← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 89

Sashe 22

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aamna Tace Kai ku kiyayeni matar oganku ce Aunty ya kamata Kuna kirana bana Wasa da ku,Dariya sukayi Suka ce Aunty Balaraba daga yau,tun daga wannan Rana kaf abokan Ahmad sai dai sucewa Aamna Aunty Balaraba ita Kuma amsawa takeyi.
Washe gari da dare Aamna ta kawowa Ahmad Abinci ganin baici komai ba tun Rana,Ashe hakan data Yi shi haushinta yaji ya tsaneta ya gaji da takura Masa da take yi Kawai ya dauki abincin ya watsa Mata a jikinta stew din Allah yasa ba zafi ta Bata Mata riga,Taji Matukar haushi har ta fusata Tace barin gidan zata Yi ,da sauri ta dakko mayafinta,Yana ganin Haka sai murna ta kamashi,Aamna sai ta ganshi har murmushi yakeyi sai ta fasa tafiyar ta dawo gabansa Tace ranka ya Dade zanje na siyo Abu a shago tayi waje,ransa yayi bakikirin sabo da bacin rai tashi yayi ya tafi wajen Me Gadi Musa,Musa Yana Zaune a Bench Yana waya da matarsa Ahmad ya zauna a Bench din.

Musa cikin wayarsa yace da matarsa na Baki Ruhina gaba Daya,da sauri Ahmad ya kalli Musa yace baka da hankali idan ka Bata Ruhinka Kai Kuma ya zaka Yi da rayuwarka kenan ka bata Ruhin ka mutu kenan? Musa ya dagawa Ahmad Hannu Wai yayi shuru yaci gaba da cewa Ni gaba Daya na Baki duniyar Nan gaba daya ma Uwar gida na,Baki Ahmad ya bude da bala'i irin na Yan kwaya yace Kai...wai...to nufinka idan ka Bata Duniya mu da sauran mutane da muke ciki mu tafi Ina a Ina zamu zauna?ko sama ta Daya zamu koma,Musa ya kashe wayar yace a'a ikon Allah Oga Ni Matukar zata ji Dadi ku tafi sama ta goma Mana,Ahmad yace Kai Musa wallahi Indai zaka ci gaba da wannan furucin na soyayya wani ka Bata Duniya wallahi sai na koreka a aiki,akan me Dan wulakanci Muna zaman mu lafiya cikin duniya kace wani kayiwa wata banzar matarka kyautar ta,Baki Musa ya Bude sai Kuma ya tuna Ogan nasa Dan giya ne kwakwalwarsa da motsi Kuma Bai taba soyayya ba shi yasa.

Musa yayi Dariya yace Allah huci zuciyarka Oga ai duk kalaman soyayya ne ai duk abin karya ce,Kenan duk karya kake mata? Ahmad ya tambaya Musa yace ai Dan aji Dadi ne,yace kenan soyayyar da ake fada duk karya ce? Musa yace duk ita ake zugawa juna,Nima fa Oga cewa tayi ta bani zuciyarta,Baki Ahmad ya bude yace to yau duk sai kunci ubanku wallahi maza tashi ka dakko Cooler dole ta Ciro zuciyarta ta baka ka saka a Cooler,Musa Dariya ta Gama Kama shi,Yace zaka Yi Dariya da kyau yau sai naga ta inda zaka Ciro Ruhinka Dan Ubanka,Kai ba mala'ikan daukan Rai ba komai ba kace wani ka Bata ranka Dan Ubanka gashi kana motsi kana numfashi yau sai ka Bata ka mutu yanzun Nan,Musa ya sake kecewa da dariya shi Ahmad Bai San soyayya ba,yace tsuguna yau sai ka kinkimi duniya a kanka Baki Daya ka Kai mata har kauyenku sannan bayan ka Kai Mata mu Kuma kazo kasan inda zaka Kai mu,Musa yace kayi Hakuri Oga na fasa Bata wallahi bazan Bata ba na Kuma fasa karbar zuciyar Tata,Ahmad yace Yan iskan banza da ka Bata mu gani mana,Kun zauna Kuna biyewa Mata ya Mike ya fice daga gidan.

