← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 89

Sashe 13

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana Nishi a ransa yace shegiya karfi ne da ita,Aamna kuwa mikewa tayi Tace Bari muje mu gaida Ubangiji wani kuwa sai dai su gaisa da barasa,a fusace ya Mike sai ta zura da gudu tare da fadawa dakinta ta saka key,Yana huci yace Zaki sani wallahi sai dai idan baza ki fito ba Useless kawai,Key din machine dinsa ya dauka tare da ficewa ya bar gidan gaba Daya,Ita kuwa Aamna wanka tayi tare da Gabatar da Sallar Magriba,tana zaune tana Azkhar har lokacin Sallar Isha yayi ta Gabatar sannan ta Mike tare Shiryawa cikin wasu kayan baccinta doguwar Riga ce red me sililin Hannu ta wuce gwiwa sosai ta Mata kyau,Kayanta ta Shiga Shiryawa sai da ta tsara komai fes sannan ta kwanta saman gadonta yunwa kamar zata mutu,Kitchen dole ta fito ta Nema Amma wayam babu ko Lipton a ciki bare wani Abu na dafawa,Kugu ta rike Tace Kan bala'i Bari ya shigo,Zama tayi tana jiransa Aamna Bata San shi sai safiya ko tsakar dare yake shigowa ba,Yana can Yana shaye shayensa.

Bangaren Ahmad kuwa tunda ya fita wajen su Mashkoor ya je Suka zauna Yana cewa Mummy Wai kamata Ni za ayiwa auren dole, aure ban sani ba, Mashkoor da maye Yana karkace Baki yace Mum sunyi fuck up fa,Muguntar Daddy ce Kawai cewar Ahmad,Bash yace karka kyaleta kaci uban Yarinyar ai wallahi zata gani ko mu ka Bawa dama sai munyi maganinta,Ahmad yace Guys the things is Mummy tsinuwa tayi min akanta fa,Yar Iska Wai Dazu Dani zata Yi kokawa,Jibson Yana zuka hayaki yace Eyyyeeee.....hey this girl get heart woooo....but show her you are our king,Sweet Boy just Sample the Beb,Ahmad ya kalle su, su Biyar suna ta korawa ya daga zundumemiyar kwalaba ya kurba yace gata da karfi har Elbow fa tayi min a kirji,La'ilaaaaah....cewar Mashkoor Yana dafe Kai yace aci mamanta Guys,Ahmad cike da Takaici yace Hmmmm me....me...me....Mum tayiwa haka,a bani Auren wata Ina Zan Kai wannan nauyin Kai wallahi ma dole ta karba,she must Collect...am....wayarsa ya zaro ya Shiga Kiran Mummy dinsa,Mummy lokacin tuni suna Lagos ma,ta daga Wayar tace Ya akayi Ango,Kamar zaiyi kuka yace Mummy kizo ki dauke wannan Ajiyar Taki Zan fa Iya kashe ta,Zan kashe ta ne Mum,karfa ki sa nayi mummunan laifi tam,Tsaki Mummy tayi tare da kashe wayar Baki daya.

