Sashe 42
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna zaune wata tazo siyan Citta Aamna tana ta tunanin Ahmad sai ta zuba Mata barkono,sai da ta karba Tace citta fa nace,Aamna Tace au na manta sai ta juye ta zuba mata kanunfari,Matar Tace Citta fa tunanin me kikeyi Haka ne,Sai Zuhra ce tazo ta karba ta zuba Mata,wani yazo ya siyo Wani Boxers sai Aamna ta karbi kudin dari biyar ne Kuma dari biyar din ya Bata Amma sai ta irgo dari takwas ta bashi tace ga canjinka lokacin Zuhra ta tafi shi kuwa mutumin ya sani Amma ya karbe abinsa yayi gaba.
Kusan kwana Uku Aamna duk ribar Mama ta tafi Aamna tana ta yin aringizon kudi.
Yau ma da safe zata hada tea a kitchen sai ta dakko gishiri ta saka a madadin sugar sai da ta kurba ta feso da shayin waje sai taga gashiri ne,gaba Daya Bata cikin hayyacinta.
Ahmad Kam abokansa suna zuwa suna ebe Masa kewa,Jibson ne ya shigo ya same su tun kafin ya zauna yace ku fara Yi min jaje, Mashkoor yace na me? yace ku tausaya min suka ce Mene? Jibson yace Jiya kafin na kwanta bacci 9:30pm, Allah yaji Kan Sameera me Hannun kwano badan ta mutu ba sai Kawai na dinga ganin fatalwarta a kaina,tsorata nayi na Kira Wayarta a daren tunanina ta rasu ne an binneta tayi min fatalwa.
Sai kuwa ta daga tace ita kalau take Nan na gano mayya ce zata kamani nayi Mata fata fata nace Kar ta sake na sake ganinta a Ido na,Dariya suka dinga Yi,Jibson yace Kasurgumar mayya ce ban sani ba,na Kai kaina babu dama na Dan kebe Ni kadai sai ta dinga min fatalwa, Jibson yace yanzu ma Haka Ina ganinta a idona,Bash yace ko dai so ne? Jibson yace Bazawarar Allah kiyaye,Idonsa ya Shiga murzawa yace gata tazo... tazo bazan lamunci wannan ba idan na gaji Kara Zan shigar kotu Mayya ta kamani,Tawaga yace Wai da gaske kake?yace ae Mana, Mashkoor yace kirata a waya muji,Jibson ya dakko waya tare da Kiran Sameera,bugu Daya ta daga.
Yace ke Kwano Mene Haka bana son wasan da kike min,gaskiya na daina ganinki Maganar gaskiya Ina daga Miki kafa Zan kaiki Kara akan me Zan dinga ganinki,ko bacci nayi sai kizo min Mene Haka Dan Allah Ni bana so Gaskiya,Dariya Sameera tayi ya dameta da zargi Wai ita mayya ce Bayan ita Bata San komai ba,tsokanarsa tayi Tace Yau Danwake kaci ko? Tsoro ya Kama Jibson sabo da Tabbas yau Danwake kannensa suka Yi a gidan Kuma sai da yaci ya fito,da sauri ya kashe wayarsa su Tawaga Suka dinga dariya Jibson yace ba abin Dariya bane wannan wallahi Danwake naci na fito idan ba mayya ba Taya tasan naci Danwake? Gaskiya a Nemo min maganin mayu wallahi,Bari Brown yazo Dan Uwarsa ya sa munje wajen Mayya,Suna ta dariya Bash yace Ashe duk wankan da muke dauka a banza tana kallon Hanjin mu me muka ci,Jibson da sauri yace Kuma ranar tuwo naci kaga zata kalle Ni a banza Ina cin tuwo,da ace nasan Haka ne ai Kwai da nama zamu ci idan munje ta ganmu Yan gayu,yanzu ta ganmu cikinmu duk tuwo,Bash yace kyaleta anjima zamu je kaza zamu siyo muci muje Suka ce Haka za ayi su Ahmad suna jinsu suna ta dariya,Amma Ahmad duk da Haka hankalinsa Yana wani wajen.
Da Yamma su Jibson kazar kuwa Suka siyo Suka ci harda Shan Yogourt,Bash yace Bari na Kara da Biscuits sabo da ta ganmu muma ba baya bane,Jibson yace Apple zanci Ni Haka Suka dinga Ciye ciye su Tawaga suna ta dariya,yau da Sameera ta shigar da su Palon Baki kallonsu tayi Tace Bari na kawo muku lemo ko da yake nasan kunyi ciye ciye da yawa,Bash da sauri ya kalli Jibson,Jibson tsoro ya kamashi yace Wai ke Kwano Taki da ita aka haife ki ko kuwa siyanta kika Yi? Sameera ta Gama Gane shi Amma sai Tace me fa? Kasa fada yayi Dan kar ya ci Mata Fuska sai yayi Shuru kawai,Sameera ta fita a ranta tana ta dariya Bash ne yace ai ance ta bangaren Uwa tafi karfi Wala Allah ita a nono ta Sha,Abban Brown ne yazo zance yau ma yaga su Jibson Ashe Basu daina zuwa ba,Takaici yasa ya shiga palon shima ya nemi wuri ya zauna sabo da shima Abban Dan rigima ne baya tsoron abin kunya gashi ya makance Akan son Sameera,Su Jibson Suma suka ki tashi mirsisi sukayi,Abban Yana ta harararsu Suka share abinsu,Sameera ta fito tare da ajiyewa su Jibson lemo ta zauna tare da maida hankalinta wajen su Jibson,Abba ko Kallonsa Bata Yi ba,kwafa ya ja ya Mike ya fice Kamar zaiyi duka.
Su kuwa sai magrib sannan Suka tafi.
