Sashe 28
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajen sha ɗaya da minti biyar suka iso ƙofar gidan a waje Kamalu yayi parking suka fito Hauwa ta buga gate mai gadi ya tambaya su waye sai Alhasan yace sune, ganin ya gane muryansu ya buɗe musu suka shiga, shima yayi mamakin ganin su sai ya bisu da Allah yasa lafiya a zuciyarsa, da sallama suka shiga falon amma ba kowa ga wayoyin Aminu da jakarsa, hakan ya basu tabbacin ya dawo, sai Kamali ya wuce falon Aminu yana buga ƙofa, itama Hauwa ta wuce ɗakin Sameeha ta tura kofa tana sallama, jin ba a amsa ba kuma ba kowa data gani a ciki ta fito falon tana cewa bata ga kowa a ɗakin Sameeha ba, Aminu dake kwance yaji buga gate sai dai bai tsammaci 'yan uwansa bane a wannan lokacin, jin muryansu da yayi a falo yayi matuƙar ɗaga masa hankali amma sai ya yi sauri ya miƙe ya shige bedroom ɗinsa ya cire kayansa ya zura jallabiya ya wanke fuskarsa a bayi, ya fito falonsa kenan sai ga Kamalu ya shigo suka yi kiciɓis suna kallon juna, yanayinsa kawai da Kamalu ya gani ya tabbatar da ba lafiya ba, sai ya juya Aminu yabi bayansa zuwa falo ya tsaya kamar yadda ya gansu a tsaitsaye sunyi cirko cirko suna zuba masa ido, Alhasan yace cikin damuwa.
Aminu meke faruwa ne? Ina Sameeha? Hauwa ta leƙa ɗakinta bata ganta ba, ita take sanar damu wai mai aikinku ce ta kira ta ta sanar da ita gidan ba lafiya.
Saɓani na samu da Sameeha kuma na saketa ta wuce gidansu.
Ya samu basu wannan amsar jin basu ga Sameeha a ɗakin ta ba, yasan tana cikin gidan bata fita ba ƙila tana bayi ne, addu'arsa Allah yasa har su tafi ba zata fito ba dan baya so su ganta cikin maye, salati duk suka haɗa baki suna ambata, Alhasan yace cikin faɗa.
Kana da hankali kuwa Aminu me Sameeha zata yi maka yarinyar da take da mutunci da hankali har ta cancanci Saki? wlh ka bani mamaki, anya kana cikin hayyacinka?
Yaya ina da dalili kuma itama sakin ta ga ya fi mata, dan haka dan Allah ku fita daga cikin maganar nan.
Wlh ba kai bane Aminu an sauyaka domin Aminunmu da na sani yana matuƙar son Matarsa wanda zai ita aikata komai akan farin cikinta, kodai ka fara haɗuwa da matan banza sun fara hure maka kunne ne.
Cewar Kamalu kamar zai rufe shi da duka. Aminu ya cije yace cikin dakiya.
To ban isa na kula matan bane? kawai dai na gaji da ita ina buƙatar hutu taje gidansu ta huta nima na huta tunda saki ɗaya nayi mata ai ba yawa.
Alhasan ne ya sauke mata kyakkyawar mari yana cewa.
Dan ubanka mu zaka faɗawa haka ashe ka fara shaye shaye bamu sani ba, to wlh baka isa ka jawo mana abin kunya ba dole goben nan In Sha Allah zamu je ka dawo da matarka, kuma idan na bincika ka fara bin matan banza sai nayi matuƙar saɓa maka sha sha sha, ina yi maka kallon mai hankali ashe mutumin banza ne kai.
Ko me zaku ce kuce kuma ko me zaku mini ku mini amma wlh bazan dawo da Sameeha ba na gama yayinta, ku barni na wataya naji daɗin duniyata, shiyasa na sauwaƙe mata dan na rage nauyinta akaina yadda zan more rayuwata. Kuma nan gaba kadan aurena zan yi da wacce ta dace dani.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Alhasan da Kamalu suketa ambata jikinsu sosai yayi sanyi da furucinsa dan gabaÉ—aya sun bayar ko asiri aka yi masa dan sam ba Aminunsu bane, shi kuma Aminu da gangan yayi haka domin ya bada laifin sakin akansa dan ya rufawa matarsa asiri ya dauki laifin gabaÉ—aya, Hauwa kuwa wani mugun farin ciki take ji dan gani take yi kamar asiri wata budurwarsa tayi masa suka samu galabar rabashi da Sameeha, sai ta nisa tace.
Yaya da alama anyi masa asiri ne dan baya cikin hayyacinsa, ni wlh duk wacce tayi wannan aiki ta yi matuƙar burgeni domin ta yi nasarar karya kadarin Sameeha, dan wlh itama ba ƙaramin asirin mallaka take yi masa ba, ku kuke ganinta mutumiyar kirki amma tuni ta gama da Aminu shiyasa bayi da zance sai nata, dan haka godiya za muyi ga Alkah daya kuttoshi daga hannun Sameeha, itama wacce ta asirce shi Allah bazai bata nasara ba dan nima masa magani za muyi har Allah yasa ya dawo hayyacinsa ya samu matar kirki ya aura, dan tuntuni nake masa hangen wata yarinya ɗiyar mutunci, amma saboda nasan halinsa zai bani kunya shiyasa nayi shuru ban faɗa ba, kuma Sameeha ba zata taɓa barinsa ya ƙara aure ba.
Idan baki yi mini shuru ba sai na ci mutuncinki Hauwa, ai dama nasan soyayyar da kika dawo kina yiwa Sameeha na dole ne dan munfi karfinki, kuma ki kuka da kanki.
