← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 89

Sashe 79

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aamna Kuwa da dare Ahmad ya tura driver ya dakko Masa matarsa,Suna Hanya Aamna tace Musa tsaya Amai nake ji, Musa da sauri yayi parking tare da mikawa Aamna bakar Leda har biyu yace Hajiya Yi anan sai ki jefa a kwalabati ai Aamna ko kula Ledar Bata Yi ba ta fita waje tare da tsugunawa ta Shiga sheka Amai Kamar zata fito da hanjinta,Musa ya Kira Ahmad yace Oga Muna dai dai sabon masallaci ka ganmu Hajiya ba lafiya gata tana ta Amai na tsorata fa Oga tun dazu take Amai yaki karewa,Ahmad gabansa ya Fadi yace me taci a gidan bikin? Karfa su kashe min Mata sauri ka kaita Hospital kafin na karaso,Sai da Musa ya jira Aamna ta gama tas ya Bata ruwan Roba ta wanke bakinta sannan ta shiga mota tana Nishi tace muje Musa naji sauki,Musa yace Oga Yana hospital yace na kaiki can,Aamna itama abinda takeji a jikinta kullum ya isheta Tace muje to.

Suna shiga Likita ta gani ta fada musu abinda take ji,Dake private ne Nan aka Mata wasu gwaje gwaje,tana jiran Result Ahmad ya shigo da sauri daga shi sai 3qtr da t-shirt fara,Zama yayi a inda take zaune ta jingina da bango tare da lumshe Ido,Ahmad yace Sannu My World,me kika ci a can? Aamna tace daga ganin Alala sai nayi sha'awa na ci Shikenan na fara Jin Amai,Ahmad yace Oh....me ya kaiki cin wani alalar biki kema,Ana zaune lafiya idan so kike Yi ai sai ki dafa da kanki.
Doctor ne ya karbi result din gwaji ya duba nan yace ranka ya dade na tayaka murna matarka ciki ne da ita na wata biyu, Ahmad murna tasa yayi mutuwar zaune ya wani Bude baki Yana murmushi,Takardar ya karba a wani slow ya duba,Aamna ya kalla da fara'a ya rike kafadunta tare da gýÿÿÿ‚
ƒ




ˆ

Š

Œ

Ž









˜

š

œ

ž
Ÿ

¡
¢
£
¤
¥
¦
§
¨
©
ª
«
¬
­
®
¯
°
±
²
³
´
µ

·
¸
¹
º
»
¼
½
¾
¿
À
Á
Â
Ã
Ä
Å
Æ
Ç
È
É
Ê
Ë
Ì
Í
Î
Ï
Ð
Ñ
Ò
Ó
Ô
Õ
Ö
×
Ø
Ù
Ú
Û
Ü
Ý
Þ
ß
à
á
â
ã
ä
å
æ
ç
è
é
ê
ë
ì
í
î
ï
ð
ñ
ò
ó
ô
õ
ö
÷
ø
ù
ú
û
ü
ý
þ
ÿ
irgiza ta sosai yace I make it my world,Haba Ni San Ina buga game din Nan dai dai ah ki tayani murna na samu first score,kallon Doctor yayi yace Likita mace ko namiji? tsaya karma kace min Namiji Baby girl ce ko? Zanyi Yar Budurwa kwana Nan,Ya kalli Aamna yace ki dinga Mata irin Calabar Nan tawa ta da kin tuna? Ai kullum da ita Zan dinga fita sai duniya tasan King yayi 'ya,Likita ya Bude Baki Yana kallon Murna Ahmad ya mike ya Hana Kansa sukuni gaba Daya, Doctor yace Dan Bamu waje Zan Mata wani gwaji,Ahmad yace ban Gane na baku waje ba? Ina mijinta wallahi baka Isa ba nasan latse latsen Nan da kukeyi zaka Mata ka Kira mace ta mata,sabo da ka Mai Dani gara ka kalli matata one in million na barta ka saki wannan shegen labilen naku ka latsa mata kafafu da ciki baka Isa ba bada Ni ba.

Likita yace Allah ya bada Hakuri ya Kira mace tazo ita tayi abinda ya dace ta basu shawarwari da Maganar zuwa awo etc.Aamna karar murna ta saki da sauri Kuma ta rufe bakinta tare da furta au na manta,Ahmad yace Adana ta sai munje gida,Hannunta ya rike Suka taho a hankali,Musa yace ya maida motar gida,tsohon me gadin Ahmad an Kara Masa matsayi ya tashi daga me Gadi ya koma Driver sabo da Amana irin ta Musa,tun kafin su koma gida Ahmad yace a shirya yau akwai party a gidan,Su Jibson duk Suka Zama ready Suka tafi da matayensu sashen Ahmad suna Jiran dawowarsu,Kafin ma Ahmad ya dawo Su Jibson an tanaji lemuka wannan karon babu Shan barasa,Tare da Aamna Suka shigo,tana rike a hannunsa,Ahmad ba jira yace a goal,Suma Kamar Yan siyasa Suka amsa da a goallllll......a goal....suka ce a goallllll......Yar China tace na Gane zancen,Ahmad yace na Zama Daddy matata tana da ciki na 2mnths tafi suka fara raf raf raf.....Jibson yace music .. Bash ne DJ ya danna,Su dai matan Dariya suke ta Yi,Yar China harda cewa a kashe kida sai na fara rera Mata wakar Dana tanaja,aka tsaya Nafeesat tace Muna jinki,Yar China ta fara Waka wai me ciki turtsi bulli.....me ciki turtsi bulli,Tawaga yace a amshe mata Yana Tafi suka ce Suma Me ciki turtsi bulliiii me ciki turtsi bulliiii....Tace ta kasa Zama,Tawaga yace turtsi bulli harda tafi sauran har Ahmad Dariya Kawai suke yi,Yar China taci gaba da cewa tsaiwa ta gagara....Turtsi bulli....Tawaga ya sake Amsawa,Aamna tace wannan ai wulakanci ne wallahi Zan rama, Ahmad ta kalla wannan tijarar daka min fa,Cikin murna Bash ya Danna kida Aamna sabo da kunya guduwa tayi ta kasa Zama sun Dade suna shagali suna ta tsare tsare.

