← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 89

Sashe 85

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aamna Kuwa tana ta daurewa bata kuka Shuru kawai Bata magana da Alama tana Shan wahala,private ne Single room ita Daya aka basu,Bayan an duba Suka ce Haihuwa ce tazo gaf,Ahmad suna waje hankalinsa a tashe Kawai tagumi ya buga,Mama da Su Sameera suna ciki tare da Likitoci,taimakawa Aamna sukeyi har aka samu Aamna ta santalo katon danta namiji Kamar yanda suka gani a scanning,tana Haihuwa ta suma sai da kyar Aamna ta farfado ta Sha wahala Amma tayi Hakuri tayi juriya matuka,Jaririn Nafeesat ta goge da man Zaitoon dana Habb fes a towel aka nadeshi,Yaron girmansa ya Isa Kamar ba daga jikinta ya fito ba,Sameera ce ta kaiwa Ahmad jaririn,Bai ma San ta Haihu ba suna Zaune da Mashkoor hankali a tashe sai jariri Suka gani, Ahmad ko jaririn Bai karba ba yace ya My world take? Ras take Ahmdllh Bata da wata matsala yanzu ma gyarata akeyi,Sai lokacin Ahmad ya saki ransa tare da godiya ga Allah Yana me karbar Jaririn,shagala yayi da Kallonsa Baki Nan a Bude, Mashkoor yace to Malam Addua fa zaka Masa,Sai lokacin ya shiga Masa Addua a kunne sannan Mashkoor ma ya karba tare da Yi Masa,sai ga su Tawaga Suma a daren sunzo sun Iske an Haihu ma,Jibson ya karbe Jariri Yana cewa mun zama Iyaye yau,Bash da Brown ma Suka karba suna ta Masa Addua,sai Tawaga shima har da cewa bari na Masa shillo ya daga karmar zai shillashi sama,Ahmad da bala'i ya dakawa Tawaga Tsawa zai kwace dansa Yana masifa aikin banza so kake ka hallaka min yaro,Dariya Suka dinga Masa gaba daya,sanadin Haka ya karbe dansa ya Hana Tawaga fafur.

Humaira sai Waya take bugawa taji ko ta Haihu aka ce Haihu lafiya,Haka Hafsat da Yar China Suka ji a waya,sai bayan Aamna ma tayi wanka ta canja Kaya aka canja Mata dakin hutu,komai an gyara Neat ba matsala sannan aka bada dama su Ahmad Suka shiga,Tana kwance ta lumshe Ido tana hutawa,Ahmad kamar zai shige cikinta duk yabi ya kankane ta,Sannu su Tawaga suka Mata da Barka sannan kowa yayi waje ya barta da Ahmad dinta da jaririnsu.

Aamna ta kalle shi Suka hada Ido tare da sakarwa juna murmushin kauna,Yace me Kama Dani aka Haifo,Aamna tace Haka naji su Sameera suna fada,Ahmad ya nuna Mata Yaron ta karba ta Masa Addua itama sannan tace ka duba jakar can akwai Ribbom Dina ka Kama min gashin Nan ya dameni,Ahmad ya ajiye jaririn a gefenta tare da dakko Ribbon din ya daure Mata gashin sosai yanda bazai dameta ba,yunwa nake ji ta furta,Yanzu Jibson zai kawo abinda Zaki ci ki Dan Kara Hakuri ya Furta Yana shafa fuskar jaririn,Aamna tana satar Kallonsa tace ai fuskata zaka shafa ba ta Jariri ba idan da a baya ne kafin na Haihu ai fuskata kake shafawa,Dariya ta bawa Ahmad ma shi,ba a Dade ba Jibson ya dawo da ledoji Naman kaza da fruits sai gida da yaje ya taho Mata da tea a flask da komai na amfani,yace Mama tace na taho Miki da me Dan nauyi gashi Nan Humaira ce Kawai Allah yasa tayi faten doya ya rage kiyi manage kafin safiya,Aamna tace hakan ma yayi,Nafeesat ce ta hada Mata tea me kauri da kaza taci ta koshi har faten doyar.