Cewar Kamalu, Aminu mamakim furucin Hauwa kawai yake yi amma lokaci yayi da shima zai yi maganinta cikin ruwan sanyi, sai yace.
Yaya dama kin san Sameeha asiri take yi mini kika yi shuru? amma kin cuceni zumunci bai ce haka ba, aikuwa tunda naji haka na ƙarasa saki biyun ya koma saki uku wlh na saki Sameeha saki uku ko duniya zata haɗu akaina ta saku, kuma ina maraba da duk wacce zaki kawo mini domin nasan ba zaki taɓa yi mini zaɓin banza ba.
Kaci ubanka Aminu lallai na yadda ba kada hankali, to bata saku ba tunda ba a hayyacinka kake ba.
Alhasan ya faɗa kamar zai ƙara marinsa, Aminu yayi murmushin daya fi kuka ciwo.
Wlh Tallahi Billahi ina cikin hankalina kuma na saki Saneeha saki uku ko kuso ko kar kuso na gama yankewa kaina hukunci tunda ba kune zaku zauna min da ita ba, rayuwata ce hakan shine yafi mini.
Yana gama faɗar haka ya juya ɗakinsa ya shige yana mai rufe Kofar da key ya zauna dirshen jikin ƙofa yana yin wqni marayan kuka mara sauti, shi kanshi yasan yayi jarumtar yi musu rashin ɗa'a da bai taɓa yi musu irinsa ba, hakan shine kaɗai mafitarsa domin ya ɗaurawa kansa laifi kowa yaga baƙinsa akan asirin Sameeha ya tonu. Hauwa kuwa kamar ta fasa guɗa dan mugun farin ciki domin hakan ma ya bayyana karara a fusarta, a fusace Alhasan ya bar gidan Kamalu ma yabi bayansa Hauwa kuwa sai da tayi wani rawa da duwawu kafin tabi bayansu tana shanye farin cikinta dan kar faɗan ya dawo kanta tasan halinsu sosai.
Sameeha duk taji taƙaddamar da ya faru dan lokacin data ji Hauwa ta fita daga ɗakin ta yi saurin fitowa da bin bango ta zura jallabiya, sai dai lokacin data ji suna magana ta tsaya jikin ƙofa ta gama saurarensu, kuka kawai take yi yadda taji Aminu ya ɗaurawa kansa laifi kacokan, tasan tayi rashin miji mai matuƙar sonta da son farin cikinta, Allah ya isa ta shiga ja ga duk wanda nayi nasarar rabata da shi, sai da suka tafi kafin ta buɗe ƙofar ta isa ɗakin Aminu tana bugawa, miƙewa yayi ya buɗe, yana ganinta yayi saurin bata hanya ta shigo sai ya rufe Kofar yana cewa.
Su Hauwa basu ganki ba ko? nace musu kin je gida.
Ban fito ba sai da suka tafi.
Ta faɗa cikin sanyin murya, sai ta tsuguna akan ƙafarta ta fara kuka tana cewa.
Wallahi Tallahi Billahi Amimu bansan waɗan nan matan na, bani ce na gayyato su suka zo ba, ban san waye ya shirya mani wannan gadar zaren ba, ban taɓa aikata wani masha'a ba saboda kore sha'awa ta ba, a karan kaina ban taɓa biyawa kaina buƙata ba. Dan Allah ka yarda dani ka janye sakin daka yi mini.
Aminu shima durƙusawa yayi a gabanta yana kuka yace.
Sameeha na riga na gama yanke mana hukunci wanda nasan hakan shine dai dai, kuma na yarda dake baki aikata komai ba domin maganganun Hauwa ya saka mini shakku da zargin wani abu, mu barwa Allah In Sha Allah Allah sai ya bayyana gaskiya. Idan kinje gida ki sanar dasu nine na sauya na fara shaye shaye dabin matan banza, to da kika mini magana shine na fusata na sakeki bana son kowa yasan asalin matsalarmu Sameeha.
Idan na ɓoye wa kowa to wlh bazan ɓoyewa umma ba, kuma bazan taɓa iya yi maka wannan sharrin ba, Allah yasa hakan ya zama mana alkahiri amma wlh Abin da ciwo a zuciyata wanda babu ranar warkewa.
Nima Sameeha ciwon da kike ji nawa yafi naku, wannan ita ce ƙaddararmu Allah ya bamu juriya yasa munci jarabawarmu. Tashi ki koma ɗakinki dan yanzu babu igiyar aurena akanki, kuma ki kwashe kayan ɗakinki da kayan kitchen gaba ɗaya da kujerun falo, hatta abinci da komai na store na bar miki karki bar komai, yara kuma In an kwana biyu zan zo na ɗauke su.
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ya barta a tsugune tana rusa kuka, ta jima a gurin kafin ta rarrafa ta miƙe ta wuce ɗaki ta kwanta a gado, akan idonta aka kira sallar asuba, zuwa lokacin maganin ya fara sakinta sai dai jiri da bugun zuciya ke damunta, hakan yasa har taji fitar Aminu daga gidan ya kuma dawo bata iya tashi tayi sallah ba, sai wajen shida na safe ta tashi da kyar ta shiga bayi dan ji take kamar iska na ɗibarta saboda ramar data yi a dare ɗaya, wanka ta sake yi da ruwa mai zafi sai ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar asubahi a zaune, data idar ta cigaba da jan istigfari a zuciyarta ta ɗaura kanta a gefen gadon, a lokacin wajen bakwai saura matsin fitowar Aminu taji ta ɗauka ko zai leƙota amma shuru.