← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 89

Sashe 80

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tafiya a mota Baba yaga wani Dan fari Yana tafiya a titi Baba yace wannan da gani bako ne shima baiyi Kama da su Rahilu ba duk yanda akayi daga Seria yazo gashi Nan a koshe bulbul,Driver dai suna ta larabci da Ahmad Yana Kiran Rahilu Yana Basu Address,Baba ya kalli wani Symbol kato Ana tallan omo Klin,yace Ashe Daya muke da su kaga jaraba Klin a Nan inama Aishatu tana Nan Sarkin ta'adi tazo ga mutuminta a Nan ma,Baba shi kadai yake surutunsa har Suka sauka a wani gida Kato me bene Hawa biyar, Aamna tace Baba anzo gidan Abbi na kaga gidan me kyau,Na Haya ne uban wa yace Miki gidansa ne,?Ahmad Yana jinsu dai suna Fitowa a taxi sai ga Rahilu ya fito sanye da jallabiya wata baka,Baba yace kaga bakin mutum ga bakin Kaya Rahilu manyan gari wuya kamar na zalbe,Rahil da fara'a ya tarbesu ya dauki akwatin Ahmad Suka nufi ciki,wani Palo yasha adon Larabawa shi aka kaisu,Babba yana kallon gidan Yana Kallon Rahilu yace Yan karya an iya tsara gida,Matar Rahilu ce ta fito wata balarabiya fara tas,ta zauna sai da Ahmad Suka yi maga suka gaisa su Baba basa Jin yaren,Wata ce ta fito itama fara ce Amma ba Kal ba irin dai Bata fi farin mu na Yan Nigeria ba,bayan sun gaisa itama ta Mike tayi ciki,gabansu aka cika musu da Abinci iri iri na Larabawa,Baba yana kallo,wani kwano me kyau ya bude yaga kubewa Danya Guda Guda a cikin kwano da wani ruwa tsululu Yana yauki ya Sha tafsrnuwa da kayan Hadi,Wani kwanon ya bude yaga wani Abu shi kamar Tuwon Zuma da Dabino,Rufewa yayi ya Bude wani kwanon yaga miyar ganyen kabewa,Can Kuma wani tuwo ne Kamar na madara har da Cheese,Ga Fruits iri iri,Baba yace Rahilu Ina shinkafa inda Muka Fi wayo,Dan Iskanci kasan wannan ba abincin mu bane na awaki ne zaka sa a kawo mana,kalli kubewa Guda Guda, Rahilu Yana murmushi yace yanzu shinkafa zata Zo harda lemon Tsaki,Karka sake ku matsa min lemon tsami salon na barke da zawo.

Suna zaune sai ga wata shinkafa taji Hadi da hadin salat,Sai ga kaji an kawo,Baba yace yanzu naji zance Baba ya sauka kasa ya shiga cin Abincinsa Suma su Aamna suka gyara Zama tayi Serving Ahmad,Bayan sunci sun Sha suka Yi Sallah sannan aka kirawo Yaran Rahilu Suka dinga gaisar da su,Dake suna makaranta suna Jin turanci sai suka dinga magana da Aamna,Baba yace mu Kuwa sai kallo Allah wadaran rashin Boko,Sai dai Kawai Baba ya dinga cewa Hey...Hey....Ahmad Yana ta dariya a zuciyarsa yanda Baba yake ta aikin Furta Hey ga Yaran da yawa,Yaran Rahilu basa Bari suyi baccin kirki sabo da Hayaniya, Baba cikin dare kullum sai ya tsine musu Wai sun hanashi bacci,yace Rahilu Dan Iskan banza ya dinga dirkawa Mata ciki suna ta zazzago yara Haka kamar zomaye.