Ahmad harda cewa a Ina za a Kama ayi suna? Humaira tace Kai Yaya ko kunya,Hararta yayi tayi Shuru tana dariya,Hafsat Tace ba Wani suna an daina yanzu,Inji uban wa? Cewar Tawaga zamu samu karuwa baza muyi murna ba sai mun kashe kudi,Nafeesat tace Ni dai nice me kula da me jego,Yar China Tace Muna wajen Bikin suna mu Allah ya sauketa lafiya,Ahmad yace Halina Dake hankali Yar China,ba Wanda yayi Addua sai ke,party fa kace za ayi cewar Mashkoor,to naji an Gama kuje Kun korar min ita sabo da kunyarku,Jibson ne ya fara mikewa ya rike Sameeransa zai tafi Ahmad yace gobe karku manta akwai zuwa Office,Allah ya kaimu suka tafi Yar China kin tashi tayi tace Allah bazan koma da kafata ba sai dai ka goyani,Abu me sauki cewar Tawaga ya goyata Kuwa Suka tafi Yar China akwai son wasa Kamar me.

Washe gari Ahmad waya ya Kira Mummy ya sanar Mata ta dinga Murna tana bawa Daddy labari,su Saddeeq da Mufeedansa sai murna sukeyi,Basu Dade ba Kuma ya dauki Aamna Suka tafi Lagos,can ta Sha kallon kudi satinsu Daya Suka dawo,lokacin Kuma Ahmad yana Shirin tafiya da Aamna da Baba Sudan suje gano Rahilu,Baba ya rike wuta sai anje da shi,Kuma ya kamata aje da Baba sabo da shi ya rike Aamna,Baba ranar da Ahmad yaje ya sanar Masa ya Zama cikin shiri bayan an Masa passport,Baba yace Nima ka siyo min Sut (suit) irin ta Rahilu da ita zanje Masa Nima,Ahmad ba musu ya nemowa Baba size dinsa kala Uku,yace da jallabiya shima sai ya saje da Rahilu a Sudan.

Ranar da zasu tafi Aamna harda Shan abaya baka,Ahmad shi dai kana Nan Kaya yasa Yan ubansu,Baba kuwa harda sa jallabiya fara yayi Nadi da rawanin larabawa,Baba yace nasan mutanen Sudan ma tun a jirgi zasu fara Yi min larabci su Aamna suna ta dariya Mashkoor ya ajiyesu a airport Basu Dade ba jirginsu ya daga,Baba yace wayyo kunne na ya toshe wani dummm nake ji ice ko kamfanin mu na Najeria be? Basu iya jirgi me kyau ba,Ana ta yiwa Baba Dariya,duk ma'aikaciyar data wuce sai Baba yace baiwar Allah abincin jirgi ko baza a Bamu bane sai dai suyi ta kwantarwa da Baba hankali suce za a bayar idan lokaci ya cika,Wata Yar Budurwa ta fito cakwas cakwas itama ma'aikaciyar jirgi ce ta dafa kujerar Baba tare da cewa Baba a sa Belt,Baba yace yau Naga fitsara da gani ba'a kulla abin arziki ba ace ma'aikatan jirgi gaba Daya Yan Mata fella fella suke yawo suna kashe ma Ido sabo da a koya min fasikanci idan gaskiya ne a zuba maza Mana su dinga dakawa pasinja tsawa wallahi Baku da halin arziki kunyi asara an maida ku hotiho Ana talla daku a sararin samaniya,sai kunyi sama sosai sannan kuke tafka tsiya wallahi da Allah kuke bada mu ba,sai Dariya akeyi a jirgi Baba Yana ta masifa har aka kawo abincin jirgi.

Baba yace aikin banza shinkafa ce da nama Baba ya cinye nasa ya dauke na Aamna ya cinye,Ahmad ma ya bashi nasa ya cinye Baba yace abinci Kamar na Yaron Yaye Haka dama jiragan suke wannan rowar mutum ya biya kudi a bashi abinci naira Hamsim a dubu goma.
Baba Yana ta murna ya fita kasar waje zaiga Sudan yankin Larabawa,sai da suka sauka a jirgi Suka Shiga lafiyayyar Taxi Suka shigo har wata state,Baba yace me Zan gani? Sahara nake gani fa Ahmad,me Zan gani Haka? Yo wannan ai gwara naje Kano Kuma Sudan din ne? Aamna tana ta da dariya,Baba yace cab Dole Rahilu ya Shiga Uku a Haka amma Yaran wasu masu kudin suke Mana Iyayi Ana wallahi Yana can Sudan Yana karatu,tana Sudan tana karatu,ai wlh gwara Kayi Ado bayero iniversity (University) Ahmad Yana so ya dan rike ko Aamna amma yasan Baba.
Chapter 79 · 0% Book details