← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 103

Sashe 99

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tunda ta koma ƙauyensu rayuwa ta juya mata baya, ɗan daɗin da take samu a gidan aiki babu shi a nan, a hankali ta cinye duk kuɗin data koma da shi gida a ci banza ci wofi ya ƙare tas, daga bisani sai ta fara sace na mutane da zarar mutum yayi sakaci sai ta wafce, tun ba asan tana satar ba har abu yazo aka sani da an ganta ake kafa kafa dan karta yi barna, wannan dalilin yasa aka sanya mata suna Jamila asulluru, ganin an ganota yasa ta soma niman wacce take samar mata aiki a birni bata nan, data dawo matar tace ba zata tura ta ba taje ta riƙa yiwa mutane sata, a haka dai rayuwar Jamila ya zama sai addu'a ganin ba tada mashinshini dan wannan satan da take yi ya zame mata baƙin fenti, babanta ya bawa wani mahauci aurenta bisa dalilin biyan bashi daya yi da ita, dan mahaucin yana binsa bashi ya rasa yadda zai biya sai ya bashi auren Jamila. Tunda aka yi auren ta shiga cikin tashin hankali dan matansa biyu ita ce ta uku ga uban 'ya'ya, wahalar gidan ya gama nukurkusa ƙuruciyarta, kullun in ta zauna tana tuna baya sai ta yi kuka tare da tarin nadamar abinda ta aikatawa Sameeha, tana kuma tsinewa Najwa, wanda a kullun tana fatan su haɗu da Sameeha ta nima yafiyarta sai dai ba hanya, in ta zo Kaduna ma bata san a ina zata ganta ba tunda bata san gidan iyayenta ba, haka ta cigaba da rayuwa cikin ƙunci da rashin galihu, ta tabbatar alhakin mutane data zalunta kaɗai ba zai barta ta samu sauƙi ba, sai dai fatanta ta samu sauƙi a gurin Allah.

Hauwa...
[5/27, 8:54 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

59.

Hauwa.

Tun lokacin bikin Aminu da Najwa ta tattara kuɗinta ta zuba a cikin sha'ani, tun daga suturar data ɗinki na fitar biki zuwa siyan kayan abinci wanda zata girkawa baƙinta, hakan yasa bayan biki ya zama ba ko sisi a hannunta Allah yasa suna da abimci a gida, to da 'yan kame kame suke samu suke dafa abinda zasu ci, duk da a lokacin bata bar alwashin lalata rayuwar Aminu ba kamar yadda ya wulaƙantata kuɗi kawai take jira ta samu, sai dai sunƙi samuwa tunda suna ta abinda zasu saka a bakin salati ne, ga Adama ta dawo gidan itama ba kuɗin take da shi ba, tunda dama a jikin mijinta take samu to yanzu ba auren har sun kwaso kaya, a hankali duniya tayi musu ɗaurin kazar kuku dan har bashi Hauwa ta soma ci ganin abincinsu ma ya tasarwa ƙarewa, ga su yaya Alhasan sosai suka ɗauki fushi da ita daga gaisuwarta basa sake yi mata magana, har kokenta takai gurin Sa'a akan ta yiwa Kamalu magana ya taimaka mata da wani abu tana so tafara sana'a, koda Sa'a ta sanar da shi shashantar da maganar yayi dan so yake sai ta gane kurenta akan duk irin tuggun da take aikatawa yana so ta gane Aminu yana da rana a gunta, jin shuru shuru ba aike yasa tazo Sa'a ta ce ta faɗa masa amma yace ta bashi lokaci, koda taje gun Laure cewa tayi ta rufa mata asiri ba zata jewa Alhasan da wannan maganar ba dan ko sunan Hauwa ta ambata hakan zai zame mata matsala, taimako ɗaya tayi mata ta bata dubu biya kyauta, kuɗin data bata yasa Hauwa farin ciki ta yi mata godiya ta dawo gida. To da wannan dubu biyun da kuɗin wayar kanin Adama data matsa dole ya sayar dubu goma sha biyu, shine suka ɗan saya kayan abinci sauran kuɗi dubu shida Hauwa ta yi cefanen waina ta soma sayarwa a ƙofar gida da safe. A hankali mutane suka fara ganewa da yake kan layi ne da kuma mutane sosai a anguwar, nan da nan sai Allah ya saka mata albarka har ta samu ta biya bashi sannan ta saka wani yaro kafinta ya buga mata runfar kwano a jikin gidanta da bancinan zaman mutane, daga gefe ta kafa tandar wainarta tana suya Adama tana rabawa mutane tana amsar kuɗi, cikin kwanaki Hauwa ta zama mai waina har daga nesan guri ake zuwa siya, ta soma tara 'yan kuɗinta suna cin mai kyau dan har kumari suka yi, sai dai wahalar aikin waina yanada yawa tun basu saba ba har abin ya soma bin jikinsu, daga waina loka ɗaya aka dawo yin biyu har zuwa biyar yanzu ma sun ƙara hannu suna yin loka bakwai kuma daga ƙarfe bakwan safe zuwa sha ɗayan rana ya ƙare.

