← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki taja tace waye wannan da wannan daren? Kin dagawa tayi har ta katse, Mashkoor ya kalli Ahmad yace King Bata daga ba a kyaleta tayi bacci,da masifa yace ka Kara kiranta Mana,to tana bukatar tayi bacci fa cewar Mashkoor,Bata bacci da wuri na sani ka sake Kira Wai me yasa kake min Haka Zan sa ma poison a lemo ka Sha ka mutu ka kirata again, Mashkoor yace Nifa baza ka Jani cikin haukarka ba,Kawai ka shigar Ni ciki mun haukace yau gaba Daya bansha ko kwalaba Daya ba mun Kare akan kwaila,wata Harara Ahmad ya aika Masa Nan take Mashkoor ya sake Kiranta lokacin wata Budurwa Yar Uwar Aamna Minal ta kwanta a gefen Aamna Tace Wai waye yake ta Kira ne Haka? Aamna Tace ban sani ba,Bari na daga naji cewar minal ta dauki Wayar tare da dagawa, Mashkoor yace an daga....an daga...Ahmad yace ehem Yi magana Mana.

Mashkoor yace hello Aunty Balaraba Mashkoor ne? Minal tace ba ita bace Yar uwarta ce Minal ce,Aamna tana ji ance Mashkoor ta Mike zaune,Mashkoor yace ehem Dan Allah Bata kusa me Wayar? Minal Tace gata ma Bari na Bata, Wayar Aamna ta karba,Lokacin Ahmad ya gyara Zama tare da furta ehem a hankali, Mashkoor yace Aunty Balaraba Barka da dare,yawwa Mashkoor ya gida? Lfy Alhmdllh,dama...dama...Ni da King munje gidanku ance bakya Nan kinyi tafiya,Aamna Tace Yana Ina King din,Tsoro ya Kama Ahmad shi Taya zai iya magana me zai ce Mata, Mashkoor yace Bari na Baki shi ya mikowa Ahmad Wayar.

Yana karba sai da yayi minti Daya Aamna tana ta faman hello hello sannan yace hello cikin Muryarsa da ya saita me Dadi ta nutsuwa....uhm...ahm...ahhh....munje gidanku dazu ance bakya Nan? Aamna Tace eyya sorry Friend Ina ta so na fada maka Bamu hadu ba Amma jibi Zan dawo Inshaallah,Ahmad yace okay...Allah ya kaimu, Mashkoor da rada yake cewa matarka ce fa ka daina wannan abin taya zaka barta tana tafiya inda taga dama Haka? Ahmad Bai kulashi ba yace Friend sai da safe Bai San me zai ce ba,Tace okay bye ta kashe Wayarta,Ahmad yace Nifa ba Maganar Mata nake maka ba ya za ayi Naga na birgeta shine magana Kawai,Dariya Mashkoor ya dinga yi yanda Ahmad duk yake ta murna akan yaji muryar Aamna,yace to yanzu Zan iya bacci,Mashkoor yace ka haukace Nima ka sani na Zama mahaukaci,Bari naje nayi bacci,Ahmad yace ungo wannan banzar akwakwar Wayar taka tunda nadauki number dinta,Ae ai dole ka zagi Wayar tunda ta Gama biya maka bukatarka.

Washe gari da sassafe Ahmad ya farka ya dawo Palo inda Mashkoor yake bacci ya dinga dukan Mashkoor a gadon baya,da kyar Mashkoor ya farka Yana masifa Wai Dan Allah mene Haka jiya ka hanani nayi bacci yanzu ma Haka Mene ne? Baka tashi da wuri mene yanzu abin tashi again,Ahmad yace Yarinyar Nan nake so ka kirata ku gaisa sai ka sa min Wayar a Handsfree naji muryarta,Tsaki Mashkoor Yaja da muryar Yan kwaya yace wai a'ahhh....wannan wanne bala'i ne Haka? Okay kace min kawarka ce Kai ba sonta kakeyi ba wa yace maka Ana Kiran kawa Haka a waya,so kake Yarinyar Nan ta tsaneka sabo da yawan takura Haba su Mata basa son takura,kana nutsuwa fa King,Shuru Ahmad yayi yace okay Bari to bazan kirata ba sai ta neme ni Zan daure,Ehemmmm...Abeg jeka kitchen ka Mana girki King kasan ka iya girki cewar Mashkoor.