Masauki me kyau aka Basu Aamna cikin Yan uwanta Mata ta shiga,washe gari Kuwa Daya gidan Rahil Suka je Suma Mata biyu da Yara da yawa Ahmad yayi Larabci ko turanci Aamna ma Haka Baba Kuwa sai Hey kawai,Nan ma kwanansu Daya aka raka su wajen Dangin Aamna na uba sannan wani babban matashi Mahmood shi ya dinga fita da su Aamna yawo suna ganin gari suna pics,Baba duk inda akaje sai yace ayi Masa pics shima,Ana dauka zai ce da Aamna maza dorani a yanar gizo duniya ta ganni a Sudan,Rahilu ya Gama tsorata da cin mutuncin da Baba ke Masa amma wannan lokacin sai yaga Dan kadan ya masa,kwana hudu tsakani Ahmad ya kafe shi gida Za'a taho Rabonsa daya kwanta a jikin matarsa kwana hudu kullum tana wajen Yan uwanta shi bazai iya ba,Baba yace Kai Nima na gaji da garin Nan mutane kamar konannu kowa baki sai Larabcin tsiya akan me,Aamna ita tana Jin dadin haduwa da Yan uwanta sai Ahmad ya yini Bai ganta ba,ai Kuwa Yace gida,kwanansu biyar Suka dawo gida Nigeria Aamna tana ta faman Fushi da shi har Bash ya dakko su a Airport aka sauke Baba a gidansa da tarin tsarabarsa.

Baba Yana shiga ya Rungume Mama,Tace yau me Zan gani Baban Zuhra sai kace yaro? Baba yace na dakko darasi baza a barni a Baya ba,a gabana Rahilu yake Rungume matansa Yana musu kiss da shegen bakinsa kamar Kofar gari,Ni nafi Rahilu fasali shine bazan Yi ba sai ace na tsufa,shi yasa aka Yi Mana nisa a duniya,da Allah tsaya Rahilu ya mannawa Mama kiss a kumatunta biyu yace Haka akeyi yanzu duniya ta waye anci gaba kina Nan a dinkime Baki zaga duniya kin Sha kallo ba,kije Sudan kiga yanda tsoho tukuf Wanda ya haifeni yake tarairayar matarsa itama tana Masa,ke Baki waye ba,Mama tace Indai wannan ne bada Ni ba,ai Kuwa wallahi Baki Isa ba kullum sai na dinga Miki da safe da Rana da dare ko ta karfi,Baba ya zuge akwatunsa ya dinga fito da tsaraba daga Kan sutura har su turare da lallen Sudan kala kala,Ya mikawa Mama yace Henna sunan wannan lallen Haka ake cewa gobe ki Kira me lalle ta lallaba Miki shi,karki sake da Yamma na dawo daga kasuwa Banga Henna na tashi a Hannunki ba,Mama tace Kai Baban Zuhra ka canja gaba Daya ka koma Wani Dan bariki,Baba yace shine ai wlh idan Baki Yi Henna din nan ba sai nayi sati banci abincinka ba Karki ce ban fada Miki ba yawwa ya Mike ya shige daki Yana cewa na koyo soyayya wajen Larabawa Zo kui cude Ni ki wanke min gadon bayana,Mama tace Ni wannan Sudan din Bata Yi ba wallahi Ka dawo Dan Iska gaba Daya,Baba daga daki yace Dan Guguwa na dawo karewarta.

Tun kafin Bash ya Kai su Aamna gida Ahmad ya like ya nane mata ya hanata sakat,kwana har hudu ko Rungume matarsa baiyi ba tana can wajen danginta ko ya kirata a gurguje take zuwa ta tafi Sam shi baiji dadin Sudan ba ga Baba ya hanashi ya Kama hotel bare ya dan samu ya shakata da Aamna a sudan shi yasa yaji Kamar akan Kaya yake,Aamna Kuma haushinsa take ji yace sati biyu zasu Yi Amma kwana hudu Kawai Ana biyar ya kafe su dawo gida ko Yan uwanta Bai Bari sun Dan Shaku ba,Bash Yana kallonsu ta Mirror Aamna tana Fushi Ahmad ya manne a jikinta Kamar zai shige cikinta gaba Daya ya haukace baya ganin kowa baya tunanin wani Bash ma Yana kallo,Aamna ta hade rai tace Kawai ko Gama ganin dangina banyi ba ka damu sai fada kake min Kai ka gaji gida zaka taho,yanzu ka min Adalci? Baki Ahmad ya bude yace kutmar...yace yanzu duk abinda nayi Miki banyi komai ba? My world???? Na kashe kudina na dauke ki har Baba Muka je har can sabo da na faranta Miki kiga danginki Ashe ban birge ki ba? Yanzu da Allah bai hore min ba da wanne kudin Zan kaiku? Kin min Adalci kenan? Fine and Good zamansa ya gyara ko yatsa Bai sake rike Mata ba.

