Sashe 5
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari da Ahmad ya fita Wata hanya Suka samu tare da tare hanyar mota kowa idan yazo sai dai ya juya Inda ya fito,sai da aka kawo Yan Sanda wajen suka dinga fada da Yan Sanda,Bincike Dpo yayi Dan waye? Ai Yana ji an Fadi waye Baban Ahmad a kasar sai ya tsorata yaje har gidan ya samu Babansa tunda ance yazo Yana Kd ma,Bayan sun gaisa Dpo ya Kai karar Ahmad yace mun kyale shi ne sabo da Kai da irin taimako da kake Yi a kasar nan sabo da Haka Dan Allah Ka Jawa danka kunne,Daddy ya Basu Hakuri tare da sanar musu duk irin kangarewar Dansa,Dpo yace sai dai ku dage da Addua Amma a tsawatar Masa Kar mu dauki mataki aga Bamu kyauta ba,Bayan sun tafi Shuru Ahmad Bai dawo ba sai cikin dare Daddy,Mummy da Saddeeq duk suna jiransa sai kuwa gashi ya dawo a make,Daddy ya lullube shi da fada ba ji ba gani,Kaninsa Sadeeq yasa Baki Nan take Ahmad ya shaki kwalar Sadeeq zai Duke shi,Mommy ta rirrike shi tana kuka tana cewa ka Bari Mana Ahmad wayyo na Shiga Uku Ni,Daddy kuwa Mari ya kwadawa Ahmad,Nan take ya dafe kuncinsa Daya da mamaki sai Kuma ya sheke da Mahaukaciyar Dariya Yana Nuna Daddy da yatsa Yana ka mareni akan wannan kanina shi zai ce zai min fada,Daddy yace banza shashasha sai na sake marinka wallahi,Juyawa Ahmad yayi ya haura samansa a fusace,Humaira kanwarsa da Mommy suka bi bayansa suna ta bashi Hakuri suna lallaba shi,Ahmad yace kina gani Mommy marina fa yayi Akan kanina,Ni dama nasan Daddy Baya kauna ta,Bai so aka haife Ni ba gaba daya,Ba Haka bane Ahmad Yana sonka Nima Ina sonka,Yace ai nasan ke kina so na Amma Daddy Baya kauna ta Ni ku tafi ku bani waje Kawai ya dakko kwalabar barasarsa ya shiga korawa,Mummy suka fita sun San halinsa idan yayi Fushi.
Ranar da su Mymmy suka kwana Uku da Yamma Ahmad,Mufida matar Saddeeq da Humaira Autarsu suna Garden suna Hira Ahmad Yana ta musu magana irin ta Niggogi irin ta Yan kwaya suna ta dariya, Sadeeq ta sama ya hango su ta window kishin matarsa ya kamashi ya sakko tare da Fitowa Haka ya dinga zaga garden Yana kunci,ya Shiga ya fita ya dawo ya wuce ya sake dawowa,Mufida ta fuskanci wani Abu Tace lafiya dai Baby? Cike da bala'i yace ba lafiya ba ki taso ki kula da mijinki kin zauna kina wani dariyar banza da wofi,Ahmad yace ya zaka dauke ta muna Hira,Hira mukeyi Kai wanne irin yaro ne? Tsaki Saddeeq Yaja ya Fisgi matarsa Suka tafi,Juyawa yayi Suka ci gaba da Hira da Mufida kanwarsa suna ta dariya abinsu,Wayar Humaira ya karba ya juya yace irin wannan waya Haka sis idan kika hadu da irinmu Yan duniya ai sai mu tare Miki Hanya muyi Miki fashin ta,Dariya Suka sake yi Yana ta Dariya ba ji ba gani irin ta Yan kwaya,yace sis yanzu ma Dan na sanki ce ke kanwata ce da su Jibson Zan turo su kwace ta,Dariya Suka sake Yi a tare Humaira ta daki kafadarsa tare da furta Kai Yaya,Kallon Kanwar tasa yayi sosai yace sis you are cute wooo...see your Nose fine nose,kina sa Nikaf fa Kar ki hadu da irin su Brown abokina I swear Kamaki zasu Yi su Sha harka kina kula fa tam,hope Baki kula samari Kar wani yazo ya taba min kanwa Naga kin fara girma abubuwa sun fito Haka, zanzo har Lagos nayi yaki ne idan wani ya Bata min ke, Humaira harda rike ciki sabo da dariya ga kunyar abinda yace,shi kuwa ko a jikinsa
