa,Kuma Wanda kika haukace akan sonsa Mijin babbar kawarki ne, wata zuciyar Tace so so ne Amma son Kai yafi,a fili Tace duk yanda naso kawata ta samu farin ciki ai Bai Kai ga kaina ba,Kuma ma mene tunda Allah Bai haramta ba,abinda ya Dace na San yanda zanyi ya Gane Ina sonsa,kafin kawata ta rigani gwara Ni na rigata,zumbur ta Mike Tace dole na Kori Faisal na daina sonsa,Sam baya birge Ni yanzu,Akan Ahmad Zan iya koyar Shan barasa Nima Indai zai so ni,ta yanda Zan bullo kenan Nima na nuna Masa Ina Sha nasan zanyi Nasara,Mikewa tayi tsaye tare da jawo Wayarta ta danno Number Aamna.

Aamna kuwa daidai wannan lokacin 11am su Mashkoor su Biyar ne Suka zo tare da cike palon suna ta kurbar giya,Ahmad Yana kwance,Aamna ce ta fito sanye da Arabian gown black da Alama fita zata Yi,ta gansu a palo,kallo Suka bita da shi Banda Ahmad da ko kallo Bata ishe shi ba,Mashkoor ne ya galla Mata Harara ya furta anzo an aure Mana Sarkin mu,kina Bata Masa Rai a banza,Jibson ya ja tsaki,Aamna dai Bata ko kulasu ba,wurin Ahmad ta karasa ta Dan dukar da kanta saitin Fuskarsa Tace zanje kasuwa ba kayan Miya da kayan lambu ka bani kudi da Izni,Tsaki Yaja yace dalla Wai Ni na kawo ki ne,ki tafi ko Ina kika ga dama,Kudi ya jaro dubu Ashirin ya jefa Mata a Fuska yace dauki ki bani waje mayya,Su Jibson Suka kyakyace da dariya ba ji ba gani,Aamna ranta ya baci ta Harare su tayi waje abinta.

Napep ta shiga har kasuwar kayan Miya,duk abinda take bukata sai da ta siya,ta zuba komai a Napep zasu tafi Kiran Siyama ya shigo Wayarta,Fuskarta dauke da murmushi Tace Yar halak ya kike? Siyama Tace Ina Kofar gidan mijinki kina gida na shigo? Aamna Tace Ina kasuwa wlh Amma bani 10mnt yanzu Zaki ganni,Kawai ki shiga gidan Ahmad Yana Nan da abokansa kije kafin na zo Amma ki kula karki kulasu zasu iya Miki wulakanci,Siyama Tace to tare da kashe wayar Tace dama ba Dan ke nazo ba ai ta shiga taci Uwar gayu cikin lace Riga da skert wani ruwan kunun kanwa,Sallama tayi tare da Bude Kofar ta shiga dauke da Sallama,wani kamshi da sanyi ya daki Siyama, Siyama a ranta Tace shegiya Aamna akwai iya gyara,babu Wanda ya amsa Sallamarta cikinsu,shiga tayi Kawai ta zauna a wata kujera da bakowa,Ahmad ta kalla Suka hada Ido ta bangale Baki da murmushi Tace Ina kwanan ku,Suka kece Mata da dariya banda Ahmad da ya sake hade girar sama data kasa,a ransa yace an kawo min yarinya gida danginta sun dameni da zuwa gidana,Siyama tayi Shuru tana ta kallon Ahmad Kamar zata cinye shi,gefen Bash ta zauna Tace lemo kuke Sha ne? Kallonta Suka Yi Suka sake kwashewa da dariya,Bata hakura ba Tace Kai dama na sanka ma Brown ake ce maka ko ta nuna Mubaraq Brown,Siyama a ranta Tace Kan uba Taya Zan samu ko number Daya daga cikinsu ne? Tana wannan tunanin sai kuwa Jibson Sarkin son Mata yace Yan Mata kin hadu fa,Siyama tayi murmushi hankalinta na Kan Ahmad,Jibson yace da Allah bani number dinki Mana,ai da sauri Siyama Tace to dama abinda take so kenan ta kulla alaka da wani a ciki ko zata samu hanyar Shiga jikin Ahmad ta Haka,ta Bawa Jibson number ya Kira ta Nan take tayi Saving tana cewa ya matar gidan Bata kawo muku girki bane?

Abdul Tawaga yace ta fita fa,Cab Miji yayi Baki Amma matar baza ta kawowa abokan Miji abinci ba wannan wacce irin mace ce,Ahmad ne ya kalli Siyama kadan ya dauke kai,Tace Bari ta dawo ai dole ma na tayata ta shirya muku better,Jibson yace da kin kyauta Uwar Kinibabba,Siyama ta kalleshi da sauri Wato itace Kinababba,yace dama yunwa muke ji,suna Haka sai ga Aamna ta dawo da fara'a tayi Sallama.

Siyama ce Kawai ta amsa itama da fara'a Tace kawata kin dawo kenan,Aamna ta mikawa Siyama Hannu Suka tafa tace kinsan Ni jinin Larabawa ce Zan koma na tuno da Dan larabcina na Islamiyya Marhababiki ya Siyama,Kyaifal Ummati? Siyama tana Dariya itama da kalkala Tace Alhamdulillah...Alhamdulillah,Shukran cewar Aamna,Kujera ta nunawa Siyama tare da Furta Ijlis kawata,Siyama ta koma ta zauna tana cewa jalasna ya kawata,duk sai da suka Bawa su Jibson Dariya,Ahmad Kam Kawai Dan Baki ya tabe sabo da shi Yana mugun Jin larabci Dan Basu Sani bane.
Chapter 17 · 0% Book details