← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 103

Sashe 34

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai wlh ke ce kike bawa Kamalu dama yake yi miki mulkin mallaka, ki daina tsoronsa yadda zaki ji dadin rayuwarki, dan ni Wlh Alhasan bai isa ba ni da shi kar ta san kar ne, sai dai ya gama bambamin faÉ—arsa ya rabu dani.

Gaya mata dai Laure dan na kula kan Sa'a har yanzu yana a murfi bata san kan dawon garin ba, kinga dai su 'yan uwana ne ko amma wlh ban goyi bayan ku riƙa jin tsoronsu ba ai maza ba a yi musu haka tunda ba bayi suka aura ba, dole sai kin tsaya tsayin daka kin karɓawa kanki 'yan ci. Ni yanzu Sa'a ɗauko tabarma ku zauna mu tattauna batun auren Aminu da yarinyar nan tun kafin yazo yace ya fasa.

Ta kare maganar tana kallon Sa'a sai ta juya ta wuce ɗaki tana tunanin maganar da Kamalu yayi mata jiya da daddare akan ta kiyayi su Hauwa duk da yasan 'yar uwarsa ce amma yace ta fita harkansu ita da Laure, in ba haka ba sai sun sabauta mata aure tunda yasan ba alkairi suke shukawa ba. Taje dawo daga ɗauko tabarma ta shimfida suka zauna, a nan suka cigaba da hira har Hauwa ta yanke shawarar kiran Najwa akan tayi mata albishir, duk a kunnensu tayi maganar daga bisani ta yi sallama da Najwa suka ɗaura hira, sai wajen ɗaya suka tsaida hirar akan zasu yi sallah su tafi rafin guza gidansu Sameeha amso yara. Hauwa a ɓangaren Laure tayi sallah da suka idar sai da Laure ta dafa musu taliya dafadukan man ja suka ci wajen biyu da kwata suka fito suka tsaya Kofar ɗakin Sa'a suna kwala mata kira, tana jinsu ta shige bayi dan ba zata je ba ta jawa kanta matsala tunda tasan halin Kamalu da ɗaukar zafi, Hauwa tace su tafi tasan Sa'a ba zuwa zata yi ba saboda shegen tsoron Kamalu da take yi, haka suka kama hanya suna fita titi suka samu napep ya wuce dasu.

****

Sameeha.

Suna shiga gida umma dake zaune kan ƙaramar kujera a tsakar gida ta miƙe tana binsu da kallo har suka ƙaraso in da take suka tsaya cirko cirko umma ta rigasu da cewa.

Meke faruwa ne? Kar dai zargin da nake yi shine ya tabbata. Sameeha me kika aikatawa Aminu da zafi haka har kika ƙure haƙurinsa?

Umma da kin bari mun natsa sai ayi maganar.

Rufe mini baki Zaidu kafin in saɓa maka, wato kai ubanta ba da ka tasa su kuka yi gaban kanku ni kun aje ni a gefe, saboda baku san darajata ba da baza ku nima shawarata ba ko.

Umma ba haka bane dan Allah kiyi haƙuri muna gudun sakaki tashi hankali ne shi yasa muka yi komai bamu sanar dake ba amma tunda mun sawo zaki ji komai.

Cewar Ikram da idonta ke kawo kallo dan a cikin sanyin murya tayi maganar, yadda umma taga yanayinta yasa ta yi shuru Sameeha kuma ta sunne kai kasa tana danne kukan daya ke zuwa mata. Zuwan Amrah da Abi suna yi mata oyoyo yasa ta fashe da kuka ta tsuguna a gabansu tana kallonsu tare da yin kuka mara sauti sai hawaye ke ambaliya da nishin kukan, suma yaran sai suka saka kuka suna tayata, umma kasa tsayuwa tayi ta koma kujerar da take zaune tana kallonsu duk jikinta a sanyaye, su Zaidu suna bawa Sameeha haƙuri tare da tunatar da ita akan tayi haƙuri ta karɓi ƙaddararta hannu biyu.

Dan Allah ku fitar dani haske duk kun É—aureni da jijiyoyina, ko dai Aminun ya rasu ne?

Umma da rasuwa yayi ai sai dai mu tafi tare dake gidanta. Kuma da ma rauwar ne daya fi sauƙi.

Cewar Zaidu daya samu guri ya zauna dan ya gaji da tsayuwa, Sameeha ta jaye yaran daga jikinta ta rarrafa zuwa gaban umma ta kama hannunta tana cewa.

Umma ki yafe mini bisa rashin cika miki alƙawarin dana yi miki akan zama da Aminu duk wuya duk runtsi, wlh ba yin kaina bane mummunar ƙaddara ce ta faɗa mini wanda banda cumi banda dabara. Umma Aminu ya sakeni saki uku, haka ya rabu dani akan ya kamani da laifin da ban aikata ba, umma wai kamani yayi da 'yan mata muna masha'a shine yasakeniiiii.

Ta ƙare tana maganar da matsanancin kuka kamar zata shiɗe, umma ta damƙi hannunta da ƙarfi jikinta yana rawa.

Wlh ba zan taɓa yarda da wannan maganar ba domin nasan tarbiyya da nayi miki, ki yi mini bayani dalla dalla yadda zaki fiddani daga ruɗani Sameeha, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, saki har uku lokaci guda wannan wani irin ƙaddara ce.

Umma nifa gwara da auren nan ya mutu dan in har bai mutu ba gaba zata iya aikata abinda ya kashe mata auren.

