← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 89

Sashe 26

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka ya sake Shiga Yana dirje jikinsa Yana rumtse Ido sabo da zafin soson,Haka ya Gama tas ya fito Yana goge jikinsa yace yawwa Iska tafi shigata Ina Nan Ashe Ina ta cutar kaina da ace da irin wannan nake wanka tun farko ai da nafi Haka haske da Zama Fresh.
Lotion dinsa ya shafa me kamshi ya shiga gyara kitsonsa yace ya kamata nayi sabo wannan kwanansa biyar ya fara tsufa Amma Bari dai naje,sai da ya Gama feshe feshensa sannan ya Bude ma'ajiyar kayansa Yana binsu da kallo yace Suit Zan saka ko me?can ya hango shaddoji da yadika masu tsada da kyau Wanda Mummy ta kawo Masa lokacin da za a daura aurensa kala bakwai,Wata Shadda ya dakko sea Blue Tasha dinki me kyau Hannun dogo me links,Nan ya sa Boxers ya fara kici kicin saka wando Wai Bai iya ba,da kyar da wahala Yana uban Nishi ya saka cif cif shi dinki ya zanu,Singlet ya saka yanda Mummy ta koya Masa sannan ya saka Rigar Shaddar wacce ta Sha guga ga kamshi Shaddar nayi sabo da me tsada ce,calabarsa ya gyara ya shafe Kansa da man gashi me kamshi Nan take ya dauki sheki,Fuska ya kalla ya matsa baya Yana kallon kansa a mudubi ya hau taje Sajensa da gemusa,fuskar ya goge sosai ya gyara sai gashi ya fito fes da shi,Sarkar azufarsa wata sabuwa ya dakko ya saka,Yana cewa duk da hausawa basa so Amma tana min kyau sai na saka sabo da wannan shine wankan sugar sai da ya Gama ya fesa turaruka masu kamshi,Ya tsaya jikin mirror ya kame a wajen yayi mutuwar tsaye yace ya Ilahi Ashe Haka nake? Dan Allah kalli kyau a wajen Nan ai Dole ma na birge,ya sake kallon kansa yace ah.. ah kalli kyau Dan Allah,irin wannan saurayi ai sai an wanke Hannu daka taba,wani Dan lipgloss na maza ya dauka ya Dan goga a lips dinsa yace yawwa.....Kar Kuma na Zama Dan Daudu Mana ya Isa haka....tsayawa yayi yace to me zance Mata idan naje Kantin nasu? Tunani yayi yace na tuna ma Bari naje,Illar idan na ganta sai naji tsoronta Kuma Haka Zan daure,Fitowa yayi Yana Taku dai dai Yana wani Gadara,yace me kyau sai da takama Nan ya Shiga wata tafiya Yana takama Yana basarwa,Musa Baki ya Bude tunda yake a duniya Bai taba ganin me kyau irin Ogansa ba,Bai taba ganin wankan da yayi ya zuba Uban kyau Haka ba sai yau,Musa yace Oga gaskiya kayi kyau,Murmushi yayi yace Allah Musa?

Musa yace wallahi Oga Kar fa kasa Mata su haukace,Dariya Ahmad yayi ta Jin dadi yace Musa yanzu kana ganin duk wacce ta ganni zan birge ta? Bafa soyayya nake nufi ba Kai Musa Ni kasan ba ruwana da soyayya,Musa ya kalli sama ya nuna sama da yatsa yace Na rantse Oga duk wacce ta ganka sai ta kwana tana tunaninka yau ita da bacci haihata haihata,Machine Ahmad ya hau Wanda Musa ya wanke Masa Shar,a hankali yake tukin sai binsa ake da kallo da gani an San Yafi karfin yawo a Machine ko Ina ya gifta sai an koka.

Aamna kuwa yau wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigarta peach color ta lefe ce tayi rolling da mayafi ta dauki hand bag da takalminta me Dan tudu Kalar adon rigar Golden tayi kyau ta dauki bokitin chin chin da takeyi da kanta tana siyarwa a shagon wannan da kundinta takeyi tana samu Yar riba,da kanta ta gyara kantin fes ta shirya komai sannan ta zauna tare da dakko Wayarta tana karanta novel,idan masu siyan Abu sunzo ta Basu ta koma karatunta.

