← Book details Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 89

Sashe 24

Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Aamna gajiya tayi ta fito lokacin zai fita tace Yau zaka nemeni ka rasa a gidanka yau Zan tafi gidan ubana,wani farin ciki ya Kama Ahmad yace Dan Allah da gaske kikeyi? Aamna Tace da gaske yau a gidan ubana Zan kwana,wani murmushi ya saki yace gaskiya ban taba sanin kina da kirki ba sai yau,Sabo da Haka yau dole Nima na gwangwaje ki,fada min me kike so? Aamna ta turo Baki ta samu waje,yace ai yau ko me kike so Zan miki,Aamna ta Kama shagwaba Tace koma mene ka bani kyautar Ina so,Ido ya zaro Mata wasu farare tas sai da ta tsorata Yace Gaskiya Zan fada Miki ke Yar Albarka ce babarki ta iya haihuwar Yar halak Haka nake so,yanda kika faranta min yau ace ban Miki kyauta ba nayi asara bani da amfani Kawai na mutu yanzu,Dariya ta Kama Aamna duk akan Tace zata bar Masa gida shine yake wannan murna Haka,wannan kiyayya wacce iri ce,Tunaninta ya katse Mata yace shirya kizo mu tafi na kaiki Shopping ki zabi abinda kike so na ban kwana,Dan Allah Kuma idan kin tafi karki dawo har abada kinji,Aamna Tace to,yace ko Mummy Tace kice a'a ke ba 'yarta bace ta juya Humaira Yarta data haifa Amma ba ke ba,Aamna Tace to,yace Ina jiranki,Da gudu taje sama ta canja wata Arabian gown Dark green me adon black ta Sha kyau ta fito.

Machine dinsa ya gyara ta hau ya fisgeta Suka tafi sai wani katafaren Mall,tare suka shiga yace Ina jiranki zabi duk abinda ya miki,Aamna Bata zabi komai ba ta wuce Bangaren Gold ta zabi wata sarka me kyau da zobenta da Dankunne,yace shike Nan abinda kike so? Tace ae,Kai ya girgiza yace to dauka,Haka ta dauka yaje ya biya kudin Suka tafi,ya maidata gida zai fita Tace to saka min da Hannunka kaga anjima Zan tafi,yace ai yau ba abinda Zaki ce banyi ba tunda Zaki bar rayuwata na huta kawo,Mika Masa tayi ya saka Mata sarkar da kansa da dankunnen,Yatsanta ta Mika Masa ya sa Mata zoben,yace Nice one, karfe Nawa Zaki tafi? Aamna Tace 6pm yace Good,ya Mike zai fita Yana ta murna yau zai rabu da Kaya ya huta,Aamna Tace Idan ka dawo sai na tafi,yace to ai da wuri kuwa Zan dawo ya fita Yana ta murna Kamar an Masa albishir da Aljanna,Tun kafin 6pm ya dawo gidan ya shigo Yana wakar Bob merly Yana Bappalo Soldier........Ye...yiye....yiye.....Yee...Yee....yiye...

Sharhi fans Dan Allah.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM - A Maryam: Ī)\Ī)\DUNIYA TA AAMNAĪ)\Ī)\

