← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 89

Sashe 83

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ nasan zai bani,Hafsat ta Mike tsam ta dakko cup a kitchen ku bani dama Bash ba Hakuri ne da shi ba Nima baya daga min kafa ku bani Nima,Suna Haka sai ga Sameera da Humaira sunzo,Ai Sameera mayya tace Kan bala'i ai na shanye tawa irin wannan dama Ina ta Nema ki bani na kurba,Humaira tace Mene ne bayin Allah? Aamna tace kayan harka ne Wanda ke sa me gida Hawaye,Yar China harda shewa tace har kuka ma Wiwi zai Miki,Humaira Tace ba ruwana Haka Kawai ma ya Muka Kare da shi bare na Kara da wannan Ina da wasu abubuwan ma so nake sai na Saba sai na fara,Yar China tace ke dalla kauyis Kamar bada Lagos kika fito ba yanda kike Yar balarabiyar Nan ai ya kamata Brown yasan can ciki dinma Balarabe ne idan Zaki daina zancen zafi da wani takura ki daina mu mun watsar Gazal ake sa Mana kullum,Suka dinga kyalkyala dariya,Yar China ta Zama fetsararriya bayan itace karama kuma.

Humaira tana Dariya Tace Gazal? Tozali ba yarinya zauna mu ba ruwanmu shi ake gwaguda Mana kullum kin zauna can wata katuwar tana wajen
tana siyen gishirin Mata tana yafawa ciki ke a barki a Nan,to mazan yanzu Zina ba komai bace a wajensu Allah kiyaye idan Zaki Sha ki sha,Aamna tace wallahi ai mu Bama daga kafa Bama Free,Nafeesat Tace ku bani Dan Allah tsarin Nan yayi Yar China Uwar Mata,Hafsat ta bulbulawa cikinta,Aamna Robar ruwa ta dakko aka zuba Mata sannan ta Sha wani,Haka su Nafeesat ma aka barwa Yar China ragowar nata itama ta Sha kadan tace kadan Zan Sha sabo da tun safe na Sha wani,ta mayar da abinta,suna hirarsu Aamna dake dama Yaya bare anyi Kari tace Kai na tafi Good Night yanzu zai dawo,Yar China Tace za dai kije kwada Masa Kira a waya ya dawo,Nafeesat tace Nima nayi Nan,Daya Bayan daya suka tafi kowacce.
Baba kuwa ya Canjawa Mama sabon suna daga Aishatu ta koma Ya Hajja,Mama tayi ta Jin kunya Amma Baba yace Ina ya dakko darasi wajen Rahilu,Mama Tace kaji kunya wallahi,Yana daga kwance yace kalle Ni Nan nafi Rahilu komai Amma Rahilu yanda naji Yana Kiran Hubby abin ya firgitani Dole Nima na dauki mataki Ina laifi ma dana Yi Kara nace Ya Hajja karki jawo wallahi ma koma sweetner ma,Mama tayi Mukus.

