← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 89

Sashe 38

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun safe Aamna ta fara amfani da Magungunan Infection dinta,ciwon yaji magani da Allura ya tabo shi sai ta fara Jin kaikayi a gabanta,dama Likita yace idan ta fara Sha zata ji sabo da an tabo ciwon,Sanye take cikin wata Riga karama me Hannun Vest fara da tight baki,Ahmad ya Mata waya zaizo da dare zai Bata labarin Wa'azin da Tace ya zauna ya ji,Bata Yi zaton cikin gidan zai shigo ba,sai Jin sallamarsa tayi a palonsu,Mama ya gaisar ta amsa sama sama Amma ganinsa dauke da ledojin take away sai ta washe Baki harda cewa shiga mutuniyar taka tana ciki, ai kuwa ya wuce bedroom din Aamna,Mama sai kallo sai Harara baza su iya komai ba dama,Aamna sai soshe soshe takeyi duk ta rasa sukuni.
Yana shigowa ta janye Hannunta da sauri Amma ya rigada ya gani,Dariya ce ta kwace masa yace ai sai ki fada min nazo na tayaki,Kuka ta saki masa yace yanzu zanzo na tayaki kwantar da hankalinki.

Ba kinyi zaton nine ba lafiyayye ba to gashi reshe ya juye da mujiya,Kuma yau Hira zamu Sha babu soshe soshe,Aamna ta goge Hawayenta tana Dariya Tace Allah baka Isa ba ka tafi gaskiya,Amma Kuma gaskiya yasha kyau cikin wani yadi brown me azabar kyau sai kamshi yake zubawa,Tana kwance Bata tashi ba,Saman bed din ya haura tare da kwanciya shima,Tace ka rufe Kofar da key kasan Mama Kar ta shigo,ai ba Wani Abu zanyi ba Dan Kawai na kwanta mene a ciki ya furta tare da gyara kwanciyarsa.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYATA AAMNAĪ)\Ī)\

NA KUDI NE

DAN ALLAH KARKI FITAR DA NOVEL DIN NAN,BADAN NI BA DAN GIRMAN ALLAH.
IDAN BAKI BIYA BA KARKI KARANTA DAN DARAJAR ALLAH.

61-65

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

AUTA
ALHAMDULILLAHI
AISHA

Aamna kunyarsa taji ta juya Masa baya,Juyo da ita yayi suna facing juna,Hannu tasa tare da rufe idonta,Hannun ya janye yace idan fuskar Zaki rufe tashi zanyi nayi tafiyata,tsayawa tayi tana murmushi Dan Bata iya jurewa,Baki da Aiki Sai Dariya ko gajiya bakya yi,wata dariyar tayi tare da Kai Hannunta zata rufe fuskarta Hannun ya rike tare da furta kiyi dariyarki a Haka,Laaa My world har gurun wuya gareki?wanne gurun wuya kamar wata me kiba,dama Yana sani ya fada Dan Kawai ya kalli Kirjinta ne,sai yace ga shi Nan duk yayi zane,Aamna Tace Naga ta kaina ta Mike da Niyyar dakko karamin mudubi a handbag dinta ta duba,Hips dinta ya riko da Hannu biyu yace Wasa nake Miki dawo ki zauna tunda Baki da lafiya,Zama tayi a bakin bed din yace ki kwanta karki taso da kaikayinki,Dariya ya Bata ya takura Mata,yace ki dinga Jin tsoron Allah harda kaini Hospital ko Ina da cuta sai gashi ta kwaje a kanki,Mukus tayi ita duk yasa ta rude Yana kwance a gefenta.