Ba karamin dauriya Ahmad yayi ba yaki Neman Aamna a waya,Aamna taga Shuru Bai nemeta ba ranar da ta dawo Kaduna yau Ahmad Yana kitchen shi da Mashkoor suna magana Yana girki sai ga Kiran Aamna ya shigo wayarsa,Wata nutsuwa Ahmad yayi tare da cewa yeee...ta Kira ni...daga Wayar yayi yace Hello.....Kawata,Aamna Dariya takeyi Wai Dan rainin hankali ma ba matarsa bace kawarsa ce ma,a Wayar Tace dama fada maka zanyi na dawo dazu,Wata Uwar Zabura Ahmad yayi sai da Mashkoor ya firgita,Ahmad yace Kin dawo lafiya Kamar Yana gabanta har wani zufa yake Yi,Tace lfy Alhmdllh,yace Zan zo gobe,okay Aamna ta furta ta so ace yanzu zai zo Amma Wai wani gobe, Wayar ya kashe ya saki Dan Ihu yace she done come back Yana dukan kafadar Mashkoor, Mashkoor kallon mamaki yake Masa Kawai ganin king dinsu ya haukace.

Wanka sukayi Mashkoor ya dauke shi Suka tafi Shopping Wai Ahmad shaddoji zai siyo da yadika masu tsada za Masa dinki sabo da ya birge Aamna.
Ko da Suka shiga inda ake siyar da shaddoji da yadikan maza Ahmad ya kalli me kayan ya zaro Masa Ido yace Guy Kalar birgewa muke bukata masu tsada,Me Shadda yace gasu Nan ku zaba,Ahmad ya dinga zaba Mashkoor ya koma gefe Yana ta kallon ikon Allah har ya Gama sannan Suka wuce wurin tela,Ahmad yace Kai tela fa Wanda yasan me yakeyi yawwa idan kasan tela bana kirki bane karka kaini, Mashkoor Yana ta Dariya yace Wai Ni Kam ko Lilamin Masallaci za'a nada ka ne? Ko kula Mashkoor Ahmad baiyi ba,wani Shagon dinki Suka shiga,Ahmad yace Bari na gwada basirarsa Kai tela nawa zaka min Dinki na karshen tsada? Tela yace dubu bakwai, dubu biyar dubu goma sama da Haka,Ahmad yace wannan dinkin da gani bana arziki bane baka iya komai ba baka San me kakeyi ba Malam ja can dalla, mu bar Nan, Mashkoor ya sake daukansa Suka tafi Wani wajen na masu tsadar dinki Amma da kyau,Ahmad Yana ji an zuga Masa tsada yace yes.. .yanzu nasan Kai telan kirki ne Nan ya bashi kayan,yace auna Ni ko Ina dai dai Ni, wallahi ka min hauka sai na sa an kone shagon dinkinka da kayan ciki sabo da Haka don't Mess up,tela yace zaka ga Aiki ai bana Wasa,sai da suka Gama komai Suka je ya siyo takalma Designers da agoguna etc.

Sai dare Suka Gama sannan Mashkoor yace Zan tafi gida,da masifa Ahmad yace akan me ai wallahi ba inda zaka je Sai an Gama tsare tsare da Kai, Mashkoor yace Nifa na gaji Haba ka rike Ni na kwana na yini Yar giyar ma ban Sha ba tun jiya Ni bazan iya ba, baza ka saka Ni a wannan haukar ba,Fuska Ahmad ya Bata tare da furta Kai meke damunka ina magana kana magana are you mad?

