← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 89

Sashe 19

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka koshi,Baba yace zuba min wani farfesun a flask na tafi dashi idan munje gida zamu ci da breadi,Aamna cikin sauri ta samo flask karami ta kwashe ta bar kadan ta hada musu harda lemuka,cikin lefenta ta dakko wata atamfa da turaruka ta bawa Mama atamfar turaren Kuma ta bawa Baba,Sai Jin dadi sukeyi,Mama ta zuge Jakarta ta sake zaro wata laya da guru na damtse ta mikawa Aamna Tace ungo Bude Damtsanki ki daura wannan,Aamna ta Bata Fuska kamar zatayi kuka Tace Mama Kinga fa wani a hips Dina kince idan na cire Baku yafe min ba Haka kaina layu ne fa har biyu idan zanyi wanka nake cirewa Ina Yi nake maidawa Kamar yanda kika ce shima Kar na cire,Mama ta Bata Rai Tace saka wannan layar a gashinki itama ki soketa ga pin Nan a jiki Kuma wallahi kika cire Bamu yafe ba,Aamna ta karba ta soke Laya ta Uku cikin gashinta,ta dauki guru ta bude farin damtsenta ta daura,Dake tana da haske sai ya Mata kyau.

Mama Tace to Haka ake so,sai magana ta karshe zamu Kira surakanki a waya mu fada musu kina cikin wahala zamu dauke Yar mu idan suna so ki zauna sai sun turo Mana kudi sabo da Haka ko sun kiraki sun tambaya kice Haka magana take wallahi idan kika ce ba Haka ba kinji mun rantse sai kin bar gidan Nan ta karfi sannan sai Kinga matakin da zamu dauka a kanki.

Aamna tace Haba Baba Wai me yasa kuke Haka ne,Ni fa ba sonsa nakeyi ba,Kuma ma Ni Nan gaba barin gidan zanyi Akan me zaku karbar Musu kudi,a gidan Ubanwa Zaki bar gida? Sai mun Gama kwasar rabon mu tukun yarinya,Shuru Aamna tayi Tace shike Nan to kuje Allah ya kiyaye Hanya na gode,sauri takeyi su tafi Kar ya dawo gidan,Mikewa sukayi ta rakasu Suka tafi,Suna tafiya ta dawo ta hau gyaran gidan sai da ko Ina ya fito fes sannan taci abinci ta sheka wanka tayi Sallar Azahar,Kwalliya tayi cikin wata English gown silk maroon,me Hannun vest tayi mugun Mata kyau ta fito da shape dinta matuka,Fitowa tayi ta koma kitchen ta duba farfesun data ragewa Ahmad,Sai tayi cabbage soup ta Sha kifi tayi sakwara,me Gadi ta bawa sauran ta Ajiye ta zauna a Palo tana kallo,Bayan tayi Sallar la'asar tana karatun novel a Wayarta taji ya shigo Yana waya yace Daddy Kuma me ya same shi? Yana asibiti? Bazan zo ba Allah ya bashi lafiya ya furta tare da Zama a saman kujera ya rufe Ido tare da dafe Kansa.

Duk da baiyi Sallama ba sai tace me ya samu Daddy din? Wani kallon wulakanci ya Mata yace ina ruwanki ko son gulma,na fada Miki ki daina shiga safgata Zan Tara Miki gajiya wallahi tam,Shuru tayi Tace abincin fa? Baza'a ci ba ko dole ne sai naci girkinki? Wai me yasa kike son takura min ne? Sabo da Kai Mijina na ne shi yasa,Baki gaji da duka bane Naga Alama,Kai baka gajiya da fada da mace? Ko kunya baka ji fada da mace,idan kana Jin Kai Namiji ne kaje can waje kuyi da maza Mana kaga yanda zasu maka jina jina,ka zauna a Nan Ni sabo da mace ce sai dukana kake Yi wallahi sai Allah ya tambayeka,ranar lahira sai Allah ya Kamaka da hakki na,Murmushi yayi na rainin hankali yace sai na karasa wannan idon Daya shima a manne shi,Sai lokacin Aamna ta tuna ma Idonta a manne yake,Haka duk inda aka ganta sai dai taji Ana ta Mata Sannu da Allah ya sawwake,tana sani Tace zo na yanke maka farce gasu Nan sun fara taruwa,kwanciya yayi a kujerar tare da juya Mata Baya yace wannan karon wallahi kika kuskura ko da Wasa kika taba min farce saina ballaki aýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿ gidan Nan,ka godewa Allah ba sajenka da gemunka na yanke ba,Banza ya mata yana tunanin Daddy da akace Hawan jini ya kamashi saura kadan yayi paralyse.