Aamna zaune take suna waya da Mummy,Mummy Tace Aamna me kike so a duniya ki fada min ko mene Zan Baki,Aamna Tace Mummy da gaske ko mene?Mummy Tace kwarai ai tunda kika iya jure Zama da Dana Ahmad a wannan halin ba abinda bazan Miki ba,Aamna Tace dama Ni burina idan na samu kudi naje Hotel na kama daki nayi kwana Uku Ina Shan ac,azo a gyara min room nayi order abinci naci nayi bacci,sannan Buri na na biyu idan samu kudi nayi wanka da ruwa Eva ko Swan,sannan naci abinci na wanke Hannu na da ruwan Roba,Dariya Mummy tayi Tace Anya kuwa Aamna kin Kai 25yrs ko kema kin fara Shan kwayar ne?Dariya Aamna tayi Tace Allah Mummy,to shike Nan ba yanzu ba ki Bari sai Nan gaba cewar Mummy sannan ta kashe wayar.

Da dare Ahmad zaune yake a bedroom dinsa Yana Danna System Aamna ta shiga dauke da tiren Abinci ta Ajiye Masa,Tsaki Yaja da masifa yace ce Miki akayi yunwa nake ji? Bazan ci ba ki dauke abinki tun kafin nayi fatali da shi,Wayarsa ce ta shiga Kara yaja tsaki sannan ya dauka yaga Humaira ce kanwarsa dagawa yayi,yace sis ya akayi ne Mene ne Zaki dameni? Yaya dama gobe zanzo na kawo maka Ziyara,Fuska ya Bata yace ke karki zo min Ni Kun dameni kije gidan Saddeeq Mana sai Dole waje na Zaki zo wannan Candy da kika Yi ai ta zame min masifa tunda damuna zakiyi Dan Allah ki fadawa Daddy ya saka ki a University da wuri Haba,Dariya Humaira tayi ta Shiga rokonsa Dan Allah Yaya so nake fa nazo na ganka please.....Shuru yayi mata,Tace Yaya Dan Allah zanzo kaji....ke mayya karki lashe ni ki tsotse min bargo yau she Zaki zo? Kwana biyu ko Uku Kuma Zaki Yi,Tace to Gobe Yaya da wuri zan bi flight sai kazo ka daukeni a Airport,Alright sai kinzo murna Humaira ke Yi harda godiya,Aamna tana jinsu ta dauke Abincin tayi gaba,me Gadi ta kaiwa gaba Daya.

Washe gari 2pm Humaira ta sauka,Aamna gani tayi ya Sha wanka cikin kananan Kaya wasu masu kyau ya fito ya hau wani machine dinsa Irin na Yan achaba Quilin ya tafi Airport,Humaira ta ganshi a machine ita Bata taba Hawa machine ba,ta Rungume shi tana murna ya janye jikinsa Yana dariya yace sis bana son wannan haukan kin girma ku Yan Lagos Baku da tarbiyya,Dariya tayi Tace Kai Yaya Kai fa yanzu muharramina nane fa,ku dai Kawai Kun dauki aladun turawa ya furta tare da rike Mata Hannu yace Oya hau mu tafi,ta kalli machine Tace Yaya kasan fa ban Iya hawa machine ba Kuma ai ya kamata ka aro mota ko ta abokai ce ka dauke Ni,Wanda Basu da motar kuma fa gasu Nan Ni ban Iya aro ba idan Zaki hau ki hau ko wallahi na tafi na barki iskancin banza Kawai ya fara bala'i,Humaira tayi Dariya Tace Kai Yaya ta ja kitson calabarsa tace da a Kano ne da tuni Yan Hisba sun Kamaka,Yace su ma Wanda suka Raina suke wa.