Tana zaune ta dukufa taji machine yayi parking a bakin wajen,kanta ta dago da sauri Jin wani kamshi na daban me Dadi,Ahmad ta gani Wani tafiya yayi da Imaninta ita kanta sai taga kamar yau ta taba ganinsa,zuciyarta ta hau Bugawa da karfi,Kallonsa takeyi ba kyafta Ido tare da Mikewa tsaye,Babu alamun fara a Fuskarsa Yana wani Isa,a cikin ransa Kuma wani kwarjini ta Masa yaji wani tsoronta da shakkarta,duk kwarin gwiwarsa sai ya neme shi ya rasa,jikinsa yayi sanyi a hankali ya taka zuwa gabanta ya tsareta da idanunsa,Itama shi take kallo,can ganin Shirun yayi yawa sai Tace am...me kake so zaka siya Ahmad? Yayi Shuru ya kasa magana,ta kalle shi tayi murmushi Tace wow kayi kyau Wannan shigar tayi maka kyau,Wani sanyi yaji a ransa dama Dan ita yayi Kuma ta yaba,a hankali yana Ina Ina yace shi...shigar...ta...tayi Miki?da sauri ta daga kai Tace sosai wace zata ce ma baka Yi kyau ba,Yaji wani Dadi ya jinjina Kai kawai,sharewa tayi Tace me zaka siya? Kasa magana yayi sai da kyar yace Uhm....uhmm.....Yana ta kallon shagon Yana so yaga me zai iya siya....gumi ya hada Nan take tsabar abinda yake ji a ransa da kwarjinin da ta Masa gashi Bai Iya yiwa mace magana ba tunda ya taso a rayuwarsa wannan ne na farko,Tace Kayi magana Mana me zaka siya? Yace Uhmm....ahhh....ehmmm.....can ya hango chin chin yace Chin chin tare da nunawa da yatsansa,murmushi tayi Tace na nawa? Yace na....naira dari.....murmushi ta saki ta bude ta zuba Masa Guda uku dari cif a farar Leda ta Mika Masa,karba yayi Yana ta kallonta yace Zan....Zan...Iya Zama a Nan naci? Tace me zai Hana shigo ciki,kujera fara ta jawo Masa a ciki ya zauna Suka jere taci gaba da karatun Novel dinta.

Kallonta Kawai yake ta faman Yi idan yaga zata dago sai yayi sauri ya dauke Kansa,Daya gaji sai ya fara cin Chin Chin din,harga Allah baya son chin chin Amma Haka yake ta ci Yana kallonta,ita Kuma tana ji a jikinta Yana kallonta duk sai ta kasa sakewa da kunya,juyowa tayi karaf suka hada ido,Tace ya kake kallo na? Yace kallo? Kallo Kuma? Ni na kalle ki ai kece ma naga kina ta kallo na tun dazu ya fada Yana dauke Kai,Tace Ni nake kallonka din? Yayi Murmushi yace ae Mana,Kai ta girgiza taci gaba da karatunta,cikin Wayar ya leka yace me kike karantawa? Novel ta bashi amsa, ko kana karanta Novel? Yace No...me zanci da Harkar love ai Ni sai dai dambe, murmushi tayi Kawai.
Yace me yasa Mata kuke son Love ne? Wannan duk Bata lokaci ne,Dariya tayi Tace Kai baka so ta juyo tana murmushi wani kyau ta Masa ya gigice zuciyarsa taci gaba da bugawa,kasa magana yayi ya rike Hannunta wani mugun shock taji ko Ina a jikinta yace Ring din ya Miki kyau,Tace na gode Hannunta ya dauka ya maida Mata saman cinyarta yace kina boye Hannun Nan Kar wani yaga ya Masa kyau da yawa ya yanke Miki shi ya tafi dashi gida,Dariya ta dinga Yi shi kuwa ita Kawai yake kallo,komai nata Dariya a ransa ya furta,Yana sani ya dinga cin Chin Chin din kadan kadan sai da ya Dade lokacin Azahar tayi sannan ya Mike yace Zan tafi Tace ka Gaida gida yace to Zan fada Masa,Dariya ta sake Yi ta rako shi har bakin machine dinsa ya hau ya tafi da mugun gudu,Tun kafin ya karasa gidansa ya tsaya a Hanya ya cire rigar Shaddar tasa sabo da zafi yake ji ta dame shi Bai Saba ba,a kafada ya sakale ta har zuwa gidan.