Siyama tunda aka kaita Hashim Bai wani Bari sai ta so shi ba ko wani abu ba jira yake karbar Hakkinsa kullum,Siyama ba yanda ta iya gashi Yana kyautata Mata sai abinda take so Bata da bakin Yi Masa musu akan komai,Jin Dadi ba Wanda baya Bata sabo da duk Samunsa gida yake kawowa mutum ne me zuciya, da ka samu me kudi da mota marar zuciyar kyautatawa Iyali gwara Dan dako me zuciya.
Ga Aiki tuni Ahmad ya dauke shi bashi da matsala shi kam,Ita kanta Siyama sai ya fara birgeta,Waya ta Kira Aamna suna waya,Aamna Tace ya me gidan fatan ba a bashi wahala? Dan Allah karki amfani da kiyayya ki cutar da shi,Dariya Siyama tayi tace wa? Ai in fada Miki Ni wallahi ya fara birgeni,Ni yanzu masifar birgeni yakeyi in fada Miki ga tsafta ga iya daukan wanka,ke in fada Miki ga iya love har mamaki nake yanda ya iya Romancing ko bature Albarka mutuniya ta,Aamna tana dariya tace kice yafi Faisal? Siyama tace Faisal din banza Ni sai yanzu Naga ma Ashe yafi Faisal kyau da komai wlh kawai kudi Faisal ya fishi Kuma Inshaallah shima kwanan Nan zamu Faso gari tunda ya fara Aiki da Ahmad,Baki gani ba sai abinda nake so abinci yanda me kudi yake cin me kyau Haka Nima komai available,sunansa ma me Dadi Hashim Dan Allah yaushe Zaki hada shi da sunan Faisal,Wai Faisal Abu ba Dadi Haka Kalar karya feso karya shine Faisal,Aamna tace iyye Dan Adam kenan kayan Allah,Kawai Hashim ya tafi Dake? Siyama tace Ni yanzu ma na gano ba birgeni yake Yi ba sonsa nakeyi,Lokacin da suke Wayar Hashim ya shigo da danyun kajinsa a Leda za a zuba farfesu,farin ciki ya kamashi yaji da kunnensa tana sonsa shi Kam ya Gama dacewa,tun Siyama tana jaririya yake kaunarta,ba irin wulakancin da Bai Sha ba a wajenta sabo da baida kudi Amma gashi yanzu cikin sauki,Godiya yayiwa Allah Dan murna ji yake kamar ya tashi sama,Sabo da murna fita ya sakeyi ya sake siyo kifi da wasu tarin abin makulashe.
Siyama yau taga tattali da soyayya wajen Hashim,sai ta Kuma Jin sabon sonsa.

Lokaci na ja cike da kwanciyar hankali da kaunar juna cikin Aamna ya shiga wata Biyar har ya fito Ana gani,Bata wani laulayi me wahala,a satin Kuma Humaira ta fara zazzabi da Amai yaki karewa,Ana zuwa Asibiti akace ciki ne da ita har na wata biyu,Brown harda rawa a Palo a Gaban su Tawaga ya fara Break dance suna ta dariya,lokacin Kuma Nafeesat canjin da taji a jikinta tana zuwa hospital wurin aikinta Tace a Mata test sai gashi tana da ciki na wata daya sai Result ta kawowa Mashkoor,Yar China tana ji tace Allah ya tsare watakil muma Muna hanya badan Allah yasa last month nayi period ba da Nima asibiti Zan tafi a gwada Ni Naga abin Kamar gasa ne ai muma ana Mana aikin ba finmu rakashewa aka Yi ba sai dai a nuna Mana shekaru,Hafsat tafi kowa son ta samu ciki tana son Yara a rayuwarta Amma itama Shuru Tace to Muna jiran tsammani,Sameera Kuwa da Jibson dama su ko a jikinsu idan sun samu suna maraba.

Kwanci tashi sai da cikin Aamna ya shiga wata Shida sannan Sameera ta samu cikinta,Jibson harda yanga zaiyi da shima,Hafsat ma ta samu ciki,Yar China ta damu kanta Bata San tana da cikin ba ma garin jarabar wasanninta ta tafi part din Aamna ta hau lilo tana ta shillo a kai daga lokacin Mararta ta daure ta Shiga kwala Ihu ba ji ba gani,Aamna ta fito,Allah yasa sun Iya mota mazajensu sun koya musu Yar China ce Kawai Tawaga yaki koya Mata sabo wasan tsiyarta Kar ta kashe kanta da mota shi yasa duk inda zata shi ke kaita ko Driver, Aamna ce ta fito ta hango Yar China a kasa ta zube Jini malalala Fitowa ta kasanta,a gigice ta Kira Nafeesat Suka saka ta a mota sai asibiti suna kaita aka Kira Tawaga Suka sanar musu suna Office ma,Tawaga ya gigice yace me ya sameta? Aamna Tace ka kwantar da hankalinka Bari tayi,yace Ni ba barin ba ya lafiyarta? Tana Nan ma an canja Mana dakin Hutu har mun gyarata bacci ma takeyi, Kasa tuka motar yayi sai Jibson ne ya dakko shi Suka wuce Asibitin Basu Dade da shiga ba Yar China ta farka da kuka,sai ihun kuka takeyi an zaci ma wani ciwo takeji aka yo kanta,Ana tambaya lafiya? Yar China ta sake rushewa da kuka tana shafa cikinta ta kalli Tawaga Wanda ya rike Daya Hannunta Tace ance Wai Bari nayi? to menene tunda lafiya kike ai Yaron yaje zamu samu wani,yar China ta sake rushewa da kuka wallahi bazan yarda ba sai an bi min hakki na sakakin likitocin Asibitin Nan ne,sune Suka jawo cikina ya zube,Wa yace ki hau lilo da shegen wasanki cewar Iyalle da ta shigo yanzu hankali a tashe,Yar China tace sai an biyani cikina bazan yafe ba,duk wahalar da Muka Sha ai ban San Ina da ciki ba da ace na sani yaushe Zan hau lilo,Wata Likita Tace dalla malama rufe Mana Baki kin cika Mana asibiti da kuka mijinki gashi Nan Zaki sake samun wani.