Damuwa ya Shiga a ransa sosai gashi shi bazai iya Addua ba baida time,juyowa yayi Aamna ta kalleshi da sauri,Je kiyi Alwala,tsoro ya Kama Aamna a ranta tace ko hakkinsa zai karba yau na Shiga Uku maybe nafeelar sunna zamuyi daga Nan sai Sex,Idonta ne ya kawo kwalla Tace Alwalar me Kuma? Fuska ya Bata yace Zan fa zaneki wallahi kije nace kiyi Alwala ki zo,Aamna Tace wayyo Uwata na shiga Uku,shi ya manta ma Daren farko Ana Alwala da Nafeela,Aamna tace ka Bari sai dare Dan Allah kayi min Rai,Yace Bari na tashi kiga tsayi na,da sauri ta tafi tayi Alwala ta fito da Hijab a Hannunta tana kuka Hawaye shabe Shabe a fuskarta,Alwalar kikewa kuka duk tsoron Allah naki da kurin Sallah da waye waye,Aamna tayi Shuru tana Hawaye Tace Dan Allah kayi hakuri ance da zafi,zafin me? Alwalar ce da zafi? Ya tambaya Yana zaro Mata Ido,Sallayar Dake Hannunta ta shimfida yace to kalli gabas ki fara Nafeela,Aamna Tace bangane ba,ba tare zamu Yi ba? Yace Kiyi Nafeela nace ki yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya a madadi na,Ni bazan iya Yi bane.
Baki Aamna ta Bude sai lokacin taji kunyar kukanta na banza na tunanin banzan ta,Tace Bari ayi magrib,tana yin Sallar Magriba ta fara Nafeela.

Haka tayi ta Nafeela tana yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya,sai da ta idar Tace nayi to,ko magana baiyi ba,Wayarta ta jawo ta Kira Mummy, bugu Daya ta daga Bayan sun gaisa Aamna Tace Mummy ya jikin Daddy din? Mummy tana murmushi tace waye ya fada Miki? Aamna ta saci Kallonsa yace in kika ce Ni na fada Miki sai na karya ki yau,Aamna Tace lokacin da kuke waya Ina wajen,Mummy Tace okay da sauki sosai gobe ma muke sa ran Sallama mu koma gida,yaya fatan dai rigimar Bata Yi yawa ba? Aamna Tace ae Mummy,Baba ya kirani jiya,Gaban Aamna ya fadi,Mummy Tace banji Dadin abinda suka Iske Ahmad ya Miki ba,naga Baba yaji Haushi da yawa yace zai dauke ki daga gidan,Kunya ta Kama Aamna Tace Mummy ki kyale Baba rikicin tsufa yake Yi.

