← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 89

Sashe 18

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama Aamna tayi itama,Siyama Tace Hauwa'u kuwa tace tana Gaida ki,Hauwa'u Yar class dinmu,na Gane ai kice Ina Amsawa na gode,Siyama da larabci tace Ma Fi mishkla,ya kamata mu shiga kitchen ayiwa abokan mijinki girki Bai kamata su zauna da yunwa ba,ya kike Abu kamar Baki San darajar mijinki da abokansa ba,Aamna Bata kawo komai a ranta ba Tace Kuma fa Haka ne muje to ki tayani.

Kitchen Suka Shiga Siyama tana ta wani kwarkwasa Wanda take Yi Dan shi Bai gani ba su Jibson sune Suka bita da kallo suna Hadiyar yawu.
Fried rice suka Yi hadaddiya taji hadi da soyayyar kaji,ga zobo sun hada me Dan Karan dadi,salat ma an hada daban,a Dining suka shirya komai tare da gyara ko Ina sannan Siyama da Shishigi tazo Tace mun Gama guys gashi can a Dining,Ahmad Bai ko motsa ba sai su Jibson ne Suka zagaye abinci suka far Masa,kafin kace me sun cinye komai suna Santi sun shanye komai,Siyama tana zaune a cikinsu Suka ci tare sai taga Aamna ta fito da katon tire da wasu miyagu food flasks na musamman komai ta jera a Gaban Ahmad kasancewar tasan Bai zuwa Dining side.

Serving dinsa tayi komai ta zauna a gefen kafafunsa tace tashi kaci Abincin,Siyama ta Bata Rai tana daga can Dining ta tsura musu Ido ranta a bace tana Jin Ina ma itace a wajen Ahmad Haka ba Aamna ba,Abinda Aamna ta fuskanta Kamar Bai da lafiya kwana biyu tunda yayi zazzabin Nan,Bata San tsabar kwayace ba take sashi Yana slow.
Ka tashi please tun safe baka ci komai ba,Ahmad yaki tashi,Siyama ta saki murmushin Jin dadi,a hankali Kuma da ya gaji ya Mike tare da Zama ya saki jiki sharaf yayi wani Slow ya tsaya a Haka yaki Kuma magana.

Aamna tasa spoon ta ebo abincin Tace to Bismillah,kamar bazai karba ba sai Kuma Yaja Tsaki tare da bude bakin kadan Tace ka Bude Mana ya Dan Kara budewa ta zuba masa,Kamar Yana tauna madaci Haka yake ci,a hankali yace kice waccen Yar Uwar Taki ta bar min gida kallo na take Yi bana son kallo,Dan kar ya fasa cin abincin Aamna Tace to Bari ka Gama cin abincin tana ta bashi a Baki Yana ci sai uban Tsaki yake ja,ya ci da yawa yasha Zobon ya daure Fuska Kuma yace cikin tsawa ta bar gidan Nan,ba Aamna ba Siyama ita kanta sai da ta firgita ta Mike ba shiri,ya kalli su Jibson yace daAllah kuje Ina son Zama Ni Daya Yana magana ya girgiza kitsonsa,gaba Daya Suka ce an Gama sarki Suka kwashe kayan mayensu Suka Yi gaba,Siyama ta kalli Aamna tayi murmushin yaudara Tace kawata na wuce,Aamna ta Mike ta saka Hijab Tace muje na rakaki,har bakin Titi ta raka Siyama,ta Bawa Siyama dubu Uku tace gashi kawata kiyi kudin Napep.

Siyama ta karbe Tace na gode kawas,Aamna Tace kiyi Hakuri da korar da ya Miki wallahi banji Dadi ba Amma Kinga ba yanda zanyi da shi idan kin dawo next time sai na Bude Miki kayan lefen Nawa ki zabi abinda kike so ciki,Siyama ta washe Baki Tace na gode kawata ai na matsu na fara daukan wanka zanzo jibi sai na zaba,Aamna Tace ba damuwa Amma me kike ganin Zan bawa Zuhra itama?Siyama ta daure Fuska Tace zuhran data auri me rufin asiri uban me za a bata,irin mu ai mune muke bukatar taimako,Aamna Tace haba Siyama ya Zaki canja Hali Allah ya Hana mutum zaiyi Alheri ka Hana hakan,ko mutum Yana tayar da Kai da million ai Alheri Dadi gareshi Kuma ma ai kamar Yar Uwata ce tare Muka taso itama abinda take so zata zaba,me Napep ja muje dalla cewar Siyama cikin Fushi,Dariya Aamna tayi ta juya gida,tana zuwa ta tura Kofar palon taji Gam an rufe,tasan Ahmad ne ya rufe Wato Bai so ma ta shiga Kar a takura Masa,Murmushi tayi Kawai ta Danna door bell har ta gaji Bai bude ba,a bakin Kofar ta zauna ta zuba tagumi Tace kaddara kenan,Allah ya jarabce ni,Kwalla ce ta cika Idonta taf.

Wasa Wasa har Magriba tayi Bai Bude ba sai jikin tap taje Wanda ke Garden tayi Alwala tare da Gabatar da Sallah a Nan tayi har Sallar Isha sannan ta dawo tayi bugun duniya Ahmad Yana can Yana baccinsa yaki budewa Kawai Kuma Yana sani yayi haka..
A bakin Kofar Aamna ta zauna tare da jingina da jikin bango a Haka bacci ya kwashe ta,har 9am lokacin Kuma Mama da Baba sunzo kawo Mata Ziyara,a Nan Suka hango ta,Mama Tace cab ga Alama mun gani Aamna Bata cikin Jin dadi,Baba yace Yar jakar uba gwara duniya ta koya Mata hankali ko ta koyi darasi,gida har gida sai Takaici a ciki,Allah yasa ba Zuhra bace a wannan halin, Mama ce ta taba jikin Aamna da Kalar tausayi Tace tashi Aamna,firgit ta farka taga gari ya waye sai Rana ta gani kwall a kanta,Salati tayi ta Mike tsaye cike da kunya Bata so su Baba suka ganta a wannan halin ba sabo da tasan zasu shiga damuwa.