Cewar Zaidu sai ya cigaba da faÉ—awa umma duk abinda Sameeha ta faÉ—a musu, itama Sameeha cikin kuka ta bawa umma labarin komai, umma ta share hawayen daya gangaro kuncinta ta kama hannun Sameeha tana cewa.

Inna fahimce ki gadar zare aka ƙulla miki ya rufta dake, to ai shikenan sunyi nasara akanki amma kuma Allah yaga komai kuma shine zai wanke ki Sameeha, In Sha Allah rayuwarki sai tayi albarka, sai maƙiya sunji kunya matuƙa, Allah ya shiga lamarinki ya rabaki da baƙin ciki da ƙuncin duniya. Ki daina kuka domin Allah bai manta dake ba kuma akwai ranar sakamako, Allah yasa hakan shine mafi Alkairi. Bari na ɗaura muku ruwan wanka kuyi dan nasan kun ɗebo gajiya, Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, kuma sai mu taru mu amsa wannan jarabawar duka ko.

Amsa mata suka yi da Amin kana ta miƙe cike da dakiya dan ta ƙara musu ƙarfin guiwa, sai ta wuce kitchen dan ɗaura musu ruwan wanka kamar yadda ta faɗa, shigowar su Hauwa da sallamarsu yasa ta fito da sauri, suma su Sameeha suka kafesu da ido har suka ƙaraso cikin gidan suka tsaya.
[2/24, 10:26 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

23.

Hauwa sai da tayi musu kallon tsaf kafin ta taɓe baki tana cewa.

Ina yini umma, ashe abin da ya faru da Sameeha kenan to Allah ya kyauta ya tsayar a kanta, kuma In Sha Allah nan ba da jimawa ba Aminu zai gwaggoje da Amaryarsa sabuwa fil a leda.

Dan Allah idan ba Alkhairi y kawo ku ba ku fice mana daga gida.

Cewar Zaidu cikin daga murya, Laure tace tana nuna shi da yatsa.

Kai kuma a suwa kare da gudun layya, ba gunka muka zo ba sai ka ja Please ka rungumi sorry É—an saurayi.

Hauwa da Laure dan Allah ban son tashin hankali, tunda mai haÉ—awa ya raba banga amfanin É—aukar baÉ—i ba rai ba.

Cewar Umma, Hauwa tace tana kallon Sameeha.

Muma ba tashin ha kali ya kawo mu ba mun zo gurin Sameeha ce gata nan zaune, yara zata bamu dan ba zamu yarda su cigaba da zama a gunta ba.

To ba zan bada ba idan Aminu ya aiko ku kuce yazo da kansa ya karɓesu, kuma ku sani ƙaddara tana kan kowa.

Eh mun san da ƙaddara tana kan kowa, amma mu muna murna da rabuwarku domin kadarinki ne ya karye, duk asirin da kike yi masa yazo ƙarshe, to Alhamdulillahi zamu ce kuma aniyar kowa zata bishi.

Dan Allah ku bar gidan nan ni bana son fitina, nan ba gidan Sameeha bane da kuka saba yin duk abinda kuka ga dama, wlh bazan ɗauka ba, zoku fice tun kan raina ya ɓaci.

Wlh ba zamu bar gidan nan ba sai Sameeha ta bamu yara, idan ba haka ba zaku ga tashin hankalin da baku taɓa gani ba, yara dai ba mai shan nono duk da wayonsu balle kuce ba zamu riƙe su ba.

Cewar Laure a fusace, Hauwa tana cewa Faɗa musu dai, sai karkaɗa jiki take yi cike da masifa, yaya Zaidu ya miƙe ya fara zuba musu masifa dan duk abinda yazo bakinsa taɓa musu suke yi, Ikram ma ta miƙe tana mayar musu da martani, nan fa musayar magana ta cigaba, umma tana cewa su Zaidu suyi shuru amma ina ransu ya ɓaci, Sameeha dai da yara suna zaune a kasa sai rusa kuka suke yi, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota suka fara shigowa ga kuma yara da suka yi cincirindo a Kofar gidan, saboda Tsananin zuciya Sameeha ta fusata ta wuce dakin umma ta jawo jakunan yaran, kayan data gani a kasa ta buɗe ta riƙa sakawa tana kuka kamar ranta zai fita, sai ta jawo akwatinan yaran guda biyu sai jakan takalma guda ɗaya ta zo har gabansu Hauwa da suke masifa baki har kumfa yake, ta dire jakunan ta juya ta damƙo hannun yaran duka biyu suka sakata a tsakiya tazo gaban su Hauwa ta ce cikin tsawa da kuka.

Hauwa Laure, Gasu nan ku tafi dasu bada su dama naje gidan Aminu ba kuma zan iya rayuwa ko babu su, ku fice mana daga gida tun kafin na kira hukuma, kuma daga yau duk shegiyar data kuma tako ƙafarta gidan nan kotu ce zata raba mu, 'ya'yan iska marasa imani da mutunci, ku fita nace.

Sameeha ta ƙare maganar da tsawa da matsanancin kuka sai ta yi baya ta durƙushe akan guiwarta tana wani irin kuka da jijjiga, umma ta matsa kusa da su Abi.

Kuyi haƙuri kunji mamanku zata riƙa zuwa tana dubaku Allah yayi muku albarka.

Wlh ni ba zan bisu ba da mamana zan zauna.

Cewar Abi yana kuka, Amrah ma tace.

Nima ba zanje ba ga mamana a nan.

Haƙuri za kuyi domin tafiyarku shine zai kawo karshen rikicin nan. Idan Abbanku ya dawo zai kawo ku.
Chapter 34 · 0% Book details