Sashe 70
Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haka wasu kawayen duk sunje sun Sha kallo sun dawo dake wasu Yan Mata Yan Uwan Yar China suna can sune suka Kara gyara gidan,kayan kitchen da kayan kyale kyale da Suka Kara siyo Mata na dangi masu kyau Suka Kara a gidan, gidan Suka shirya Mata komai yanda zai bada kala,komai a tsari suka Yi,Brown Kuwa shi ya maida Aamna gida ta wuce part din Humaira sabo da Humaira aka fara kaiwa Basu da yawa daga ita sai Kawayenta su hudu,Suma duk sune suka gyara gidan da komai,Humaira an sake saka Mata wasu kyalekyalen masu tsada sabo da su akwai abin.
Itama Sameera lokacin da aka kawota sun sake zuba abinda babu da Kuma wasu abin na bukata na Yan gayu tunda an Gama musu me wahalar, Bangaren Nafeesat Kuwa wow itama ba karya sabo da Naira itama an Kara zuba wasu abin masu tsada musamman a kitchen,Ita Babanta da babarta su Suka kawota dakin Miji su biyu rak sabo da Yar Malam ce,sai da yayi Mata Nasiha,dama angwaye tun kafin bikin ya tarasu ya musu Nasiha sosai da sosai,Humaira da Sameera ma daidai gwargwado sun Sha Nasiha wajen Iyayensu sannan aka kawo su.
Hafsat ce ta hudu da aka kawo da dunbun Yan Mata da Yan uwa,Basu Dade ba Suka tafi aka bar Hafsat tana ta kuka Ita Daya tal,duk cikinsu Sameera ce Bata Yi kuka ba,Itama Hafsat ita Daya tal aka bari ba ko mutum Daya dama su tuni duk gyaran gidan da zasuyi sunyi dama komai a Leda yake ba abinda yayi Kura da kansu Suka bare komai Suka shirya Mata,Suma abinda ya Dace zasu karawa Hafsat duk anyi komai ko wacce gidanta sai kamshi yake zubawa Yana walwali,ko wanne gida a kasa 2 bedroom and Palo ne sai kitchen store da dining area,sama Kuma 2bedroom and Palo shima ko wanne daki da toilet dinsa masu Fadi da kyau gidan ya kayatu,kowa ya gani sai abin ya birge shi, compound din ko wacce yasha Interlock da fulawoyi ga parking space,harda Dan wurin hutawa anyi wata rumfa ta haduwa da shuke shuke ga wasu kujeru da table masu kyan gaske a wajen.
Yar China kawaye sun sata a gaba sai tsokanarta sukeyi yau zata gane kurenta,Dariya Yar China tayi tace to algungumai ya gaji da yawa Angon yau bacci zaiyi yace ko motsi bazai iya ba ta Allah ba Taku ba,Dariya Suka dinga kyalkyalawa Yar China Suna cewa wlh wayo ya Miki,Yar China Tace bama wasan karya da Tawaga na,wanka tayi ta fito Suka kwashe kayan data cire da komai nata Suka zuba a leda,wata kaza Salamatu ta kawowa Yar China kafin ta shirya aka takura Mata sai da ta cinye,aka Bata wasu tsumin ta Sha,Salamatu Tace kayan maganin tsuminki ki ya bedroom dinki an ajiye Miki su Safiyya zasu nuna Miki ki boye Banda hauka karki Bari ya gani Kuma,Tace to tana shafa lotion bayan ta gama wata atamfa super aka Bata ta saka dinkin Riga da skert sun kamata cif,Yar China ta tsula kyau,Atamfar Wata brown and red ta tsaru ka rantse ma ba atamfa bace wani material ne daban,gashin da yasha gyara Yan matan suka gyara Mata shi aka Mata wani acuci da shi Suka ce baza ta daura dankwali ba ai Amarya za a Kai Mayafi zata yafa,Mayafi Kato Amma me sharara da kyalli mayafin ya hadu shi aka bawa Yar China ta yafa sai ta fito kamar wata Yar India,takalminta me tudu Kalar mayafin red Haka jakar ma,Habiba ce ta rike kayan da Yar China ta cire a Leda har Inner wears baza su Bari ba sai an Kai gidanta,Kuma Iyalle ce ta sasu,Sallar Nafeela aka sa Yar China tayi tare da adduoi,tana Idarwa taji ance motoci sun Zama Ready Amarya ake jira,Yar China tana Jin Haka ta fara kuka Tace karyata ta Kare Ashe da gaske akeyi bikin Nan,Ashe ba karya bane kaini za ayi wayyo Iyalleta,Yan Mata suka dinga ihu da shewa Ana dariya,Habiba tace masu Algaita ma sun Zama ready suna mota sun shiga,Yar China Tace sunci Uwarsu Shegu dasu aka hada baki za a kaini yau,mutane Suka dinga dariya itace fa tace sune zasu rakata da Algaita.