A wannan yanayin ne Mijinta ya dawo daga Lagos dan dama can yake ciraninsa yana sayar da kayan gwari, daga nan kuma mata su tattara 'yan kuɗin dan mazinaci ne na bugawa a jarida, shiyasa yake ɗaukar lokaci bai waiwayo gida ba, a wannan dawowar nasa da rashin lafiya ya sauka dan a can ciwon ya kama shi sosai duk kuɗinsa daya tara a magani ya ƙare, ganin in bai dawo gida ba zai iya yin mushe a can yasa shi roƙan abokansa suka saka shi a mota tare da biya masa kuɗin motan ya dawo Kaduna, Hauwa ta shiga tashin hankali sosai ganin mijinta a wannan yanayin dan tana matuƙar sonsa, dole 'yan kuɗin data tara dasu suka fara jinyarsa dan har kwanciya yayi a asibiti, wanda bincike ya tabbatar ciwon sida ya kwaso wato kanjamau, Allah ya taimako Hauwa ba tada shi dan bai goga mata, tunda ta gane cutar daya ke dashi kenan sai ta bara ja baya da lamarinsa ta nuna ta gaji dan ba zai yuwu tayi ta asarar kuɗi akansa ba, albarkacin yaransu kawai take dubawa yasa har take shiga lamarinsa, duk da haka dole tace a sallame su su nima na gida, da suka dawo ƙanin Adama shi ya cigaba da kula da shi ita kuma tana aikin waina, dan sai da suka yi kusan sati ba suyi ba, har an samu wata ta fara a unguwar, amma da yake kowa rabonsa yake samu bai hana Hauwa ta cigaba da yi ba, sai dai ya zama basa cinikin da saboda mutane sun fara tsegumin mijinta ya ɗauko misu ciwon sida, tun suna yi da yawa har suka koma yi loka biyu da kyar yake ƙarewa, wani lokacin ma sai dai su su cinye kayansu a abincin gida, Hauwa a wannan lokacin lamura sun fara haɗe mata sai ta zauna ɗaki taci kukanta ta gode wa Allah ba mai taimakonta dan duk 'yan uwansu sun zuba mata ido ne. Mijinta ya dawo da wata biyu Allah yayi masa rasuwa, bayan anyi zaman makoki aka watse sai Adama ta cigaba da suyar waina amma ba wani kasuwa, dalilin daya saka kenan suka daina wainar ta koma tana dafa shinkafa da wake dasu doya da miya tana kaiwa can bakin hanya gefen wani mai shago, a nan kuma ita Adama ta buɗe sabon nata rayuwar ta zama sakakkiya ba kamun kai, kowa nata ne duk wanda yace yana sonta koda ƙaramin yaro ne tana amince masa matuƙar zai riƙa sakar mata kuɗi, hakan yasa nan da nan rayuwarta ta soma sauyawa ta feƙe da rashin kunya, tana sayar da abinci tana haɗawa da rons da maza, nan da nan kuɗi suka zauna mata, Hauwa dai ta kasa yadda zata ɓullo mata domin ta nuna bata isa ta hanata rayuwar da take so ba, tunda ita ce ke ƙoƙarin ciyar da gidan, Hauwa sai dai ta zuba mata ido tana ta zaman takaba.
Chapter 99 · 0% Book details