Sai a ranta ta tuna Bata kyauta ba,tunda take arayuwarta Bata San ma inda Dangin Ubanta suke ba sai ta Silar Ahmad,Daddy dinsa kudi ya saka ya dakko Mata Babanta har Nigeria ita Kuwa me zatace da su,Jikinta ne yayi sanyi ta riko Hannun Ahmad ya fisge Hannunsa,Bash ta Glass yake kallo Yana ta dariya a ransa,Yana yin parking Ahmad shi ya fara fita yayiwa Musa Magana ya dakko Masa jakarsa,Aamna ta dauki tata da kyar ta bishi da sauri tana kwala Masa Kira My King kayan Nan sun min nauyi cikina zai zube,ko kulata baiyi ba,a compound ta bar kayan tayi ciki,Bash a waya ya Kira Ahmad yace please karka kulata kuyi fada,kayi Hakuri akan Dan abinda Bai Kai ya kawo ba haba King, Ahmad yace Yarinyar ta rainani da yawa in kashe kudi in kaita har can kaji Maganar data fada min,Matane sai hakuri King Haka suke sai anyi Hakuri shine zaman Auren karka biye mata Shedan ya dinga hadaku fada please, alright Ahmad ya furta tare da kashe wayar,Wanka zai shiga Aamna ta shigo da sauri tana cewa I'm sorry My King, me kika Yi? Aamna tace laifin da nayi maka,Baki ya tabe yace ba Wani abu ai ya shiga wanka,ya fara wanka kenan Aamna ta shiga tare da tube kayanta taje,ko kulata baiyi ba,Tace har yanzu Fushi kakeyi dani? Fushin me Kuma? Gashi Nan kana share ni kayi Hakuri nace kaji ta furta da shagwaba tana riko hannayensa,a kirjinsa ta kwanta ruwan Yana zubo musu ta Rungume shi tare da fashewa da kuka,Yaron cikinta ya tuna ya shafa bayanta yace it's Okay ya wuce,Ki kiyayeni Aamna wallahi Dan kece kin Sanni a baya bana son taurin Kai da raini,Dan Ina sonki bazai hana na dauki mataki a kanki ba,Ni bazan dinga daukan wannan abin naku na Mata ba na shirme,ke ba yarinya bace,Ya isa Allah bazan sake ba cewar Aamna,cikinta ya shafa yace Babyna ya fara girma,Aamna tace muyi sauri naje na Mana abinci,nayi Order fa za a kawo kiyi zamanki sai gobe Inshaallah.

Wanka sukayi tace yunwa nake ji ka danyi Hakuri muci abinci sai na baka manta uwa,Ahmad Yana Jin Dadi harda cewa yau kwana zamuyi ko? Aamna tace as you wish,I'm all yours,I miss you ya furta,miss you much more My King,Abinci Musa ya shigo da shi wata sakwara da miyar kwai taji nama,yasan tana sonta shi yasa sai wani gasashen Naman rago Suka baje ya Bata a Baki da Kansa Suka koshi sannan ta daga Kai tana Shan Watermalon Juice ya fara zare Mata rigar wankan da take jikinta Dake ma Basu cire ba Suka zauna cin abinci.
Kirjinta Wanda Suka sake girma sunyi sake sake sai kyalli sukeyi ya shiga Matsawa Yana sarrafa su,Yace dama dai su dinga zubo da ruwan milk,Aamna tace sai an Haihu to,Allah ya kaimu a dinga Dan rage min Nima Ina zuka,sunyi missing juna kamar zasu cinye kansu Haka suke sarrafa juna suna wasanni iri iri daga Nan suka fada Manta Uwa.
Chapter 80 · 0% Book details