Wajen Iyalle aka shigar da Yar China Iyalle taga Yar China tana kuka sai itama ta fashe da kuka tace bazan iya nasihar Nan ba naje daga baya nayi Mata a dakin mijinta,Yar China tana kuka tace Iyalle ki min Nasiha Allah idan Baki min ba sai tafka tsiya gobe bazan Yi girki ba a gidan,Iyalle kukanta ya tsaya cak ta bude Baki Tace Dan Ubanki karki girkin Mana yunwa ta Miki Illa,Yar China tace dama Baki Iya Nasiha ba tsoro kike ji Kar a kureki Baki iya ba komai ba,irin na mutanen da kike Yi,Iyalle maimakon Nasiha sai Suka bige da fada tace bazan Yi nasihar ba Dan ubanki idan nazo nayi Miki ai zanzo ganin gida salamatu ku tafi da ita ana jiranki,na fasa yin kukan rabuwar dake Yar banza fitsararriya cewar Iyalle, aka dinga dariya,Yar China taji ance a tafi sai kuka ta dinga Shure Shure da burburwa ana riketa taki fita daga dakin an rasa yanda za ayi da Yar China,tana kuka tana cewa Allah...Allah sai na fasa kofin da kika siya min Iyalle,Iyalle tace kinwa kanki marar kunyar karya,ke Baki ji kunya ba duk bikin da kika Yi kin koma kuka,ba fitsarar da bakiyi ba Ashe karamar marar kunya ce,Yar China kuka ta dage Jin koshi ko kunya babu,babu Wanda Bai lallabata ba taki hakura ta tashi a tafi,Iyalle tace ku jata ta karfi ku tafi,Yar China ta Dan Bude mayafinta ta leko tare da gallawa Iyalle harara ta rufe fuskarta again,Iyalle Tace Zaki ci Ubanki Kuwa wlh ku Kira min Tawaga Angonta Yana Nan a waje suna Jiran Amarya,ai Kuwa su Habiba suka tafi da sauri Suka Kira shi tare da fada Masa Taki yarda ta fito tana ta kuka an rasa yanda za ayi da ita,Tawaga Wanda da shi za a dauki Amarya yace gani Nan,su Jibson suna ta Masa dariya ya tafi gidan Haka ya kutsa har dakin Iyalle,yaga Yar China a lullube ta dunkule tana kuka,tana Jin Muryarsa tayi Mukus tsoron Tawaga take ji,duk haukarta tana nutsuwa idan ta ganshi,Iyalle tace gata Nan anyi anyi ta fita Taki,Yar China tana shesheka tace Haka nace Miki bazan fita ba? ai dai bance ba ko daga nace a Bari na huta,Iyalle tace to tashi ki bisu ko wallahi na Hana kowa zuwa rakaki ya dauke ki shi da Kansa,tun kafin Tawaga yayi magana ma ta Mike ta cikin Mayafi ta gallawa Salamatu Harara tace ai sai kuje ko.
Tafiya akayi aka sa Amarya a tsakiya,Sadiya tana kusa da Yar China ta Mata rada tace wai Yar China Ina kika samo wannan guy ne? Kinga yanda har abokansa duk hadaddu,Yar China ta daina kukan tace daga zagi wallahi,suna magana ai tana tunawa kaita za ayi gidanta sai ta sake fashewa da kuka tace shike Nan Yar unguwarmu,ga makwaftanmu duk su Maman Yusrah shiken nan ta sake sakin kuka angwaye suna ji,motar Ahmad da tafi ta kowa kyau Nan aka shigar da Amarya da Kawayenta su biyu sun sata a tsakiya,Yar China tana Zama tace kudi na Dana Tara a gidan Maman Yusra a karbo min abina na tafi da shi nasan kafin nazo Unguwar Nan sai da tsohon ciki na Dan Allah Habiba karbo min Tawaga ba mutunci ya sani ba wallahi ciki zai min da wuri,su Habiba suka dinga dariya Allah yasa Ahmad Bai shigo motar ba.
Haka suka je Suka karbi Mata dubu ukun ta duk akan dubu Uku take wannan abin,lokacin Ahmad ya Shiga motar Ana karbowa yaji Amarya duk uban kukan ta daina Tace ku rike kudin dubu ukun ku raba idan kun koma gida ku Siyo maltina da Madara ku Sha jininku ya tsatsafo sabo da a bikin Nan Kun Sha wahala,Suka ce mun gode Amarya.
wurin motoci goma Suka Yi harda ta masu Algaita sun sauke gilasai suna ta uban hurawa suna kida a motarsu an sasu a tsakiya,wannan algaitar ta jawo duk inda motocin suka wuce sai an kalla babu tambaya mutane ke cewa wata Yar Sarkin ce ake bikinta,wasu suce kaga masu abin Yar sarki ce wlh,Har aka Shiga Unguwar Wanda Basu je ba Suka dinga Santi,dayar kawar Yar China Bilkisu tace Yar Chi na Kan uba wlh kin bar mu a baya Kinga Unguwar da zaku zauna,lokacin kuka Yar China takeyi amma sai ta daina kukan tace ai Baki gama kallo ba sai anje latinmu da gidana Dan Uwarki harda lilo,Ahmad Yana jinsu Yana ta dariya a hankali,Habiba tace bayan biki da sati Daya zamu Zo cin abincin Amarya,Yar China harda dukan Cinyar Habiba Tace rankem Zan Muku ranar shinkafa dafaduka zazzafa,suna ta dariya ta manta ma da wani kukanta sai ta Bude mayafin sai ta Gama kalle kallenta sai tace uhm bari na rufe Ni Amaryace,da taji su Habiba suna yabon wani wajen sai ta sake dage mayafin, sai da aka zo gidan tace Kun gani ko sai kuka Kuma wayyo Iyalleta wayyooo.....duk sun cikawa Ahmad kunne sun isheshi da surutu shi Aamnansa ma yake tunawa yanda kwalliyar yau ta Gama tafiya da Imaninsa gashi ba sukuni bare yaje ya bada tukwici,a ransa yace Nima yau wani First Night din zanyi.