Bacci ne ya kwashe Aamna,su Ahmad sai murna da bige bigen waya duk sun cika Asibitin da surutunsu,Su Yar China Kuwa suna tare da Humaira a gidan Hafsa Suma sun hadu suna zuba Hira,Yar China tace Yau Aamna karshen Sirri ya Kare yau likitoci sunga Hq,Basu da mutunci matan Nan Haka suke zura Masa Ido,Dole su makance da wuri cewar Hafsat,Humaira Tace to yanzu ma ba mu zo Haihuwa ba Ana ta duba mu Ina ga Haihuwa,Yar China tace ai ku shirya ba Wani sirri idan da duhu ma wata shegiyar touch suke sawa me haske,Dan ma matane Amma ai da kunya,lokacin Dana Yi Bari Ina dawowa nace to Tawaga sai dai kayi hakuri dakinka dai yanzu ba sirri ,Humaira suka Kama dariyar Yar China,Yar China Tace shegiya ai Kuwa likitar ta kiyaya wlh taga tsafta iya tsafta da kamshi sai da ta min jinjina Tace da wasu matan ne Haka dagajaja ake gani,Humaira tana Dariya Tace a gidan Ubanwa ta ganshi fes lokacin kina Bleeding,Ke banza ce yanzu fa Dana warke ai mun koma Hospital ta dubani taga ko Mai normal,Humaira tace sai kace wacce ta haihu,Yar China tace su Ina ruwansu Abu ba abu ba sai suce sai sun duba ya na iya,Hafsat tace ni wlh Nima abin ya isheni ayi ta sa ma yatsu.

A daren Mazan Suka dawo gida har Ahmad,Yar China Suka koma part dinsu,Ahmad sabo da Murna da kyar yayi bacci,Nafeesat aka Bari sabo da ita Nurse ce sai Mama,Itama Sameera mayenta ya taho da abarsa gida,a daren Ahmad ya sanarwa su Mummy suna ta murna,Washe gari jikin Aamna yayi kwari ka rantse ba ita ta Haihu ba,da wuri Yar China,Hafsat da Humaira Suka zo da kayan Kari,Yar China ta kinkimi Jariri tana wayyo Allah ji Dan Allah yaro zukeke me Kama da ubansa,Ina ma Nawa ne mashaallah,Kai Aamna kinyi Aiki yanzu daga jikinki ya fito? Gaskiya kin Sha wahala,Aamna tana dariya tace wlh abin ba a cewa komai,ai naso jiya nazo ko darasi na dauka Amma Yaya Tawaga ya hanani,Aamna tace akwai azaba wallahi da ikon Allah bazan sake ba Allah ya tsayar min iya Nan,Karya ma kike fada wlh sai kin Karo Ina laifin ma biyar ko hudu,Humaira Tace ai fa Amma Daya jal idan aka Miki kishiya ta wuce ki fa? Aamna Tace ga fili Nan Indai wannan abar ce taje ayi ta sa Mata Ana Mata ciki Ni na hakura,Na rantse da Allah nayi zaton a kabari Zan farka na ganni,tunda nake ban taba Jin azaba ko rabi rabin wannan ba,kukan ma kasa Yi nayi na koma kurma Kawai.

Yar China harda cewa Ahayye taji uwar Bari,Ni kaina Kinga dai Bari ne Dan Blood ne Amma naji a jikina,Kai Ina tausaya Mana Mata,Mama da shigowar ta kenan tana ta kallon Yar China Kamar Tv Tace wannan yarinya da jarabar iya zance take sai kace Babbar mace ko dai tsohuwa ce ta rike ki? Yar China tace a Hannun Kakata na girma,Yanzu naji zance cewar Mama.