Kwanan su Mummy biyar suka fito cikin Shirin tafiya Ahmad Yana binsu a baya Yana ta murna zasu tafi yanzu ma su barshi ya sakata ya Wala,Mummy ta Rungume shi Tace ka Zama mutumin kirki Dana tunda baza ka bimu ba ka kula da kanka,yace to Mummy na, Saddeeq yace wannan ba Wani shiryuwa da zaiyi Nan take Ahmad yayi Kansa da bala'i,Mufida tazo Tace Yi Hakuri kyale shi Yaya King,yace yawwa matar mu ki kula da kanki,Da sauri Saddeeq ya janye matarsa cike da kishi,Ahmad yace wannan wanne irin Dan Uwa ne Haka? Daddy ne ya Kira Driver su wurin Tara yace ya kwace Motocin Dake Hannun Ahmad kaf,Dama Bai damu ba yace tunda Yana da kudin machine ya ishe shi,Daddy kuwa yace tunda baza ka nutsu ba ai Motocin da kudi na ka siya na karbe,Ko a jikin Ahmad yace kuje da ita,Daddy yace dole ma ko baka fada ba,kudi dai Zan na tura maka na kula da kanka sabo da hakki na ne,gida ma kayi ta Zama Amma ka sani ba gidanka bane Nawa ne.
Mummy Tace please Ahmad ka daure nasan kana Sallah Amma baka Yi sai Sanda kaga dama ka gyara Sallah ita ce komai awajen musulmi,Ahmad yace sured Mum Zan gyara ki yarda Dani,Nafa sanka Ahmad tun yaushe kake cewa zaka gyara Amma kaki,Ki yarda Mum Inshaallah,nine fa Ahmad dinki,Sunana fa aka kalla aka yo Guarantee trust Bank,Dariya sukayi har Daddy,Yawwa ehem Dad karka manta na tura maka new accnt number Dina Ina bukatar kudi kudina sunyi low,Daddy yace Zan tura ai Ina sane sakaran banza.
Ahmad Yana ji suka shiga mota Gate man ya Bude Musu suka tafi Basu bar mota ko Daya a Hannun Ahmad ba aka su Suka kwashe su,Suna tafiya ya dauki waya tare da Kiran Abokansa su zo Iyayensa sun tafi sai murna sukeyi yau suna gidan King.
Me Gadi ya kalle shi kawai ya jinjina Kai Amma Ogansa Yana da Hali me kyau Kawai matsalarsa shaye shaye da Rashin Ibada sosai.
Aamna tana cikin Restaurant dinsu tana ta Kai abinci wajen masu ci,sannan Kuma suna Hira da Babbar kawarta Siyama wacce aikinsu Daya,tare suka Yi HND a Poly,Rashin samun Aiki yasa suka nemi Aiki a sabon Restaurant da Maman kawarsu Saratu ta bude sabo da Talaucin da suke fama da shi, Siyama Tace kawata Nima fa Allah ya kusa daga Ni,na manta ban fada Miki ba Nafa fada cikin kogin son Faisal,kwanan nan ma nake so na bashi dama ya turo magabata,Murmushi Aamna tayi Tace wow I'm Happy for you Kawa But Ina ganin Kamar kinyi gaggawa ya kamata ki Bari ku fahimci juna sosai Bai Yi ko 1month da fara zuwa wajenki ba,Karki je garin sauri da matsuwar Aure a samu matsala,Siyama ce ta dakatar da Aamna ta hanyar daga Mata Hannu tare da Bata rai,Tace Ni fa Aamna ban Gane Miki ba,ai sai kisa nayi zargin ko bakya kauna ta kina bakin ciki na samu Miji ke Baki samu, Subhannallahi Siyama Allah ya kiyaye ko wani da musulmi bazan Masa bakin ciki ba bare ke da kike kawata wacce muke kashewa mu rufe tare Allah ya kiyaye min,sabo da Haka Dan Allah gobe a daura aurenki da Faisal ma Bai Dame Ni ba Bai shafe Ni ba,babu abinda Zan tsinta ciki,idan wahala ce ma ke Zaki Sha abarki mu Yan jaje ne.