Ledojin Daya shigo da shi yace gashi Nan ki duba kici abinda kike so,Dama yunwa take ji Mama taliya ta dafa da Mai da yaji ita Kuma Bata sonta,Ledar farko tana budewa taga sabuwar waya me tsada Samsung Yar gaske,dama tana ta fama da Vivo karama,Farin ciki ne ya lullube ta,Ahmad Kuma yaga yanda take murna yaji Dadi Amma sai ya maze,Daya Ledar ta Bude taga agogo kala Uku masu tsada na Mata kamar yasan tana bukatarsu sabo da a lefenta shi aka manta ba a sa Mata ba,Daya Ledar Kuma wasu dogayen rigunane Yan Turkey kala Uku masu shegen kyau da shape,Ledar karshe itace ta shawarma katuwar gasashiyar kaza,da Icecream manyan Roba har uku,Sai wasu Snacks da lemuka, Yogourt,sai da ta Gama dubawa sannan ta juyo ta kalleshi cike da shauki da mamakin irin son da yake mata,kafeshi tayi da Ido shi kuwa wayarsa yake latsawa,Wayar ta karbe tare da fadawa jikinsa ta Rungume shi tare da kankame shi tana ta zuba godiya ba adadi tana Masa Addua,Tace gobe zanzo gidanka tun safe har Yamma zaka koya min Jullof din Nan,Allah ya kaimu ya furta tare da shafa dogon gashinta me santsi.

Lips dinsa taci gaba da karewa kallo kamar tayi kissing dinsa sai Kuma ta tuna wani Abu ta fasa,junansu suke karewa kallo,Idonsa ne ya Dan canja Yana tunanin wani Abu,Fuskewa yayi yace kici Mana Kar yayi sanyi,Tace Kai fa? Bana ci Ni ki Bawa Mama Zalama Naga yau har saukata akayi anga kayana,Dariya Aamna tayi ta dauki duk abinda zata iya ci ta kaiwa Mama sauran,lokacin Baba ya dawo.

Mama Tace shine sai da kika Gama kwashewa Zaki kawo mana Yar bakin Hali,Aamna tace idan Kuna so to idan Baku bukata ku bani? Baba ya Bude Baki tare da kwada Mata hularsa a kanta yace Yar Iska Mara kunya Dama badan Allah kika kawo Mana ba bakar kadara karuwar banza wacce ubanta ya gudu ya barta ba galibu,Aamna Ta musu Shuru kawai tayi tafiyarta.
Aamna da Hawaye ta shigo bedroom dinta tare da fashewa da kuka,Hankalin Ahmad ya tashi yace lafiya? Aamna Tace Mama ce da Baba ta bashi labarin me Suka ce,ganin Su Baba ne yasan ba abinda zai iya musu Dole ya girmamasu komai haukarsa,Aamna ya shiga lallashi Amma Taki daina kukan,Ganin Taki dainawa ya santa da taurin Kai sai ya Mata wayo ya Mike a zuciye yace bazan dauki wannan ba akan wannan Zan Iya fatali da mutum in tattakashi ya dire kasa zai fita duk ya gigice kwaya ta motsa jikinsa har rawa yakeyi kamar gaske..

Aamna ta rikeshi da sauri tana cewa tsaya Mana su Baba ne fa,Iyayena nane fa,Suna Iyayenki zasu Miki Haka sake Ni na tafi wajensu ya fisge zai fita Aamna ta cikwikwiye shi tana rokonsa yace to kin daina kukan? Da sauri Tace ae na daina,kin tabbatar? Tace ae yace to ci abinci,Zama yayi a bakin bed din kusa da ita kafadarsu tana gugan juna,a kafadarsa ta kwantar da kanta tana shagwaba tace a ramawa Kura aniyarta ka bani a baki Nima,yace an Gama My Queen,ya Shiga Bata tana ci tana ta shagwaba sai da ta kusa cinyewa sannan Tace ta koshi.

Toilet dinta ya shiga ya wanke hannunsa ita kuwa brush tayi ya kulle ta a ciki Yace Yi wanka to,Dariya tayi Kawai tayi wanka tare da gasa Hq dinta da ruwan zafi da salt sabo da Doctor ne yace tanayi Kuma sai taji Dadi sosai,ta ciki Tace Miko min lotion Dina Zan shirya,yace da kin fito ma ba abinda Zan Miki Kuma karki manta na Gama ganin komai ki daina batawa kanki lokaci,Hijab ta daura a saman towel din ta fito,kallo daya ya Mata ya dauke Kai a cikin hijab ta shafa komai,harda zabo rigar bacci me kauri ta saka,Zo na gyara Miki gashin,Ba musu ta zo ya gyara Mata kuwa ya Kama Mata,tayi kyau agogon hannunsa ya duba yace almost 10pm zo kiji me liman yace yau ya Danna mata recording,tunda Aamna taji Ana magana Akan Kara aure sabo da kin gaskiya sai Tace Ni Nace ka zauna Jin wa'azi yau ne?