Siyama ma da duk wasu abokan arzuka Haka Suka dinga sintiri,Baba yazo shima ya dauki Jariri Yana Masa Addua karshe yace Allah yasa karka gado taurin Kan Mamanka,sannan karka dakko rashin kunyar Babanka kaji,yaro Babanka har satar min kayan kallo yayi Akan son Mamanka,maza ka girma idan Ina da Rai ka biyani startime Dita da radio,kakanka Rahilu Haka Muka je Sudan Muka dawo ko kyallen Handkerchief Bai Bamu ba sai da kudinmu Muka Yi tsaraba,Yana can Yara da jikoki zasu hallaka shi Yana ta karmashewa,kaf kamfanonuwan duniya babu wando Size dinsa,idan ka girma ka kalli Rahilu sai kayi Takaicin Fitowa a tsatsonsa,ga tsayi Kamar bishiyar turare wani zamarke da shi,Mama ce ta kwace jaririn tana cewa Kai dama ai baka son mutum idan ba kudi zai baka ba,yanzu da Rahilu zai maka kyauta me tsoka cewa zaka Yi yafi kowa kyau,Baba yace to ayi min kyautar a gani Mana dama yace zaizo idan Aamna ta Haihu yau Zan fada Masa a waya sabo da dama ya min Alkawarin wani takalmin fata da yace zai kawo min Yana da kwari sai nayi shekara goma Ina sawa ba tare da ya tsinke ba Rahilu duk Harkar tsumulmula ya kware a cikinta.

Aamna Tace gaskiya Baba ka daina,In daina Ubanki? Sanda na Sha wahalar rike ki ya taimaka min da kwandala ai wlh Rahilu Matukar Bai min kyauta ba ya shiga uku,har yanzu Bai iya Yi min godiya ba a matsayina Wanda na rike Masa yarsa ta girma na Bata Ilimi na Aurar da ita,shi ba ruwansa ko a jikinsa ai kin gani da idonki ko yayi min godiya? Aamna tace a'a amma ai Dan Allah kayi,to bazan daina ba idan kinyi zuciya kisa ya gode min Sannan ya girmamani ta hanyar Yi min kyauta,ai Ni babbar girmamawa ayi min kyauta,Mama Tace a Haka zaka Kare,Suna Haka Ahmad suka shigo ya Sha wani shegen wanka cikin kana Nan Kaya Yana kamshi,Baba yace Iyye kaga Wanda basa tsufa Kamar ba shi ya Haihu ba,kaga Danka fa Kato Amma bakwa saduda da daukan wanka wannan kamshi Haka kamar turaren dakin Ka'aba,su Ahmad suka dinga dariya,Baba yace ga Aski na banza Kun iya to dai Kun fara Haihuwa,Ahmad Yana dariya yace Baba ai wanka yanzu ne ma zamu fara,Kin shiga Uku Aamna Mata yanzu zasu fara sintiri a gidanki kuwa cewar Baba,Aka dinga dariya Aamna tace wlh Bai Isa ba gida Zan dawo,Baba Baki Bude yace gidan wa? Gidanka Mana,karya kikeyi Kai yaro idan tace zata hanaka aure kayi Mata shegen suka ka kirani a waya ka Kara min kukanta kana jibgarta Ina jiyo kukanta ta waya,Ahmad suna ta dariya da su Jibson,Yar China tace Baba kana ba damu wlh wa yake Yayin Kara aure yanzu ai tsohon yayi ne,Tawaga harda cewa wlh Ina zamu Kai Yara wannan ta Haihu wannan ma Haka,Baba Baki Bude yace sun shanye ku,ku daina Kiran kanku mazaje sam,Mata sun Gama da ku,a Haka kamar wasu mazajen kirki,Hafsat tace Baba kaima fa Daya ce jal,Gata can itace ta kankaneni ya nuna Mama da baki,Baba da abin Dariya Yana ta Basu Dariya ana Wasa da dariya ba ruwansa,Sai Yamma aka sallami Aamna,Mama Tace zasu tafi da ita Ahmad yace bazai yuwa ba,da kyar ya Amince zata Yi sati daya tal.
Chapter 85 · 0% Book details