41-45

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

ZEE NANDU
KALTUMA ZANNA
SADEEY(QUEEN)
TEEMA'S COLLECTION

.Aamna daga kitchen ta fito tana amsa Masa wakar tasa tana girgiza Kai ta kwala da karfi Ohhhhh.....yeyi..yiye...your.....bappalo soldier....tsit Ahmad yayi murna ta koma ciki da Alama Bata da Niyyar tafiya,Girar sama data kasa ya hade kamar an Aiko Masa da Mummy ta rasu,Aamna kuwa Bayan ya fita zuciyarta ce tayi sanyi ta huce,kafin ya dawo Allah ya yayyafawa zuciyarta sanyi da Hakuri sai ta fasa,Siyama kuwa tunda ta tafi tana sa ran Aamna zata bar gida take ta murna tana uban Kiran Aamna akan taji ko ta bar gidan Amma karshe ma Sai Aamna data Kira Aamna tana dagawa sai taji tana dariya Tace ke Siyama na fasa tafiya na huce,na tuna ma fa Dan kwaya ne ba a ba'a hankalinsa yake ba nayi Masa Uzuru,ko ba komai ma ai Ibada nakeyi,aure Ibada ne zanci gaba da Masa Addua Allah ya shirye shi,Siyama ta danno Mata ashariya Tace wannan bazai taba shiryuwa ba,Ibadar me aure ne kadai Ibada a duniya,Aamna Tace Sanda Zaki auri Faisal ai masifa kika Kama Yi min akan nace kinyi gaggawa yanzu Kuma Ni da gidan mijina Zaki shigo kina min katsaladan a gidan aure na,kin fa Sanni Siyama ki daina uzura min Ina ta Miki Kara bakya gani,Ya kashe Ni ma Mana Ina ruwanki,Siyama Tace Iyyeee....Mrs Ahmad shike Nan kije ki zauna a wahalar,Tsaki Aamna tayi tare da kashe wayarta.

Yana Zaune sai kunci yake faman yi,Aamna ta kamo Sunna tv taci sa'a kuwa an saka Wa'azin Malam Ahmad Tijjani,Yana magana akan hatsarin shaye shaye,Yace yanzu Duniya Malam ta lalace da shaye shaye,maza,Mata,Yara,manya,Dattijai,abin haushi ma Yara kanana matasa sun Gama kashe kansu da shaye shayen kayan Maye,abin Allah wadai matashi lafiyayye ya jefa Kansa a halaka,ya Zama marar amfani a rayuwar Musulmai,Musulunci bazai Yi alfahari da su ba,Shan Alkhabis,baza a Sha Aldayyib ba,Mene Alkhabis? Alkhabis shine abinda idan anci ko an Sha bashi da dandano me Dadi a Baki sannan a jiki Yana cutarwa,Aldayyib shine a Baki da Dadi a jiki Kuma Yana da amfani me kyau.

Ko matasa jira kuke sai an lissafa muku a Alqurni ance Giya,taba,Wiwi,har Ana kawo ayar Allah Kuna cewa babu Aya,Ina Iyaye wallahi ku farka,Matasa maza da Mata Kuna da hankali,shaye shaye na kwaya,na hayaki na ruwan barasa da sauransu bashi da amfani ga rayuwarku sai cutarwa,Kun Zama marasa amfani a cikin Musulunci,shaye shaye shi kadai yana barna ba adadi a wajenka matashi,na farko shine Kai da lafiya kunyi bankwana,zai kassara maka lafiyar kayan ciki da dama,sannan babbar Illa zai rabaka da Allah,zai rabaka da addinin Allah,zai hanaka Sallah ko kayi ma kana cikin maye baza a karba ba,Azumi ma Sai ya hanaka domin zaka dauka ka kasa kaiwa sabo da dole sai ka Sha kayan Maye zaka zauna lafiya ya Gama bin jininka,sannan zaka sabawa Iyayenka babbar matsala sabo da dole sai ka kangare,ka bijire musu zaka cutar da su.

Kasan kuwa wa ake cewa iyaye,ya ku matasa wallahi wallahi ku guji fushin iyaye,masifa ne Mahaifiyar ko Mahaifi su zubar da Hawaye a kanka,basai sun maka Addua ba Kai da ganin dai dai a rayuwarka sai in ka tuba sun yafe maka,wani abin haushin ma Iyalinsa zai dinga zalintar matarsa da yaransa,ya mazaje ku San hakkin matanku mataye Kuma wallahi wallahi kuji tsoron Allah duniyar Nawa take,bakwa ganin halin da ake ciki mafi yawan alamomin tashin kiyama sun bayyana,nuni ake mana mu Kara gyara Hali lokaci Yana matsowa,wallahi a Haka Ana da saura da saura Ana ganin kamar da saura a Haka za a wayi gari aga manyan alamomin tashin Alkiyama sun fara Bayyana.....