Da murna ya shiga Yana sauka a machine ya zaro dubu biyu ya damkawa Musa yace je kaci pizza Musa yau Ranar murna ce,Musa yace Allah Oga? Allah kuwa cewar Ahmad ya sake zaro dubu biyu yace kudin lemo ne wannan,Musa ya daka tsalle Yana murna da Ihu har Ahmad ya tafi ya sake dawowa ya zaro dubu Daya yace ungo Musa ka sawa matarka Kati a waya ku kwana kula hirar ku ta Yan karya Kuma karka sake ka Bata duniyar mu Dan Bamu San Inda zamu shiga ba idan ka bata.,,Musa yace Allah Kai sai kayi,Ahmad ya daga hannaye sama yace nine nan yayi ciki Yana wata tafiya ta musamman.

Yana shiga ya cire duka kayan jikinsa ya watsa su a inda yake Tara wanki,saitin zuciyarsa ya dafe tare da furta shu'uma har ta dawo dai dai,Wato har wani bugu kike Yi a hankali da kika ga bana gabanta ai shike Nan kin kyauta,zuciya kin kyauta hakan ya Miki kyau kin Mai Dani wani Wawa Akan yarinya karama Ina ta zubar da aji na ai shike Nan Zaki sani ne.

Washe gari ma wani sabon wankan yayi tare da saka wani yadi Milk color sharara da shi ya Masa kyau matuka an kashe shi da dinki na haduwa,wani takalmin ya zabo me tsada,waje ya fito ya mikawa Musa takalman yace sauri ka kaiwa Shoe maker ya wanke min yanzu Ina jira,Dan Allah Musa kayi sauri ka kawo min su Suna kyalli,Musa ya fita da gudu ya tafi Bai Dade ba ya dawo,Ahmad ya shirya tsaýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿf kyau ba a magana yace yau barkono da citta Zan tayata siyarwa,yau ma Aamna tana zaune ta Gama sallamar wani ya siyo Singlet sai gashi ya Parker machine,Aamna tayi murmushi Tace Sannu da zuwa,Irin Dan gayun Nan harda wani basarwa Direct ya shige ciki ya zubawa Kansa chin chin yace na Naira Dari biyu yau Zan siya Aamna Tace to,Zama yayi Nan ma Yana kallonta duk kunya ta isheta,Wani magidanci ne yazo yasan Ahmad da irin iya shegensu mamaki ya kamashi ganinsa a Haka da wannan shiga ta Kaya,Bai taba ganinsa da shigar hausawa ba,Kuma Yana Zaune a shago kamarsa me kudi,Shuru yayi yace a bani barkono da citta,Aamna ta Mike zata zuba da sauri Ahmad yace No zauna Bari na tayaki Mana Haba,Tace Kai din? Bai kulata ba yace na nawa? Yace na Hamsim,Aamna tace ga kullin Hamsim can ka saka,ya dauki bakar Leda ya saka Masa ,Citta Kuma Tace gongoni Daya zaka zuba,ya fito ya auna gwangwani Daya ya zuba,mutumin yace babu gyara? Ahmad yace a gindinku kuke so mu kare ne Ina laifi ma duk arahar Nan Baku gani ba,Tsaki Yaja ya dauki citta Daya ya jefa masa a Leda yace gashi Nan anyi gyara,Mutumin ya karba ya tafi shi Kuma ya dawo ya zauna a ciki,Aamna tana ta mamakinsa.
Chapter 26 · 0% Book details