Harararta yayi yace maida Ni yaro yarinya ko Abu na Sha ni bana mantuwa,Aamna ta kafe Tace Ni kashe min Dan Allah ai na ranar Juma'a nace kaji,Kuma ma ai Kai Bai kamaceka ba Sam,Mata biyu baza su maka ba,ai baza ka iya da su ba,Kai da ko lafiyar Romancing baka da ita dayar ma Taya zata Kare bare biyu,Uku,hudu,ai Kai Bai halatta ba ma kayi zancen mata biyu Ina Sam,Ahmad ya kalleta Kawai yayi Murmushi yace Zaki San kin fada min Maganar nan,sai kin maimaita wannan kalaman naki,Aamna Bata Gane ba Tace au Kai da gaske yarda kayi zaka Yi auren? to Malam ku ya rufe Yana Nan da matarsa daya,ku zauna ya zuga ku,au Ashe kema a addinin zaba kikeyi Kamar a super market abinda ranki ke so shi Zaki dauka Wanda Baki so baza ki dauka, Haka ake addinin?

Aamna a ranta Tace ya yarda wallahi da Wa'azin dama ance sabon musulunta akwai daukan Addini Gam,Aamna Tace kenan Mata biyun zaka Yi? Ahmad yace Ana fada Miki gaskiya kina takewa,Aamna ai sai ta birkice Tace to wallahi kaje kayi ka gani,Wayarsa ya dauka zai tafi haushi yasa ta jawo shi da karfi Tace Kai Malam ban Gane ba,ki dawo gida idan bakya so,au ta Nan ka bullo to bazan dawo ba,dama kayi Niyya zaka fake tanan,Kazo ka dameni da love love Ashe duk a Baki ne,wannan malamin shima Watarana sai an sauke shi daga limancin nasa ya daina samun Salary, Kallonta yayi duk ta tashi hankalinta kadan take jira ta tsage,Murmushi yayi yace ni nace zanyi Aure? Ke fa kika ce naji wa'azi nayi Aiki da shi Kuma Zaki zo kina damuwa,wayarsa ta fisge tare da goge recording din ta Mika Masa wayarsa,Dariya ta bashi yace Yana babban Memory na kwakwalwa tare da rungumeta tsam a jikinsa,kuncin da take ciki ne ya yaye taji wani farin ciki marar misaltuwa dalilin Kawai yayi Hugging nata.

Hannaye tasa tare da zagaye shi ta Rungume shi itama,gefen Fuskarsa yasa tare da gugan Tata gefen fuskar,Aamna ji tayi kamar ta fadi wani Abu na fisgarta ta sake makale shi,jikinsa ya raba da nata ganin Yana Neman yin bacci me Dadi,Kallonsa take Yi shima haka,kunyar kanta taji ta sadda Kai kasa,yace na tafi My world Good Night,Bata so hakan ba to Kawai ta iya Furtawa,Har ya juya zai tafi sai ya dawo tare da tsayawa a gabanta kamar zai shige jikinta,Yatsansa ya daura a Dan kasan Habarta tare da dago kanta sama,Yatsansa Yana Haka a Habarta ya shiga kissing dinta cikin wani Arnen salonsa,Aamna wani nishadi ta tsinci kanta ciki,a ranta ta furta Ashe ya Iya,jinsa takeyi har tsakiyar kwanyarta Tace Allah yasa Kar ya daina da wuri,Hannayenta ta mayar saman wuyansa tana shafa Masa wuya zuwa kitson calabarsa,Aamna martani ta shiga maida Masa cikin nutsuwa Kamar zasu cinye lips dinsu su huta sabo da yanda suke kissing din ba a cewa komai,a hankali ya zare bakinsa a nata Muryarsa na rawa yace Zan wuce dare yayi Su Baba.
Chapter 38 · 0% Book details