Baba yace Ashe yau za ayi yaki a gidan Nan,yata Dana rike da Hannu na muka Raine ta in dauka in bada ita Amana Amma a wulakanta min ita Haka karya ne wallahi,ba a haifi mutum ba,Baba Yana bala'i ya kaiwa Kofar Naushi zai daki kofa Mama ta kifta Masa Ido tare da yin wuf ta damko hannunsa tana Haba Baban Aamna da Zuhra Haba,gidan suruki ne Bai kamata ba,Abi komai a Sannu,Aamna tana Jin tsoro Ta durkusa a kasa tana rokon Baba tana Dan Allah Baba kayi Hakuri ka rufamin asiri,Kayi min Rai Baba wallahi idan kuka tafi Ni zai duka,dukan tsiya zai min,a hakan ma ya muke karewa kusan kullum sai ya dakeni,Dan Allah Baba ku tafi gida Ni zanzo,Kamar gaske Baba yace Ina ai wallahi yau sai na Kira Uwarsa da ubansa Akan Haka baza mu lamunci wannan ba,Mama tace ai batun tafiya gida Bai taso ba akwai abubuwan da mukazo tattaunawa da yawa sannan Kuma yau a Nan zamu yini muci mu koshi muna Nan har sai ya Bude Kofar,Aamna ta dafe Kai Tace wayyo Allah na Shiga Uku,Baba Kar ya wulakantaku a gabana bazan jure ba sai dai ya kashe Ni a kanku Dan sai na Rama,Ashe akwai hargitsi da balbalin bala'i kuwa yau a gidan Nan cewar Baba ya nemi waje ya zauna daram,Mama ta gyara Mayafinta ta zauna itama,Aamna kuwa Tap ta nufa tayi Alwala tayi Sallah sannan ta dawo wajen,Suna zaune sai Suka ji baram an Bude kofa da karfin tsiya,kamshi ne na daban ya daki hancinsu,Yasha wata jallabiya Brown Yar tsangalalliya Takalminsa flat Brown yayi kyau kace baya Shan komai,Fuska ya sake daurewa ganin Dangin Aamna,Tsaki Yaja da karfi ya furta sai kace Uban tsohonki ne ya Gina min gida,Kun da dameni da wannan tsofaffin Banzan,Aamna Tace wallahi ba sune tsofaffin banza ba sai dai in naka ne na banza na wofi.

A fusace ya juyo Yana huci yace Mummy na data auro min ke wacce ta nace tana sonki kika zageta yau? Jikin Aamna ne yayi sanyi Tace ai ba da ita nake ba Ni,ko kaji nace Mummy? Mummy ai na fika kaunarta Aamna ta wayance Kar yaci ubanta,Baba ne yayi karfin Hali yace ae da ita ake din sai me? Aamna Tace Ni bada ita nake ba Baba,Mama Tace Iyyee.....Juyawa Ahmad yayi yace Zan dawo gidan Nan zamu hadu ya Haye machine dinsa ya bashi wuta sannan ya dage kafa Daya sama yazo har Gaban su Baba ya kotse machine din tare da bashi wuta ya bulbulesu da hayaki ya fita a tsiyace.

Aamna ce ta daka tsalle tare da nuna Bayan Ahmad da yatsa Tace sai nayi maganinka zaka dawo ne sai ka sani,sai na cije ka wallahi a gadon baya,Iyayen Nawa zaka yiwa haka,zaka San ni Yar halak ce.

Mama Tace ke dalla rufe Mana Baki, banza matsoraciyar banza kin Gama cika Mana Baki gashi a gabanki ya ci Mana mutunci Baki ce komai ba sai da ya tafi,Baba Kuwa Takaicin Aamna yasa yace tir dake Aamna muje ciki mu kiyi Mana girki muci mu Sha.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYA TAĪ)\Ī)\

31-35

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

MAMAN MURTALA
HAFSATOU
'YAR BAIWA
INNARO
AISHA
SALIHU UBAIDAT HARUNA

Aamna da sauri ta fada kitchen sabo da so takeyi suyi sauri su tafi,babu Bata lokaci tayi musu farfesun kaji,ta musu jallof din taliya Tasha kifi da kayan lambu sai lemuka da ruwa ta kawo musu,Suka zauna Suka dinga kwasar girki, Baba Yana yin Loma Daya yace Allahu Akbar sai na tuna da Uwar dakina Dake Kano Hajiya Sahura lokacin da aka kaini almajiranta na Zama Yaron gidanta,Haka take dafa Taliya Malam Kamar daga Otel(Hotel),Mama Tace taji tarihu kaga inda tsiya tayi tafiyar dogon zango,ai a Nan gidan Tsiya Balaguro tayi ba tafiya ba cewar Baba,Aamna tana ta dariya Tace ai kudi yake bani da yawa,kwana na Daya na fara fita,ba ruwansa da wani Ni Amaryace inda Naga Dame nake zuwa,Baba ya tsurawa Aamna Ido yace indai akan irin wannan cefanen ne ki dinga ficiwarki daga Nan ki dinga biyowa ta gida kina yaga mana.
Chapter 18 · 0% Book details