Bed din Yar China ta doka da karfi tana burbuwa ta nuna Likita da yatsa Uwarki ce zata min Cikin shegiya tsinanniya duk ba kune kuka jawo ba da kunyi aikinku da kyau cikin zai zube ne Shegu Yan Practical duk irinku ake zubawa kuna kashe Yaran mutane,Tawaga ta kalla tace sai an biyani Diyyar dana da aka kashe min a Asibitin nan, Iyalle da karfi Tace Diyyaaa? Yar China Tace ae,Likita tayi Dariya tace to madam ki Gama zamuzo muyi Miki wankin ciki,Yar China ta saki sabon kuka tana za a zura karafa a cikina so suke su karasa min mahaifata,yahudawa ne America ce ta dauki nauyinsu sabo da a rage yawanmu a duniya,yahudawa ne suke biyansu ta karkashin kasa,Duk Wanda yaji haukar Yar China sai yayi Dariya,Yar China tace ko America ce ta Basu kwangila ko kasar Denmark matsiyata sune basa kaunar musulunci kasar Denmark sune ma.

Barin tayin Dan aka bawa Tawaga a kwali Yar China tace ku Bude min Naga gudan jiinina tana kuka sosai Iyalle ta karba ta Bude Mata Yar China ta bangale Baki tana murmushi Yaron da ko halitta ba a fara Masa ba Amma take zuba Uban murmushi tace Allah sarki zamu hadu da Kai a makarantar Annabi Ibrahim,aka kyalkyale da dariya,Yar China ko kulasu batayi ba tayin dan da kusan ma jini ne shi take kallo Tace ga jini na can na Gane shi ga bangaren Tawagana can Suka hadu a broader, da tuni sunanka Ahmad sunan Babana za a mayar idan mace ce Kuma Salma sunan Babata Amma Ina,Iyalle ce zata rufe kwalin Yar China ta dage sai ta sake ganin Danta aka Bude Mata Karo na biyu tace Babanka ya Sha wahala kaji Amma mun yafe maka sai munzo ka jiramu a madakata kaji Allah yayi maka Albarka sai Watarana Amma kayi Hakuri zaka Dade baka ga munzo darul salamu ba sabo da Inshaallah baza mutu da wuri ba sai mun Haifo kannenka Suma sun Haihu yayan kannenka sun Haihu sannan ka ganmu,kayi gaggawa Dana, da ace ka zauna ai da kaga kaun....Yar China ta karasa da kuka Tace First Night dinmu nake tunawa Iyalle ke Baki San turanci ba First Night Iyalle shike nan,Allah sai na Suma Yar China tayi luuuu akan bed Wai ta Suma,Dariya aka dinga Yi har Tawagan nata Haka ya tafi da tayin,Yar China tana cewa karku cike Masa Ido da kasar kabari Kai Jibson wallahi karka sake ka taba min da baka Yi Addua ba nasan halinka.
Chapter 83 · 0% Book details