Dariya Mummy tayi tace Mama Kuma Ashe Business take so ta fara lokacin Muna cikin damuwa a asibiti abinda ta Nema Bai samu ba sai dubu dari hudu ta samu kacal Amma Inshaallah Zan Kara Mata wasu,Aamna tayi Shuru sabo da Matukar kunya da nauyi data ji, Tace kuyi Hakuri Mummy wallahi Ni ba sa Hannun na ciki,ban San zancen ba ma,Mummy ta fuskanci Aamna ta Kuma Gane su Baba Kawai kyalewa tayi,karki damu Aamna na fihimci lamarin,kici gaba da Hakuri Zama Dan Allah kinji,Aamna Tace Inshaallah ba matsala,kina bukatar kudi ko wani Abu? Aamna tayi murmushi Tace a'a Mummy ba abinda nake bukata komai Yana Yi min idan na tambaya,kin tabbatar? Aamna Tace ae Mummy kiyiwa Daddy Sannu da jiki a gaisar min da Humaira Kuma,Mummy ta dinga yiwa Aamna godiya sannan ta kashe wayar.

Ahmad ransa ya tunzura Jin irin godiyar da Mummy ke Mata to uban me tayi ake gode mata,Cikin masifa yace ni baza a gode min ba Dana dauki kaddara nake zama dake cikin kunci sai ke Za'a godewa Ana wani sa Miki Albarka ke ga fitsararriya ko? Harda wani Jin dadi kina to Mummy...ya makale Murya tare da gwada muryar Aamna yanda take magana,Aamna Tace Wai Kai me yasa baka da kirki ne? Yace ke dalla rufe min Baki ke Wato an Baki lasisi ko harda wani Kara siyo waya Vivo sabuwa,wannan ba gata bane, ke ga tsigalalliya ko kina wani girgiza da kafada ya gwada girgizar Aamna Idan tana masifa,Aamna ta kyalkyale da Dariya gashinsa ya girgiza tare da gyara sabon kitson calabarsa,Aamna Tace shike Nan Zan Kai karar ka wajen Mummy,Yace idan kina yiwa bushashen tsohonki kije ki Kai karar tawa ki gani idan akwai Wanda ya Isa ya tankwara Ni ko yasa naji magana,an fada Miki wani Jin Magana nakeyi.

Baki Aamna ta Bude Tace ai Ni tsoho na ka ganshi me kiba ne,Ashe Ahmad ba Baba yake nufi ba yasan Baban Aamna na asali Dan Sudan wani mugun bushashen tsoho ne,ramarsa ta baci tunda lokacin da wayonsa Bai manta shi ba,Sai yace kije ki binciki tarihinki yarinya kiji waye tsohonki Dan lukuti ne ko kuwa,Aamna ta Mike tsaye tace Allah ban yafe ba sai na cijeka ta fado Kansa Kamar wata Kura ta Bude Baki da gaske ta Kai Masa cizo a wuya,wuyanta ya cafka da hannunsa ya shaketa sosai ta fara kakari Idonta ya firfito kamar zata sheka lahira ya hankadata gefe ta Fadi a kasa dabar, mikewa yayi zai fita ta jawo rigarsa Iya karfinta,ya juyo ya dauketa gaba Daya ya jefata saman kujera Kamar Yana wrestling,Aamna ta cakumo kafafunsa ya Fado gefenta,Idonsa Wanda ya canja yayi ja sabo da kwaya ta motsa ya watsa Mata wani kallo ai sai ta Mike ta arce da gudu.

Key din machine dinsa ya dauka ya fice abinsa ya hau machine kenan yaji an jefo Masa Robar ruwa a Kansa kwas,Kansa ya daga sama yaga Aamna ce ta baya balcony dinta ta sama tana cewa aje a Kai karata wajen human Right idan an isa,ko kazo ka dokeni,Yatsunsa ya wara ya Mata dakuwa Wato ambola Aamna ta Masa gwalo,yace zamu hadu ne da karfi yanda zata ji,mu hadu Mana gani ta matso jikin karfen wajen Dan Allah taho mu hadu tayi girgizarta da kafada,saura kadan yayi Dariya ya matse yace Fuck you....Aamna Tace Dadi ne da shi come and fuck me,Dariyarsa ya guntse yace Yar Iska ce ke ai,nafi karfin Iska sai dai Guguwa,Machine dinsa ya kotse yayi waje abinsa ya barta tana ta dariya.
Chapter 19 · 0% Book details