Bayan Kwana biyu duka abokan Ahmad na kusa Mashkoor, Jibson,Bash,Tawaga da Brown wajen Ahmad Suka zo,Brown yace Ahmad ka shirya muje daurin auren Cousin Dina a Kano gobe,Ahmad yace a halin da nake ciki bazan iya binku ba ga motar Nan ku dauka kuje da ita koma Ina ne ai komai Nawa naku ne,Suka ce to ba damuwa,washe gari da Sassafe Suka shirya tare da tafiya Kano,Ahmad da Rana Yana kwance Yana ta tunani iri iri akan abinda Aamna ta Masa sai ga kiran Wayar Mashkoor sabo da shine Kawai Suka Yi waya yanzu yanzu,Yana dagawa akace masu wannan motar sunyi hatsari ayi sauri azo Kan gawarsu gaba Daya sun mutu na Daya motar ne babu Wanda ya mutu suna asibiti,Zumbur Ahmad ya mike tuni ya rasa inda zai sa Kansa,yanzu abokan nasa ne suka Suka mutu? Kayan dakinsa ya shiga watsi dasu.
Kuka Kawai ya fara ya rude Kawai Iyayensu ya Kira ya sanarwa kowa hankalinsa ya tashi ko wanne danginsa Suka tafi can inda akace anyi hatsarin,Shi kuwa Ahmad a rude ya Kira Mummy ya fada mata,Yana kashe wayarsa ya fita shima ya bazama,tare da Baban Jibson Suka tafi can hanyar Kano,Suna zuwa Suka hango Yan Sanda da mutane da yawa a wajen Ana ta zaro gawarwaki,motar Ahmad gaba Daya tayi fata fata,da gani yawan gawarwakin Ahmad ya Fadi ya sume yin duniya Bai farfado ba,da shi aka hada aka tafi Asibitin da Wanda Basu mutu ba,Daya motar ita bata wani lalace sosai ba da gani kasan a motar Ahmad sune Wanda Suka mutu Kawai.
Duka Emergency aka wuce da su,Mummy ce ta Kira Aamna tare da sanar Mata Tace kiyi sauri idan sun dawo ki je wajen Ahmad kar ki Bari ya koma shaye shaye,Ahmad Yana son abokansa wannan abin zai taba shi,kece kadai Zaki iya kwantar Masa da hankali,Aamna tana kuka Tace to Mummy.
Ahmad da kuka ya farka Yana Kiran sunayen abokansa Muryar Mashkoor yaji yace Kai dalla mace ne ka ganmu Bamu mutu ba wallahi raunuka Muka ji na Daya motar ne Suka mutu,Zumbur Ahmad ya mike Yana bin dakin Emergency da kallo yaga dukkan abokansa suna numfashi Brown dake Jan motar ya Dan fisu Shan wahala,Farin ciki ya Kama Ahmad yace ya akayi Baku mutu ba yanda motar Nan ta dagargaje Haka? Mashkoor yace ikon Allah wallahi,ai Watarana mutuwa ba a Nan take ba sai kaga motar da Bata wani ki jiki ba an mutu wacce tayi raga raga Kuma ba a mutu ba,Jibson yaji wuya duk jikinsu raunuka yace na daina shaye shaye daga yau na jiyo kamshin mutuwa,Tawaga cikin wahala yace yan kannena marayu da tuni an musu sakiyar da ba ruwa,Ba Baba ba Ni sun Shiga Uku wayyo Allah na tuba,Ahmad yace Ni yau wacce irin godiya Zan yiwa Allah,Bash yace kaje kayi ta Sallah,Iyayen su Jibson kowa kuka ya Kare sai murna da godiya ga Allah,Ahmad ya fadawa Mummy Basu mutu ba,Itama Mummy cike da murna ta sanarwa Aamna Tace Idan an dawo dasu asibitin Kaduna taje can lallai ta kula da Ahmad.
Haka kuwa Ahmad shi ya biya kudin Hospital,har Wanda Suka mutu ya Bawa Iyayensu tallafi,Transfer aka musu zuwa Kaduna private hospital Ahmad ya dau nauyin komai Dukkansu ba Wani rauni me wahalar warkewa Suka ji ba,Sameera a guje tazo Asibitin tana ta kuka a gefen bed din Jibson ita dai tana son Jibson a rayuwa,Jibson kallonta yayi kadan yanda ta tashi hankalinta a hankali ya daura hannnunsa saman nata Hannun dake saman cikinsa,Idonta da Hawaye tace ya jikin? Murmushi yayi yace da sauki Me Hannun kwano yau cuta tasa bani da kitse,namana ba maiko zaiyi ba yanzu ki tausaya karki lashi kadan,Dariya Sameera ta dinga yi,Ahmad Yana kallonsu yayi Dariya tare da zuwa gefen Jibson ya zauna yace Malam me zaka iya ci? Kannen Jibson ne Suka shigo da Abinci iri iri,Ahmad suka gaisar tare da Sameera duk da Basu San wace ba.
Jibson yace kaima kasan bazan wuce farfesun hanta ba Malam,Maye Ahmad ya Furta suna Dariya yace Sameera ki taimaka a bashi,Sameera ta zuba a plate Ahmad ya tallafa Jibson ya jingina da jikin pillow,Kanwarsa Fa'iza Tace wannan Surukar mu ce ne?Ahmad yace ae Kawai,sai murna sukeyi suna kallon Sameera,Sameera harda kunya,Jibson yace me Hannun Kwano a bani Mana yunwa,Sameera kuwa Fa'iza ta mikawa Wai ta bashi ya ci,Fa'iza Tace ai mu fita zamuyi ma kiyi aikinki suka fice tare da komawa Room din Mashkoor.