Siyama Tace ai ke dama bakya kaunar Aure bakya so kiyi Kuma bakya kauna wani yayi,gaba kike da Sunnar ma'aiki sabo da ke Kinga Baki da samari idan ma kin samu guduwa suke yi,idan Zaki hakura ki auri kowa kika samu ki hakura yanzu an daina auren Soyayya wa zai Iya rike ka Kawai ake Nema ya zaka ci ka Sha ka rayu inda zaka huta da iyayenka,Faisal Doctor ne matarsa mutuwa tayi wajen haihuwar fari,yaro matashi ga kudi me nake jira ai yanzu ba a jira Yan Secondary ma idan suka samu Miji aure suke Yi,kiwa kanki fada,shekaru tafiya suke Yi mu matane,ko ba komai kar tsufa ba aure har mu zo lokacin Haihuwar mu ya wuce,Aamna Tace Allah Baki Hakuri ayi aure lafiya mu muna Nan daram za muci gaba da Addua Allah Bai manta damu ba Yana sane da mu,Siyama Tace ae aci gaba da Zama lafiya Ana gantali, wanne gantali mu da muka yo rako duniya,gamu an halicce mu a Nigeria babbar jarabawa,ga talauci,wannan duniyar Ina Dadi cikinta, aikinsu Suka ci gaba Yi suna Hira kamar ba sune Suka Yi fada ba,dama sun Saba fada da junansu.
Washe gari Bayan ta tafi wajen Aiki Sai ta Iske Siyama Bata karaso ba sai Aamna da sauran ma'aikatan,Siyama kuwa Direct gidan Su Aamna ta wuce,Mama ta tarbe ta,Tayi sa'a Baba ma Yana gida,Bayan sun gaisa Tace Baba wata magana ce ke tafe Dani da Kuma shawara,Baba yace Muna jinki Siyama,Siyama ta Basu labarin yanda sukayi da Aamna Akan Maganar Aurenta da Faisal,Baba yace na rasa dalilin Yarinyar Nan da Bata kaunar Aure,Siyama Tace Ni abinda na fahimta Baba Aljani ne ya auri Aamna Kawai shawara ku kaita gidan malamai a Nema Mata magani shine Kawai,Mama Tace tabbas yarinya kinyi nisan hankali,shi yasa ake son kawa irinku ta gari,Haba biri yayi Kama da mutum cewar Baba,yace Inshaallah gobe zamu dauketa mu tafi da ita kauyenmu can Sokoto mu Nema Mata magani,dama jiya anyi Mana Albashi sai a fasa siyan komai mu tafi neman magani Allah yasa a Dace kafin ayi Auren Zuhra itama ta samu nata Mijin mu hada a Sha rikitiba sosai,Haka Siyama ta fito ta zo wajen Aiki a makare ranar Aamna Bata San dalili ba tana komawa gida taga Baba da fara'a ya amsa Sallamarta,ta Gaida shi Kuma ya amsa,Mama ma Haka,Aamna dai hankalinta Bai kwanta ba tayi mamaki,Zuhra kuwa tana ta karasa miyar Taushe,Mama Tace Aamna Sannu da Aiki zauna na kawo Miki abinci,Aamna mamaki ya kamata sai binsu take da kallo har taga an kawo Mata abincin a flask Wanda a baya ko rufe Mata ba ayi bare wani Flask,ta kalli abincin ta kalli Mama Tace Mama ko dai maganin bera kuka saka min zaku kashe Ni?Mama tana gyara daurin zaninta Tace haba Aamna kin taba ganin Iyaye sun kashe yarsu? Aamna Tace na nawa Kuma,bazan ci ba gaskiya wallahi,Ina so na Kara tsawon Rai,bana so na mutu yanzu sabo da Haka Ni bazan ci ba ko ruwan gidan Nan na daina Sha gaskiya.