Daukanta yayi tare da daura ta a saman machine din,Jakarta Kuma ya daura a gabansa ya figi machine Kamar zai tashi sama Haka yake fyalla uban gudu da Humaira tana ta dariya ita Dariya yake Bata.
Aamna tana cin abinci a Dining suka shugo,Humaira ta taho da gudu zata tafi wajen Aamna Tace laaa Auntynmu...Auntynmu...da sauri Ahmad ya cafke ta yace ke wace Auntynki? Baza kije wajenta ba wajena kika zo ko wajenta? Humaira tayi Shuru yace muje sama,Murmushi Aamna tayi tace Barka da zuwa kanwata,Humaira ta dago Mata Hannu zanzo mu gaisa Aunty.....fisgar Hannunta Ahmad yayi Suka tafi sama Yana Hararar Aamna,Aamna Dariya tayi Kawai duk tayi laushi ta nutsu sabo da Duniya garata takeyi.

Hana Humaira Fitowa yayi sai da ya tabbatar ta shiga wanka sannan ya fita ya Mata take Away na abinci Wai baza taci na Aamna ba,Yana dawowa ya Iske Aamna da Humaira suna ta Hira suna dariya,Muzurai ya fara Yi ya karaso tare da fisgo hannun Humaira yace wa yace ki kula min kanwata ko kanwarki ce? Aamna tayi Masa shuru kawai, a palon Suka zauna Humaira gudun masifarsa yasa taci abincin nasa ta koshi,Humaira Tace Yaya yanzu a machine kake yawo?gaskiya Daddy Bai kyauta ba,Ke share wannan zancen Ni nafi Jin dadin ma machine Dina,Aamna ya kalla yace Baban wasu kuwa ko Tyre Bai da ita bare mota,Aamna Dariya Kawai tayi,Humaira tana ta Mata magana da Ido,itama Aamna tana maida Mata da Hannu da ido,Ahmad idonsu Kawai yake gani Yana motsi, tashi yayi Kawai ya fice abinsa,Nan Humaira Suka zauna da Aamna suna ta Hira abinsu.

Tunda Humaira tazo Aamna ta samu kawa har fita kasuwa sukeyi da yawo Ahmad ya kyalesu harkarsa yake yi,Haka shima Humaira ta takura Masa Wai sai ya kaita yawo a Machine,da ya fita da ita yawo yau suna ta zagawa duk Wanda ya kalli Humaira sai yayi Masa bala'i.
Wani guy ya ga Humaira kyakyawa ta birgeshi suna tsaye da Ahmad a jikin machine Yana ce Mata Sis na fada Miki kina saka Nikaf tunda ku Kuna kula da Addini Kawai ku rungumi Islama hannu biyu kina saka Hijab da Nikaf kin fa girma tam,I'm warning you Sis,Humaira tana ta dariya shima ya kalleta ya dinga dariya a jere a jere irin ta Yan Kwaya ba kakkautawa,Humaira Tace Yaya kaima kana ganin kyanka Mata sai kallonka sukeyi,Ke dalla rabu da su sun kalle Ni a banza ai duk wacce ta Soni to Allah ya jarabce ta sabo da ban Dace da a so ni ba sis,Humaira taji tausayinsa kwalla ta cika Mata Ido Tace Yaya Wai waye ya koya maka shaye shaye ne Wai? Handkerchief din Dake hannunsa ya zabga Mata a Fuska yace muje gida Yana Juyawa yaga saurayin Nan ya kafe Humaira da kallo,a fusace ya nufi wajen saurayin yace zaka lalata min kanwa Dan uwarka me kake kallonta kana ayyanawa a ranka? Kana Nan kana ta kallonta kana ayyana wani Abu ko ya Kai Hannu zai chakumo shi Humaira ta rike shi tana bashi Hakuri Dan Allah Yaya ka barshi mu tafi,Fisgewa yayi ya dauki wani karfe da ya gani a kasa zai buga masa,Humaira tace ka gudu wlh,Matashin Nan ya arce a tamanin Dan yaga Ahmad ya birkice lokaci Daya ya haukace,Masifarsa ya maida Kan Humaira yace gobe Zaki tafi,Kuka ta saki Tace Allah Yaya Ni sai nayi sati Daya,Zan mareki gobe ki shirya ai kinyi 3days tafiya dole hau machine mu koma gida.
Chapter 22 · 0% Book details