Mikewa yayi Zumbur yace akan wannan trash din Mummy ta juya min baya,dole naci uban Yarinyar Nan,Zaga wajen ya Shiga yi,Ya dauki kwalabar Giya ya tarwatsa ta,kujerar da yake zaune ya dauka tare da yin jifa da ita,Su Kuma sauran sunyi tagumi kamar an musu mutuwa Wai Ana Taya Oga bacin Rai ne,Ahmad Bai koma gida ba sai 4pm ya shigo a make ya wuce palonsa tare da fadawa saman kujera ya kwanta Nan take bacci me nauyi ya kwashe shi,Ita kuwa Aamna da Yunwarta ta kwanta Haka da Asuba yunwa ce ta tasheta,Bayan tayi Sallah da Azkhar ta koma baccin Yunwa,sai 11am ta sake farkawa,Gidan ta hau gyarawa sai da ta Gama da room dinta da toilet sannan ta shiga dayan ta gyara,ta Shiga Dakinsa Nan taga Haduwar furniture gadon Kawai abin kallo ne, a Nan ta lalace tana kallo,sai da ta gaji ta gyara Masa ko Ina Neat Yana kyalli da sheki,Har Toilet duk ta Gama sannan ta dawo kasa a Nan ta ganshi Yana ta bacci hankali kwance,kitson calabarsa ta kalla ta leka Fuskarsa tana kallon Halittar Allah Iya Halitta,Tace tab Allah yayi Kira a Nan,waye zaiyi wannan in ba Allah ba,cikin Creazy Jean dinsa fatarsa duk a waje fara Kar da gashi kwantacce luf luf,Aamna Tace Uhmmmm.....sunanka Dan Zarra daga yau,kayi Zarra wallahi kafin a samu me Kama kafarka a kyau sai an tona,Habarta ta tallafe Tace kaga Dan baiwa....Fresh dashi...karya suke wani sweet Boy...ai wannan ya wuce Sweet Boy sai dai Honey Boy,Aamna tana nuna shi da yatsa Tace See Nose Alqur'an,Juyi yayi tare da Sosa Dan wuyansa,Aamna Tace ga Chest lafiyayye,Lips dinsa ta kalla ta Bude Dan bakinta tare da lumshe Ido Tace kiss mukeyi da shi ita kadai ta cuno Baki gaba tana feeling Wai suna kissing,Wani Iri taji a jikinta,Tace Kai da gaske na fara Jin dadin,Tunaninta ta kautar Tace kalli dalla ya wani kwanta da takalmi a kafarsa,a hankali ta tsuguna a kasa tare da zare Masa takalmin kafarsa a hankali ba tare da ya farka ba,Aikinta taci gaba da Yi sai da ko Ina ya dau kyalli da kamshi sannan ta leka waje taga me kula da Compound ya Gama gyara ko Ina na wajen,da Hijab a jikinta ta karasa wajen me Gadi,ya gaisar da ita Tace Musa ya kakeyi da cin Abinci a Nan gidan? Musa yace ai Hajiya duk wata Bayan Oga ya biyani kudin aikina Yana bani kudin Abinci na wata wata safe,Rana Dana dare,ai Hajiya Oga mutum ne me kyauta,Baki ga yanda yake taimakon na kasa ba,abinda nake so shi nake siya naci,ga kyautar kudi akai akai Yana bani,idan zanje ganin Iyali na Sha Tara ta arziki yake min,wayata ma Tekno dubu Arbain da biyar shi ya Siya min sabuwa dal,Aamna Tace yanzu dai kullum siyo abinci kakeyi? Yace me dadi ma kuwa Hajiya,tafiya Aamna tayi yunwa kamar zata kashe ta,Tace Bari ya tashi wallahi dole Nima ya dinga bani kudin Abinci na,Palo ta koma da Idonta Daya a manne ta Iske ya koma Bedroom Yana ta baccinsa,Bai tashi ba sai 2pm lokacin Yayi wanka ya hada Sallar Asuba da Azahar yayi ya shirya cikin jallabiyya ruwan toka,Yana zuba kamshi ya sakko kasa da Niyyar fita,Aamna wacce yunwa ta Gama cinyeta ta Mike da sauri ta kulle Kofar palon tare da sa key ta datse ta jefa key din cikin bra dinta tana kallonsa da masifa Tace wallahi ba inda zaka je sai ka bani kudin Abinci,matarka ce Ni a gidan Mijina nake sabo da Haka hakkinka ne nauyin ka ne ka sauke,Kai ya girgiza yace kina Neman rigima Dani,bana son Wasa da shirme,Ina da aikin Yi bani key Zan wuce Aamna Tace wallahi bazan baka ba sai ka bani kudin Abinci,Kai ya girgiza yace karki Bari kwakwalwata ta dau chaji Zan Miki Illa,Zan Miki Illa ki bude na fita ban son wasa,Aamna Tace wallahi yau baka Isa ba sai ka bani abinci,ka nakasa min Ido sannan zaka kashe Ni da yunwa,yace Mum ce ta kawoki kije wajenta ta Baki ko Ni Nace kizo gidana,bana sonki na tsaneki Akan me Zan Baki kudi na dalla Bude min kofa ya taso da masifa,Aamna ta rike Kugu sanye da Hijab Tace wallahi bazan bude ba,yace look ni bana taba Nonon Mata jikinsu ma bana tabawa ki dakko key ki Bude min kofa kin San Zan iya kwata a cikin Bra din Taki Kawai ban son tabawa ne ya Furta Yana yatsina Fuska,Tace Bazan Bude ba wallahiiii.. ta karasa da kukan wahalar Yunwa.

Sauri yake yi zai fita sai ya koma Sama ya fito da kudi dubu Hamsim Bundle na Yan dari biyar biyar yace gashi Zan Baki badan Ina tsoronki ba badan Kuma tausayinki ba Dan Ina so na fita ne Ina da Abinyi,Kudin ta karba Tace da karka bayar Mana Idan ka Isa,kaji dai tsoro na Yaro woooooo......cikin tsawar data razana ta yace Open the door,Ba shiri jiki na rawa ta zaro key ta Bude Masa ya fice a fusace tare da banko Kofar kamar zai ballata.

Ita kuwa murna da farin ciki ya kamata ta dauki dubu biyu ko wanka Bata Yi ba ta gyara Hijab dinta tayi waje,ko me Gadi Bata aika ba ta fice daga gidan,a Unguwar tana tafiya taga wani Resturant da sauri ta Shiga ciki tayi Order taje Away na Jullof rice with salat and chicken,ta siyo lemuka harda su Icecrewm Yogourt ta dawo gida ta baje abinta a Palo taci ta koshi tayi dam sannan taje tayi wanka tasa wani gajeren Wandonsa ta zabo fari ya Mata yawa Amma ta saka Haka,ta dauki t-shirt dinsa baka ta saka sun Mata yawa Amma abinka da me kyau sai tayi kyau,Haka ta gyara palon ta Karo karfin Ac tare da kunna kallo tana kallo ta wani can saman Hannun kujera baza ma ta zauna a kujerar ba ta tale kafafu tana Shan Iceream dinta tana ta Dariya a Haka ya shigo gidan ya sameta,Kallo ya bita da shi ganin kayansa a jikinta tana Shan Icecream,Wayar charger ya fisgo da sauri yace kayana are you Mad,Da gudu tayi cikin wani daki ya bita da kyar ta samu ta buya a toilet,yace Zaki fito ne,idan kin Isa kina ji ke kece ki fito,Tace kaima idan ka Isa ka shugo,baka kunya fada da mace,Namiji da Kai kaje kayi da maza Mana idan ka Isa a tumurmusa ka,Yace Zaki fito ne sai na Ballaki Kuma wannan kayan da kika sa wallahi sai dai a kone su ban Haka skin da ke Idiot ya juya tare da komawa palo.
Chapter 13 · 0% Book details