Shuru Mashkoor yayi yace to kayi Hakuri na zauna Amma a kawo min ruwa da kayan aiki,Nan Ahmad ya koma bedroom dinsa ya kwaso kayan shaye shaye ya ajiye musu Suka dinga Kora abinsu,Ahmad Yana murmushi yace yawwa na tuno nasan dole tana yin Facebook babu Wanda baya Facebook a duniya,Nan take ya fara latsa wayarsa Yana duba Facebook Yana Searching sai dai Bai San sunan Baban Aamna ba,Amma sai ya gwada Aamna Hussain,Nan take sunan Aamna ya bayyana da hotonta,Yana murmushi yace Yes....see fine Beb,see Beb....naaa..wow...see her lips...oh.....My God...a'a...kaga kyau Haka,...fuskar Wayar ya shiga nunawa da yatsa Yana shafa gemunsa Yana murmushi yace abinda kike min baya dacewa,bakya kyauta min Sam,ki daina...ki daina Tam.....Mashkoor ya saki Baki Yana kallon ikon Allah, Pictures dinta ya shiga dubawa kala kala can ya hango Aamna da wani saurayinta a pic Wato Affan,Glass din wayarsa ya shiga Rankwashi da karfi a saitin Affan Yana ka...ga...shege...Dan... Iska,me yasa zaka tsaya kusa da ita....mugu....Tsaki Yaja ya fita daga Facebook din gaba daya Yana Fushi yace Taya zai tsaya a kusa da ita aikin banza,Cikin Maye Mashkoor yace Wai...Wai...ba kace kawarka bace?Yeah Ahmad ya furta,yace to Mene na damuwa Haka? Maganar gaskiya King ka fa haukace.

Ahmad Yana Zaune yayi Shuru Mashkoor yace ya akayi ne? Yarinyar Nan nake so na gani yau da Daren Nan Amma bana son ta ganni kuma bana so ta San na ganta Kawai na ganta a boye ba tare da ta ganni ba,kaga yanzu 10pm muje ka kaini sai na tsallaka gidan, yau ko bacci takeyi har dakinta sai na ganta,Mashkoor tsoron Ahmad ya shige shi Kamar zaiyi kuka yace Wai Mene yake damunka kafa haukace King,Kaga Idan zaka kaini Malam ka kaini Zan zuba ma guba a abinci ka mutu Tam, Mashkoor yayi Dariya irin ta yan kwaya yace muje,a daren Suka hau machine suka tafi,a nesa da gidan Mashkoor ya sauke Ahmad,Ahmad yace karka tafi Ina ganinta Zan fito mu wuce,ta Kofar gidan Ahmad yabi ganin a bude Basu rufe ba,kamar barawo Haka yake Sanda yace bana so ta San Zan kalle ta,da sauri yabi ta bayan gidan wajen Flowers,Baba ne ya fito Yana masifa Dan Iskanci sai a bar gida a bude tun yaushe nacewa shedaniyar Yarinyar Nan ta rufe gidan Nan Amma dake Aamna ba Yar Albarka bace ta bar gidan Abude,Ahmad Yana ji Baba ya zagi Aamna sai ya kasa jurewa Yana bayan ginin gidan yace karya ne kaina Mara Albarka.....tsorata Baba yayi ya rasa a Ina yaji an ramawa Aamna ya shiga waige waige ko zai ga mutum baiga kowa ba,Tsoro ya kamashi ko aljanun Aamna ne suke tare Mata fada,da sauri ya rufe gidan ya kulle ko Ina ya koma ciki da saurin gaske.

Ahmad ta Kofar kitchen yabi Dake kitchen akwai kofa ta waje ta ciki sai yabi ta Nan ya shiga Palo Yana shiga Baba ya shigo da sauri ya fada bayan kujera ya buya,Baba Yana masifa ya kulle Palo ma ya sa key, yace aikin banza kitchen dinma a Bude aka barshi Bari na rufe,kafin ya karaso Ahmad da rarrafe ya koma Bayan Daya kujerar,Baba ya kulle kitchen Yana cewa beraye sun fara addabata a Palo naji Kamar sun shiga cikin kujeru Bari gobe da wuri Zan samo mage tayi maganinsu.
Chapter 28 · 0% Book details