Ahmad Yana ji ko a gefen rigarsa sabo da yaji Wa'azin Daya fi wannan zafi ma, Canja Chanel yayi yace idan Kinga dama ki gayyato malaman Nigeria kaf su zagayeni ki gani idan zanji na gyara,Aamna Tace ikon Allah a ranta Tace lallai wannan bazai canja ba gwara na nemi mafita,Giyarsa ma taga ya dakko ya Balle Yana korawa, Tsoronsa ya sake shigarta,jiki a sanyaye ta koma dakinta,a palon ya dinga zage zage tana ji,Haka tayi kwana Uku lokacin tuni taje ancire Mata plasta da aka manne Mata ido,sai ganin Idonta yayi tar da Alama ba abinda ya sameshi,Kallo daya ya Mata yace makaryaciyar banza,Shuru tayi sabo da ta gaji da kulashi Yana dukanta,da Yamma kwayarsa ta motsa Aamna taga yanayinsa ba mutunci,taja mutuncinta tana zaune a Palo Siyama ta kwada Sallama,tana shigowa Ahmad ya daka Mata Tsawa yace koma inda kika fito,da sauri ta juya ta fita,Ya zaka koreta?Aamna ta tambaya yace ke wallahi idan Baki daina min magana ba Zan sa wuka na Miki yankan rago,Aamna Jin irin kashen kashen rayuka da akeyi yanzu sai ta tsorata tayi sama da sauri kayan sawarta akwati biyu da duk wani abin bukata shi ta kwasa tayo kasa,Murna wajen Ahmad ba a magana,ko kulashi Bata Yi ba tayi waje,da kanta ta Bude gate sabo da me Gadi baya Nan,Tana fita Napep ta Shiga da kayanta sai gidansu.

Su Mama suna ganinta sun San ma matsalar,Baba yace ya Koro ki ne? Aamna tana Hawaye Tace a'a nice Naga bazan Iya Zama ba Yana min barazana da rayuwata shi yasa na taho Kawai,Mama Kamar gaske Tace Allah sarki kiyi Hakuri komai zai dai daita,dama nasan wannan ba abin yarda bane,karki koma ko Iyayensa sun zo Kuma ko me za ayi karki koma,Aamna Tace dama bazan koma ba,kin San shagona yanzu sai kici gaba da kular min da shi kawai sai na sallami Yaron ciki,Aamna da murna Tace Kinga na huta da zaman Kawai,Mama Tace ae kina hada hadarki da customers me ya dameki da wani banza,Zauna ki huta sai gobe ki fara zuwa cewar Baba,Allah sarki Aamna sai murna takeyi.

Washe gari kuskuren Aamna da su Baba sun Aamna matar aure da igoyoyi a kanta Bata nemi Izni ba ta shirya ta nufi kantin Mama,Yaron Dake ciki shi ya nunawa Aamna komai yanda abin ke tafiya sannan ya tafi gida shi dadi ma yaji sabo da Mama Bata biyansa Hakkinsa yanda ya kamata sai wahala a banza,Wayar Aamna ce tayi Kara ta duba sai taga Mummy ce,Sai lokacin ta tuna da Aurenta,dagawa tayi Suka gaisa sannan Aamna Bata boye ma Mummy ba ta fada mata komai,Mummy cike da damuwa Tace kinyi kokari Aamna bazan ce ki koma ba,na hakura kiyi zamanki Kawai Ina Jin Ahmad bashi da rabon shiryuwa,Zan ci gaba da Masa Addua,to Mummy Maganar fita fa?ko naje ya bani takardar saki,Mum Dariya tayi Tace karki nemi saki Ni na Baki Izni ki fita duk inda ya Dace Amma ki kula ki Kama kanki ki sani da Aure a kanki,to Inshaallah cewar Aamna sannan Suka Gama waya ,Siyama ta Kira ta Bata labari,Siyama sai murna Tace kinyi dai dai wannan shine magana karki sake ko da Wasa ki koma,ai dama bazan koma ba cewar Aamna kin ganni Ina kula da shagon Mama,Kinyi dai dai kawata Nan suka Sha Hira sannan suka kashe Wayar,Aamna Ana zaune a kujera ga table da kayan aikinta na calculation,Haka ta kwashe kwana Uku tana zuwa Kantin ta Gama Gane komai tana ta ciniki.
Chapter 24 · 0% Book details